Showing 240001 words to 243000 words out of 411050 words

Chapter 81 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

20128

,

Ya ɗan ɗaga sauti yana murza yatsun ta dake cikin hannun sa ,

" Fatima ki nutsu nace zan faɗa miki watarana a gaba ,

Warce hannunta tayi da ƙarfi daga cikin nasa ta matsa daga kusa da shi cikin ɗaga sauti ita ma ta ce masa

" Ba gaskiya bane muddin baka faɗa min yadda kuka yi aure da Yakaka ba kai ba kaine Baban Mama ba ƙarya kake min ,

  Tsawar da ya daka mata tare da buga teburin gaban su shi yasa Mama fashewa da kuka da gudu tayi jikin Falmata ,
   wannan karon ya kaurara murya da wani irin amo da bata taɓa jin sa da irin ta ba cikin sigar gargaɗi yace mata ,

  " Fatima ki min shiru , ki min shiru nace kar ki sake cewa ƙala ,

Fuskar sa tayi jazir , jijiyoyin kansa sun fito ruɗu-rudu , baki ɗayan jikin sa yana rawa , ɓacin rai sosai ya sauƙo masa , zafin zuciyar sa irin ta soji ta hayyaƙo ,

A zabari ya miƙe ya shiga ɗaki , yayi tsaye hannun sa a dunƙule , ya rasa me yake yi masa daɗi wani irin ɓacin rai me tafe da tsoro-tsoro da a lokacin ya rasa tsoron meye ? Shine yake cin sa ,

Jibgegiyar rigar sanyin sa iya guiwa dake ajiye a gefen gado ya ɗauka ya rufa akan kayan sanyin da daman suke jikin sa ya fito daga ɗakin ,

Satar kallon inda suke yayi ya ga Falmatan tayi baya da kanta ta kwantar akan kujerar Mama kuma tana maƙale a jikinta tana kallon sa da raunanan idanun ta ,

Tausayin 'yar sa ya kawo masa , da hannu ya yafice ta , da sauri ta sauƙa tayi wajen sa ,

Ɗaukar ta yayi ya koma cikin ɗakin ita ma ya ƙara mata rigar sanyi tare da sauya mata hular da tafi ta kan ta nawi ya sungume ta suka fito falon ba tare da ya dubi sashin da Falmata take ba ya nufi ƙofar fita ,

Mama da idanun ta ke kan Mamar ta cikin siririyar Muryar ta tace

"Papa ma....

'shit

Yace mata yana ɗora yatsan sa manuni akan bakin ta , shiru tayi tana kallon sa suka ƙarasa ficewa daga gidan ya ja ƙofar

Ƙarar rufuwar ƙofar ya zo tare da zubowar kauraran hawayen ta , da duk motsin su daman yana kunnen ta ,

Kuka ta fashe da shi mai sauti tare da jin wani sabon tashin hankali har ta rasa takamaimai da wanne zata ji ?

Shin laifi ne dan ta tambaye shi game da yayar ta ? A sautin sa ta tsinkayo tashin hankalin da yake tafe da rashin gaskiya shin meye yake boye mata bayan wanda a yau ya bayyana mata da ta haƙiƙance ta kuma yarda ɗari cikin ɗari gaskiyar sa ya feɗe mata da ita kuma ganin wannan damar ne ya sa tayi amfani da ita wajen shigo masa da tambayar da ta kwashi shekaru tana cinta a rai ,

" Yaushe suka yi aure shi da Yakaka alhalin ita bata san lokacin ba ??

Tana share hawaye wasu na zubowa ,

"Wai ashe daman har yana da mata biyu ita bata sani ba ?ashe mijin su ne su uku ? Tausayin kanta ta ji ya kawo mata , tabbas ita ba kome bace a wajen sa face wacce ya taimaka ya aure ta sanadin 'yar yayar ta , ba kuma zata taɓa zama kome a wajen sa  ba ,

'idan kuwa haka ne dole tayi haƙuri ta haɗiye kome ta kuma bar kome domin ta cigaba da zama a ƙarƙashin sa tare da Mama , a zahiri yake ai shi yafi ƙarfin auren ta , wacece ita ? Miskiniyar ɗiyar talakawa 'yar gudun hijira ? Babu shakka bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane ,

Ya zama dole ta bashi haƙuri idan ya dawo ta kuma alƙawarta cikin ran ta baza ta sake yi masa batun Yakaka ba .

