Showing 369001 words to 372000 words out of 411050 words
Chapter 124 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
ta fito saɗaf-saɗaf ta nufi inda ta ajiye abincin ta kafin ta ɗauka sai da ta buɗe ƙaramin fridge da yake ɗakin ta ɗau ruwan roba mai sanyi guda ɗaya .
Tana juyawa kamar ance masa ya miƙe kawai sai ganin sa tayi akan ƙafafun sa huɗu yana kallon ta .
Wani irin ihu ta sa tana sakin ruwan hannun ta da warmer ɗin ta tarwatse a ƙasa da hakan yasa Sam ya dako tsalle yana zuwa a yunwace yasa bakin sa akan Basisen ya fara lasa yana haɗawa da pancake yana cinyewa bai ko bi ta kan Yakaka ba wacce tayi suman tsaye tana jira ta ji shi a kan ta yana kachal-chala mata tsoƙar jiki da faratan sa .
Wani irin riƙe jikin ta tayi har yatsun ta na shiga cikin carfet ɗin da yake shimfiɗe a ƙasa ji da tayi yana lasar rumfar ƙafar ta da basisen ya zuba akai a lokaci ɗaya wani irin tsoro mai haɗe da raɗaɗi ya ratsa tun daga ƙafar ta har ƙwaƙwalwar ta ta saki wani irin ihu da ya ratsa baki ɗayan gidan .
Numfashin ta kuma ya shiga ƙoƙarin barin jikin ta .
Ba zata iya sanin iyakar daɗewar da tayi ba kawai dai ta ji wani irin sanyi yana ratsa rumfar ƙafar ta da yasa ta buɗe ido a hankali .
Abunda ta gani ya matuƙar bata mamaki lokaci ɗaya da shiga sabon ruɗani .
Sam ne ta yake ta faman jido robar ruwan sanyi daga cikin fridge a bakin sa yana zuwa yana ɗora mata a jiki tamkar wanda aka sa shi yana yi yana kaɗa jela.
Tsam tayi tana kallon sa da idanun ta da suka rine jazur , sai da ya jido ruwan cikin fridge ɗin kaf sannan ya dawo gaban ta ya tsugunna yana kallon ta tamkar mai jiran ta masa wani umarnin Sai zaro harshe yake yana lallago .
Kallon sa Yakaka tayi ta kawar da idanun ta zuwa lokacin har ta kai maƙura a tsoro alhalin babu mai ceton ta ba kuma wajen tsira dan haka ta fara dawowa cikin hankalin ta .
Tun tana tunanin zai bazamo kan ta har dai ta fahimci baya wani yunkuri na cutar da ita da ya wuce banga-banga da yayi a gaban ta dan haka a hankali ta kai hannu ta ɗau ɗaya daga cikin ruwan da ya jera mata bayan ta gama jujjuya robar ruwan a hannu ta ta ɓalle murfin ta sha ruwan da ɗan yawa kafin ta sauƙe gorar .
Mamakin ta ya ƙaru lokacin da ya sake kai fuskar sa ya daɗa turo mata wata gorar ruwan kusa da ƙafar ta .
Tana kallon sa ta kai hannu ta ɗauka , sai ta ga yayi baya ya kwanta shirim! daga nesa kaɗan da ita .
Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya tayi tana jin 'yar guntuwar nutsuwa na shigar ta sai ta gyara zaman ta da bata san yaushe ma ta zaunan ba ta miƙe kafafun ta da suka mata tsami saboda daɗewa da tayi a durkushe .
Cikin siririyar muryar ta ta fara yin karatun Alqur'ani bayan ta jingina kan ta da jikin gado.
Wata irin nutsuwa ce mai girma ta mamaye ta da ta lura hatta Sam shi ma ya samu kwatankwacin nutsuwar domin kwance yayi shiru ya kwantar da kunnuwan sa lanbar lokaci-lokaci yana kaɗa jelar sa .
