Showing 168001 words to 171000 words out of 411050 words

Chapter 57 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14473

, tabbas maƙiya zasu cija yatsa , girma da martaba kouwa zasu tabbata ga Yarima Youssouf ,"
    Nan ta kudurce sanar da maimartaba a daren na yau da ita ke da turakar !

          *****

Biyamuradi Youssouf yana barin airport inda ya raka Tafeeda gidan su Dr Hamza ya nufa , maigadi shi ya nema masa izni,

  Yana shiga ya tadda prof yana karin kumallo , suka gaisa faram-faram nan ya masa umarnin ya matso su ci abincin ,

Babu musu ya wanke hannun sa ya matso suka fara cin abun ƙarin ,"Fankaso ne da miyar ganyen alayyahu , sai kuma danderun tsokar ƙaramar dabba , gefe guda kuma kwaɗon zogale ne da yake mahaɗin kowanne cin abinci na prof ,sai kuma green tea ,

    Sosai ya nutsu ya ci abincin yana yabawa girkin maiduguri , bayan sun gama cin abincin ne prof ya gyara zama yana fuskantar Youssouf ɗin ,cikin nazari yace
    Zan so ka sanar da ni takaitatcen tarihin ka da kuma halin da ka kasance a ciki bayan rabuwar ka da iyalin ka da ta sanar da mu cewa ka mutu sanadin ƴan tawayen nan na boko haram ,"

     Shiru yayi yana jin yadda tausayin ta ke sake mamayar sa , Allah sarki ashe ta rufe kome , ta rufa musu asiri , ta lulluɓe laifin sa , ta gyara masa asalin ɗiyar sa a idanun jama'ar ta , idan haka ne shi kuwa zai cigaba da kare martabar ta a idanun su har abada , shi ma bazai taɓa tono laifin su da ta binne ba ,

  Asali na ni mutumin niger dagga yankin ,"Malbaza Uzine," dake ƙassar Tahoua ," ni sojja ne aiki ya shiggo da ni nan nigeria har munka yi amre da itta , bayan amren mu bada jimawa ba boko haram sunka kawo hari mahaɗar mu inda sunka far mouna da yakin da yayi sanadiyyar rabouwar mu har ta kai ga tayi zaton na moutu, sun ka yi gudun hijira zouwa nan ,"

  Lokacin da kuka yi aure a hannun iyayen ta ta karbi auren ta ?
  
   Mukut ! Biyamuradi ya haɗiyi yawu , shi wannan mutumin matsayin me yake gare ta ? Zaton sa ɗan ouwa ne ga mahaifi ko mahaifiyar yarinyar ,"

Cikin ƙosawa yace

   Mahaifi gare ta ya rassu , sai dangin ta ,"
 
  Kayi hakuri ina maka tambayoyi ne domin mu tabbatar da gaskiyar Alaƙar ku saboda yau duniya babu gaskiya ,"

Mu ma ta shaida mana mahaifin ta ya rasu sanadin tarzomar boko haram , mahaifiyar ta tare da sauran dangin ta sun bata , ta zo nan mun ƙarbe ta tare da ƴar uwar ta sai kuma juna biyu tare da ita wanda ta rasu wajen haihuwar ƴar,  ɗan waje na shine ya kawo su nan bayan ya tsince su suna walagigi cikin wahalar rayuwa a bakin titi ,

  Ya tsahirta ,

Yana duban Youssouf wanda idanun sa suka yi jaa saboda jin tausayin Yakaka da ahalin ta,

   Idan har dattijon nan da ya ɗauka wani jigo ne ga yakaka , yace shi bashi da wata alaƙa da su asalima taimakon su ɗan sa yayi suka kasance ƙarƙashin inuwar su , shi kuwa ai babu dalili ɗaya da zai sa ya bar ɗiyar sa hannun su , wajibi ne ya tafi da ƴar sa ,

Kamar Prof ya san tunanin da Youssouf ɗin yake yi , sai yace da shi
 
  Idan ka shirya tafiya da ƴar ka , koyaushe zaka iya zuwa ka amshe ta , tana tare ne da ƳAR UWA ga mahaifiyar ta wacce ka gan ta riƙe da ita jiya ,"

A hankali ya ɗago kan sa , yace zan iya ganin su ?

