Showing 234001 words to 237000 words out of 411050 words
Chapter 79 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
faɗi ba ? Zaki warke ko ba du ba , waye ya faɗi miki zata zam asara doumun nayi jinyar ki daga jakka ta ?
" kiyi ta addu'a Allah shi sa a cimma nasara bissa ga neman lafiyar ki kin ji kou ?
Shiru tayi , ita ganin zancen likitan take soki-burutsu tayaya idanun ta zasu fara gani ? Bayan a iya sanin ta bata taɓa ganin hasken duniya ba .
Muryar sa ta katse tunaninta "
Kou baki so watarana ki ga fuskar mijinki ? Kou baki so watarana ki ga fuskar ɗiyar ki Mama tare da 'ɗiyan da zaki haifa nan gaba ?
Jin ya sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi sai ta ɗago kanta , '
" inaso , amma nafi son na samu ɗa domin ya sadauƙar da ɓargon sa ga Mama , ta warke kamar yadda likita ya faɗa ,
Sai yayi shiru yana kallon ta da taimakon hasken da bai cika yawa ba da ya hasko daga jikin ƙwan fitilan dake ajiye saman teburin gaban su ,
zancen ta ya zo masa a bazata , ya ratsa ƙwaƙwalwar sa a jirkitatcen yanayi da ya kasa tantancewa .
Ita ma shiru tayi cike da fargabar kasassaɓar da tayi , kada dai tayi masa laifi ? Ko dai zantukanta basu dace ba ? Tayi masa tsaurin ido ko ?
Sauƙar hannun sa cikin nata ya katse mata tunanin zucin da take yi ,
"Fatima mu tafi muyi sallar isha'i kiyi kwana (bacci ) dare yayi ,"
A sanyaye ta amsa da "To,
Har suka kwanta bacci babu wanda ya kuma magana kowanne a tsakanin su yana tunani,
Wayar sa ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira , da azama ya ɗauka ganin wacce ke ƙiransa ya sanya shi miƙewa a hankali ya nufi ƙofar ɗakin , ya zo fita ya juya gami da kai kallon sa kanta da tayi lamo cikin bargo kamar mai bacci ,
ajiyar zuciya ya sauƙe ransa cike da tunaninnika barkatai ya fita gami da jaa musu ƙofar ,
Falmata wacce duk motsinsa a kunnen ta , ta miƙe zaune gami da yaye bargon , cikin ranta sam babu daɗi gani take kamar ta ɓata masa rai da maganganun ta tunda gashi daga lokacin bai sake cewa da ita kome ba , ko fushi yayi ?
Tashin muryar sa da yake magana kamar a gabanta "kasantuwar ta mai buɗaɗɗen kunne " ya sa ta saurarawa zagayayyar fuskarta na bayyana wani yanayi irin na wanda aka shammata lokacin da taji yana cewa ,
"bonjour ma princesse comment allez-vous aujourd'hui mon amour? ( Alo gimbiyata yaya kike yau masoyiya ? )
Cigaba yayi da cewa
"Je vais très bien et tu me manques aussi , ( ina lafiya lau nima nayi ƙewar ki )
Ƴar dariyar nishaɗi yayi , kana ya cigaba da cewa ,
" wannan kalma ke kin ka faɗe ta , ni kouwa gurina ba haka ne ba , duk wani bigeren da babu ke cikin sa wajena daɗin sa ragagge ne , babu kome anan sai matsanancin sanyi tafe da tarin nawi da wahalwalu bisa kaina ,
Murmushi yayi mai sauti ,
" a gida nake Yarima , ga gurin aikina kuma Mai muƙamin Major , nan kuwa ai ban wucce matsayin bawa dake hidima ga wassu rayukan ba ,
Gicciyewa yayi ya kishingiɗa yana me cigaba da sauraron ta ,
" ba domin yanayi da bashi yiwuwa na taho da ke ba, kin sani ban iya tafiya ga nissan duniya batare da ke gefena ba maimounatu ke ai sashi ce daga jikina ,
Falmata da take sauraran sa , sai ta koma ta kwanta tare da lulluɓuwa ta cure jikinta guri ɗaya ga barin sauraran zantukan sa , zuciyarta ke wani irin bugu da yake tafe da zallar tashin hankali ,
Sunan wacce aka ƙira da Maimounatu tare da irin Kalmomi masu daraja da aka mallaka mata , sun gaftare tare da ruguza duk wani ɗan guntun tunanin banza da ta fara yi ,"Ah to na banza mana , tunda 'yar kulawar da yake bata ya sa ta hasashen hawa wani matsayi da bata kai shi ba a wajen sa ashe ita ɗin ba kome bace face tarin nawi da wahalhalu .
