Showing 381001 words to 384000 words out of 411050 words
Chapter 128 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
tana yin baya da gudu ta rufo ƙofar tana jin wata matsananciyar kunya na neman sa ta kuka .
"Shine kana jina ba zaka amsa ba wallahi ka bani tsoro meyasa za ka leƙo ni ina banɗaki ?
Muryar sa tana bayyana dariyar da ta taho masa yace "ah leƙa ki nayi ? Ba ke kika ƙirani ba ?
"To meyasa baka amsa ba kawai ? Ta furta hakan muryar ta a shagwaɓe da jin haushin sa .
"Gani nayi zuwa da kai yafi saƙo , kuma ban sani ba ko ƙira na kike na wanke miki baya .
Ya furta hakan lokacin da ya koma ya zauna har yanzu dariyar shirmen ta yake gefe guda wani irin nishaɗi ne yake ji yana ratsa shi .
bayan ta gama wankan tana ƙudindine cikin Hijabi ta fito kai tsaye wajen da akwatin kayan ta yake ta nufa tana ƙin kallon sa .
Bata wani bincika ba ta ɗau wata jar atamfar ta da take sama sabon ɗinki ne fil acikin kayan da Baaa ya mata .
Banɗakin ta koma ta sanya kayan bayan ta ɗan shafa mai da ta gani a ajiye gaban makeup-mirror da yake banɗakin .
Riga da siket ɗin da ta sa sun zauna mata ɗas a ɗan tsararren murmurarren dogon jikin ta da mazauna ƙasar Amurka ke kiran mata masu zubin jikin ta da Miss-champagne, Mutan ƙasar ingila kuwa suka ƙira ta da Miss-Magnificent.
Lokacin da ta fito tana gyara ɗaurin ɗankwalin ta Doctor Hamza shagala yayi wajen kallon ta ya manta da abokin aikin sa da suke yin wata tattaunawa da shi a laptop.
Gaba ɗaya kyaun ta ya ɗau hankalin sa kafin ƙamshin sassanyar haɗin Humra ya game masa hanci da ta buɗe cikin kayan ta ta ɗauko ɗaya daga cikin kwalaben da ta taho da su ta tsiyaya kaɗan a tafin hannu ta shafe jikin ta da shi .
Yanayin ta na sanyi da nutsuwa shine yanayin da yafi so da ita komen ta sannu kan hankali take yi babu kwarafniya , irin ta irin matan da yake mafarkin samu kenan .
Da ɗan murmushin da yake cikon halittar ta tace "Yaya Dakta nagama .
Shiru ya ɗan yi yana kallon ta bai ƙi ba ace tayi tsaye haka nan gaban shi yayi ta kallon ta zuciyar sa na daɗa ƙawata masa kyaun halittar ta.
Yamutsa fuska ta ɗanyi saboda ta fara siƙewa da yunwar da take ji ,
"Yunwa nake ji..
Kafin ta ƙarasa magana ya miƙe ya tako a hankali ya kama hannun ta suka fita tare "muje ki ci abinci Wafaa .
Basu tarar da Sofi a falon ba , dan haka Doctor Hamza ya zaunar da ita akan ɗaya daga cikin kujerun falon yace "bari na ƙira Sofi kafin nan zuba mana abincin .
Da ɗan saurin sa ya nufi sama , Sofi wacce daman tana laɓe daga sama jin tahowar sa yasa tayi sauri ta fito daga maɓoyar ta ,
Tayi wanka ta sake sabon shiri cikin wata evening gown backless, launin sararin samaniya da ta bi tsarin jikin ta irin na matan da suka ɗau duniyar su da faɗi suke bin dare da rana wajen ganin zubin jikin su ya koma haka watau (Wisdom tooth body).
Rigar ta bi jikin ta ta lafe sassan jikin ta da suke da ɗaukar hankali sun bayyana a sarari.
Jikin ta ta haɗa da nashi ta fara masa salo , da sauri ya riƙe hannun ta da ta ɗaura akan ƙirjin sa yana dawo da nutsuwar sa dai-dai yace "Sofia wannan kayan bai yi ba ki je ki sauya kin san dai ba mu kaɗai bane a gidan nan ? Bai dace ba ki fito a haka .
