Showing 42001 words to 45000 words out of 411050 words

Chapter 15 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14291

son fita domin zuwa neman kuɗi cikin gari ni kuwa zan muku hanyar da koh kwanaki nawa zaku je kuyi ku dawo idan ma kuma zuwa zaku dunga yi kullum kuna dawowa duk zan taimaka muku , ku dai da farko yanzu kuyi tunanin sana'ar yi , idan kun fitan

Cikin zumuɗi yagana tace toh ai ke kolo da kike fita cikin garin ke zaki fi mu sanin sana'o'in da zasu dace da mu kuma wanda zamu samu , ni dai ko ma meye zan yi , haka kuma nasan kawayena ma zasu yi ta furta hakan tana mai maida kallon ta ga yakaka wacce tayi shiru kamar ruwa ya cita , cikin ran ta wasi-wasin fitar su daga sansanin su take da fargabar abun da ka iya zuwa ya dawo a matsayin su na ɓaki da basu san ko'ina ba ,muryar kolo ta katse mata tunani

Toh kun dai ga ana aikatau a gidajen mutanen gari ,"ana bara , ana aikatau a gidajen saida abinci idan baka tare da ƙazanta ,ana yin aikatau har a cikin kasuwanni , idan kana so tashi biya idan kuma kana so biyan wata yanzu haka nima ina wanke-wanke da shara gidan wata mata amma tashi biya muke , kullum naira ɗari biyu take biyana kuma na ci abinci nasha ruwan leda ga kaya kuma tana bani  ,

bata tsagaita ba ta cigaba da cewa tun da ku baku da naƙasa zaku iya yin aikatau ita kuma ƙanwar ku tayi bara a bakin kasuwa wallahi zaku yi mamakin kuɗin da zaku samu akalla ɗari bakwai zuwa dubu ɗaƴa a kullum banda kuma kwancen kaya da za'a dunga baku da sadakar ɗanyen kayan abinci ,

Cikin nazari yagana da yakaka suke kallon kallo yayin da falmata tayi jugum ta ƙurawa guri ɗaya idanu tana tunani ,"

    *Toh mana bari mu ɗan huta koh* ?😁😍
    *Mu bar su Yakaka/Falmata/Yagana su yi tunani cikin tsanaki*

   

#Comnents
#Vote
#Share
#Fikrh
[6/24, 9:59 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association


*MAFARI.......*
( _hargitsin rayuwa )_




*umm'muaz*


10



Shiri yakaka take sauri-sauri , tana yi tana taya falmata yin nata shirin , cikin mintocin da basu gaza goma ba har sun kammala , duk da dai kayan su na jikin su da suka cire suka sake mayarwa amma bisa ga dukkan alamu da su da kayan nasu sun ɗan samu tsafta domin sun ɗan yi haske , hakan kuwa bai rasa nasaba da wanka da wankin da suka samu damar yi tun a dare jiya bayan da suka tsaida shawarar fara fita neman na kansu cikin gari a ƙarƙashin jagorancin kolo da yagana ,

Kamar yadda kolo ta tsara musu shine su yakaka da yagana kowacce zata fita neman aikatau , yayin da falmata kuma zata zauna a bakin kasuwa tayi bara ,"

Da farko yakaka bata amince da yin barar falmatan ba , turjewa tayi sam tace sai dai falmata ta bita inda zata samu aikin ta zauna ta dunga jiran ta har zuwa lokacin da zata kammala ayukan sai  su koma tare , abun da duk ta samu tayi musu hidima tare , kuma abun da duk ta ci , ta bawa falmatan ,

Sai dai ga mamakin ta firr falmata taki ta amince da tsarin ta , ta tsaya kai da fata akan lalle ita ma sai ta nemi hanyar taimakawa kan su wanda kuma hanyar a yanzu ɗaya ce ita ce yin bara , idan har kuwa baza ta amince tayi bara ba toh sai dai tayi zaman ta kawai a cikin camp domin bata ga amfanin bin ta da zata yi kawai ta zauna ba .

Ala tilas ta amince mata domin gudun bacin ran ta,  da kuma sanin cewa baza ta iya fita daga camp ɗin ta bar falmatan ba , toh ta bar ta a hannun wa ? Ga larurar da take tare da ita , amincewar ta shi ya zama dole sai dai bisa sharaɗin baza su nisanta da juna ba , dole a tsukin gurin da falmatan zata yi zaman barar ta anan ita ma zata nemi nata aikin .