Lokacin da ta fahimci rana ta kusa faɗuwa a hankali ta miƙe abun da ya bata tsoro a lokacin bai wuce ganin yadda shi ma Sam ya miƙe ba tsam ya tsaya '
da sassarfa ta nufi banɗaki tana waigen sa ganin yadda yake bin ta , yasa ta ɗan ƙara da gudu ta shige banɗaki bayan ta shiga ta rufo ƙofar kafin ta fara wanka sai da ta leƙa shi ta ga ya tsugunna a bakin ƙofar .
Cikin nutsuwa tayi wankan ta , kan ta tsaye ta murɗo ƙofar ta fito , yana ganin ta ya matsa mata a hanya ta wuce kafin ya bi bayan ta zuwa gaban madubi.
Ɗan kallo shi tayi tana mamakin sa cikin ran ta ta aiyana "ashe ma ba zai min kome ba ?
Lokacin da ta gama shiryawa tsaf sai ta ɗauko sabbin kayan ta wani lallausan yadi da aka yiwa adon manyan furanni launin ruwan dorawa da fari , ɗinkin rigar iyakar guiwa irin ta matan N'djamena da aka mata tattara da roba daga kugun ta da ɗan guntun hannu .
Ta ƙasa ɗan dogon wondo ne mahadin rigar da bai ƙarasa idon sawun ta ba , a fuskar ta bata wani cika kwalliya ba powder kawai ta shafa sai ta zizara kwalli a ƙasan idanun ta ɗaurin ɗankwalin da tayi sassauƙa ne ta nannaɗe gashin ta da shi ta baya yayi ɗan tum-tum ta ɗau turaren ta na humra ta shafa sai kuma ta fesa wani kaɗan da ta gani a gaban madubin ɗakin.
Cikin nutsuwa duk kuwa da bibikon da Sam yake mata amma ta dake zuciyar ta tayi ƙam-ƙam ta hana tsoron da take ji har yana mata wani yam-yam a cikin jini ya yi tasirin da zai haukata ta ,ta fara tattara ɗakin duk inda Sam ya ɓata ta tattare ta goge da Moper ta gyara ko'ina tsaf har gado , tana yi tana kallon Sam da yake mayar da ta shi ƙafar a duk inda ta cire ta ta .
Bayan ta gama gefen gado ta samu ta zauna ta ɗau wayar ta da bata san lokacin da aka wargaza mata ita ba batirin daban wayar daban a take sofi ta faɗo mata a rai tana zaton ita ta mata haka da wayar .
Girgiza kai kawai tayi ta fara neman layin Hajja sai dai tayi ta ƙara daga can ba'a ɗaga ba.
Ɗan saurarawa tayi lokacin da ta ji ana ƙoƙarin buɗo ƙofar ta mayar da hankalin ta ga ƙofar ,
Kamar wacce aka tunkuɗo ta Sofia ta buɗe ƙofar ta shigo , turus ! Ta jaa ta tsaya tana rarraba ido a ɗakin da yake tashin ƙamshin humrar Yakaka ba kamar yadda take zato ba ko'ina tsaf yana ɗaukar ido kafin ta tsayar da ganin ta kan Yakaka wacce tun shigowar ta kallo ɗaya kawai tayi mata ta mayar da ganin ta kan Waya duk kuwa da cewar ta tsorata amma taƙi yarda tsoron ya fito fili .
"Sam .
Sofia ta ƙira shi a tsawace da wata irin muryar da ba Yakaka kaɗai ba har Sam da yake kwance daga ƙasa kusa da ƙafafun Yakaka sai da ya tsorata ya miƙe a safure ya shiga haushi ba ƙaƙƙautawa.
Sofia wacce a dai-dai lokacin duk wata dabarar ta tayi ƙaurar wucin gadi sai ta taho kawai fangam-fangam bayan ta zare takalmin da yake ƙafar ta ta takarkare iyakar ƙarfin ta ta kwaɗawa Sam tsinin takalmin a kan sa har sai da ya durƙushe.
,"Ɗan iska cewa nayi ka zo kuyi soyayya da ita ? ba cewa nayi ka cije ta ka kashe min ita ba?
Wani irin kuwwa yayi da yasa Yakaka daka tsalle ta hau kan gadon tsoron ta yana dawowa sabo fil .