Ƙwarai kuwa bari a ƙira su ,"

Cikin mintuna kaɗan falmata riƙe da baby mama ƙarƙashin jagorancin hajja mai wurya suka bayyana a falon , fuskar falmata babu walwala , saboda ƙiran da aka mata na cewa ta kawo baby mutumin jiya ya dawo ganin ta , tambayar kan ta take yi wanene wannan mutumin da yake ta zaryar ganin baby mama ,?  Ita fa sam bata ƙaunar abunda zai ratsa tsakanin ta da ƴar kome ƙanƙantar sa ,

Bayan ta gaishe da prof da take jin tashin muryar sa tun shigowar ta falon ,

  Yace da hajja mai wurya
   Ƙarbi ƴar ki miƙa ta ga mahaifin ta , mun riga dai mun mata hudhuba tare da yanka kamar yadda addini ya zartar , ƙarƙashin yaddar uwar riƙon ta kuma ƴar uwa ta jini ɗaya da muka sani tare da yarinyar kafin bayyanar ka , amma kana da ikon sauyawa ƴar ka suna !

    Janye ƴar falmata tayi ta hana hajja mai wurya damar ɗaukar ta ,"

Waye baban baby ? Waye yace shine baban baby ? Baby ƴar mu ce ni da yakaka na , mu kaɗai muka haife ta , yanzu da babu yakaka ni ce mama , baba , yaya , kanwa , da gabaɗayan danginta , ko waye ma yace shine baban ta ƙarya yake muku wallahi ƙarya ne , ta ƙarasa zancen tana fashewa da kuka !

  Turus !
Biyamuradi Youssouf yayi yana bin fuskar ta da kallo , ƙwarai ya shaida waɗannan idanuwan nata masu girma , ita ce wannan ƴar yarinyar da ta nemi yi masa faleƙe lokacin da ya fara tako kafafun sa cikin wannan gidan , biki , a watanni baya , ashe rashin sani shi yafi dare duhu , ashe ya tako har gidan da take lokacin da yake bulayin neman ta ? Allah ya raba ganawa a tsakanin su ,

Wani tsoro ne ya ji yana taso masa daga ƙarƙashin ran sa , tsoron kar ƙanwar ta ta san kome ? Kar ta tona asirin da shi da yakaka suka binne ,! Kar ta furta kalmar da zai shata layi tsakanin sa da mallakar ƴar sa , dan haka cikin sarƙewar harce yace ,

    Du-duba kin ka ce baki shaida ni ba ?  Baki gane ni ba ?
  
  Cikin hargagin kuka tace waye kai ?  ni ban san muryar ka ba , aina ka san mu ?  Ni da yakaka bamu da kowa a duniya kowann mu sun mutu , sai mu biyu a karshe Yakaka ma ta mutu ta bar ni tare da baby , bamu da kowa ni da baby , Baba wallahi ƙarya yake yana so ya ƙwace min baby dan Allah ku hana shi taɓa ta ,

  Wani kallon yatsutsu hajja mai wurya da daman cike take da halin ƙwalafaci da rashin yardar da falmata take gwadawa kowa akan baby mama , tace
   Ji min karfin hali ?? Ji min abun mamaki ƙurege da faɗa wa zomo daɗin ƙanzo , yanzu ke saboda Allah yarinyar nan un un un Falmata kike da suna ko wa ?? Yanzu ke uba zaki hanawa ɗaukar ƴar sa ?? Ina kika taɓa jin anyi haka ? Ina kika taɓa jin ɗa ya zama ɗan mace da dangin ta ita kaɗai ?? A rashin yardar taki da kowa kuma har da uban ƴar ?? Ni dalla bani ƴa na miƙata ga uban ta , har akwai martabar da ta zarta ta mahaifi ga ɗan sa , ?

