Showing 135001 words to 138000 words out of 411050 words
Chapter 46 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ne dan ku sa kuyi kwalliya kuma ku shiga cikin jama'a ayi biki tare da ku ,
ta ƙarasa zancen muryar ta na bayyana jin haushin su , bayan kusan mintoci ishirin da ta kwashe tana bin su da lallama akan su zo su tafi ,"
A hankali yakaka ta miƙe tana sake gyara babban mayafin da ta lulluɓe kan ta da shi wanda shi da kan sa doctor hamza ya zaɓa mata shi , jikin ta sanye da doguwar rigar nan , kyau kam tayi sa iyakar kyau , tamkar irin wayayyun yaran matan nan da suka fara tashe a duniyar shahara ," cikin ta ya ɓoyu a cikin rigar sai an lura da kyau za'a hango tudun sa,"
Yi hakuri Rahima , falmata ta shi muje ,"
Ni kam yakaka ko naje ma me zan yi a wurin ? ni da ba gani nake ba...
Eh dai koma me zaki ce kizo mu tafi har ke ," ai zaki saurari kiɗan
Rahima ta katse ta da sauri
Miƙewa ita ma tayi tana gyara ɗan siririn mayafin da ta rufe kan ta da shi , ɗan jim yakaka tayi ,"
Falmata ko dai na baki babban gyale na naga wannan kamar yayi ƙarami ? tana bin ƙawar ta ta da ido ganin yadda kayan suka mata cif-cif kamar wata babbar budurwa ,
Wai ma ji yakaka toh ai haka ake yayi bakya ganin rigar doguwa ce mai dogon hannu ? Dan Allah kar ki ɓata mata kwalliya ku zo mu tafi ,"
A hankali suke tafiya saboda takalman kafafun su da basu saba sa irin su ba , tafiyar kan ta a tsorace suke ji suke tamkar zasu faɗi ,"
Sun baro ƙofar sashin doctor hamza sun ɓullo ɗan wani siririn fili da zai sadar da mutum da harabar gidan falmata ta dogare ta ce ita daga nan zata tsaya , jin yadda take jiyo sautin kiɗan tamkar a gaban ta ,"
Rahima bata tsaya saurarar ta ba ta jaa hannun yakaka tana cewa
Ai sai kiyi ta tsayuwar idan kin ga dama ma ki koma ɗaki ," yakaka zo mu tafi ,
Ba da son ran yakaka ba ta bi bayan rahimar tana waiwayan falmata , wacce take murmushi jin yadda rahima take nuna jin haushin ta ," cikin ran ta tana ayyana taje gurin kiɗa tayi me ?? Ita ba gani ba bare tayi kallon jama'a ,' zata jira su anan har su dawo ,'
Ta tsakankanin jama'a rahima ta dunga kutsawa riƙe da hannun yakaka har sai da suka bullo gaban filin ya zama , suna ganin duk wanda ke tsakiyar filin rawar ,"
Biyamuradi youssouf yayi tsaki yafi a ƙirga , ya kuma yi danasanin zuwan sa wurin wannan hayaniyar , tun asali daman shi ya tsani kiɗa domin ko nasu na masarautar su baya yadda su buga masa a gaban sa suna nufo shi yake sawa a tare su ya sallame su ,"
uwa uba tashin hankalin da zuciyar sa ke ciki , wanda duk wata ƴar sakewa da yayi suka ɗan taɓa hira da abokan tafeedan kawai ɗaurewa yake , sam bashi da nutsuwar zuci , tafeedan da kan sa ya fahimci hakan .
Duk yadda yaso janye tafeeda su bar gidan ƙi yayi a cewar sa shi tsarin yanayin al'adar su ta burge shi dan haka zai ɗaukar wa mairamar sarki hotunan su haɗi da videos ya je ya nuna mata ,"
Da ace ya san kan garin ko kuma shi ya tuƙo kan sa ya zo , da tuni yayi tafiyar sa daga wajen , domin a halin yanzu ma chan gefe ya samu ya tsaya yana faman ciccin magani ,da ginshirin su irin na sarakai ," '"ah toh yarima anan wa zaka yiwa ??
