Showing 333001 words to 336000 words out of 411050 words

Chapter 112 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14386

cikin matayen da zasu tai Nigeria dole ya zama da na jiki ne sosai zasu yi tahiyar nan , sannan a tanadi kome da ya dace domin zouwa tahowa da ita , a yi kome cikin girma idan ta iso a mata masauƙi a sashin ki kussa da ke daɗa ita ɗin ai ɗiya ce Mai girma a wajen mu , Waziri shi zai jagoranci tafiyar tare da shi da Ɗan Malikin Maradi da wasu zaɓɓaɓu amintattun fada.

Kallon ba yadda zan yi Hajiya Umma take bin Maimartaba da shi har ya gama jawabinsa da cikin muryarsa ta fahimci a tsaurare yayi maganar cike da sautin umarta dan haka bata da wani zaɓi sai yin yadda yace , sai ta miƙe a hankali bayan ta ce " Ranka ya dade da yardar Allah yadda kace haka za'a yi .

MAIDUGURI-NIGERIA .

Fatima , ta ji ya ƙira sunan ta can a ƙasan maƙoshi ,
"Na'am ta amsa tana ɗago kan ta da ta kwantar a ƙirjin sa ,

" Ranar da duk za ki haihu tare zamu yi naƙuda kiyi rabi nima nayi rabi kin ji ko ?

Murmushi mai sauti tayi tana mayar da kanta ta kwantar "Daman ana yin haka ? Ta tambaye shi ,
"Nima ban sani ba Fatima , sabbada duk ɗiyana biyu bana wajen lokacin haihuwar su , amma wannan ya furta hakan lokacin da yake kai hannun sa marar ta ya shafa , "tare zamu yi haihuwar sa , ɗiyana ko ɗana zasu safko a hannuna idan macce ce kin san sunan wa zan sanya mata ?
A hankali ta girgiza kai yace, "Rahamatullah , sabadda haɗuwata da Mahaifiyar ta Rahama ce mai girma Allah shi yi min , Idan kouma ɗa Namiji ne ?, shiru yayi kaɗan , da yasa ta ɗago kan ta tana leƙen fuskar sa , wani irin farin-ciki kalamansa suka ɗarsa a ran ta ," dagaske yake ita tamkar Rahama ce a wajen sa ?
Sumbatar goshin ta yayi a hankali yace " na bar miki zaɓi Fatima ke za kiyi masa zaɓin sunan , wanne suna za ki sa masa ?

Hannun ta da yake kan ruwan jikin sa ta matsar ta lalubi hannun sa ta haɗe tafukan su waje guda kafin ta sarƙe ƴan yatsunsu cikin na juna kamar mai raɗa tace " Babana .

Hannun Yakaka da ta ji ya taɓa fuskar ta shiyasa tayi firgit tana kirkiro murmushin yaƙe , ganin ta ta mayar inda wasu ma'aurata dake zaune suke ta zuba soyayyar su Mijin sai tarairayar matar sa wacce take ɗauke da ƙaramin ciki yake yi kamar zai tayata ɗaukar cikin ita kuma sai zuba shagwaba take tana daɗa narke masa , wayam ta ga basa nan da alama sun shiga wajen likita .

tun zuwan su Asibitin da yau zata fara awu da Yakaka tare da Amnee suka rako ta Amnee ita tayi duk wasu kai kawon da bai cika wahala ba kasancewar Asibitin private ne yasa nan da nan ta buɗe mata file tare da biyan duk wasu kuɗaɗen da aka buƙata sannan aka turo su gurin likitan da zai dunga ganin ta .

mata Uku kawai suka tarar da a wajen , biyun tare suke da Mazajen su sai ita da wata mata wacce da gani ba haihuwar fari bace sune kaɗai ba mazajen su a wajen .

Soyayyar da ta tarar waɗannan ma'auratan na yi ya taɓa ranta , kewar sa da take ta dannewa kuma ta bijiro mata , baki ɗaya a lokacin , "Falmata meyasa kike kuka ? Kin san fa damuwa zata iya sa ki samu ciwo a halin da kike ciki .