Ta ɗau lokaci a haka cikin kukan zuci da damuwa , kafin ta kintata tayi sallar la'asar da take da tabbacin lokacin ta ya shigo ,

A ƙasa inda tayi sallar ta cigaba da zama tunaninnika sun mata yawa , ta ƙagauta ƙwarai ta ji motsin shigowar sa ta bashi haƙuri ,

Daƙiƙoki suka dunga hanzarin wucewa suna zama mintoci har suka ɗebi awannin da Falmata ta ji su tamkar sati guda tayi tayi a zaune ,

Ta tashi ta tsaya yafi a ƙirga ta matsa jikin ƙofa ta laluba , ta kasa kunne ko zata ji motsin su , har dai ta tabbatar sun yi nisa da ita sosai ,

Wani irin mummunan tashin hankali ne ya dirar mata sakamakon tunanin da ya gitta ƙwaƙwalwar ta kan cewa ya ɗauke ɗiyar sa sun tafi sun bar mata gidan , ya sauya muhalli sun yi nesa da ita har abada , ya tafi ya bar ta a uwa duniya ƙasar da bata san kowa ba ko yaren su bata ji ,

Wannan karon kukan da ta fashe da shi tafe yake da amon matsanancin tsoro da ruɗewa ,

Da gudu ta taka tayi nufin fita sai dai karon da ta ci da kujera yasa tayi baya  cikin sa'a ta zauna daɓas akan kujerar kusa da ita ,

Ta sake ajiye hannu da zummar miƙewa hannunta taji ya sauƙa akan sandar ta , cikin sauri ta laluba ta ɗau sandar , ta kama hanya fita daga gidan tare da taimakon sandar hannunta,

Bata damu da ta sake ɗora wata rigar sanyi ba illa ta jikinta da take iya guiwar ta sai kuma siririn siket da hular sanyi a kanta ta fice a gidan ba tare da ta san ina ta dosa ba ,

Tsananin sanyin da ya ratsa ƙasusuwan ta lokacin da ta fito waje bai sa ba ta koma illa tafiya da ta cigaba da yi tana laluben hanya da sanda ,

Unguwar da suke shal babu kowa sai tsilla-tsilla motoci ke wucewa haske ya wadaci ko'ina da taimakon fitulun gefen hanya duk kuwa da duhun dare da ya fara mamayar sararin sama.

Tayi tafiya mai nisa lokacin da tsoro ya gama cin galaba akan ta nadamar fitowar ta ya ziyarce ta ,

Matsanancin sanyin da ya fara cin ƙarfin ta sakamakon dusar ƙanƙarar da ya fara sauƙa ya sa ta gaza ci gaba da tafiya gaba ɗaya ji take kamar jinin jikinta ya daskare ,

Durƙushewa tayi a wajen da bata da masaniyar ina ne ?tana jin yadda sanyin wajen da ta zauna yake ratso jikin kayanta yana daskarar da duk wani ruwa na jikinta ,

Idanunta da hancinta suna tsiyaya ta dunƙule jikinta waje guda tana karkarwa ,

A cikin ran ta ta haƙiƙance rayuwar ta  ta zo gangara , ashe ita kuma irin tata sanadin mutuwar kenan sanyi  ?

****

Biyamuradi Youssouf tunda ya fita saɓe da Mama , yayi ɗan tattaki cike da rashin sani takamaimai ina zasu ??