Sofi bata ankara ba ta ji ya kawo mata wafta da sai da ta kusa tuntsurawa tana ɗaga Ido ta hango takalmin ta a bakin sa ganin yadda yake gurnani yana nufo ta yasa ta fara jaa baya mamakance , laɓɓan ta na ɗan rawa ta fara ƙiran sunan sa
"Sam.Sam.Don't....
Ganin yadda yayi kan ta gadan-gadan ya san kasa ƙarasa kalmomin da take nufin furtawa sai juya ta ruga a guje Sam ya rufa mata baya da gudu da haushin sa da ya karaɗe gidan .
Yakaka wacce jikinta har rawa yake tsabar tsoro da gudu ta duro daga gadon ƙafafun ta babu takalmi ta fito daga ɗakin kai tsaye hanyar fita a gidan tayi a ruɗe "har a ran ta ta zaɓi barin gidan akan ta zauna Sam ya gama da Sofia da take uwarɗakin sa ya dawo kan ta .
Bata san da tahowar sa ba kamar yadda shima bai yi zaton fitowar ta ba a wannan lokacin suka ci karo.
Gaba ɗaya ta faɗa masa a jiki ta chakume shi..
"Yaya Dakta wallahi kare nan zai cinye Anty Sofi ga su can ya bita da gudu zai kashe ta ya dawo kaina....
Da sauri ya ɗago ta tana sake ƙwaƙwume shi yanayin sa da galabaita sosai da tarin damuwa ya ɗago ta da kyar daga jikin sa bayan ya saki jakar hannun sa ta faɗi ƙasa ya riƙe fuskar ta a tsakanin tafukan sa .
"Me yake damun ki ne Wafaa ? Waye yake tsorata ki da kare ? Faɗa min aina kike ganin kare ? Yaushe haka ya fara faruwa da ke ?
Ya furta hakan idanun sa na tara ƙwalla saboda can daga cikin kan sa ya fara hasashen wani abu da baya fatan tabbatuwar sa a gare ta.
Laɓɓan ta na rawa tace "wallahi akwai kare a gidan nan kullum da shi nake wuni a ɗaki , Sofi ,Sofi ita take kai min shi kum....
"Safiya ?
Ya tambaya da wani irin yanayi a muryar sa bayan yanayin fuskar sa ya jirkitu da tsantsar ɓacin rai .
"Eh , Ah' ah ba ita ba amma akwai kare yanzu ma ya bi ta zai cinye ta dan Allah dan Allah yaya dakta ka mayar da ni gida , zan koma Maiduguri ko kum..
"Shit yace yana rufe mata baki "wafaa ki nutsu ni duk bana fahimtar inda maganganun ki ke dosa kika ce Sofia take kai miki kare ɗaki ? Sofia ce take kawo kare gidan nan ?
A hankali ta sunkuyar da kan ta tana jin zuciyar ta na rabuwa biyu sashi ɗaya tsoron Sofia yayi rinjaye ɗayan kuwa tsoron karen tare da son a fitar mata da shi daga rayuwar ta yana tunzura ta kan ta faɗi abunda ke faruwa.
"Sofia ta ke tura miki kare a ɗaki ? Ya sake tambayar ta da taushin muryar da ta ratsa duk wani firgicin da ya cika mata zuci ya mata lulluɓi da nutsuwar da yasa ta dawo hayyacin ta dan haka ta ɗago kan ta a hankali ta motsa laɓɓan ta "Yaya Dacta aun....
"Amarya da ango kenan watau shigar sauri kika min Yakaka shi ne har kika riga ni fitowa taren Miji ? To ai shikenan na ci girma na bar miki .
Sofia wacce take ƙarasowa ta furta hakan tana bin Yakaka da wani kallon da yasa Dactor Hamza kafe ta da ido yana nazarin ƙwarar idanun ta kafin ya bi jikin ta da kallo .
"Sofia me ya same ki haka ? Ya rigar ki a yage ?
Ya furta hakan yana mata nuni da jikin ta ba tare da ya saki hannun Yakaka ba .
"Ƙusa ce ta yaga min .
Ta furta hakan da yanayi na ko'in kula
"Ƙusa ya tambaya muryar sa cike da shakku .