Hawaye masu ɗumi suka gangaro daga idanunta suna ɗiga bisa hular sanyin kan Mama .
Maiduguri Nigeria
Tun ranar da Doctor Hamza ya gargaɗi Yakaka akan kada ya sake ganin fuskarta bata sake bari sun haɗu ba ,
Ko muryar sa ta ji yayi Sallama da shi bai cika shigowa ma sashin nasu ba , da sauri zata nemi gurin ɓuya , duk cewa tun daga ranar duk lokacin da ya buƙaci abinci daga Rahima ita take girka masa , sai ita kuma Rahima ta kai masa .
Yau Asabar ya shigo gidan da safe misalin ƙarfe tara shirye yake tsaf cikin shirin sa na zuwa ɗaurin auren ƙanin Abokin sa .
Yana yin Sallama , Yakaka da take goge Falon bayan ta gama sharewa tayi saurin ajiye moper ( mofi ) ta tsallaka da ɗan gudu ta shige ɗaki ta rufo ƙofar ,
Hajja da take zaune a gefe tana karin kumallo ta harari bayanta ta wutsiyar ido kafin ta taɓe baki ,
" Ni hauwa'u naga abunda yafi ƙarfi na , ke kenan kullum a tsalle-tsalle da guje-guje ? Uwa wata tunkiyar da take rawar turke ? Allah ya kyauta .
Washe baki tayi tana dariya ,lokacin da Doctor Hamza ya shigo
" a ah kaga manya ɗiban farko , Babban likita ,
Fuskar sa ɗauke da murmushi suka gaisa , ba tare da ya zauna ba yace
"Hajja ina Rahima ?
" Yanzu ta hau sama , a ƙira ta ne ?
" a ah yi zaman ki Hajja idan dai ta fito ace ta min girki kafin dawowata ta kai min ɗakina .
" To babu laifi zan faɗa mata .
" Nagode Hajja .
Ya juyawa da nufin fita idanun sa suka sauƙa kan Hoton Mama da tun ranar da ya fara ganin hoton yake son tambayar Rahima 'yar waye ? Ƙwarai hoton yarinyar yake fusgar hankalin sa ,
Dan haka ya dawo da baya yana tambayar Hajja ,
" Hajja wannan 'yar waye haka aka samu kyakkyawa ?
Da dariya Hajja ta amsa masa
" 'yar wajen Fatima ce , Mama sunan ta ai sun ma yi tafiya ne can Amurka ita da iyayen nata .
"Fatima ?
Ya maimaita ,
" wacce Fatima Hajja ?
" Ƙanwar wannan yarinyar Yakaka take ko wa ?
'okay ,
Ya amsa yana barin wajen ba domin ya gane wacce ake nufi ba kai tsaye sai dan ƙiran sunan Yakaka da Hajja tayi .
ƙarfe biyu na rana suka shirya tafiya gidan Amne su Uku Rahima , Yakaka da kuma Hajja da itama tace zata je .
Shatar shatar adai-daita Rahima ta ɗaukar musu wanda ya tokare daga bakin hanya yaƙi gangarawa kwarin unguwar a cewar sa gargadar cikin unguwar zai ɓata masa mashin , dan haka dolen su suka sauƙa Rahima tana ta mitar wahalar tafiyar da zasu yi a ƙafa kafin isar su gidan .