Gani yayi gurin bai masa ba saboda yadda hankalin ƴan mata dayawa yake kan sa , dan haka kawai sai ya bi wata ƴar hanyar da ya gani daga gaba da inda yake tsaye kaɗan ," ba tare da ya san ina bane , sai dan gani da yayi akwai alamun rashin mutane ta wajen ,"
Ƴar siriyar hanyar ya shiga inda yake hango wani ɗan tudu da zai iya zama akai , sai da ya isa wajen ya lura da tsayuwar wata yarinya daga gefe a raɓe da jikin bango tana fuskantar ciki ,"
bai kula da wanzuwar ta ba ya zaro wayar sa ya shiga dubawa bayan ya zauna ,"
Tun takun sa na farko a wajen ta ji shi , ta cigaba da jin tahowar sa kafin daga baya ta ji an zauna a ɗan nesa da ita , jin shiru ya sa ta waiwayo ba domin tana son ganin wanene ba sai domin ta fargar da wanda ke wajen samuwar ta a wurin ,"
sun jima a haka shi ya manta ma da ya ga mutum a farkon zuwan sa wurin ,
Kamar ance ya ɗago kan sa , karaf ya sauke akan ta tana nan a inda ya gan ta tun farkon zuwan sa wajen ," idanun ta fes akan sa bata ko kifta su ,"
Shima kallon ta yayi sosai , ya ga dai ta tsare shi da manyan idanun ta da yake iya hango girman su da sheƙin da suke a sauran hasken ranar da take gaf da faɗuwa , " kamar shi take kallo kamar kuma ba shi ɗin take gani kai tsaye ba ,"
Yarinya ce a idanun sa bata wuce mairamar sa ba , a idanun sa ma sai ya ga tana yimar yanayi da mairamar yanayin yadda ta tsaya daga jikin bango alama fushi tayi taƙi fita zuwa wajen bikin nasu ,"
ɗan murmushi yayi tunowa da yayi da rigimar mairama yana jin kewar ta na taso masa ,"
Tsintar kan sa yayi da son yayi mata magana tun da ta rasa mai rarrashin ta ta huce,"
Ƙanwa ta ke baki gajiya ne da tsayuwa ??
Wara idanun ta tayi lokacin da ta ji tashin muryar sa , wannan ba doctor hamza bane ,toh WANENE ???
Da sauri yakaka take ratsa mutane tana son fitowa daga cinkoson gurin da ya sake ruɗawa da buɗa haɗi da sowa ana ɓarin kuɗi sakamakon shigowar ango da amarya cikin filin rawar ,"
dakyar ta samu fitowa ta nufi hanyar sashin doctor hamza , duk hankalin ta yayi kan falmata , bikin ya ɗauki hankalin ta har bata san ta ɗauki lokaci haka ba sai da ta ga duhun dare ya fara shigowa ta farga !
GAN,GAN ,GANNN ! GA ƁARAWO GA MAI KAYA , ƘAƘA TSARA ƘAƘA ???
DAFATAN ZAKU BAIBAYENI DA RUWAN RA'AYOYIN KU , GAME DA WANNAN SHAFIN , ME KUKA HANGO ME KUKA FAHIMTA ME KUMA KE SHIRIN FARUWA ?? KAI ABUBUWA DAYAWA FA , GA SUNAN DAKI-DAKI . BAN SAN KO KUN GANE BA ???
BARKA DA SALLAH ONCE AGAIN ! 😍🙏[10/3, 2:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: Mafari ....
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
26
Ji tayi an riƙo hannun ta ta baya , tana daf da ƙarasawa sashin doctor hamza , fuskar ta da murmushi ta juyo ga zaton ta rahima ce ,"
Rahima , Falmata nake son na duba , kin ga dare ya fara yi bana son .....
Sauran kalmomin ta maƙalewa suka yi a fatar bakin ta lokacin da tayi arba da fuskar samy baby a maimakon rahimar da take zato ,
An-anty samy ke ce ??
Ba tare da samy baby ta saki hannun ta ba ta fara tafiya tana nufar cikin gidan da ita sashin su rahima , ba musu ta bita tana waiwayen hanyar sashin doctor hamza , da fatan ko zata hango falmata , yayin da ran ta yake cike taf da fargaban abun da samy baby zata bijiro mata da shi ,"
Waye ne a anan ?
Falmata ta furta hakan tana mai sake wara ƙwayar idanun ta ,"
Shiru youssouf yayi tare da kafe ta da ido ,
Watau dai ita mace kome ƙanƙantar ta mace ce ," ji wannan ƴar yarinyar ma wai dan kawai nayi mata magana shine har zata min gwalangwaso da fi'ili ta nuna ma bata ma ganni ba sam.," tsaki ya jaa gami da mayar da hankalin sa kan wayar sa ,
Sarai ta ji tsakin da yayi mata kasantuwar ta mai nisan ji , ko yaya abu yayi motsi tana iya ji tun daga ƙasan ran ta ," jikin ta taji yayi sanyi ," koma waye bai gane bata gani ba , " ba laifin ta bane ,"
Dan haka ta juya a hankali tana laluben jikin bango da nufin komawa ɗakin doctor hamza ,"
Kiran wayar sa da Tafeedah yayi shi ya sanya shi miƙewa bayan ya ɗaga kiran inda yake sanar da shi ya zo su tafi masallaci daga chan kuma su wuce masauƙin su sai kuma gobe su dawo ɗaurin aure !
