Showing 117001 words to 120000 words out of 411050 words
Chapter 40 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ya gwada su domin gujewa kuskure ,"
Da rahima ya haɗa su yace su shiga a gwada su , ya kuma faɗa musu ranar da za'a zo ɗaukar ɗinki saboda ya riga ya biya sa kuɗin ɗinkin baki ɗaya ! Har sun fara taku ya kira ta
Rahima ki sake jaddadawa tailor kar fa yayi musu ƙaramin ɗinki , ita babbar ma kawai duk yayi mata dogayen riguna buɗaɗɗu ,"
Toh ! ta amsa masa
Ba'a ɗauki lokaci ba suka fito daga shagon , rahima sai faman dariya take tana tsokanar falmata ,"
Fatima da kuɗi goggagun mata suke zuwa a maida musu fasalin jikin su irin naki , kin gan ki kuwa kamar wata "Kim Kardashian "ta ƙarasa zancen da dariya ,'
Da murmushi akan fuskar su suka haɗa baki wurin tambayar ta wacece kuma , "kimkadarshia"???
Wata celeb ce
Ta amsa musu Tana ƙara ƙarfin dariyar ta jin yadda suka kira sunan a hargitse,"
Yana daga cikin motar yake hango fararen haƙoran ta tana darawa , tsawon ta da takun kafar ta yana daga cikin abun da yake daɗa jaan hankalin sa akan ta , duk da cewa yanzu da cikin ya shige watan sa na biyar ya fara bayyanuwa da ya sa tafiyar ta ta tafara sauyawa zuwa irin ta mata masu ciki ,
Shima tsintar kan sa yayi yana mai murmusawa a saboda ganin fara'ar ta , ƙwarai ya fuskance ta ita ma'abociyar murmushi da haƙora ce , kusan koyaushe fuskar ta da haskakken murmushi ƙwarsi ta dace da sunan da zuciyar sa ta raɗa mata watau nurii .
Daga nan hanyar gida ya ɗauka , suna isa suka fiffito daga motar , inda yakaka take bin illahirin gidan da kallon baƙunta ,
Ku zo muje ku fara gaishe da Baban mu ,
Suka tsinakayi muryar sa bayan ya kulle motar "
Shi ya shige gaba suka doshi kyakkyawan ginin da yake tsaye a saitin su , a bakin kofar ya ce su tsaya ya shiga ya sanar da shi tukun ,"
Nan suka tsaya duk su ukun har da rahima ,"
Bai jima ba yayi musu iznin su shigo yana daga ciki,'
Tsayawa suka yi daga baya har sai da rahima ta fara shiga sannan suka bi bayan ta hannuwan su a sarƙe ,"
Babban falo ne tafkeke , dan haka suna shiga taku biyu suka yi yakaka ta ɗurƙusa bisa kafet ɗin da yake malale a ɗakin tana mai fuskantar sa fahimtar hakan da falmata tayi ya sa ita ma ta zube guiwar ta a ƙasa , suna masu gaishe shi ,"
Da murmushi a fuskar sa yace
Ku shigo , ku shigo , kar ku tsaya daga chan ku zo daga nan , " ya musu nuni da kusa da shi a ƙasa inda rahima ta zauna ,"
Tasowa suka yi suka dawo inda ya nuna musu ," sannan suka sake gaishe sa kan su a sunkuye ,"
Ya amsa musu fuskar sa a sake yana mai musu kallon tsanaki ,"
Daga wanne gari kuke ? Ya tambaye su ,"
Mairambiri ," yakaka ta amsa masa ,
Mairambiri , ya maimaita tamkar yana nazarin sunan ,!
Ina iyayen ku ?
Nan yakaka ta bashi takaitatcen tarihin rayuwar su ,"
Ya tausaya musu sosai ,"
A ƙarshe yace su saki jikin su , insha Allah zai kula da rayuwar su gwargwadon ikon da Allah ya bashi , muddin suka tsaya akan gaskiya ɗa ai na kowa ne ,!