                                _____

Yakaka , falmata ku fito mu tafi mana kar muyi rana , kolo ta riga ta gama magana da mai tsaron kofa
           ,"yagana ke furta hakan dai-dai lokacin da take ƙarasowa bakin kofar ɗakin da su yakaka suke ,"

        Gamu nan yagana mun gama shiri sai tafiya ,"
               cewar falmata fuskar ta ɗauke da yalwatatciyar fara'a a karo na farko da yagana ta gan ta cikin farin ciki kwatankwacin wannan , wanda bata raba ɗaya biyu murnar zasu fara dasa harsashin cigaban su ne a karon farko cikin tsananin rayuwar da suka tsinci kansu ,"

    Hannunwan su sarƙe da na juna suke sanya kafafun su domin barin cikin sansanin su da suka wanzu a cikin sa tun ranar da suka shigo birnin na maiduguri , yayin da sashi guda na zuciyoyin su ke cike da fata tare da burin zuwa su nemo na kan su ,gefe guda na zuciyoyin nasu kuma fargaba ne tare da taraddadin yadda fitar ta su zata kasance ,

     Sansanin su a bakin babban titi yake dan haka basu sha wahala ba wurin samun motar bus da take jigilar mutane zuwa kowanne sashi na garin ,

      Kasuwa monday market
        Kolo ta furta bayan ta tsaida wata kwaraɓabɓiyar motar bus da take ɗauke da mutane jingim a cikin ta ,"
          Shiga muje
        Cewar conductor ( karen mota ) wanda ya wangale musu kofar motar ,
     Ni ɗaya ce zan zauna akan kujera su akan inji zasu zauna ,"
          cewar kolo dai-dai lokacin da take shigewa cikin motar domin yi wa kan ta matsugunni ,"
          Wata zamiya kondoktan yayi tare da zabura ya babbake kofar motar ,"
        Nai gamma waɗannan ƙattin ƴan matan har su uku ne zasu hau kan inji  kut ? ,"

      Kayi hakuri dan Allah yayana ka taimaka mana wallahi naira ɗari daya ce jal da ni , kuma ni zan biya musu domin su da ka gan su nan koh sisi basu da shi mu ƴan gudun hijira ne , " cewar kolo cikin marairaicewa da karya wuya ,"

      Kai ina bazai yiwu ba malama waɗannan sun yi girma da hawa kan inji a jere su uku rus ,
         ya karasa zancen yana me jifan su yakaka da kallon banza wadanda suka yi tsilli tsilli a tsaye cike da taraddadin ganin samu da rashi ,sanin cewar idan aka ƙi ɗaukar su toh fa babu su babu tafiya dole su koma cikin sansanin su .

      Tsalle konduktan yayi ya ɗale motar gami da bubbuga murfin tare da cewa ",Muje oga,"

      Tsaya tsaya nima zan sauka tun da baza ka ɗauke mu tare da ƴan uwana ba ,"  Burki direban motar ya jaa lokaci guda ya juyo cikin hargagi yake tambayar me ya faru ne ?
      Konducto yayi masa bayani ," sake tambaya yayi akwai sarari ne akan injin ,"
     Akwai sarari oga sai dai sun yi girma sosai mutanen da ke kan sit zasu takura sosai ,"
     Wani banzan kallo direban ya wurga masa da jajayen idon sa ,"
   Ganin hakan ya sa da sauri konducton ya sauka gami da buɗe motar , yayi wa su yakaka alamun kira da hannun sa saboda har motar ta ɗan gifta ,"
         Miƙo kuɗin ku
       Cewar karen motar lokacin da direba ya daidaita motar sa akan titi
   Da sauri kolo ta miƙa masa tsohuwar naira ɗarin da ta gama shan wahala a hannuwan jama'a
    
         Azabar zafin inji da zafin ranar da motar ta ɗauka suka haɗu suka sa su yakaka , falmata da yagana haɗa gumi kirshiɓ suna ta ɗiga , yayin da suka kasa zama wuri ɗaya akan injin sai mutsu-mutsu suke suna jin zafin ƙunar da injin motar yake musu a ɗuwaiwai , uwa uba yadda suka takura suka cure guri guda kamar "kifayen gongon" gefe guda ga warin da konducton yake wanda ya buɗe hannayen sa ya tokare ɗaya hannun dai-dai fuskar falmata wari da tsamin hammatar sa na barazanar sanya su haraswa ,"

     Bayan tsawon lokacin da bai kamata ace sun yi shi ba daga tsakanin sansanin su zuwa bakin kasuwar , amma a sakamakon rashin kyaun motar ,tsufan ta da kuma tsayawa a sauke fasinja a ɗau wasu a hanya ,ya sa suka kusan shafe mintuna arba'in a kan hanyar da bai fi suyi mintoci goma zuwa sha biyar ba , "

       Cikin jigata suka sauko daga cikin motar , fuskar kowaccen su na nuna wahalar da ta sha a yayin tafiyar ,"

    Yawatawa da idanun su yakaka da yagana suke yi cikin mamakin ganin yawan jama'ar da suke ta hada-hadar su a wurin duk kuwa da cewa hantsi ne bai wuce karfe tara da rabi zuwa goma na safiya ba ,"

    Toh ku zo mu tsallaka titi kun ga chan ita ce kasuwar monday market maiduguri ( ita ce babbar kasuwar da take ci a kullum cikin birnin na maiduguri )
          kolo ke yi musu wannan bayanin .