Shiru tayi bata amsa ba , kamar yadda hawayen ta ya ƙi tsayawa , a dai-dai lokacin zuciyar ta tayi rauni wajen riƙe ciwon da yake damunta a rai ta hana shi bayyanuwa.

" Kiyi haƙuri zai zo ku tafi ,yana son ki dayawa Falmata inshaAllah a gidan ki za ki haihu .

" bai taɓa ƙiran mu ba tunda muka zo fa Yakaka , watakila ma ya sake ni bansani ba ni tausayin abunda yake ciki na nake yi ban..

" Youssouf ba zai taɓa sakin auren ki ba ya furta hakan da bakin sa kuma a aikace ma ya nuna ki kwantar da hankalin ki kiyi ta addu'a kin ji ko ?

Gyaɗa kai tayi tana share hawayen ta dai-dai da dawowar Amne da ta shiga cikin asibitin yin dubiya , damuwar da take damunta ta ɗan ragu .

Da layi yazo kan ta ita kaɗa ta shiga , su ka gaisa da likitar mace ce , ta yi mata duk wasu tambayoyin da aune-aunen da suka dace , bata da matsalar kome dan haka magungunan da yakamata masu ciki su dunga sha kawai ta rubuta mata .

Rashin ji daga Youssouf ba Falmata kaɗai yake damu ba , har Khaalty Rahima , Amnee da Prof da kan shi , rashin jin wani bayani ko da na ƙiran waya ne daga Youssoufa ya sa su a tunanin makomar auren sa da Falmata ?

Sau biyu Prof da Amnee suna tattaunawa a tattaunawar su ta ƙarshe prof ya yanke shawarar kan cewa idan har Falmata ta cika watanni biyu a gida , zai tashi ɗan aike zuwa masarautar Maradi dan sanin halin da Youssouf yake ciki da kuma makomar auren 'yar su , saboda rana ɗaiɗaiku ne bai ƙiran layin wayar Youssouf ɗin amma bai tafiya , ya zama dole yayi wani abu akai a matsayin sa na waliyyin auren kuma a yanzu shi matsayin Uba yake a wajen ta .

Falmata taso a bar ta ta dunga bin Yakaka Islamiyar da ko bayan auren ta da Doctor Hamza bata daina zuwa ba .

Da farko Prof ya ƙi yarda domin yace babu iznin Mijinta , tayi zamanta kawai a gida sai dai yadda a kwana biyun take yawan zaman shiru damuwar ta kamar ƙaruwa tayi tun bayan zuwanta awu , har 'yar rama tayi gaba ɗaya bata walwala .

daga Yakaka ta tafi islamiyyar da take kusan yini a can dan ƙarfe tara na safe take tafiya sai huɗu da rabi na yamma suke tashi kafin ta iso gida biyar saura .

Shikenan Falmata sai ta zama shiru a ɗaki ita ɗaya ƙwal, tun Khaalty Rahima na nunawa Amnee kar ta damu kan ta indai Falmata ce daman tun asali ita ba mai yawan son shiga jama'a bace kamar Baban ta take marar son hayaniya

Har ita da kan ta Khaalty Rahima ta fara damuwar saboda sai ta yini a ɗaki abinci ma da kyar take fitowa ta ci , Hajja ce daman mai shiga ɗakin ta dame ta har sai ta fito da ita , ita kuma wannan satin duk tana wajen danginta ana biki bata zauna ba .

Dan haka sai Amnee ta sake yiwa Prof maganar shiga islamiyyar Falmata ta sake masa ƙorafin zaman kaɗaicin da Falmatan take yawan yi kar ya sa mata ciwo .
Prof yace " zai duba lamarin .