  Kukan da falmata ta fashe da shi wanda ya ja ƴar jaririyar ma ta tsanyara kuka shi ya sa Youssouf zabura akan kafafun sa ya miƙe ya tsaye ,

    Kyale matta ɗiyar , batta ta cigaba da riƙon ta ,

Fatima zahra, yi shiru abun ki babu mai raba ki da ɗiyar nan , ɗiya ai taki ce , ki daina kuka kin ga ita ma kuka take ,

    Lallashin ƴar ta shiga yi tana yi tana share hawayen ta , '

Duban sa ya maida kan prof da yake yawo da idanun sa a kan su, cikin ruɗani yana son fahimtar mai gaskiya a tsakanin su ,"

Baba Fatima ta samou watta larura ne ?
  Ya furta hakan da sigar tambaya cikin son cire zargin da ya fara hangowa a idanun prof ɗin ,

  Bata da wata larura bayan wacce muka gan ta da ita ta rashin gani , sai dai ko rashin ƴar uwar ta ya sa ta a ruɗani ,!

Hamdala Youssouf yayi a cikin ran sa , ashe ma makauniya ce , idan haka ne kome zai zo masa da sauƙi ,

Babu shakka ta shiga ɗimuwa da yassa ta gaza gane ni , a bar ta kar ayi mata zancen kome har zouwa lokacin da zan dawo bayan kammaluwar aiki na ,

  Toh babu damuwa Allah ya kai mu lokacin ,
   Fatima ku koma ciki tunda dai kin ƙi a bashi ƴar ,

  Falmata da bata saurarar zantukan su ta himmatu wurin rarrashin ɗiyar da take gaba da sauran mutanen da suke wajen a wurin ta ,
cimak!  ta miƙe tsaye ,  riƙe da jaririyar da take ƙoƙarin komawa baccin ta ,
    Hajja mayar da ni ciki
Tace ga hajja mai wurya wacce take ta faman kyeɓe baki ,
   Yanzu Allah baza ki bada ƴar nan ba Baban ta ya gan ta falmata ?

   Da sauri Youssouf da har lokacin bai zauna ba yace , ƙƴale mata ɗiyar nan Babaa , batta ta cigaba da riƙon ta , ita ma ɗiyar ai tata ce ,"
  
  Ta gaban sa suka zo giftawa , yana bin su da kallon ƙwalafacin son ya ga ko ƴar fuskar ƴar ta sa,  yadda falmata ta kumburo fuska ta haɗe girar sama da ta ƙasa yaso bashi dariya ,ita a dole kar a taɓa mata ƴar ta ,

  ƙwarai sai ya ji ta burge shi , yadda ta jajirce take ƙoƙarin bada kariya ga ɗiyar sa ya motso shauƙi daga ƙasan ran sa , ashe ba shi kaɗai bane yake jarumi akan ƴar ta sa , ashe ba shi kaɗai bane yake Ƙoƙarin bata kariya , ashe bayan shi ƴar sa tana da wata ƴar ƙaramar katangar da take kare da ita , da idan ta bunƙasa zata iya zama dangar dutse da babu saran da ya isa ya samu na bayan ta , madallah da ke FATIMA ZAHRA .

A gurguje Youssouf yayiwa Prof sallama da zummar dawowa nan da ƙasa da kwanaki arba'in lokacin da zai kammala aikin sa , zai dawo tafiya da ƴar sa ,

    Zaro damin kuɗi yayi daga Aljihun sa ya ajiye a gaban prof ,

  Baba ga wannan a ƙara cikin hidimar gida madallah nagode da karamcin ku ina nan dawowa ba da jimawa ba !