Daga haka ya basu umarnin tafiya !
Ɗakin da yake gefen na rahima wanda a da yake rufe babu kome cikin sa sai shimfiɗar kafet , nan doctor hamza ya gyara musu , aka sa musu labule da katifu madaidaita biyu , sai ƙaton wardrobe mai kofa shidda , sai fanka da bulb, akwai banɗaki a ciki , babu laifi ɗakin yayi kyau musamman a wurin su yakaka da basu taɓa shiga ɗakin da ya kai haka sun kwana ba tun da suke , dan haka su yau ran su fes zasu yi kwanan ƙarƙashin fanka bisa lallausar sabuwar katifar da ta ji sababbin shimfiɗu har da tausasan matasai ,!
Biyamuradi youssouf ne a tsaye kan ɗan wani dutse , waya ce a hannun sa yana ta faman neman layin hajiya umma fiye da mintoci ashirin amma ya gagara samun ta , yau kwanaki biyu kenan rabon da su gaisa da gida , ya san duk inda take yanzu hankalin ta yana gare shi ,
Duk da ta san cewa a yanayin aikin su akwai haka , wani lokaci su kan rasa samun layin wayar sa muddin anka tura shi wurin da yake da matsalar hanyoyin sadarwa , kamar dai yadda ya fatu a yanzu , wajen da aka matso da su sam babu kyaun hanyar sadarwa , saboda ya sake nesa sosai da cikin gari , cikin surƙuƙin daji ne da yake gaf da bakin bodar da ta raba tsakanin niger da nigeria , babu mahalukin da ya isa ya san da mutane a gurin sai fa jami'an tsaro ƴan uwan su ,"
Motsin da yaji daga ƙasan ɗan dutsen da yake tsaye bisan sa wanda ruwa yake ɓulɓula ta tsakanin sa ya sanya shi ɗan rankwafawa ya leƙa ,zuwa ɗan kwarin da ruwan ke bi , da yake lulluɓe da bishiyoyi da Koren tsirrai shar ,
nan ya hango wata barewa tana tsaye akan ƴar ta wacce alamu ya nuna yanzu ta haife ta , domin sai faman lashe ƴar take tana ƙoƙarin ɗago ta ta tsaya bisa kafafun ta ,
Mafarkin da yake yi a jere kwanaki biyu mai yanayin kama da halin da yaga barewar nan ciki shine ya dawo cikin tunanin sa ,"
Kwanaki biyu kenan a jere yake mafarki da wata barewa tare da ƙaramar ƴar ta , maharba sun biyo su , sai faman gudu suke a sanadin haka ya sa uwar ta faɗa a rami ƴar kuma ta wuce da matsanancin gudun da ya wuce na ƴar jaririyar barewa kamar ta ," gaban sa ƴar kyakyawar barewar take zuwa ta tsaya , shi kuma ya sunkuya ya ɗauke ta zuwa jikin sa tare da juyawa ya fara gudu da ita maharban na sake bin sa a ƙokarin su na son ganin sun karɓe ƴar barewar daga hannun sa ,' !
