Showing 336001 words to 339000 words out of 411050 words
Chapter 113 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
" Maman mu da Amnee ku yi haƙuri ku yafe min , amma ni bazan koma ba.
Kallon da suka bita da shi bai sa ta tsaya ba cikin kuka ta cigaba da cewa
" 'yan uwan sa basa sona zagin mu suka dunga yi suna min gori har iyayena suka aibata sun ce ɗan uwan su ya sake ni me zai yi da ni 'yar gudun Hijira 'yar matsiyata Mama har cewa suka yi ...
" Khalass Amnee tace tana zama a gefen ta ta riko ta zuwa jikin ta , kukan da take yi ya taɓa ran su sun kuma fahimce ta , daman Khaalty Rahima ta riga ta san akwai wani dalilin da yasa falmata ta yi mu su yadda tayi , tasan halin 'yar ta Falmata mutum ce mai zuciya da gudun raini , ko kusa bata yadda a taka ta ba tare da ta rama ba .
Amnee ta cigaba da cewa
"Ko ma me suka ce miki ai ga su dai yanzu iyayen su sun taso su da aiken zuwa su koma da ke cikin girmamawa saboda kin riga kin zama wata ɓangare na jikin su , kiyi haƙuri ɗaukaka bata zuwa a sauƙaƙe , sai an zage damtse an ware ƙwanji wajen neman ta an kuma haɗa da haƙuri da juriya , wa ya faɗa miki inda samun ɗaukakar ka yake zai kasance kewaye da masoyan ka ? Ai ɗaukaka mai tasiri ita ce wacce aka ratsa tsakanin maƙiya wajen samun ta .
" ki zama jaruma Fatima-zara gidan sarauta kike aure , Yarima kike aure watarana idan da rai Matar sarki za ki zama dan haka saurin fushi ai ba naki bane .
"Sau da dama akwai wuraren da fushi baya yin tasiri sai fa saɓanin sa watau kwantar da kai da kawaici , hannun da ya juri miƙo maka gorar duma kana shan ruwan ciki da ɗaci , sannu kan hankali watarana shi zai miƙo maka gorar zuma tattaciya ka kwankwaɗa daga zaƙin ta , muddin kayi haƙuri saboda kome na duniya ɗan haƙuri ne kiyi haƙuri ki maida kome ba kome ba , kin ji ko ?
Gyaɗa kai tayi tana share hawayen ta , zuciyar ta taji tana sanyaya daga ɗacin da ya cunkushe mata rai , ko ba kome yau sun tako sun ga tushen ta inda Mahaifiyar ta ta taso gidan wanda yake matsayin Mahaifi a wajen su , sun kuma san cewa ita ba walaƙantatciya bace har irin yadda suke zato tare da yin iƙirari , daidai gwargawdo Prof ya zama inuwar fakewar su .
" shiga wankan maza ki fito na shirya ki kin ji ko ?
Amnee ta sake cewa hakan lokacin da Khaalty Rahima ta juya tana barin ɗakin .
Da taimakon Hasken da yake falon tar kamar rana Siyama ta ɗora ganin ta akan Falmata wacce tun kafin ƙarasowar ta wajen ƙamshin sassanyan turaren wutan da Amnee ta turare ta da shi iri daban-daban da kuma humra ya ratsa ƙofofin hancin su .
'yar ƙibar da tayi bai sa takun tafiyar ta mai kyau sauyawa ba , tana shirye cikin turarriyar koriyar lafaya mai adon manyan furanni launin jaa mai duhu , da ta naɗa ta akan wata doguwar rigar atamfa mai launin kore mai haske tayi ɗaurin ɗankwali sassauƙa fuskar ta babu wata kwalliya sai ɗan kunnen ta dogo ruwan silver da ya amshi 'yar zagayyar fuskar ta mai ƙaramin kyau .
fuskar ta ɗauke da 'yar madaidaiciyar fara'a ta ƙaraso .