Da sassarfa ya bar gurin da daman jin sa yake tamkar akan ƙaya !
Tsumu yakaka tayi a gaban samy baby wacce ta tsare ta da tarin tambayoyi wani kan wani ,"
Sake ɗagowa tayi a karo biyu ta dubi samy baby kafin ta muskuta cikin yin ƙasa da murya tace :
Antƴ samy a gidan nan muke da zama ni da falmata , kuma yaya dakta shi ya kawo mu ,"
Wanene yaya doctor ? Kina nufin likita yayan su zainab ?
Gyaɗa kai tayi
Shi ne !
Daman ya san ku ne ? Ko ƴan uwan ku ne ??
Kawai ya taimake mu ne bamu san shi ba amma tun farkon zuwan mu garin nan tun muna sansanin mu yake taimaka mana !
Jimm samy baby tayi tana aunawa tare da juya zantukan Yakaka cikin ran ta ,"
Meye tsakanin ku da shi ? Ya taɓa cewa yana son ki ne ?
Da sauri ta girgiza kan ta
A ah ni baya so na !
Bai tambaye ki akan cikin jikin ki ba ? Me kika ce masa game da cikin ?
Cewa yayi waye ya min cikin ? Ni kuma ban faɗa masa ba , tun daga ranar bai sake tambaya ta akan cikin ba , sai ya kawo mu gidan su nan , yace mu zauna , yana kula da mu sosai ni da falmata , har asibiti yake kai ni ayiwa baby photo dan Allah kar ki sa su kore mu anty samy bamu da wani wajen da zamu je a yanzu da ya fi nan ,
Ta ƙarasa zancen hawayen da take tarawa a ido suna silmiyowa ,"
Guntun murmushi tayi
Ni bazan sa su kore ku ba yaks , ki daina kuka ,!
iyeeh watau har hoto aka yiwa baby ? kice dai kin shirya zama uwa sosai yaks
jaan numfashi tayi kafin ta sake wurgo mata wata tambayar da ta sa zuciyar yakaka tsalle ,"
Ya labarin yarima uban cikin jikin ki ko har kin haƙura da neman na shi kin daina son shi saboda kin samu gidan hutu ?
Ban - ban daina son shi ba anty samy kullum yana raina inason sake ganin sa , ban san yadda zan yi na gan shi ba ne ,! Ko kin samu labarin inda yake ?
Murmushi tayi
Nasan inda yake yaks !
Zuruf ta miƙe tsaye batare da ta ji nawin cikin jikin ta ba ta matsa ta kamo hannun samy baby ta riƙe gam.,
Aina yake anty samy dan Allah ki kaini wajen sa , wallahi ina son shi , ina son na gan shi ki taimake ni !
Koma ki zauna yaks ba abun gaggawa bane , ki nutsu akwai maganar da nake so muyi da ke , amma....
Shigowar sofi ta katse abun da samy baby take nufin cewa ,
Da wani irin hargitsatsen kallo ta bi yakaka , kafin ta juya akalar hararar ta ta kan samy baby ,"
Ke kuma me ya haɗa ki da wannan koɗaɗɗiyar ƴar gudun hijrar ?? Ko wani aiki zata miki ? Nifa na tsane su yi sauri ki sallame ta duk ta cika mana wuri da tsami da hamami ,"
Ba tare da samy baby ta amsa mata ba tace ga yakaka
Ta shi ki tafi abin ki ,
Cikin sanyin jiki yakaka ta miƙe tana satar kallon sofi ,haushin ta na cinkushe mata rai ," sam ran ta bai so ba da zata bar gurin ba tare da taji wani ƙwaƙƙwaran bayani game da bature kam silum ba ," ta so ta ji ina yake da zama da babu abun da zai hana gobe ta je ta gan shi ko da kuwa da kwatance ne!
Dai-dai tazo barin ɗakin ta waiwayo suka haɗa ido da sofi wacce take bin ta da kallon banza ," bata yi ƙasa a guiwa ba ita ma ta galla mata harara tana mai ƙarasa barin ɗakin ,"
Duka samy baby ta ɗakawa sofi a cinyar ta wacce take ta faman baloƙoƙo akan hararar da yakaka tayi mata sai faman zagin ta take tamkar zararriya
Ƙawata ke fa banza ce yanzu akan wannan ƙanƙanuwar yarinyar kike ta ɗaga murya haka ? Alhali ma tayi tafiyar ta ," ko dai haushin kaza kike huce akan dami ," hala shi autan mazan ya miki abunda ya saba ?