Ya zaɓi ya fita ne saboda yana da yaƙini zuciyar sa ba zata jure ganin fushin ta ba , da shi kuma a wannan gaɓar bai yarda yayi wani yunƙurin ds zsi fallasa halin da zuciyar sa ke ciki ba a kan ta bai so ta gano lagon sa tunda wuri haka ,

Cigaba yayi da tafiya har ya cimma babban titi , nan ya hango wani shagon sayar da coffee ,

Bayan ya ƙarba musu coffee me zafi ya zaunar da Mama a kujerar da ke fuskantar ta shi ,

Juya ɗan chokalin hannun sa yake yi ya gagara shan coffee ɗin , damuwa tayi masa ƙawanya duk wata walwalarsa ta kau ,

Ko kusa ba zai iya duban ta ya fayyace mata lamuran da suka auku tsakanin sa da 'yar uwar ta ba , yana jin kunya , yana kuma tsoro .

Meyasa ta kasa fahimtar barin abunda ya riga ya wuce a muhallin shuɗaɗɗan lamari shi yafi alheri fiye da tone-tone . ?

Duban sa ya kai ga Mama wacce tayi shiru ta lanƙwasa kai fuskar ta bayyane da damuwa ,

Tausayin ta ya ji domin ya san damuwar ta ta samo asali ne ga abunda ya faru tsakanin sa da Falmata , da shima zuwa yanzu nadamar ihun da yayi mata yake yi ,

Bai yi hakan da wata manufa ba illa ruɗanin da ya tsinci kan sa a ciki da ya sa bashi da wata hanyar daƙile yunƙurin ta tare da kawo ƙarshen maganar idan ba ta hakan ba .

Tashi yayi ya zagaya ya ɗauki Mama suka fito daga Coffee Home ɗin ba tare da ya sha coffee da ya saya ba ,

Sake nusawa yayi bakin titi yana tafe sannu kan hankali har ya tadda ɗan wani killacaccen wajen yin sallah , nan yayi sallar la'asar tare da Mama a gefen sa  ,

Bayan ya idar hankalin sa ya kai kan wani fili gaban wasu gidaje da matasa da yara suka taru suna wasan ƴar zamiya akan dusar ƙanƙara Tobogganing , kama hannun Mama yayi suka ƙarasa wajen ,

Ya zauna daga gefe kan kujerar gefen hanya tare da ɗaura Mama a cinyar sa ,

Sosai wasan ya ɗau hankalin Mama ganin yara ƙanana sa'o'in ta nata faɗuwa da tashi cikin dusar ƙanƙara , nan take ta shagala da kallon su har tana taya su dariya idan wasun su sun faɗi ,

Ganin walwalar Mama ya bashi damar zurfafa a tunani , sashi guda na ran sa na shawartar sa akan idan ya koma gida ya faɗa mata gaskiya ksn abunda take son sani , yayin da sashi mafi rinjaye ke ƙwabar sa tare da tsoratar da shi abunda faɗa mata gaskiyar zai iya haifarwa ,

Abunda ya haƙiƙancewa ba zai iya jurar fushin ta da damuwar ta ba domin kusa take sosai da ruhin sa ,

Bai ankara ba har duhun dare ya fara shigowa , dan haka ya sake komawa wajen da yayi sallah , ya sallaci Magarib  , 

Yana idarwa ya kamo hanyar gida bayan ya saɓa Mama a bayan sa da tayi laushi tuɓus ,

Ta gaban manyan shagunan sayar da kayan ƙele-ƙele na mata ya zo wucewa , idanun sa suka kai kan wata 'yar kyakkyawar sarƙa da take ɗaukar ido tare da taimakon hasken lantarki da ya haske cikin gilashin da sarƙar take .

Murmushi yayi lokacin da idanun sa suka hasko masa sarƙar a cikakken wuyan Falmata ,

Da hanzari ya shiga shagon ya sayi  sarƙar da take ta farin zinare ƙirar ƙasar Amurka suka zare kuɗin su ta katin sa tare da zura masa akwatin sarkar cikin 'yar jakar da take ɗauke da tambarin Manns jewelry .