Yanzu ne ta ga Fatima-zahra sosai , sai dai bata hango abu guda da ya razana ta game da ita ba da ya wuce yarintar ta , ko ba a faɗa mata ba ta ga alamu da dama a bayyane yarinya ce ɗanya da bata wuce shekaru goma sha tara zuwa ishirin ba da in kuwa hakane a kiyaste zata iya girme mata da shekaru aƙalla takwas zuwa tara , ba shakka tauraruwar ta zata daɗe tana haskawa .
Murmushi tayi lokacin da take miƙewa , kafin falmata ta ƙarasa durkuson da take shirin yi ta ɗago ta , ɗago kan ta Falmata tayi suka yi musayar kallo kowaccen su da taƙaitatcen murmushi akan fuskar ta ,
" Kul ki daina yawan durƙuso ƙamna ta , so kike ki yiwa ɗiyan mu lahani ? Ƙaraso ki zamna ni na amshi durƙuson na gaishe da yayun mu ,
Hannun ta ta jaa suka ƙarasa kujerar da ta taso daga kai , maimakon Falmata ta zauna akan kujerar da take mata nuni sai ta zauna a ƙasa ta shiga gaishe da Ammi da Asma'u da suke bin su da kallo , suka amsa mata kamar ɗazu a taƙaice suka ɗora da tambayar ta lafiyar jikin ta ? Murmushi tayi bata amsa ba .
Ta waiga ga Siyama wacce take kallon ta fuskar ta cike da murmushi , "sannu ku da zuwa Mamar Yumna yaya hanya ?
"lafiya lau Fatima ƙamna ta da fatan mun cimmuku ƙalau ?
"Lafiya .
Falmata ta amsa mata a ɗan taƙaice , a mutunce suka gaisa da Aisha Mairama .
Shiru ya ɗan biyo baya kafin Asma'u ta juya ga Amnee da son jin ƙarin bayanin da take mata kan haɗin wani turarurruka ( humra )na musamman da matan N'Djamena ke amfani da shi a sassan jikin su da tun shigowar su Amnee ta tare su da tururrukan humran launi-launi cikin wasu 'yan ƙananun kwalabe da aka jera su akan ɗan wani faranti na musamman , ta basu suka shasshafa da daman haka al'adar su take na tarar ɓako da turare musamman idan baƙon na girma ne ,
Ƙamshin sun yiwa Asma'u daɗi kamar yadda ruwan turaren da kansa ya burge ta launi-launi gwanin sha'awa ga turaren ya zauna musu a jiki ko yaya suka motsa ƙamshin sake tashi yake .shine take son sanin yadda ake harhaɗa su , Amnee kuwa tayi alƙawarin koya mata .
Ita kuwa Ammi takaicin Siyama ne fal ya cika mata rai cikin ran ta cewa take "haba me ake da lusaranci irin na Siyama ? Yanzu kishiyar ce abun tarairaya da gatatawa ya haka ? Tun a can ta so a hana Siyamar tahowa saboda ita bata ga dalili ba zuwa bikon kishiya , amma Siyama ta kafa naci har da yin fushin da guntuwar ƙwallar ta , ganin haka yasa Umma amincewa aka taho da ita domin da farko ita ma ƙin amincewa tayi da tafiyar ta Siyama .
" en loi kin yi kyau sosai , ƙwalliyar ki ta burge ainun .
Mairamar sarki ta furta hakan lokacin da take baro inda take zaune ta dawo kusa da Falmata ta zauna , gani na farko da ta yi mata ta ji ta burge ta ,tana ƙaunar ta musamman da ta gan ta yarinya kamar ma zata girme mata .
"Nagode , Falmata tace tana 'yar dariya idanun ta ta sauƙe kan Yumna da aka mata Shimfiɗa da wani lallausan bargo daga gefe tana ta baccin ta da alamun gajiya a tattare da ita ,
" tayi bacci ne ?
tace da ƙaramar murya ,
Murmushi Siyama tayi tana cewa "ɗiyar ki tayi baccin gajiyar hanya bata saba ba , ga shi kouma baku ko gaisa ba da alama dai yau a ɗakin ki zata kwana da dare idan ta farka kun gaisa ...
"Da gaske ?