"Eh
Ta amsa masa a daƙile kafin ta matsa kusa da Yakaka ta zira hannun ta a cikin nata tana karyar da murya tace "muje na taya ki girkin kin ga tun ɗazu nake ta cewa ki tashi muje ki fara ina taya ki kika ƙi kika jibge a gaban Tv kina kallo .
Yakaka wacce take kallon Sofia a tsorace ɗimbin mamaki na tasowa yana rufe ta ta ɗan kifta ido .
"Sofia muje ciki .
Doctor Hamza ya furta haka yana wucewa jaye da hannun Yakaka da ta bi shi da sauri bayan ta zare hannun ta daga cikin na Sofia da take jin sa kamar garwashi .
A falon ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun Yakaka kuma ta zauna a ƙasa.
Sofia da ta shigo daga bayan su ta zauna a kujerar da take kusa da wacce yake zaune bisa.
Sai da ya ɗan nisa sannan ya tattara ganin sa akan Sofia fuskar sa ba alamar wasa yace "Sofia akwai kare a gidan nan ne ?
Mui-mui tayi da baki kafin ta dafe ƙirji tace "kare dai Doctor ? Ta ina ya shigo mana ? Ko d...
"Tambayar ki nayi kina sake tambaya ta Sofia ki bani amsa kawai .
Hararar sa tayi ta ƙasan ido kafin ta taɓe baki "babu kare a gidan nan idan akwai kuma ni bana ganin sa .
Yakaka wacce kan ta ke ƙasa ta ɗago da kan ta ta dubi Sofi da bata yi ƙasa a guiwa ba ta jefa mata wani kallon da yake ɗauke da saƙon gargaɗi .
"Ok
Yace yana miƙewa kai tsaye Sama ya dosa inda ɗakin Sofia yake da sauri ta miƙe ta bi shi a baya muryar ta tana ɗan shaƙewa tace "Doctor ko na zo ne akwai magana ? Ko wani abun kake nema ?
Bai kula ta ba ya cigaba da tafiyar sa zuciyar sa tana sake ba shi tabbacin rashin gaskiyar Sofi da duk yadda aka yi tana da hannu wajen tsorata Yakaka , a ɗan tsukin ya fara gano wasu ɗabi'un Sofia da a da bai san tana da su ba .
Sai dai duk inda yake zaton zai iya dubawa ya ga wani abu makamanci da kare da ake tsorata Yakaka da shi a gidan ya duba bai ga kome ba hatta cikin banɗaki da kitchen sai da ya duba .
A gajiye ya dawo falon inda ya bar Yakaka a nan ya dawo ya same ta ya zauna akan kujera lokaci ɗaya ya dafe kan sa da ke ɗan masa ciwo bayan tarin gajiyar da take kassara masa gabɓan jiki .
Shiru yayi har lokacin da Sofia ta ƙaraso wajen ta zauna fuskar ta wasai kamar an mata bishara .
"Wafaa ya ƙira Yakaka da tsauri a muryar sa .
A hankali ta ɗago kan ta.
"Babu kare a gidan nan .
Hawayen da bata san yaushe suka taru ba su ne suka silalo mata .
"A karo na ƙarshe ina faɗa miki ba kare a gidan nan ya kamata ki kwantar da hankalin ki ki daina wannan firgice-firgicen da kike yi ko kina son ƙwaƙwalwar ki ta samu matsala ne ?
"Docto wai daman akan haukar .....
"Sofia idan ina magana ki daina saka min baki please behave yourself.
Yace yana mata wani mummunan kallo gaba ɗaya daga ƙasan ran sa yana zargin Sofia da bai san dalilin hakan ba shi dai zuciyar sa bata aminta da ita ba akan wannan matsalar da tayi sammakon shigowa rayuwar auren sa da Yakaka da ko kaɗan abun bai masa daɗi ganin ta koyaushe a firgice tana guje-guje da safure-safure yana ƙona masa rai tare da sauƙar masa da gajiya .
"Wafaa ya ƙira ta a tausashe , ta ɗago kan ta da idanun ta da suke narke take kallon sa .