Kul ,
  Ɗauki kuɗin ka , bazan karba ba , hidimar fatima da jaririya zai cigaba daga aljihuna kamar yadda yake a tun farkon zuwan su har sai lokacin da riƙon su ya bar hannun na , dan haka ka ɗauki kuɗin ka , Nagode

  Ganin ba fuska ya sa Youssouf ɗaukar kuɗin sa , godiya mai tarin yawa yayi masa kafin ya miƙe yana barin gidan
   Cikin ran sa da addu'ar Allah ya sa har ya dawo yarinyar nan da aka ƙira da suna fatima bata ɓata masa shiri ba , sai dai yana jin bama zata iya ba saboda ganin sa yafi kowa iko da ɗiyar sa nan duniya !

******
Abuja

Cikin sati biyu duk wani shirin makaranta ya kammala ga Yakaka , inda samy baby ta zaɓar mata ,"Eyes Scholars School ,"wacce take makarantar boko da take chakuɗe da arabi tsantsa, a matsayin makarantar da take so yakaka ta dunga karatu ,

Duk da cewa Alhaji Gali attajiri ne kuma fitatcen ɗan kwangila amma sai da aka samu tsaiko gurin ɗaukar yakaka a makarantar , domin a cewar hukumar makarantar yakaka bata chanchanta da shiga ajin gaba da primary ba bayan interview ɗin da aka mata kamar yadda samy baby ta so a sanya ta , hukumar makarantar ta tabbatar musu da cewa ko ɗaliban su ƴan primary school sun wuce yakaka a matakin karatu ,

Bayan kai kawo da Alhaji Gali da shi ke ɗauke da nawin kome na dangane da karatun yakaka , ya dunga yi

Kuɗi da Alfarma suka yi aikin su inda hukumar makaranta ta amince da shigowar yakaka cikin jerin ɗaliban su ƴan matakin ajin farko na secondry school jss1 , tare da sharaɗin Alhaji Gali zai ɗauki mai yiwa yakaka ,"extra lesson",koyarwa na mussaman daga cikin malaman su na makarantar da kuma zai dunga biyan malamar a duk wata , domin a cewar su chakuɗa irin yakaka da bata san kome ba tare da sauran ɗaliban su zai iya kawo naƙasu ga karatun sauran ɗaliban su da suke aji guda da ita wanda a ƙarshe zai tado da ƙorafi daga iyayen yaran da zai iya kaiwa ga duƙushe tasirin ingancin makaranta a idanun jama'a ,

Ba tare da ƙorafin kome ba Alhaji Gali ya amincewa sharaɗin su , ganin sa ai duk abunda yayiwa samy baby bai faɗi ba , tana biyan sa dan haka bashi da asara ,

Nan take ya lale ya biya kuɗin malamar da zata dunga yin extra lesson ɗin inda aka zaɓar mata wata yarinyar mace da ashekaru zata haifi yakakar , tana tsakanin shekaru 36-38 , malama maryam ita ke ɗaukar su yakaka fannin I.R.K , ( Isalamic Religion knowledge )  abunda kuwa ya sa hukumar makaranta ta zaɓe ta shine domin zamantowar ta jajirtatciyar malama da ta kware a harkar koyarwa , duk da cewa fannin addini take koyarwa amma sun san zata iya koyar da yakaka English da Arabic sosai ta yadda gaba zata fara gane karatu da kan ta , bugu da ƙari gani da suka yi location ɗin gidan ta da na su yakaka duk ɗaya ne , dan haka suka ɗora mata wannan nawin ,

Babu musu malama maryam ta ƙarbi form ta cike a matsayin ta na malamar da zata dunga extra lesson na musamman ga sabuwar ɗaliba yakaka , ranta cike taf da farin cikin samun wannan damar na amsar wani ƙarin kuɗi akan albashin ta na kowanne wata wanda kusan da shi rayuwar su ita da ƴaƴan ta da mijin ta suka dogara , zuciyar ta cike da burin zage ƙwanji ta koyar da yakaka da dukkanin iyawar ta har sai watarana anyi mamaki , .