Cike da fargaban halin da zai riske ta ciki ya nufo gidan , zuciyar sa na aiyana masa wataƙila tayi ta kuka ,?wataƙila kuma ran ta ya sake ɓaci da shi, koma menene zai bata haƙuri ys rarrashe ta ta bar maganar nan ,

Da Sallama ya tura ƙofar gidan ya shiga ,

Shiru ya ji bata amsa ba ,

Ya lalubi wutar falon ya kunna ,

Idanun sa akan ɗan wajen kunna witar ɗumama ɗakin da har wutar ta mutu , hakan ya sa ɗakin ya ɗau sanyi

cikin ran sa babu daɗi  , Ya zaunar da Mama akan kujera , yayi tsaye yana saƙe-saƙe , jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi da barin ta da yayi ita ɗaya ,

Takawa yayi ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin ya ɗan ƙwanƙwasa ,

" Fatima , mun dawo

Ya furta haka da sauƙaƙar murya ,

Shiru ya sake ji babu alamun motsi ,

Sai ya murɗa hannun ƙofar ya shiga ɗakin , cikin 'yan daƙiƙai ya fahimci bata ɗakin , da sauri juyo , kai tsaye ya leƙa cikin ɗaya ɗakin , babu alamarta

Tamkar an safure shi haka ya dunga bin kowanne lungu da saƙo na gidan yana neman ta tare da ƙira sunan ta ,

A ƙarshe ya hiƙanƙancewa kansa tabbas bata gidan , ta fita ne ? Ko an sace ta ? Shikenan shi kam ya shiga ukun sa , ta shi kuma ta same shi .

Da gudu ya sunkuci Mama ya fito , dusar ƙanƙara na sauƙa a kan su yayi tirus a harabar wajen , ina zai fara nufa neman ta ? Wa zai dosa ya tambaya akan ta ?

Gidan da yake maƙwaftan na su ya nufa da sauri ya danna musu ƙararawar neman iznin shiga gidan ,

Zuciyar sa na ayyana masa wataƙila ta shiga gidan ,

Tunanin sa ya katse lokacin da aka buɗo ƙofar wani mutum magidanci yayi tsaye yana kallon sa ,

Da harshen turanci ya gabatar masa da kan sa a gurguje kafin ya ɗora masa tambaya kan ko matar sa ta shigo gidan su ?

Da harshen larabci mutumin ya miƙa tambayar ga matarsa da take daga bayansa a tsaye ,

Nan suka tabbatar masa da babu wacce ta shigo musu ,

Har ya juya sai kuma ya dawo ,

Rokon su yayi akan su taimaka su riƙe masa 'yar sa zai je neman matar sa ,

Basu musa ba suka karɓi Mama da tayi rau-rau da ido tana shirin kuka ganin Babanta zai tafi ya bar ta hannun waɗanda bata kai ga sanin su ba ,

Bai kula ba ya juya da sassarfa mai haɗe da gudu ya kama doguwar hanyar da tayi cikin unguwar sosai yana tafe yana dube-dube da waige-waige , hankalinsa yayi ƙololuwar tashi , maƙogoran sa ya bushe , idanun sa har raɗaɗi suke yi masa ,

"Yaa Allah Fatima ina kike ? Yaya za ki min hakka Fatima , ? Meyasa kika fita ?

Ya furta hakan muryarsa na karkarwa , bayan hannun sa ya sa ya goge fuskar sa da iskar dusar ƙanƙara ta watso masa ,

Ganin har ya kusan ƙure unguwar bai gan ta ba ya sa shi komowa baya , yana cigaba da neman ta , addu'o'i iri-iri yake yi ,

Zai iya cewa tunda yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na tsuƙin lokacin nan ba , bai taɓa sanin ita wata kadara ce mai maɗaukakiyar daraja a wajen sa ba sai a wannan gaɓar da yake gaf da rasa ta ,

bazai yafewa mummunar zuciyar sa ba idan har wani abun cutarwa ya same ta ,

Sakin hanya yayi ya nufi wata doguwar hanyar da tayi gefe a tsakankanin dusar ƙanƙara

Fatima , Fatima , Fatima

Yake ƙwala ƙiran sunan ta ,

Ya ƙure hanyar bai ko ga alamun sawun ta ba sai zunzurutun sanyin a yake ratsa sa ,