Ranar asabat da safe kafin lokacin tafiyar Yakaka makaranta , Amnee ta shiga ɗakin su Yakaka hannun ta riƙe da baƙar leda da kaya a ciki ,

" Yakaka har kin fara shiri ne ?
Amnee ta tambaya tana ɗora ganin ta kan Yakaka wacce take sanya safa a ƙafar ta , da sauri ta ɗago fuskar ta da murmushi tace " Eh Amnee sannu da shigowa ,
" Yauwa sannu takwara ta furta hakan tana sauƙe ganin ta akan Falmata da take kwance akan gado ta basu baya ,

Ledar hannun ta ta ajiye a bakin gadon , kafin tace " Fatima tashi ki shirya yau dai ke ma za ki fara zuwa islamiyyar , tun kwanaki biyu na sake yiwa Baa Alaji zancen kin ga ashe an miki register ga Uniform ɗin ki ma da litattafan ki duk kin samu sai tafiya makaranta kawai ..

Falmata wacce tunda Amnee ta fara bayani ta tashi zaune tana murmushin da ta zarce da dariya jin ƙarshen bayanin Amnee da sauri ta sauƙa daga gadon tana cewa ," Amnee nagode , nagode Allah ya saka da Alheri ki yiwa Baa godiya , inason islmiyya sosai wallahi .

Ta ƙarasa zancen da nufar banɗaki domin watsa ruwa , Yakaka da Amnee suka bi bayanta da kallo fuskokin su ɗauke da murmushi .

Sosai fara zuwa makarantar ta ya rage mata damuwa domin kuwa yini suke karatu bata samun damar zurfafa tunani ,

Yau da ƙafa ma suka taho daga makarantar da yake tazarar tsakani ba mai yawa sosai bace Falmata tace, "Yakaka nafi jin daɗin makarantar nan fiye da Ecole ɗin mu ta Niamey wallahi ,

"Meyasa ko kin fi gane karatun nan ?

" A ah saboda a can ko na tafi ecole tunanin Mama baya bari na gane karatun sosai , Allah sarki Mama ta kusa watanni biyu da rasuwa amma koyaushe ji nake kamar ɗazu ta bar ni .

Murmushi Yakaka tayi , "ke da Mama ƙauna ku mai girma ce ai, nima naso Allah ya bani damar yin rayuwa tare da ita ko da ba mai yawa bane da nima na samu ladar jinyar ta da sanadin haka Allah zai bani lada mai yawa .

" da kuma za ki so ta dayawa fiye da son da kike mata domin Mama 'yar baiwa ce a cikin yara sa'o'in ta wayon ta daban ne kaifin hankalin ta yafi na shekarun ta .

Murmushin Yakaka tayi tana jin kewar 'yar ta na zagaya jinin ta , kewa kuwa mai tarin yawa ,

Ajiyar zuciya Falmata tayi daga nan ta shiga ba wa Yakaka labarin wayo da iyayin Mama wanda daman kusan rana ɗaiɗaiku ne da ba ta bata wasu labarai da suka shafi Mama .

Tun a harabar gidan suka fahimci akwai baƙi a gidan saboda baƙin motoci da suka gani har uku ,
"yau baƙi ne a gidan ko su waye ?
Yakaka ta furta hakan tana bin motocin wajen da kallo , can daga ƙasan ran ta tana fatan Doctor hamza baya cikin su .

" To Allah yasa baƙin alkhairi ne ,
Falmata ta furta hakan lokacin da suke nufar ciki

Tun kafin su shiga falon ƙamshin da ya karaɗe illahirin harabar wajen yake basu tabbacin baƙin na girma ne .

Da Sallama suka shiga falon , idanun su akan hamshaƙan mata huɗu da suke kan kujerun falon sai kuma Amnee da take a tsakanin su fuskar ta fal fara'a .

Ɗan taƙaitattcen kallo Falmata ta yi musu da taimakon gilashin idanun ta ta shaida fuskar Ammi , yayar Biyamuraɗi Youssouf , fuskar ta na nan zane a zuciyar ta kamar yadda munanan kalmomin da suka jefa musu yake rubuce tsaf a cikin kwakwalwar ta ,

Dan haka sai taƙi tsayawa kamar yadda Yakaka ta tsugunna gaishe su ,duk kuwa da cewa ita ma ta gane Ammi ,

sai ita ta ratsa ta bayan kujerun falon tayi hanyar ɗakin su .