Cisge ɗankwalin kan ta tayi jelar gashin dokin da tayi manyan kitson ghana suka watsu akan kafaɗun ta,"
Bari kawai kawata wannan ɗan tahalikin yana son ƙure gejin hakuri na akan sa , " bai san cewa akan sa kaɗai sashin zuciyata mai mutunci take iya tasiri ba , amma tunda yaƙi ta mutunci toh fa ko da tsiya -tsiya wallahi sai ya so ni kuma ya aure ni , sannan na juya shi yadda na so a lokacin da na so , Naga shege ko shegiyar da ta isa yin min katanga da cikar burina , wallahi ko gyatumin sa sun yi tsororo ! Hamza nawa ne ni kaɗai ,
Da kallo samy baby ta bita tana nazarin kalaman ta tare da ɗauko kulawar da hamza yake bawa su yakaka tana haɗa su tare da yin dogon nazari ,
ita tasan wacece sofi tasan bala'i da kaidin sofi , bata fata ko kusa ko kaɗan ace wani sha'ani na adawa ya ratsa tsakanin ta da yakaka ,
wacece yakaka ? Bata tunanin ko uwar yakaka ta isa karawa da sofi akan abun da take ƙwalafacin so bare yakaka ,
tana tausayin yakaka da gaske baza ta so ba ta faɗo hannun sofi ta wannan mummunar hanya , ta sani sarai cikin ƙanƙanin lokaci sofi zata ɓatar da yakaka daga doron ƙasa ,"
Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji sofi tana cewa
Wai kin kuwa san ma me yayi min ? Bata jira amsar samy baby ba ta ɗora ,
Tsawa fa ya min a bainin nasi , dan kawai na nemi ya tsaya muyi hoto ,"
Ta ƙuta , ai wallahi bashi ya ɗauka , zai kuma biya da tsada lokacin da ya shigo hannun na ,
Ta miƙe tana mai nufar bathroom ,
Da kallo samy baby ta bita ," ya zama dole tayi wani yunƙuri domin ganin ta hana wannan yaƙin faruwa tsakanin ƙaramar yarinya yakaka da sofi , dole ta zare yakaka daga rayuwar hamza muddin ta gano yana da manufar soyayya da yaks ɗin kamar yadda ta hasaso , " ai idan ka ga kare na sunsuna takalmi ɗauka zai yi ," kuma banza bata kai zomo kasuwa ,"
10:30pm
Duk yadda Tafeedah ya kai ga son sanin meke damun Youssouf da har ya firgita shi ya zama barazana ga nutsuwar sa , Youssouf ɗin yaƙi faɗi masa , iyaka yace masa ya gaji ne da zaman nigeria yana son komawa ƙasar su ,
wanda shi Tafeedah ko kusa zancen bai shige sa ba , tayaya Youssouf masoyi ga aikin sa kuma jajirtatcen jarumi a fagen daga zaƙwaƙuri wurin bawa ƙasar sa kariya tare da sadauƙarwa zai ce ya gajiya ? Babu shakka akwai wani abu wanda yayi girman da yake neman jirkita masa tunanin aboki da shi bai kai ga sanin wannan lamarin ba ,"
Kallon sa ya mayar ga Youssouf ɗin wanda yake kwance bisa gado ya takure cikin bargo gami da bashi baya , ji yayi duk wani ɗan kuzarin da yayi saura a jikin sa yana barin sa , bayan tsawon watanni tara da rabuwa da ganin junan su , yau sun haɗu amma babu wani armashi a haɗuwar ta su kamar yadda suka saba ya haka idan aiki ya shataa layi ya raba su , toh fa duk ranar da suka haɗu kusan raba dare suke suna hirarraki da dararrakin su ta hanya bawa juna labarukan bayan rabuwar su , "
Youssouf amini ne a gare shi ƙari kuma ɗan ouwan sa ne na jini , amintakar su mai ƙarfi ce ta yadda idan ɗaya ya kasance cikin damuwa ɗayan ya kan gaza sukuni har sai sun haɗu sun samarwa da kan su mafita , damuwar sa a yanzu bai wuce yadda Youssouf ɗin yake kokarin boye masa abun da ke damun sa ba , da hakan yake baƙon lamari a tsakanin su sai dai ko ma menene zai bi a sannu har ya kai ga sani ,
Ga Youssouf ɗin kuwa damuwa ce ta yi masa katutu , kan ɓacewar yakaka , mafi girman lamarin shine cikin da aka ce tana tare da shi , tunanin sa idan ba'a kai ga samun ta ba har ya bar nigeria yaya zai yi ?? Shikenan zai tafi ya cigaba da rayuwa alhalin wata na nan ta wanzu tana aikata babban zunubi ana raba musu tare ??
Wannan lamarin ya girmama a gare shi danasani kuwa yayi ta yafi sau shurin masaƙi , a bayan kowacce daƙiƙa damuwa ke sake masa lullubi , ya ƙagauta gari ya waye ya sake komawa gidan madam Saly ya ji yaya aka kwana ?
Yawan damuwar ita ta bayyana kan