Falmata ta furta hakan tana dariya cikin zumuɗi ta ɗora da cewa
"bata ƙuiya sosai ko ? Ba zata yi rikici ba ko ? Tunda bata sanni ba Bana so tayi kuka .
Siyama tana murmushin jin daɗin ganin zallar ƙaunar 'yar ta a fuskar Falmata tace
" A haka zaku saba ai 'ɗiya ba ta ƙi mamar ta ba...
Kafin ta ƙarasa faɗin abunda tayi niyya Muryar Ammi ta katse mata zancen ta ta hanyar cewa .
"So kike tayi ta ihu kenan ? Wannan ai ɗaukar hakki ne ki bar 'yar ki a katarar ki sai yafi alheri .
Shiru wajen yayi na ɗan wani lokaci kafin muryar khaalty Rahima ta ratso wajen fuskar ta da ɗan murmushi tace
" gaskiya kam bare ga baƙunta ga baƙuwar fuska abun zai zama bibbiyu , gara ta zauna a wajen Mamar ta cikin Alheri .
" Yakaka da ta lura da sanyin da jikin Falmata yayi sai tace " Falmata da son yara kike wallahi, anya ma kuwa za ki yarda a ɗau naki , zamu gani ai lokaci kaɗan ya rage ke ma ki riƙe naki a hannu inshaAllah .
Mairamar sarki ma da abunda yayar su ta ta so yi ya ɗan sanyayar mata da jiki sai tace
" ai kuwa ni ce mai raino dole ma ta ba mu ɗan mu ko 'yar mu ko mon beau-père ?
Dariya Siyama tayi tana waskewa hararar da Ammi take jefo mata ta ƙasan ido tace
" ɗakina ai nan ne wajen ajiyar kayan sa , ni zan dunga shirya shi , kafin a yaye shi daga an yi yaye kuma zai dawo wajena gabaɗaya sai dai Mamar su ta kawo mana wasu kuma .
Amnee ce katse musu hirar da suke yi lokacin da ta ce , " Aisha raka ta ta gaishe da baƙi a sashin Baban su .
Bayan dawowar su daga gaishe da su waziri Falmata bata tsaya a falon ba ta musu sai da safe kawai ta shige ɗaki , tana warware lafayyar jikin ta zuciyar ta na ga tunanin bata gan shi ba ,Ina yake ? ko dai bai zo bane ?
Gabaɗaya sai ta nemi ɗan farin-cikin da ta tsinci kan ta ciki ta rasa da daman zuwa yanzu ta fahimci kusanci da shi da ta samu sanadin ganin 'yan uwansa da zaton ta tare suka zo zata gan shi shine ya sata murna .
A yanzu kuma da ta fahimci bai zo ba duk sai ta ji ƙunci na safko mata wani sashi na zuciyar ta taji yana raɗa mata , " Falmata ke fa kike damuwa da shi dan rashin zuciyar irin taki , shi bai damu da ke ba tunda ga shi ya ƙi zuwa wajen ki sai wasu ya turo wai su tafi da ke sai kace wata kaya , zuwan nasu da bai wani burge ta ba , a gurin ta da shi kaɗai tal yazo , ta gan shi suka yi komawar su tare da hakan ne zai sanyata farin-ciki akan waɗannn da aka turo ga shi tun a gaban iyayen ta ma wannan yayar ta shi sai wani hararar take , ko meyasa ta tsane ta ? Oho .
Mts
Tayi tsaki lokacin da take zama bakin gado , tana ƙoƙarin ture tunanin sa dake damun zuciya da kwakwalwar ta .
" Falmata na , ai damuwa kuma ta ƙare tunda ga 'yan uwan sa sun zo tafiya dake , za a mayar da ke gun angon ki mu huta da jin kukan ki da ganin ƙuncin ki "oh su soyayya manya .
Yakaka ta furta haka da dariyar tsokana lokacin da take ƙarasowa cikin ɗakin ,
Yamutsa Fuska tayi ta kawar da kai gefe kafin tace " waye yake cika miki kunne da kukan Yakaka bana so .