Yadda tayi sam bai yiwa Amnee daɗi ba , dan haka ta ɗan ɗaga sauti tace " Fatima zo nan , zo ku gaisa da surukan ki mana ko baki gane su bane ? Yanzu suka iso .

Jaa tayi ta tsaya kafin ta waigo cikin rashin kuzari ta dawo baya kaɗan ta yi durƙuso daga nesa tace " Ina wunin ku ?
" Kadaran-kadahan Ammi ta amsa ,"da lafiya lau , tana janye ganin ta daga kan ta

Asma'u wacce tun shigowar su take faran-faran cike da kissa tace " tashi tashi ƙamna ta durƙuso ba naki ne ba , ɗaga yayar ki daga durƙusso Mairama .

Da sauri Aisha Mairama ta miƙe fuskar ta ɗauke da faffaɗan murmushin ganin Falmata , kafin ta ƙaraso Falmata ta miƙe akan ƙafafun ta guntun murmushi ta yiwa Aisha bata tsaya ba tayi juyawar ta ba tare da ta yadda ta sake duban kowa ba ta nufi ɗaki .

" Mama kar ki tafi ki barni ki jirayeni Mama , nan ina ne muka zo Mama ?

Chak ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin zuciyar ta na sauya bugu wannan muryar ta Mama ce , Mama ce take ƙiran ta , da kitsima hakan cikin ranta ta juyo da sauri laɓɓan bakin ta na ƙiran Mama .

Idanun ta suka sauƙa kan 'yar yarinyar da bata kai Mama a girma da wayo ba sai tsantsar kamanni da take yi da Mama , tana kokawar riƙe hannun Mamar ta da suke sauƙowa tare daga ƙafar benen a tare Khaalty Rahima na bin su a baya ,

"Yumna
Ta ƙira sunan ta da ƙaramin sautin da bai hana Yumna ta jiyo ta ba , a hankali ta ɗora ganin ta kan ta tana wara manyan idanun ta masu cike da wayo , sai ta sake matsawa jikin mamar ta tana riƙe hannun ta da kyau lokaci guda ta haɗa da maƙale kafaɗa .

" Yumna ki je wajen Mamar ki tana ƙiran ki , Siyama ta furta hakan tana ƙoƙarin zare hannun ta daga cikin na Yumma ,

A hankali Falmata ta ɗaga idanun ta ta ɗora ganin ta kan kyakkyawar doguwar matar da take tsaye gaban ta tana jifan ta da tsadaddan murmushin da yake sake fiddo zallar kyau da wayewar ta , ba sai an faɗa mata ba ta fahimci ita ce Mahaifiyar Yumna , kenan wannan ce Siyama matar Youssouf tuno da matsayin da suke kai a wajen juna ya sa tayi saurin juyawa ta ɗaga taku tana barin wajen , zuciyar ta cike da tunanin abunda ya kawo su haka ? Ko sakin nata aka zo kawo mata tare da matar tasa ?

Karɓa irin ta girma da girmamawa ita iyalan Maimartaba suka samu daga wajen Prof da nasa iyalan , duk kuwa da cewa ba'a san da zuwansu ba , hakan bai hana a shiga hidima da su ba ka'in da na'in babu ƙyashi Prof ya buɗe bakin Aljihu aka shiga hidima da su kamar daman can an san da zuwan su dan haka basu tarar da gidan tare da wata alama ta ƙasƙanci ba .

Gidan Attajiri suka tarar da ya matuƙar birge su a matsayin gidan su Matar da Youssoufa yake aure , duk sai jikin Ammi da Asma'u '( yar Hajiya Mama ) yayi sanyi da daman su biyun ne suka zo da wata manufa ta daban , sai suka ga ko su sai dai su gwadawa gidan su Falmata sarauta amma ba dai su ƙasƙantar da su ba . ( Daman Bare-bari ai ba daganan ba indai fagen bajinta ne ) .