Kaɗa ido tayi cike da shanye ruɗanin da ta shiga ganin yadda yau yake kawar da ido daga kan abubuwan da a da baya motsin kirki idan tana masa juyi a gaban sa tace "Doctor dan ka ƙaro aure ne zan kasa sakewa a gidannan ko meye ? It....
"Sofia pls ki fahimceni ko da a gaban mace 'yar uwar ki bai dace ki fita haka ba jikin ki duk a bayyane , kuma .
Ɗan tsahirtawa yayi yana kallon yadda koɗaɗɗiyar fuskar ta ta fara yin jaa da bayyanar ɓacin rai , gudun rigamar ta yake yi sosai dan ya san mahaukacin kishin ta baya so yayi wani abu da zai sa ta ƙullaci Yakaka dan haka ya riƙo hannun ta yana sake tausasa murya yace "kuma ai kin san dai ina kishin ki sosai unh my pump truck ?
Ɗan murmushi tayi tana jin zuciyar ta na farfaɗowa , haɗa jikin su ta sake yi tana kwantar da kan ta a kafadar sa a hankali tace "Doctor your Love is my strength and hope in this life always remember this.
Ajiyar zuciya yayi baki ɗaya hankalin sa yana ga Yakaka ya ɗan ɗagata daga ƙafaɗar sa "Sofi kiyi sauri ki sauya kayan ki sauƙo mu ci abinci Wafaa tana jiran mu .
Zamewa yake ƙoƙarin yi yaji ta riƙe hannun sa , cike da gajiya ya ɗaga idanun sa zuwa fuskar ta , hawaye ya gani sun ciccika gurbin matsakaitan idanun ta suna daf da fara sauƙa ,
"Sofia menene kuma ? Ya furta hakan cike da gundura .
"Ka raka ni na chanja kayan sai ka zaɓar min wanda ya maka .
Tausayin raunin da ya hango a tattare da ita da ya san son shi da tsananin kishin sa da take ya sa haka , sai ya gaza musa mata a ƙoƙarin sa na son kyautata mata ya rage mata raɗaɗin da take ji ya bi ta hannun su haɗe cikin na juna suka shiga ɗakin Sofi ta rufo ƙofar ta murɗa key .
Yakaka baki ɗaya tayi laushi a zaune kan kujera tun kan ta na sunkuye tana jiran ta ji takun sauƙowar su har ta kai ta fara ɗaga kai tana kallon ƙafar benen .
Ganin ko alamar su babu ita kuma yunwa na neman halaka ta yasa ta sauƙo.ƙasa gaban abincin ta zuba kaɗan a Plate ta cinye daɗin ɗanɗanon miyar Amnee da ta wadatu da kaji kamar zata tsinke mata kunne har wani lumshe ido take .
Kafin ta farga ta cinye cikin zaƙuwa ta daɗa wani , a cikin nutsuwa take cin abincin ta bata ankara ba sai da ta cinye kusan rabin abincin ta ɗaura da ruwa taji cikin ta dam .
Ta dawo nutsuwar ta sai lokacin ta fara farga da daɗewar da suka yi basu zo ba , ƙaton agogon falon da yake aiki ta duba ta ga har ƙarfe goma na dare saura 'yan mintoci .
Shirun da duniyar baki ɗaya ta ɗauka a kunnen ta ya tafi ya tado da maƙallalen tsoron da yunwa ta binne shi ,
Ɗas!Ɗas! Ƙirjin ta ya buga da tuno ƙaton karen da ta tabbata yana nan a cikin gidan yana shawagi .
Sauƙa tayi daga kan kujerar ta takure a ƙasa tana jin yadda baki ɗayan tsikar jikin ta ke miƙewa '
Tsoron ta yana sake hauhawa da ƙaruwar kowacce daƙiƙa ɗaya , bata san lokacin da ta miƙe ba a hankali ta nufi ƙafar benen ,sai kuma ta jaa ta tsaya tana jin shakkun hawa sanin da tayi ɗakin Sofi ne a saman , ita tsoro take ji sun bar ta ita kaɗai ko da ba zasu yi hira ba su sauƙo ta dunga ganin su .