Tsumu yayi ya tsirawa barewar idanu ," yana son samun fassarar mafarkin sa ,
Ƙarar wayar sa ita ta jaa hankalin sa ga barin kallon barewar ya maida duban sa ga fuskar wayar da fatan ganin ƙiran daga hajiya umma ne ,"
Sunan tafeeda ne ke yawo bisa fuskar wayar , da ƴar fara'a bisa fuskar sa ya kara wayar a kunnen sa
Gaisuwa suka yi irin ta aminan junan da suke tsantsar ƙaunar junan su , daga nan suka ɗora hirar su akan lamuran da suka shafi aikin su ,"
Biyamuradi youssouf ke tambayar tafeedah , yaya yaga number sa ta nijer ce maimakon ta sudan ?saboda shi ma watanni biyu da suka wuce an tura su sudan akan aiki ,"
Ya bashi amsa da cewar ya gama satittikan da aka tura sa ya yi , har wani ya amshi bakin aikin sa ,"
Nan Biyamuradi youssouf ya tambayi lafiyar mutanen fada baki ɗaya a ƙarshe ya nemi da tafeedah ya haɗa shi da hajiya umma su gaisa idan ya shiga gidan saboda ya gagara samun ta a waya kwana biyu ,"
Ya ce masa shi ma tun jiya yake gwada layukan na youssouf dakyar ya samu nasarar samun sa a yanzu ,
Nan suka tsaya akan zai tafi fada ya kira shi ya haɗa su da hajiya umma , idan kuma har bai same shi ba zai isar da saƙon gaisuwar sa gare ta tare da mai martaba baki ɗaƴa ,"
Har sun yi sallama ya sake tsinkayo muryar tafeedah inda yake cewa ,"
Da farko nayi niyyar nai maka bazzata tou amma na gaza hakurewa , watanni biyu masu zouwa , zan shigo nigeria bikin iliyas wanda za'a yi cikin babban birnin nigeria abuja ,"
Da murna youssof yake bayyana farin cikin sa , ya san iliyas abokin aikin tafeedah ne da suka taɓa aiki tare a magadishu , asalin sa ɗan nigeria ne , da yakasance babban sojin sama , "
Shi ma zai so halartar bikin iliyas ɗin kwarai da gaske , tare da farin cikin haɗuwar da zasu yi da aminin sa wanda suka kwashe kusan watanni bakwai basa tare ,"
Sauke wayar yayi daga kunnen sa bayan sun yi sallama da tafeedah , bai sake bi ta kan barewar nan ba ya kaɗa kan sa ya bar wurin ,"
Assalamu Alaykum masoya ,!
Nasan kun yi jira cikin satin nan , da zaton samun update da wuri , nima na so na baku da wuri , yanayin ne bai dai-daita agare ni ba ! Da fatan kun min afouwa ?
Nagode !
[10/3, 2:42 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
24
Kwanakin da suka biyo bayan zaman Su yakaka a gidan su doctor hamza , kwanaki ne mafiya jin daɗi da walwala agare su a bakiɗayan rayuwar su ,sun gyagije sun yi fes da su tamkar da ɗai basu taɓa shan wata wahalar rayuwa ba ,
Doctor hamza yayi bajinta sosai ta yadda ya ɗau nawin duk wasu lamuran su na yau da kullum babu gajiyawa babu ƙorafi ko tozarci irin na wasu mutanen, a gefe kuma ya gama shirin sa na sanya su a makarantu , inda ita yakaka yayi mata rajista da wata makarantar matan aure ta jeka/ka dawo boko zallah , zata fara zuwa bayan ta haihu ,
Falmata kuma yana fafutukar nema mata wata makarantar makafi mai zaman kan ta , wanda su a shekara mutane 70 kachal suke ɗauka , yana sa ran za'a samu gurbin sanya falmata , '
Amma a halin yanzu su duk biyun ya ɗauka musu wasu malamai biyu mata ɗayar tana zuwa da rana kamar karfe sha biyu bayan ta taso daga makarantar islamiyyar da take koyarwa , sai ta zo ta koyar da su karatun addini , zuwa karfe biyun rana , wacce take koyar da su boko kuma zata iso karfe huɗu na yamma zuwa karfe shidda take tafiya , ita falmata kome da baki ake koya mata tana saurara a halin yanzu tun da ba makarantar su ta makafi aka kai ta ba , yayin da ita kuma yakaka ake koya mata har da rubutu ,
Kuma babu laifi ƙwarai suna da saurin fahimta musamman ma falmata , ba'a maimaita mata karatu , daga an fadi ta haddace sa kenan, ga ta da baiwar harce iya fidda lafuza Sam bata da tsamin baki, "hakan ba ƙaramin farantawa doctor hamza yake ba , da alama yaran baza'a sha wahalar sauya musu rayuwa ba !