Tunda Falmata ta shige ɗaki bata fito ba a ciki tayi sallar ta ta magarib da isha'i ta hau gado ta lulluɓu bayan ta kashe wutar ɗakin , ta rasa takamaimai halin da zuciyar ta take ciki , farin-ciki ne ko saɓanin sa ?
"watau sai yau ya waiwayo ta ? Bayan yasan ya mata laifi , yasan cewa dole tana jiran sa , yasan kuma a halin da take ciki da halin da ta baro wajen sa a ciki .
Can ƙasan ranta kuwa , So take ta ji ko da tashin ƙamshin sa ko kuwa amon muryar sa dan ta san cewa ya zo amma ko alama bata ji ɗuriyar sa ba a gidan .

Sai juye-juye take yi akan gadon , juyi ta sake yi lokacin da taji an turo ƙofar an shigo gami da kunna wutar ɗakin haske ya gauraya da sauri ta miƙe zaune bayan ta yaye mayafin da ta rufu da shi ,

Khaalty Rahima ta gani a tsaye a bakin ƙofa , daga inda take tana iya hango ɓacin ran da yake shimfiɗe kan fuskar ta ,
" Mama sannu da shigowa .
Khaalty Rahima bata amsa ba sai da ta ƙaraso kusa da ita , sannan tace " me kike a ɗaki ke kaɗai ? Kina sane da baƙin da suke gidan nan domin ki suka zo , "yan uwan mijin ki ne na jini , wai me yake damun ki ne ? Aina kika koyo wannan mugun halin na walaƙanta mutane ?

A ɗan tsorace Falmata tace , kiyi haƙuri Maman mu , un daman ai naga Yakaka tana wajen su suna hira .

Daƙuwa Khaalty Rahima tayi mata da hannuwanta duk biyu , " kin ci gidan ku Falmata, dangin Mijin Yakaka ne ko naki ? To bari na faɗa miki gara tun wuri kiyi watsi da wannan banzan halin ki daina dan kuwa ba inda zai kai ki , Mijin ki ɗan Manyan mutane ne gaba da baya ɗan sarauta ne shi da 'yan uwan sa halin girma da girmamawa cikin sa suka taso , shi aka saba gwada musu , muddin kika ce zaki je musu da saɓanin sa ke ce za ki sha wahala kiyi baƙin jini a wajen su ba ke ba har ya'yan da zaki haifa musu .

Shigowar Amnee bai sa Khaalty Rahima ta tsagaita ba ta cigaba da cewa , " ki tashi ki shirya ki fito kije ki gaishe su da kyau da kyau biyu daga ciki yayun mijin ki ne ɗaya kuma ƙanwar sa ce ƙaramar su , ɗayar kuwa kishiyar ki ce nasan ba zaki gagara sanin cewa 'yar uwar sa bace da suke 'ya'yan Mace da Namiji dan haka gara ki nutsu kiyi hankali ki daina wannan futsancin naki da tsagerancin wofi ,idan ba ma Allah yayi ba ina ke ina su ?

Unm, unm , unm Rahima banda gori kuma , ai shi arziƙi da ɗaukaka na Allah ne , amma 'yata ke ma baki kyauta ba baƙon ka ai abun girmamawa yake a wajen ka , bare kuma waɗannan da suke tafe tun daga wata ƙasa musamman domin tafiya dake , ki shirya kije ku gaisa har can falon Baa Alaji za'a raka ki akwai Manyan mutane da suka zo tare ɗaya daga cikin su Baffan Maigidan ki ne kuma shine waziri garin su sai kuma wasu manya daga wajen su dan haka kiyi shiga ta kamala sosai ko na shirya ki ?

Sai a lokacin Falmata ta ɗago kanta da hakan ya bawa ƙwallar idanun ta da suka taru damar zubowa faɗan da Khaalty Rahima ta mata ya haɗu mata da tasowar miƙin irin cin mutuncin da 'yan uwan Youssoufa suka masu a Niamey da yana daga cikin dalilan da yasa ta bar shi wutsiya a zage.
Muryar ta na rawa tace

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login