Ba ƙaramin ɗauki ba daɗi aka yi cikin turƙa-turƙa kafin su yakaka suka iya tsallaka babban titin na Ahmadu bello da yake daura da kasuwar ta monday market ba ,"
 
                 BAYAN AWA ƊAYA

Duk wani zagaye sun gama shi amma basu yi dacen samun gurin da zasu yi aiki ba a zagayen har ma da ainahin cikin kasuwar , kama tun daga kan masu tuwo-tuwon da suke ciki da wajen kasuwar har zuwa kan goge-goge koh jiran shago , hasalima wurare da dama da suka je korar kare aka yi mu su ,"

  Yagana , yakaka , kun dai ga yadda aiki ya gagara samuwa a gare ku a cikin kasuwa , hakan ya sa ya zama dole ku shiga cikin unguwanni ku kutsa koh gida-gida da wuraren sayar da abinci na cikin gari koh Allah zai sa ku dace , ni yanzu gaskiya rana ta riga ta ɗaga aƙalla yanzu sha ɗaya da rabi ta kusa kun ga na riga na makara zuwa gidan aiki na , duk da dai cewa daga nan zuwa cikin unguwar da nake aikin babu nisa amma yakamata ace tun tuni ina bakin aiki kamar yadda na saba , saboda haka ni zan tafi idan ya so anjima da yamma mu haɗu a tasha inda mota ta sauke mu ɗazu , amma kafin nan ita falmata yakamata ta samu wurin zama domin yin barar ta domin kuwa babu inda ya kai bakin kasuwa samun sadakha , dan haka  mu matsa daga chan wurin gefen bankin chan ta tsaya ko ta zauna a wurin har zuwa lokacin da zaku dawo , ina mai tabbatar muku da zata samu kuɗaɗe sosai ,
            Duk kalma guda da take fitowa daga bakin kolo dai-dai take da ƙaruwar luguden da zukatan su yagana ke yi , wannan fa shi ake kira " anyi gudun gara an tadda zago " toh su kuwa ina zasu fuskanta cikin wannan turmutsutsu da taron jama'ah ?

Ta ina zasu fara dilmiyar da kan su cikin gari alhalin basu da tabbacin zasu iya gane hanyar da zata dawo da su nan mahaɗar ta su , wanda a zahiri cikin zagayen awa ɗaya jal da kolo tayi da su a tsukin kasuwar , a halin yanzu koh tashar da mota ta sauke su baza su iya komawa ba saboda kan su ya riga ya juye , ina ga batun kutsawa cikin gari cikin unguwanni , ai wannan zancen ma bai taso ba ,"

  Kusan a tare su ukun suka haɗa baki gurin fara magana ," amma sai yakaka da falmata suka saurara domin bawa yagana damar faɗin abun da ke nata bakin duba da cewa ta fisu kusanci da kolo ɗin ,"

    Kolo mun gode sosai da dukkanin dawainiyar da kika yi mana amma a gaskiya daga ni har yakaka babu wacce zata iya tunkarar cikin garin da nufin neman aiki ba domin kome ba kuwa dan gudun bacewa mu rasa hanyar komawa a matsayin mu na baki ," jaan numfashi tayi lokaci daƴa tana mai sake marairaicewa , dan Allah kolo ki idasa taimakon da kika yi niyyar yi mana ki yadda mu biki zuwa unguwar da kike yin naki aikin idan ya so sai mu shiga gidajen cikin unguwar mu nemi aikin koh Allah zai sa mu dace ? 