Da wani tasowar sabon yanayi a zuciyar Yakaka take bin unguwar da kallo , unguwar da ta zama tushe na hargitswar rayuwar ta da bata tsinci kome a ciki ba illa wahalhalu da tarin abubuwan ƙi , unguwar da suka sha gwagwarmaya a cikin ta ita da ƙanwar ta da ƙawarta Yagana ko ina yagana take a halin yanzu ? Wataƙila ita rayuwa tayi mata kyau , tayi aure ta fara ginin rayuwar 'ya'yan ta .
tunaninta ya katse lokacin da Rahima ke cewa su gangara ,
Tana bin layin tana tuno da haɗuwar su da Doctor Hamza a bakin layin ana ruwan sama ,taimakon da yayi mata a ranar da ba domin shi ba da ta faɗa babbar kwatar taji mummunan ciwo ko ma ta rasa ranta ,
"Allah sarki yaya dakta ,
Ta furta hakan daga ƙasan ranta lokacin da suke miƙawa cikin layin .
Daga nesa ta fara jiyo hargowar sa muryar sa a sama yana rantse-rantse , domin ta tabbatar da shi ɗin ne ? Tayi saurin ɗaga idonta ta ɗora a kan sa shi da wata matar da kallo guda tayi mata ta gane yanayinta na matan banza ,
Da sauri ta ɗauke kai tana ɗan jawo hijabinta gaba kaɗan , zuciyarta cike da fatan Allah ya rufe masa ido ya wuce bai ganta ba bare ya gane ta.
cikin rashin sa'a hasken da take da shi ya riga ya ɗau hankalinsa kasancewar sa kawali idanun sa koyaushe akan wankakkiyar mace yake babu ruwansa da matsayinta na matar aure ko akasinta .
Sun ƙaraso gaf da juna ya jaa ya tsaya , kafin ya ɗau salatin da Hajja ta ƙarasar masa ,
Sauri yayi ya zagaya ta sashin ta ya dogare , yana kallon fuskar ta da taƙi yadda su haɗa ido ,
Dariya ya kwashe da ita yana tafa hannuwan sa alamun mamaki yace ,
"Ahayye nanaye ke duniya mai abun mamaki ? Yanzu duniya da gaskiya Yaks kƴa ga Ɗanliti ki ɗauke ido ki kawar da kai ? Lalle Yaks kin zama kaza ci ki goge bakin ki , Ko da yake ai kome kika yi ba mamaki tunda baki da shayin kowa .
Yakaka ta saci kallon Hajja wacce tayi saƙare tana bin Ɗanliti da kallon banza ,
" Ɗan-Ɗan liti ya kake ?
" Ras nake Yaks .
Yayi fari da ido kafin ya ɗora da
"Ke kuma fa ? Ya na ganki haka da Bargo yaro-yaro kina yawo kadda dai kice min kin yi ƙarkon kifi , ? Kin fito daga ruwa kin faɗa wuta ? Yo ai kuwa da kin ɗibga asara a duniyar nan Yaks ace dai wai mace hamshaƙiya kamar ke kina yawo a ƙuɗunɗune cikin hirami yake ko hijabi ko jallabiya ? Bani sunan sa ɗaya .
" Ubanka yake nace Ubanka yake shashasha , wofin wofiyo banzan banza , yau ga ɗa ya zama lalatatce bayan an kashe ragon suna , to Allah ya shirye ka , ke un-un Yakaka wuce muje .
Hajja ta furta hakan tana huci tare da yiwa ɗanliti daƙuwa da hannuwanta duk biyu , ta ƙarasa zancen da fusgar hannun Yakaka ,
Buɗe baki Ɗanliti yayi da mamaki ,
," Ke tsohuwa , ki kiyayeni ki kiyayen nace da zaki zo ki shiga cikin maganata dake nake ? Nace da ke nake ? Yo Allah na tuba ke a zamanin ki waye ya san irin tsiyar da kika shuka ta rawar banjo da kiɗan gurmi daga ke sai ɗan kanfai ? Ko da yake wannan baƙin naki uwa shuni ba wani tasiri kika yi ba ko a wajen su garbati mai kalangu . ,
",Na rantse kin ci darajar yaks domin ni na falle tsohuwa da marin da zai sa ta ga star abune mai sauƙi a wajena , gaba ki kiyaye kin ji na gaya miki .
tsaki Hajja tayi suna barin wajen ,
" Allah ya shirya ka zindiƙi .