Muryar ta tana ɗan rawa tace "Yaya Dacta , Yaya Dacta '
Ko alamar motsi bata ji ba
Ɗan sake ɗaga sautin tayi tana sake ƙiran sunan sa wannan karon har da "Auntie Sofi .Amma kamar basa gidan '
Wani irin tsinkewar zuciya ta ji da ya sa ta kusan faɗuwa saboda gurnanin kare da taji a daf da ita .
A daskare ta waiga bata ga karen ba sai fa gurnanin da take cigaba da ji , addu'o'i ta fara yi da duk ayar da tazo bakin ta bata saki sai ta kai ƙarshen ayar .
A hankali ta fara yin baya-baya har ta koma kan kujera, haushin da karen yayi da ɗan ƙarfi da yake bata tabbacin yana cikin falon yasa bata san lokacin da ta shige tsakankanin kujera kudundune ta cure guri ɗaya duk kuwa da rashin sararin wajen .
Bata san tsawon lokacin da ta ɗauka a haka ba sai ji tayi hannu na ƙoƙarin zaƙulo ta a wajen da bata kai ga fahimtar hannun mutum ne ko kuwa na karen da zuwa yanzu ta fara tunanin aljani ne ba.
Wani irin ihu ta sa tana runtse idanun ta gam cikin fitar hayyaci .
Riƙo ta Doctor Hamza yake yi tana kufcewa ba tare da ta daina ihun da take yi ba ,
Jijjigata yayi da ƙarfi yace "Ke Amina ki nutsu ki dawo hayyacin ki me yake damun ki ne haka ? Tsoron ki yayi yawa .
Jikin sa ta shige tana wani irin kuka cikin muryar kukan tace "Yaya Dakta dan Allah ka mayar da ni gida wallahi idan ba haka ba karen nan zai kashe ni ..
"Wafaa ki nutsu babu kare a gidan nan ba mu da kare tsoron ki ne ya cika yawa ki daina saka tsoron abu haka a ran ki da har zai dunga yi mi ki gizo .
"Akwai wallahi ba gizo bane akwai kare yanzu ma yana nan anan ina jin kukan sa .
"Wai me ya faru ne wannan take yiwa mutane ihu da daren nan ? Kamar wata sabon kamu ...
"Sofia ki yiwa mutane shiru please .
Hamza yace haka a harzuƙe da jin haushin ta .
Yana shafa kan Yakaka wacce take ta ajiyar zuciya a ƙirjin sa .
Ƙyeɓe baki Sofia tayi kafin ta tausa murya tace "Doctor ni yanzu ka zo muje muyi wankan mu ka san dai kullum kaina kake hana ni zama da janaba.
Kamar wacce wuta ta jaa ta Yakaka ta raba jikin ta daga na shi , kallon wasu 'yan daƙiƙoƙi ta yiwa ƙwarar idanun sa da suke cike taf da so da tausayin ta , ta sauƙe nata idon ƙasa tana jin wani irin abu mai nawi yana danne mata zuciya .
Da sauri Doctor Hamza ya taka yana son sake riƙo ta , sai ta sake gocewa cikin muryar ta da kuka ya duƙusar tace "kar ka taɓa ni Yaya Dacta kaje kayi wanka .
Bata tsaya ba sai ta juya da sauri dai-dai da sauƙar wata ƙwalla da bata san takaimai ta mece ce ba daga cikin idanun ta nufi 'yar hanyar da zata kai ta ɗakin sa tana jin tsoron da ya cika mata rai na raguwa sakamakon wani baƙon yanayi da zuciyar ta bata gama tantancewa da shi ba da yake mata ciwo a zuci fiye da tsoron.
Wata 'yar ƙaramar dariya Sofia tayi da yasa Doctor Hamza da duk ya jikin shi yayi sanyi kamar wani mai laifi ya mayar da ganin sa kan ta tana tsaye daga ita sai ɗan wani guntun towel da iyakar sa cinya .