    Ɗan jim kolo tayi cikin nazari a zahiri bata son su yakaka su bita su ga irin aikin da take yi sanin cewa ta boye musu gaskiyar aikin nata , amma ita sosai take tausayawa musu musamman yagana wacce take da wani boyayyen buri akan ta , "

       Toh shikenan ku biyo ni amma da sharaɗi ," kamar yadda kuka ce kun fito neman aiki ne dan haka baku da wani zaɓi akan irin aikin da zaku yi ,"domin unguwar da nake aikina ta sha banban da sauran unguwanni ," nan ne gaba kaɗan tsallaken titin nan ta karashe zancen tana yi musu nuni da wata hanya da ta gangara kwari ta miƙe sosai daga gaban su ,"

  Ke kuma ta juya ga falmata muje ki zauna akan dutsen chan ki ɓuɗe hannun ki ki fara bara , kar ki motsa koh nan da chan zuwa yamma zamu dawo mu same ki ,",
 
       Cikin rashin kuzari yakaka take taku domin raka falmata wurin zaman ta inda gefen titi ne daf da bakin kwalta kuma ta baya jikin bangon kasuwa ne da yake kewaye da shagunan saide-saide,  gefe da gefe duk masu saide-saide ne na kayayyaki iri daban-daban wasu sun yi kashi-kashi akan buhu da algarara wasu a wulbaro wasu akan tire ,wasu kuwa ƴan tebura ne da su ,yayin  da gaba kaɗan kuma wani babban gini ne mai kama da ma'aikata ( banki ) ,"

     Dai-dai gefen wani ɗan tsoho mai sayar da kayan gwari suka cewa falmata ta zauna kan wani ɗan dutse ,'

       Cikin nutsuwar da take halittar ta ta laluba ta ɗosana duwawun ta ,",
    
Durkusawa yakaka tayi akan guwowin ta gami da kamo hannunwan falmatan tace ,"
       Falmata dan Allah ki kula da kan ki kin ga inda muka ajiye ki ɗin nan ki zauna kar ki motsa koh nan da chan ,

         "ɗaga kan ta tayi ta dubi sama taga akwai rangwamen hasken rana sakamakon manyan giza-gizan da suke yawo suna kare ranar ,

" idan kin ji kishirwa ga wannan",

ta kunce bakin zanen ta ta ciro wata tsohuwar naira goma wacce ita falmata bata san inda ta samu ba ,"

ki sayi ruwa da shi ki sha idan kuma Allah ya sa kin samu sadakha idan kin ji me tallar abun sayarwa ki sayi wani abu ki ci ,

sake damƙe hannun falmatan tayi tana me jinjina hannunwan su da suke haɗe da na juna ,

falmata kar ki je koh ina ki jira ni dan Allah , kuma ki kula min da kan ki ,"

       Yakaka ni fa sauri nake da Allah ki taso mu tafi ,"

cewar kolo cikin gundura da doguwar maganar da yakakan take yi da ƙanwar ta ta , wanda ita da yagana ba jin abun da take faɗa suke ba sakamakon ƙasa da muryar ta da tayi ,ga kuma hayaniyar motoci da ta muryoyin jama'ah  ,"

Yunƙurawa tayi ta mike tare da cewa '" yi hakuri kolo mu tafi ,
          idanun ta akan fuskar falmatan wanda a zuwa yanzu ta kasa fahimtar a wanne yanayi zuciyar falmatan ke ciki ,"

   Tayi taku biyu ta ji hannun falmatan ya sarƙe a cikin nata ,"
        ", Yakaka dan Allah kar ki ɗaɗe kuma ki lura da kyau da wurin da kuka ajiye ni kar ku manta wurin , sannan kuma kema ki kula da kan ki , Allah ya baku sa'a kije ki dawo ina jiran ki anan yakaka ,"

           Daga haka ta zame hannun ta daga cikin hannun yakaka ta buɗe zazzaƙar muryar ta tare da ware hannuwan ta biyu ,ta fara rero kalmomin bara ,"

       Alaro sadakah fisabilillah
       Alaro sadakha fisabilillah

Gurbin fararen idanun ta cike taf da hawayen da suke sheƙi a cikin hasken ranar , zuciyar ta kuwa ta jima tana kwararar da hawayen maraici da wata irin kewa maɗaukakiya ,"

     Juyawa yakaka tayi cikin sassarfa tana mai bin bayan su kolo waɗanda har sun riga sun soma tafiya ," lokaci guda tana mai share ambaliyar hawayen da suke shatata akan farar fuskar ta , "zuciyar ta kuwa wani irin raɗaɗi da zogi suke yi mata tana jin kamar baza ta iya tafiya ta bar ƙanwar ta anan ba , tana jin kamar idan ta bar ta wani abu zai taɓa ta , " tana jin kamar ta kasa bata kariyar da ta kamata ,"  sai dai sashi guda na zuciyar ta yana mai karfafa ta da cewa ta tafi ai ZATA DAWO TA SAME TA ,' kuma a yanzu wannan hanyar ce kaɗai mafitar su domin tallafawa kan su .," da haka suka tsallaka babban titin da ya raba su da sashin kasuwa ,"

     Dai-dai zasu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login