Shima ya rama Hararar da tayi masa ,
" waye yake ta taki tsohuwar guzuma , Yaks Ki samu lokaci ki leƙo mu akwai labarai da hanyoyin arziki masu tarin yawa , af na manta na faɗa miki uwarɗakin fa bata da lafiya...
Bai ƙarasa zance ba yayi shiru ganin sunyi nisa ,
" ji min tsohuwar nan zata yaɓan magana wai nine zindiƙi ? Tsohon ki ne dai zindiƙi aikin banza .
****
Da sallama suka shiga gidan Amne , tana zaune kan barandar ta tana ƙunsa lalle a ƙafafunta da basa rabuwa da ƙunshi ,
Tayi mamakin ganin su saboda Rahima bata sanar da ita zuwan nasu ba ,
ta tare su da fara'a tana yiwa baƙi barka da zuwa , idanunta da hankalinta baki ɗaya akan yakaka .
Bayan sun gaisa ta dubi Rahima ,
" aina kika sake samo min mai kama da Rahima ta ? Da ace shekaru basu jaa dayawa ba zan iya cewa Rahima ta ce wannan ,
" dariya Rahima tayi , Amne baki gane ta ba ko ? Yakaka ce fa , 'yar gudun hijarar da suka zauna a gidan mu shekarun baya da akayi zaton ta rasu wajen haihuwa ?
duk da ba wani jimawa tayi da yaran ba amma sunan su ya tsaya a ƙwaƙwalwar ta ,
" Yakaka ke ce ?
" ni ce Amne ,
" Alhamdulillah ashe Yakaka kina raye ? Ina kika tsaya tsawon lokacin nan ? Ina ƙanwar ki tare da 'yar ki ?
hannun ta ta ɗora akan na Amne da ta miƙo mata su , fuskar ta ɗauke da murmushin jin daɗin zallar ƙaunar da ta hango a idanun Amne ta matso kusa da ita ,
"Falmata su na America wai .
Hajja tace ,
" Wai ne ma ? ai ya wuce wai .,
Amne bata tsananta tambayoyi ba ga Yakakar domin ta bata damar sakewa ,
Lallen da Amne take sawa ta karɓa , tare da cewa
" kawo na sa miki Amne .
tana murmushi ta miƙa mata 'yar robar da lallen ke ciki , ta shiga sanya mata sannu kan hankali ,
da sauri Rahima tace
"Daman kin iya lalle ne Yakaka ?
tana murmushi tace ,
" ko ban iya ba zan koya a ƙafar Amne .
Hajja da Amne suka cigaba da hirar su ,
zuwa lokacin da Rahima tace ,
" Yauwa Amne ki nunawa Yakaka Hoton Khaalty Rahima da kike cewa suna kama Yakaka tana son ganin ta...
"eh Amne ina son ganin Khaalty Rahima , Yakaka ta furta hakan cike da ɗoki ..
Assalamu Alaikum masu karatu maza da mta , ina miƙo sakon gaisuwa ta tare da fatan alheri , ɗauke da yabawa bisa ga yadda kuke bin littafin nan cike da bani ƙwarin guiwa nagode ƙwarai da gaske Allah ya bar so da ƙauna ( sunan wani littafi 😂 ) sharhin ku a fejin da ya gabata ya min daɗi matuƙa da fatan za'a ɗore da haka ? .
Ghost readers muna nan da ku , za'a ji kan mu watarana .
😡
Nagode .
[11/14, 11:01 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
37
Cike da zumuɗi Yakaka ta karɓi wani ƙaramin envelop ɗin da Rahima ta ɗauko mata daga ɗaki tana cewa
" Yakaka ga hoton Khaaltƴ Rahima duba ki gani, ita ce takwarata ai ina kama da ita ko ? .
Da murmushi bayyane kan fuskar ta , ta zaro hoton bayan ta goge hannun ta da yake da ɗan danshin ruwan ƙunshi .