Ta ɓangaren ƙannan sa ma basu da wata matsala , zainab da hafsa sune manya kuma sun girme musu sosai zainab tana da ishirin da biyar hafsa tana da ishirin da uku ,dan haka tsakanin su da su yakaka gaisuwa ce kawai bayan haka ko kula sabgar su basa yi , basu ma cika zaman gidan ba domin a halin yanzu ma shirye shiryen bikin zainab ɗin ake nan da sati uku inda zata auri wani babban sojin sama ,
ita kuwa hafsa boko yayi zafi domin yanzu ne take matakin ƙarshe a jami'a ga kuma taya ƴar uwar ta shirye shiryen biki da suke , tunda ba uwa bace da su a kusa , kusan su biyun suke duk wasu tsare-tsaren su na ƴan mata , sai kuma ƙannen mahaifin su uku mata da su kuma suke gudanar da sauran lamuran da yakamata iyaye mata suyi ,"
dan haka daga su sai rahima da ta zama ƙawar su su duka biyun suke gudanar da lamuran su , domin ta biye musu sosai tana kwasar duk wasu gidancin su da ƙauyencin su da suke yi sumfuri-sumfuri kuma dai-dai gwargodo tana iyakar yin ta wurin wayar musu da kai a duk lokacin da suka yi wata katoɓarar .
A halin yanzu sun samu kusan watanni biyu kenan a gidan ,
Kamar kullum bayan dawowar sa daga aikin sa da ya wuni yana yi , ya shigo bangaren sa bayan ya baro bangaren baba inda ya daɗe suna tattaunawa mafi yawa muhawarar ta su akan sha'anin auren zainab ɗin ne , suna tsare-tsaren yadda kome zai tafi cikin tsari mai kyau , sai kuma a ƙarshe kamar koyaushe idan suka yi zama irin wannan sai hamza ya shigo da batun mahaifiyar su ko da a fakaice ne , a yau ma nema yayi da mahaifin nasu ya amince a sanyo ta cikin lamuran bikin zainab ɗin kasancewar ta babbar ɗiyar ta mace da a karon farko za'a aurar , a wannan lokacin fiye da lokutan baya ya ga bacin ran baban su , inda ya rufe ido yayi ta faɗa a ƙarshe yace kar hamza ya sake sako mahaifiyar su cikin lamuran bikin zainab , shine mahaifin su shi Allah ya ɗorawa alhakin aurar da ƴaƴan sa , ba wata chan daban ba wacce ta zaɓi rayuwar kororo akan zaman aure ,"
Idanun sa taf da hawaye ya baro sashin yana jin zuciyar sa na ƙara bunƙasa girman laifin ta ,
Kai tsaye banɗaki ya shiga yayi wanka gami da ɗauro alwalar sallar magariba da ta gabato , ya zira jallabiyar sa tare da sanya ɗan silifa ya rufe sashin nasa ya nufi cikin gidan ," hannun sa riƙe da wata ledar da ya biya ya ɗauko a mota mai tambarin "down town" , tare da wata bakar leda .
A zaune ya tadda su , suna sake biya karatun su da malamar su ta boko ta yi musu yanzu ta tafi ,' Rahima na yi musu gyaran ƴan ƙananun kalmomin english da ma'anonin su da aka fara koya musu bayan sun gama haddace Alphabet ,"..
Cikin idanun yakaka ya fara jefa kallon sa, lokacin da ya ƙaraso cikin falon ,
Da sauri rahima ta miƙe gami da karɓar ledar hannun sa suna masu haɗa baki su ukun wurin yi masa barka da zuwa tare da gaishe shi ,"
Yana daga tsaye yana ɗaura agogon da ya zaro daga aljihun wandan sa yake amsa gaisuwar su , "
Da fatan suna muku karatun yadda kuke ganewa ?