"Zan yi shirin Masallaci idan na dawo daga Sallah zamu je mu ci abincin kar ki shiga kitchen yanzu dare yayi .
Langaɓe kan ta tayi kawai bata amsa ba ko kaɗan bata son ya matsa ya bar wani sarari tsakanin ta da Sofi .
Mayar da kallon sa kan sofia yayi wacce take ta faman hura hanci tana kokawa da zuciyar ta da take jin har wani toroƙo take kamar za ta fashe
"Sofi anjima ina so nayi magana da ku baki ɗaya .
Bai jira amsar ta ba ya miƙe , Yakaka ma cikam! Ta miƙe tana riga shi wucewa ta yi hanyar ɗakin su .
Da kallo ya bi bayan ta kayan da ta sa a jikin ta ya masa kyau matuƙa sai ya gan ta kamar irin kyawawan matan nan da ake tallan sutura da su .( model's ) a hankali ya taka ya bi bayan ta
Sofia wacce take zaune ɗim!akan kujera ta kaiwa kujerar wani irin duka da hannu kafin ta toshe bakin ta da hannu wani irin kuka take yi ciki-ciki , irin kishin da take ji a ran ta akan Yakaka muddin bata ɗau mataki ba za ta iya haɗiyar zuciya ta mutu.
Lokacin da Doctor Hamza ya idar da sallar Magarib yayi niyyar komawa gida amma yunwar da yake ji da kuma sanin da yayi a gidan ma shi suke jira tunda ya hana ayi girkin sai kawai da ya shigo gidan ya ɗau motar sa ya sake fita ba tare da ya shiga cikin gidan ba .
Sofia da ta ji ƙugin tashin motar sa da sauri ta leƙa ta window ta ga fitar sa , tana ganin ya bar gidan a guje ta sauƙa ƙasa kai tsaye ɗakin Yakaka ta tasamma .
Tana murɗa ƙofar ta ji a kulle , ɗan kwankwasawa tayi cikin salon da Doctor Hamza yake yi .
Yakaka wacce take zaune ta miƙe a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar .
Haka kawai ta ji zuciyar ta ta doka da ƙarfi dan haka ta dakata ta fasa bude kofar cikin siririyar murya tace "Waye ?
Shiru Sofi tayi tana fatan ta buɗe su gamu , sake dukan ƙofar tayi da karfi da hakan ya sa nan take Yakaka ta fahimci wace ce a wajen dan haka a sarari ta furta "Auzu Billah minash Shaytanir Rajeem, baya ta koma ta zauna a inda ta ta shi.
"Ya kamata na samarwa kaina da mafita ni Yakaka lamarin Matar nan ya fara wuce iyakata ta musulunci , ta furta hakan a sarari kawo yanzu ta haƙaƙe da gasken gaske sofi ta ɗaura ɗamarar yaƙar ta dalili kawai;sun hada Miji daya.
"Ina Mafita?
Haka Sofia ta gaji da bugun ƙofar tana surutai , jin shigowar motar Doctor Hamza ya sa tayi saurin barin wajen ta koma ɗakin ta kai tsaye banɗaki ta shiga ta sakarwa kan ta ruwan sanyi .
Kusan mintuna goma sha biyar suka kwashe suna jiran sofia ta zo su ci abinci amma shiru ba alamun ta sau uku yana ƙiran layin ta wayar tana ƙara bata ɗauka ,
Ran sa ya fara ɓaci da salon rainin da yake hango take-taken sa daga Sofia wanda kuma ba zai ɗauka ba .
"Wafaa hau sama ki ƙira Sofia .
Kamar bata fahimci abunda yake cewa ba haka Yakaka take jahiltar sa da ido .
Ganin yadda tayi da fuska ya sa shi miƙewa da kan sa ya nufi saman .
Yakaka wacce ta bi shi da kallo da tuno da abunda ya faru jiya daga zuwa ƙiran Sofi ya sa ta miƙewa tsaye da sauri .
"yaya Dakta .
Ta ƙira sunan sa ,
a hankali ya waigo.
"zan bika .
tace tana yin narai-narai da ido .
Bai amsa ba sai hannun sa da ya miƙo mata alamar ta taho da sauri ta isa gare shi tana