Ƙaramin tsaki yayi yana hararar ta yace " Sofia ki dunga sanin abun da kike yi please .
Za ta yi magana ya ɗaga mata hannu tare da kewaye ta ya wuce ɗakin sa .
Da shigar sa ɗakin ya ɗora idanun sa akan ta tana kwance akan Sofa ta bada baya da alama tayi shirin bacci domin ta rufu da dogon hijabin ta daga wuya har ƙafar ta .
Wani irin tausayin sa ne ya tsirga masa baki ɗaya ya rasa me yake damun ta take irin wannan tsoron shi dai tunda ya san ta ya san ta da tsoron kare amma bai san abun nata yayi ƙamari haka ba .
Bai ce ƙala ba kamar yadda ita ma bata nuna alamun ta san da shigowar sa ɗakin ba ta ya wuce Banɗaki .
Yakaka da idanun ta suke rufe tunda ya shigo ɗakin ta buɗe idanun ta a hankali tana jin yadda damuwa take ƙara mata yawa har ta rasa da wanne zata ji ? Da tsoron Sofi wacce ta mata barazanar da take da tabbacin zata iya aikata mata abunda ta ce ko kuwa da tsoron karen da yake gidan yake rayuwar sa da take da tabbacin Sofi ta san da zaman sa tunda tare ta fara ganin su .
Gefe guda kuma ga ciwon da take ji kan yadda zuciyar ta ke ƙenƙesa mata rashin so da shi kan sa Doctor Hamza ya fara gwada mata banda haka ita ta wuni da yunwa ƙarƙashin horon Matar sa , shi kuma tunda ya dawo banda nan-nan da matar tasa da yake yi suna naniƙar juna baya ta tata da take baƙuwa a tsakanin su dan saboda tsabar cin zarafi ma daga zuwa ya ƙira ta shine.'...
Ai ita ba yarinya ƙarama bace ta san abunda ya tsaya yi da matar sa , duk da tasan yana son Matar sa amma bata san son da yake yi mata ya kai ya mayar da ita wofi ba a dararen su na farko a rayuwar aure , tun yanzu ma kenan Sofi ta fara janye shi lokacin da yakamata ace da ita yake tare ina kuma a gaba ?
Kalaman Sofia suka fara dawo mata da take gargaɗin ta kan haɗa shimfiɗa da mijinta "to a yadda ta ishe shi ɗin nan ma ita yaushe zai wani kula ta ?
Ita dai ai kawai zata zauna ne ta ga yadda rayuwa zata mata amma bata tunanin wani farin-ciki irin wanda ake samu a rayuwar aure .
Ko da ya fito tsayuwa yayi a kan ta bayan ya sanya riga da wondo na kwanciya bacci , a hankali cikin tausasa murya ya ƙira sunan ta "Wafaa , shiru tayi kamar bata ji shi ba .
Jikin sa ya ba shi idanun ta biyu tana jin sa dan haka ya taka a hankali ya matsa tare da zama a bayan ta jikin sa na gugar nata .
"Wafaa nasan kina jina ta shi muje na baki abincin nima yunwa nake ji .
Shiru ta sake yi , ganin haka ya sa hannu ya juyo da ita bayan ya janye hijabin da ta rufu , idanun ta da suke ƙasa-ƙasa yake son kallo amma taƙi da kyar ta iya cewa "yaya dacta nifa naci abinci na ƙoshi .
"Meyasa kika ci kika barni ? Daga yau idan ba bana gida ba kar ki sake cin abinci ke kaɗai ba tare da ni na baki ba kin ji ?
Shiru tayi masa .
Sake sassauta murya yayi saboda ya fara fahimtar kamar fushi take yi da shi abunda kuma ba halinta bane ita mace ce ma'abociyar fara'a da yawan murmushi.
"To yanzu muje ki zuba min ni na ɗan ci ko kaɗan ne kin ga yunwa nake ji sosai .
Ɗan jim tayi kafin tace "to .