Ƴar ƙaramar budurwa ce a jikin hoton na farko da baza ta wuce shekaru sha huɗu zuwa sha biyar ba , fara ƙal tamkar baturiya , ƙibabbiya 'yar dumur-mur jikinta sanye da doguwar rigar iya ƙwauri mai guntun hannu irin shigar su ta shuwa ,kanta ba ɗankwali sai manyan kitson guru da aka mata gwammon sa a ƙeya ,
" wai Masha Allah Rahima mai sunanki ta fiki kyau gaskiya ,
Ta furta tana 'yar dariya kafin ta zame hoton na bayan sa ya bayyana da bai kai wancen a tsufa ba domin a wannan ta ƙara girma ta zama budurwa da a lokacin zata iya kaiwa shekaru sha bakwai , da alama a makaranta ta ɗau hoton ganin jikinta sanye da uniform ,
Tsam , tayi tana ƙurewa cikakkiyar fuskar ta kallo da take dariya , tamkar dai tana rikiɗe mata zuwa fuskar da tayiwa sani na haƙiƙa ,
"fuskar wa ?
Ta tambayi kan ta da kan ta .
"Fuskar maman mu ," babu shakka dariyar ta da zubin haƙoranta irin na maman mu ne , sai dai maman mu bata da jiki da kyaun wannan mai kama da turawan,
Tunanin ta ya katse lokacin da ta tsinkayi muryar Amne wacce ita ma ta kafe ta da ido tana nazarin yanayin da take hangowa a tare da ita ,
" Yakaka ko kin san ƙanwata Rahima a wani waje ne ?
Kallon Amne tayi kamar zata ce wani abu sai kuma tayi ɗan yaƙe , tare da girgiza kanta lokacin da take ƙoƙarin mayar da hotunan cikin gidan su ,
" A ah Ban san ta ba Amne ,"
"Allah sarki , Rahima kenan ƙanwata da muke uwa ɗaya uba ɗaya jal a duniya , Yaa Allah ka san halin da na wanzu cikin sa tsawon shekarun nan akan rashin Rahima , Allah ka dawo min da Rahimatullah , ka sa muna da rabon sake ganawa a duniya .
"Amin Amne ,
suka amsa mata su duka fuskokin su na bayyana alhini , musamman Yakaka wacce ta shiga wani irin hali na ruɗani da ganin hoton khaalty Rahima ya jaza mata .
Ƙwarai fuskar ta tsaya mata a zuci da cikin tunaninta , Babu wadatar nutsuwa na sosai a tare da ita suka ƙarasa yinin su zuwa gefen La'asar suka kama hanyar komawa gida ,
Rahima ta dubi Yakaka bayan mai adai-daita ya sauƙe su a daf da ƙofar gida ,
"Yakaka ya naga duk kin yi wani iri , akwai damuwa ne ? Kafin mu fita a gida ba haka kike ba ,
Kafin Yakaka ta amsa Hajja tayi charaf ta amshe zance ,
"Ahaf zai wuce batun wannan ɗan banzan , ɗan hamsin yake ko ɗan daudu ? Idan har kika ce ƴar huɗubar wofin nan da ya wassafa miki zaki ɗauka ki aza a rai to kuwa kin kama kumfar teku , domin wannan da kike ganin sa rabon sa da alasambarka tun kwanansa bakwai ran suna , babu Alheri a tare da shi ko na aninin kobo atoh .
A ɗan kaikaice Yakaka ta dubi Hajja zata yi magana , aka buɗo babbar ƙofar gidan , Doctor Hamza ya turo kan motar sa , kallo guda ya yiwa gefen da Yakaka take ya ɗauke kan sa ,
Da sauri Yakaka ta wuce tana gyara zaman hijabinta , ta bar Rahima da Hajja suna gaisawa da shi , inda yake tambayar su daga ina suke ??
Suka sanar da shi daga gidan Amne suke , sosai ya ji daɗi tare da tambayar su yadda suka baro ta ? Suka amsa masa da tana lafiya ƙalau