Ga bangaren yakaka bata jin kowanne  irin yanayi dangane da sabuwar rayuwar ta na jin daɗi ko akasin sa , iyaka ta san har zuwa yanzu da take samun wajen sati uku a sabuwar rayuwar ta , kewa tare da so gami da tausayin rayukan nan biyu da ta bari a bayan ta yana nuƙurƙusar zuciyar ta tare da yiwa walwalar ta kisan mummike ,

Ko yaushe kewar falmata ta dame ta takan zauna tayi kuka iya kuka , tana son sanin a wanne hali suke ciki ita da ƴar jaririyar da ta bari ? Tana son jin tashin muryar falmata ,

Sai dai a ɗan tsukin zaman da ta fara yi a gidan samy baby da irin mutanen da take gani a gidan tare da saurarar wasu daga cikin hirarrakin su da fiye da rabin sa ba ganewa take ba , ya sa ta sake kafa naci akan neman ilmi ya kuma sa ta fahimci shi ilmin ashe muhimmancin sa ya kai sai ya wadata ga mutum sannan mutum yake samun cigaba da kaiwa ga wani matsayi a rayuwa ,

dan haka ta kuɗurta cikin ran ta a yanzu komawar ta ga su falmata bai da amfani , zata tsaya ne ta nemi ilmi iya yin ta , tunda dama ta samu gare ta ,  ta yadda ita ma zata tsaya da kafafun ta , ta koma rayuwar ta ta baya ta gyaro kuskuren ta , ta ɗauke ƙanwar ta da ƴar ta , su ma ta tsaya musu suyi karatu su samu ilmi ,

bata tunanin akwai azal , bata tunanin lokacin ba a hannun ta yake ba , bata tunanin shi lokaci juyawa yake yana wucewa cikin kowacce daƙiƙa da idan kuma har ya wuce baya dawowa , shin ko lokaci zai jira yakaka har zuwa cikar burin ta kome yana nan yadda yake kamar yadda ta tsara shi take kuma buri ???

Duk yadda yakaka tayi zaton samun ilmi na da sauki ta tadda abun ba haka nan yake ba domin tun ranar da ta sanya kafafun ta cikin makarantar da awanni kaɗan da suka wuce daga ta tuno da kusantowar ta ga fara zuwa makaranta neman ilmi ji take farinciki na mata lulluɓi , da har take sakin murmushi akai akai ,

Labarin ya sha banban lokacin da yakaka ta sanya ƙafafun ta cikin ajin da aka mata jagora tare da bata tabbacin nan ne ajin karatun ta ,

Tayi zaton zata tadda ƴan mata sa'o'in ta ne a ajin a matsayin abokan karatun ta , sai ta tarar da yara ƙanana da manyan cikin su ma Falmata zata iya girme musu ,

Jiki a sanyaye ta bi bayan mai mata jagora inda ya kai ta chan ƙarshen ajin ya nuna mata wajen zama ,

Zama tayi tana satar kallon yaran da kusan su dukkanin su suka waigo suna bin su da ido ,,alamun mamaki ɗauke akan fuskokin su har wasu daga ciki na magana da junan su ƙus-ƙus

Hankalin ta bai sake tashi ba sai da ta ga malami ya shigo yayi koyarwar sa ya gama , bata kai ga fahimtar ko kalma guda ba saboda bata jin yaren da yayi magana da shi , cikin rashin sanin ta bayan darasin da malamin integrated science ɗin ya koyar da su har ,"class work/aikin cikin aji ,"ya bayar yana jiran su kammala ya bi ya duba   ,

Ɗaya bayan ɗaya ya dunga bin ɗalibai yana duba class work ɗin da ya basu , ya yabawa wasu , wasu kuma ya gargaɗe su , duk dai cikin yaren da yakaka ba fahimtar sa take ba , har ya zo kan ta ,

  Wani kallon gargaɗi yake jefa mata

Hey what are you doing

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login