"Rabu da ita en loi , jibi war hakka kina cikin masarautar mu bayun ki na miki hidima daɗa ai ke ɗin sarauniya ce matar Yarima ,
Murmushi su duk biyun suka yi da ganin shigowar Aisha da ta cigaba da cewa
" kun yi waya da Biyamuradi ko ? Ya jikin na shi da sauki kou ? Ni dai nan tunda munka tasso da mun ka baro shiyar ƙasar mu Téléphone carte sim pas de service .
A hankali Falmata ta ɗago kanta zuciyar tana sauya bugu , da wani yanayi a muryar ta tace " Daman ba shi da lafiya ne ? Me ya same shi ?
Da sauri Aisha ta dafe kai tunowa da tayi da farkon zuwan su a can falon Prof bayan Waziri ya yiwa Prof taƙaitatcen bayani kan rashin lafiyar Youssoufa da shine dalilin da ya kawo jinkirin zuwan su , amma zuwa yanzu lafiya ta fara samuwa gare shi da yardar Allah , a ƙarshe suka daɗa neman afuwa tare da neman iznin tafiya da Falmata a gobe .
Prof ya jajanta musu sosai ya kuma yi musu addu'o'i sannan sai shima ya shigar da neman Alfarma kan a ƙara masa kwana guda tal a bar tafiyar tasu zuwa jibi , sannan kuma ya nemi da a sakayawa ita Falmata batun rashin lafiyar Mijinta tunda bata riga ta sani ba saboda halin da take ciki da ba'a son abunda zai tada mata da hankali .
A take duk suka yi Na'am da shawarar Prof kan cewa za'a rufe rashin lafiyar Youssoufa har sai Allah ya masa dawowa sannan kuma zasu ɗaga komawar su zuwa jibi .
"Aisha daman Youssouf jinya yake ?
Yakaka ta tambaya tana dafa kafaɗar Falmata da ta lura ta shiga damuwa sosai .
Da ƙoƙarin sauya akalar zancen Aisha tace " eh ,Ah ah ba wani ciwo bane ya dai tafi india ne , kai Mutanen Maiduguri kun ji daɗin ku ko'ina turaren wuta yana ci
Ta ƙarasa zancen tana musu nuni da ɗan burner da take cin turaren wuta a hankali .
" yayi tafiya ? Kuma kika ce ba shi da lafiya ne , dan Allah ki faɗa min mana ,
Falmata ta furta haka tana jin wani gagarumin tashin hankali na rufar mata , muryar ta har 'yar ƙyarma take yi .
Da sauri Aisha ta zo gefen ta ta zauna , ta dafa kafaɗar ta sannan cikin taushin murya da alamar rarrashi tace ,
" en loi kadda ki damou Biyamuradi ya shiga haɗarin rayuwa ne Amma Allah ya fidda shi , doumin kouwa yanzu yana samun lafiya sosai , cikin watan ga mai kamawa shi ke dawowa da yardar Allah kin ji kou ?
Gyaɗa kai kawai Falmata tayi daga haka ta miƙe daga tsakanin su , su duk biyun da kallo suka rakata har ta shige banɗaki .
Yakaka ta sauƙe ajiyar zuciya tana dawo da ganin ta kan Aisha , cikin yin ƙasa-ƙasa da murya tace .
"amma ciwon da yake damun sa ba mai tsanani bane ko ?
Ita ma cikin raɗa Aisha tace " ya fa fara samoun sauƙi nima dai baƙina ya subce min .
Miƙewa tayi tana ƙarasa cewa " bari na kouma ga masauƙin mu daman na tou yi muku sai da sahe .
" ku huta gajiya Aisha mun gode ,
Yakaka ta furta hakan da 'yar dariya ganin yadda duk Aisha ta ruɗe da ganin sauyawar Falmata .
bayan ta fita a sarari Yakaka tace "Hmm indai wannan 'yar rigimar ce ba ku ga kome ba .
" wa kenen ?
Falmata ta tambaye ta lokacin da take takowa cikin ɗakin kai tsaye ta nufi ɗan saƙon da suke yin Sallah ta hau Sallaya bayan ta zura dogon Hijab har ƙasa ta fara haramar tada iƙhamar sallar shaf'i .