Dawowa yayi da baya ya sake kama wata hanyar ta daban nan ma yana tafe yana kiran sunan ta ,

Durƙushewa yayi a gefen hanya yana jin tamkar ya ƙwala ihu ko ya ji sauƙin tashin hankalin da yake ciki ,

Kamar a sama ya fara jin amon Murya ta daga nesa , tana ƙiran sa

Da gudu ya nufi inda yake jin tashin sautin ta ,

A gefen hanya zaune cikin dusar ƙanƙara ya hango ta ,

Hannuwan sa duk biyu ya sa ya ɗago ta , ya riƙo kumatun ta dama da hagu ,

"Fatima meyasa kika fito ? Ina za ki je ?  Fatima kar ki sake tafiya ki bar mu .

Ta kifta idanun ta da suka bushe ƙemas saboda sanyi tace ,

"Baban Mama ku na fito nema , dan Allah kayi haƙuri kar ka sake tafiya ka bar ni , bazan sake yi ma laifi ba ,

Kamota yayi suka miƙe tsaye , yadda take rawar sanyi ya tashi hankalin sa , "

Juyawa yayi yayi durƙuso

"Fatima kama ni hau bissa bayana mu je gida ,

Duk da wahalar da take ciki , noƙewa tayi , muryar ta na rawar sanyi tace ,

"Baban Mama zan iya tafiya da kaina mu taf....

Bata ƙarasa zancen ba ta ji ya ɗaga ta ciɗak , ya ɗauketa , da sauri ta riƙo rigar sa , ya nufi gida da ita .

Duk da tafiyar akwai tazara amma bai gajiya ba ko dan kasancewar sa ingarman sadaukin soja ne ?

Yana ajiyeta akan kujerar falon su ya shiga haɗa wuta ,

Muryar ta can ƙasa tace masa ,

"ina Mama ,

" zan ɗauko ta tana gidan daura da mu ,
    yace

Da sauri ya dawo ya zauna a gefenta ya shiga zare mata safar ƙafafunta da suka ɗau sanyi , ya zarce da cire mata hular sanyin kan ta ,

ɗaki ya shiga ya ɗauko ƙaton bargo ya rufa mata har kan ta

Ya kamo ta ya dawo da ita gaban wutar sosai ,

Hannuwan sa biyu ya shiga karawa a gaban wutar su ɗau zafi sosai sai ya cire ya sa mata a ƙafafunta ,

A karo na biyu ta sake cewa ,

"Baban Mama , Mama tana waje ko ? Kar sanyi ya tada hargitsin ciwon ta ,

Da ido yake bin kyakkyawar fuskar ta da kallo , yadda fuskar ta ke da kyau haka ma zuciyar ta , ya aina hakan cikin ran sa , duk laifin da yayi mata , duk wahalar da ta sha a sanadin sa , ita ta lafiyar 'yar sa take ,

"bari na ɗauko ta , ya miƙe

Har ya kai bakin ƙofa , ya waigo

"Fatima kadda ki matsa dagga gaban wuta ,

Bai jira amsar ta ba ya fita da sauri , ya shiga ya ɗauko Mama wacce har tayi bacci ,

Godiya sosai ya yiwa maƙotan sa da suke musulman larabawa ,

Kai tsaye ya wuce da Mama Kan shinfiɗar ta ya ƙwantar da ita a ɗaki tare da haɗa wuta a cikin ɗakin ,

Inda ya barta nan ya dawo ya tadda ta kamar yadda ya umarceta bata motsa ba , kamar yadda bata daina rawar sanyi ba

"Zanyi Sallah tace da shi ,

Bayan ta idar da magarib ya ja su isha'i ,

Da suka idar kai tsaye ya nufi shayi me zafi ya haɗo mata ,

Da chokali ya ɗan sisita shi ya shiga bata a baki tana kurɓa kadan-kaɗan , yadda take rawar sanyi yana damun sa dan haka ya ajiye kofin hannun sa ,

ya kusanto da ita sosai cikin jikin sa , bayan ya rage kayan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login