Ya tambaye su yana mai nacewa kallon fuskar ta ,
A tare suka haɗa baki su biyun wurin amsa masa ,"
Muna ganewa sosai yaya dakta ,"
Toh madallah a cigaba da dagewa ,"babu dai wata matsala ko ?
Babu matsalar kome yaya mungode,!
Daga haka ya fice jin an fara kiran sallah ,
Da zumiɗin su suka buɗe ledar da ya kawo musu duk da sun riga sun san abunda yake ciki , ilai kuwa shawarma ce naɗi biyar , kowaccen su ta ɗau ɗaya suna murna, ɗaya ledar kuwa agwaluma ce manya-manya nunannu har cikin ledar , ai kuwa yakaka tana ganin agwalumar ta ajiye ƙunshin shawarmar ta gami da sunkutar ledar agwalumar baki ɗaya ,
da sauri ta yunƙura tana tura cikin ta wanda zuwa yanzu har ya shige watanni shidda , kitchen ta je ta wanko musu , ta miƙawa rahima da tace zata sanya musu a firiji ta ɗan yi sanyi kafin su idar da sallah ,
Bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i , kamar yadda yake ka'idar sa idan ya shiga masallaci sallar magariba bai fitowa sai yayi isha'i muddin ba wani aiki ne mai girma a gaban sa ba , zama yake yayi ta karatun Alqur'ani .
Rahima , yakaka da hafsa ya tarar suna zaune a ainahin babban falon suna hira tare da kallon wani shirin larabawa da ake nunawa a tv , hannun kowaccen su riƙe da agwalumar tana shaa ,
Da murmushi a kan fuskokin su suka masa sannu da shigowa , hafsa ta miƙe ta shiga kitchen ta fito hannun ta riƙe da babban faranti wanda aka jera kuloli bisa ,
Miƙa masa tayi ,ya karɓa tare da maida ganin sa sashin da yakaka take zaune ,"
Ki shirya gobe ne ranar komawar ki asibiti su duba ki , da safe zan kai ki saboda ina da aikin safe ,"
Charaf hafsa ta karɓi zance ,"
Big bro kayi tafiyar ka kawai aikin ni zan kaita , ko ba Galaxy hospital ba?
Nan ne , amma nafi son na kaita da kaina saboda akwai wata matsala da muke kan tattaunata da likitan ta ,"
Ki ƙira min zainab ku zo sashi na tare inason yin magana da ku ,!
Daga haka ya juya yana barin wurin ,
Ya bar hafsa nan tsaye da tarin wasi-wasin da take yi akan alaƙar yayan su da wannan ƴar gudun hijirar , kulawar da ta lura yana bata yayi yawa ya wuce na taimako ," meye a tsakanin su ? Tasan yayan su kamili ne kuma managarci bata zargin zai aikata wani mummunan abu , tunanin ta yafi karkata akan wani yanayi da take hangowa a kan fuskar sa a duk lokacin da ya ga yarinyar da kuma tsantsar kulawar da yake mata duk a sunan taimako ," ko ma menene a sannu zata kai ga fahimta fatan ta Allah ya sa ba abun da take zato bane , ,"
Cikin sati biyun da suka biyo baya shiri ake gadan-gadan na bikin zainab shi da kan sa hamza bai zauna ba , shirye shirye suke ka'in da na'in kasantuwar wannan ne biki na farko da za'a yi a gidan nasu , ƴan uwan su na nesa nesa duk sun fara isowa , haka ma wasu ƙawayen zainab ɗin sun fara sintiri ganin cewa an shigo satin fara bikin sam ƙafa bata ɗaukewa a gidan , ƴan aiki huɗu mata doctor hamza ya kawo amma duk da haka aiki da aike chakuɗe musu yake ,'
Yakaka da Falmata duk a takure suke , ko falon basu cika son fitowa ba suna ƙunshe