Showing 387001 words to 390000 words out of 411050 words
Chapter 130 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
gaida ta kullum ta ce ta dunga sanya kwana ɗaya a tsakani saboda tayi nawi kuma da 'yar tazara a tsakanin su Hajja ita ke zuwa kai gaisuwa kullum.
Tana tunanin zuci bata san ta cinye abincin ba sai da ta laluba ta ji ba kome sai 'yan tsirarun shinkafa.
Ta ɗago kan ta a hankali ta dubi Fuskar Youssouf wanda ya rafka tagumi da hannu biyu yana mata kallo mai ruwa biyu , zallar ƙaunar ta da kuma tausayin halin da take ciki .
A kunyace ta ɗan yi murmushi kafin tayi magana ya riga ta da cewa "kin ƙoshi ? Bai jira amsar ta ba ya kai hannun sa ya goge mata gefen bakin ta da miya ta ɗan sauƙa.
"Mon Bébé kin ƙoshi ?
Ya sake tambayar ta
" Na ƙoshi Baban Mama ta furta tana ƙoƙarin tashi shi ya taimaka mata ta wanke hannun ta .
Tare suka zauna yana maƙale da ita ko yaya ta motsa yana mata sannu tare da gwada mata So.
ƙiran Sallah da akayi shi yasa shi sallama da ita bayan ya fita kai tsaye sai da ya shiga sashin Siyama da tun asuba rabon shi da ita saboda girkin Falmata ne
A zaune ya same ta an yi mata zanen ƙunshi a fararen ƙafafun ta tana jiran ya bushe ta wanke .
Daga inda yake yana iya hangen jelar ƙananun kitson da aka mata da suka kwanta har a kafaɗun ta 'yar doguwar fuskar ta ta sake fitowa sai ƙyallin gyaran jikin da ta samu take yi .
Ba tare da ya zauna ba yake amsa gaisuwar da Siyamar ke yi masa bayan sun gama gaisawar ya ɗan yi murmushi kafin ya ce "wannan ƙwalliyar du ta tafiyar ce ? Ko kouwa tawa ce ?
Ɗan wara idanun ta tayi sai kuma tayi dariya cike da jin daɗi da ɗoki ta ce "ƙwalliya taka ce Baban Yumna kamar yadda tafiyar ma take taka domin kai .
Ɗaga mata gira yayi yana juyawa akan ƙafafun sa yace "idan hakka ne ayi shiri da kyau a kouma gama bisa kan lokaci doumin kamar yadda na faɗi gobbe kafin hantsi ya ɗagga zamu tai da yardar Allah .
"To Insha Allah ba zan makara ba.
Ta furta hakan tana bin bayan sa da kallo wani irin farin-ciki na ratsa ta sanin da tayi gobe iwar haka daga ita sai shi a wani yanki .
Daren ranar kusan raba shi suka yi Youssoufa yana aikin rarrashin Falmata da shima kawai daurewa yake yi amma har cikin ran sa yake jin rabuwar da zasu yi.
Dan dai babu yadda zai yi ne a cikin halin da take ciki ba zai yiwu ya ɗauke ta su tafi bariki ba can wata jahar da babu kowa nasu ko shi da kansa ba zai so hakan ba bare ma kuma Hajiya Umma da Maimartaba sun riga sun gama magana akan ya bar ta anan gida har ta haihu abunda ta haifa yayi ƙwari kafin ta fara bin sa jahar da yake aiki .
****
Washegari.
Duk yadda Falmata ta so ta ɓoyewa Siyama damuwar ta lokacin da ta shiga sashin ta domin yi mata Sallama kasawa tayi .
Idanun ta suka tara ruwan hawayen muryar ta na ɗan rawa tace "Maman Yumna zan yi kewar ku ke da Yumna sosai dan Allah ki dunga ƙirana Appel vidéo .
Riƙe hannun ta Siyama tayi cikin ran ta tana yabawa ƙwarai da juriyar da ta gwada na ɓoye mata ainahin dalilin damuwar ta , cike da rarrashi tace "ma petite soeur mu ma za muyi kewar ki amma kar ki damu kullum za mu dunga yin waya dan Allah kar kisa damuwa a ran kin san ba'a so ki zauna cikin damuwa a halin da kike ciki ko ?
"A hankali ta gyaɗa kai tana jin yadda zuciyar ta ke matsewa kamar zata fashe .
Murmushi Siyama tayi mata tana ɗan jaan hannun ta tace " to tashi ki zo ki mana rakiya le chauffeur ya zo za mu tai yanzu .
Ɗan jimm tayi tana jin wani yanayi marar daɗi na ratsa ta tayi zaton Youssoufa zai sake shigowa suyi wata Sallamar bayan Sallama bayan da Sallamomin da suka dunga yi tun daga jiya har wayewar garin yau da safe kafin ya shirya ya fita daga Sashin nata inda ya kwana .