" Ni kaɗai nake zance na Yaa Falta .
Yakaka ta furta hakan tana miƙewa ita ma ta tafi ɗauro Alwalar ta .
Washegari tun asuba masu aiki suka shiga hidimar abincin Baƙi Amnee da Khaalty Rahima basu zauna ba suna tsaye a kan su suna sa hannu a inda ya dace suna kuma gwada musu .
Kafin ƙarfe takwas illahirin harabar gidan har maƙota ya ɗau ƙamshin girki da sumfurin ƙamshi iri-iri na daga sunadaran ƙamsasa girki na mutan N'Djamena .
Mutan Niger sun ci sun gyatse sun kuma yaba sun zuba santi ba kaɗan ba domin kuwa Ɗan Malikin Maraɗi Mai ruwan kuɗi lokacin da ya gama ƙurbe shayin da aka cika masa 'yar butar shayi ( kettle ) cewa yayi " shi kuma wannan ruwan me sunan sa ? 🤔 ga shi dai yana wani zaƙi-zaƙi kamar tattaciyar zuma farar saƙa , ga kuma wani tsami-tsami da yake yi kamar matsatsen ruwan ɗan itaciyar inabi , ga kuma wani garɗi-garɗi da yake kamar ruwan zam-zam , ƙamshin da yake tashi a cikin sa ai mai samar da nutsuwa ne irin wannan idan kana shan sa kullum ai ka tsufa da ƙarƙon ka 😂
Amnee bata zauna ba ita ta shiga gyara Falmata ta sake goge mata jiki da sauran kayan gyaran jikin Amare da ya rage , kasantuwar bata iya zanen fulawa ba hakan bai hana bayan ta gama murjewa Falmata jiki ta kama kwaɓa lalle da turarurrukan ƙunshi irin nasu bayan ta jiƙa ganyen 'yar itaciyar "Sofan " ta ɗiga ruwan sa da yayi jawur a ƙwabin lallen ta ɗan ajiye shi ya jiƙu kaɗan ta kama ƙafafun Falmata ta rangaɗa mata lallen gargajiya a tafin ƙafar da kan yatsu .
Sha ɗayan rana Hajja ta iso da daman tun jiya Amnee ta ƙira ta a waya take sanar da ita batun zuwan dangin Mijin Falmata da zancen komawar su .
Da gama wayar su Hajja ta hau shiri ran ta cike da farin-cikin jin cewa Uwarɗakin zata koma ɗakin ta , daman bikin ya ƙare dan haka yau tun safe ta bi dangi ta yiwa kowa Sallama .
Prof ya nemi ganawa da Amnee tare da Khaalty Rahima bayan sun amsa ƙiran su ya tambaye su kan me da me ake buƙata da Falmata zata tafi da shi ?
Amnee tace " Baa Alaji ai lokaci ya ƙure na yin wani babban shiri sai dai kawai za'a ɗiba mata su turaren wuta a cikin na 'yar uwar ta ..
"Meyasa ita baza'a mata nata ba kada a taɓawa 'yar uwar ta kayan ta .
Prof ya katse ta , cikin kwantar da murya Amnee tace " to ai lokaci ne ya ƙure yau ne fa kawai ? Idan aka ɗibar mata kaɗan na Amfani idan ya so bayan sun tafi sai nayi waya can N'Djamena ayi mata nata a kuma ƙarowa Takwarata nata a tsanake idan Allah ya sauƙe ta lafiya sai mu tafi mata da kayayyakin ko kuwa ?
Ta tambayi khaalty Rahima . "Hakane Ukhtee ,
Prof ya ce to kayan ɗaki fa da na Amfanin gida ba za'a sauya mata wasu ba ?
"duk su ma idan ta haihu sai a mata sabbi tunda yanzu tafiyar ba ta shiri bace .
"Hakane to Allah ya kai mu kafin lokacin duk za'a tanadi kome ko ke da kan ki sai ki tafi Dubai yi mata sayayya .
Godiya mai yawa Khaalty Rahima ta yi masa bai amsa ba sai cigaba yayi da cewa a cikin ku biyun waccece zata