Tsayawa yayi yana kallon fuskar ta da ta ɗan kumbura kumatun sai ya ga kamar daɗa kyau tayi "Wafaa kome kika yi sai kiyi kyau da kike fushi kamar kar kiyi dariya idan kina murmushi kuma bana so ki daina saboda fara'ar ki haɗe take da farin-ciki na
Ɗago kai tayi ta ɗan kalle shi tana jin tasirin kalaman sa har a cikin ran ta , a hankali tace "mu tafi ka ci abincin .
Da suka koma falon ta zuba masa abincin dai-dai cikin sa yana ci yana ɗan kallon ta da tayi shiru tamkar mai tunani kafin ya fahimci gyangyaɗi take yi .
Bata san lokacin da ya gama cin abincin har ya Sha shayin sa ba saboda kwantar da kai tayi a jikin kujera sosai take bacci .
A hankali ta ji ya taɓa ta da yasa ta firgit ta buɗe idanun ta da suke cike da bacci ta kalle shi ,
"Mu je ki kwanta Wafaa dare yayi sosai .
Kama hannun ta yayi suka shiga ɗaki bayan ya kashe wutacen falon da duk wasu na'ura .
Sofia wacce duk abunda suke tana falon a laɓe daga lungun kitchen da yake da ɗan duhu ta saɗaɗo ta fito ,
Wani ƙaramin ɗaki da yake matsayin na 'yan aiki nan ta buɗe ta shiga bayan ta ɗau kwanon miyar da sauran miya da nama yake ciki ,
Tana buɗe ɗakin Sam da yake kwance ya taso da gudun sa yana ɗan gurnani , shafa kan sa tayi kafin ta ajiye masa kwanon a gaban sa .
Wani irin ɓacin rai take ji bata ƙi ba ta ɓace ta ɓulla cikin ɗakin Doctor Hamza ta ga me suke yi shi da Yakaka ? Duk da dai tasan ba shi da buƙata amma ita fa ko kallon Yakaka bata so ya dunga yi
"Ya zama dole nayi wani abu akai ba zan iya zuba ido haka ina kallon su ba kissa kaɗai ba zata gamsar da ni ba kar na tsaya galala shegiyar yarinyar nan ta min shigar basaja .
Ta furta hakan a sarari lokacin da take barin ɗakin ta jaa ƙofar ta kulle tana nufar ɗakin ta .
Duk yadda Yakaka ta so Doctor Hamza ya ƙyale ta ta kwanta kan kujera ƙi yayi dan dolen ta da kuma baccin da ya riga ya ci ƙarfin ta ta dawo kan katifar daga can ƙarshe ta kwanta .
Tana kwanciya kuwa bacci ya ɗauke ta , fahimta da yayi baccin ya mata nawi ya sa shi jaan jiki a hankali ya matsa ya haɗa ta jikin sa , yana jin wani irin nutsuwa ta musamman tana bin jijiyoyin jikin sa yayi musu addu'a yana rufe ido bacci mai daɗin gaske ya ɗauke shi .
Da asuba shi ya riga ta tashi , motsin da yayi da kuma fitsari da ya matse ta yasa ta buɗe ido a hankali .
Cikin nutsuwa ta fara fahimtar a inda take kwance kan ƙirjin Doctor Hamza .
Wani irin bugu nata ƙirjin yayi abu na farko da ya fara safkowa kwakwalwarta gargaɗin Sofi .
Kamar an soke ta ta miƙe daga jikin sa ta fara ƙoƙarin matsawa ta sauƙa daga gadon .
Idanun sa ya mayar ya rufe yana sake riƙo ta da ɗan tsauri ya jawo ta ta dawo kan sa "gudun me kike yi bayan kin kwana kin hantse kina bacci mai daɗin da baki taɓa yin irin sa ba .
Ya furta hakan muryar sa a ƙasa sosai .
Yakaka cikin yanayi na tsoro tace "Yaya Dacta dan Allah ka kyale ni kar Auntie Sofi ta shigo ta gan ni .
Da sauri ya buɗe idanun sa jin abunda