"Maman yumna bari na ɗauko Mayafi na.
Tace tana zame hannun ta daga nata ta nufi ɗaya daga cikin ɗakunan ta '
Bayan shigar ta ɗakin bata jima ba ta fito hannun ta riƙe da wata Paper-bag.
Bayan ta ƙaraso sai ta miƙawa Siyama ,muryar ta da rauni ta ce "Maman Yumna ga tsaraba ta nan kiyi amfani da kayan ciki.
Murmushi Siyama tayi kafin ta sanya hannu ta karɓa tana ɗan leƙen cikin jakar ta ce "ma petite soeur kyauta ce hakka anka min ? Na kouwa gode miki ƙamna ta Allah shi bar ƙauna a tsakani.
"Amin .
Falmata ta amsa tana Murmushin yaƙe .
A bakin mota suka tarar da Biyamuradi Youssouf yana riƙe da hannun Yumna yayi shirin sa tsaf cikin kakin sa na soji da yake matuƙar amsar jikin sa .
Tun da Falmata ta samu lafiyar idanun ta yau ce rana ta farko da ta gan shi sanye da kakin soji sai ta shagala wajen kallon sa yadda yayi mata kyau ji take kamar ta ruga da gudu ta rungume shi a ƙarshe kuma ta hana shi tafiya ya zauna a gaban ta tayi ta kallon sa haka tana miƙa godiyar ta ga Ubangiji Youssoufa Namiji ne da kowacce mace zata so ta mallaki irin sa a fagen kyaun suffa da cikar zati irin na cikakken ɗa Namiji yayi zarra .
Shi ɗin ma ita ya zubawa ido a tun fitowar su yana nazarin damuwar da take danƙare a fuskar ta wanda a take ya ji tana kassara masa gaɓɓai da a zahiri ma dan haka ne ya ƙi shiga sashin nata yayi mata bankwana saboda yana tsoron abunda ka iya biyo bayan hakan wataƙila ma ya fasa tafiyar .
Gyaran muryar da Siyama tayi yasa Falmata tayi saurin ɗauke ganin ta daga kan sa tana yin ɗan baya kaɗan ta riƙo hannun Yumna wacce ta baro Baban ta ta dawo wajen Mamar ta .
"Yumna zan yi kewar ki sosai , ta furta hakan tana shafa kan ta .
Mayar da ganin ta tayi sashin da Siyama take tsaye "to Maman Yumna Allah ya kiyaye muku hanya dan Allah idan kun isa ki sanar min .
"Nima zan yi ƙewar ki ƙamnata Amin nagode sosai dan Allah ki kula muna da kan ki da bébé mu .
Gyaɗa kai Falmata tayi tana mayar da ƙwallar da take ji tana cika mata ido taƙi yarda ta sake kallon Sashin da Biyamuradi yake tsaye duk da cewa tana jin idanun sa na yawo a kan ta.
chauffeur ya buɗe ƙofar motar Siyama da Yumna suka shiga ganin haka yasa a hankali ta juya tana ɗaga takun ta dan barin wajen.
" Fatima .
ya ƙira sunan ta .
Chak ta tsaya ba tare da ta jiyo ba , ɗan taku yayi ya matso kusa da ƙofar motar cikin amon sa mai ƙarfi yace "je t'aime tellement Et tu me manqueras.
Har cikin ran ta ta ji kalmomin sa a hankali ta runtse idanun ta hawayen da suka cika gurbin idon suka gangaro kan ƙuncin ta .
Muryar ta na rawa ta furta "Allah ya kiyaye mu ku hanya ya kai ku lafiya Amin .
Da sauri kamar ba ita ce ke ɗauke da wannan tirtsetsen cikin ba ta ƙarasa barin wajen idanun ta a rufe da ruwan hawaye .
Youssouf da yake tsaye ji yake kamar ya bita ya riƙe ta ya hana ta tafiya amma ya san idan yayi hakan zai ɓata goma ne ɗaya bata gyaru ba .
Lokacin da ta ɓacewa ganin sa dan kansa ya shiga motar direba ya jaa suka ɗau hanyar barin-gidan suka kama hanya ɗoɗar zuwa Birnin Tahoua inda yake aiki .
Lokacin da Falmata ta koma sashin ta abu na farko da ta fara yi bayan ta ci kuka har ta bawa aku lada ta ji idanun ta sun fara raurawa suna mata alamun ciwo '
Lallaɓawa tayi ta ɗau wayar ta wacce take ji tana ta ɗaukar kiɗa da ko bata duba ba ta san Biyamuradi Youssouf ne ke kira
A hankali ta shafa wayar ta kashe tana zunɓuro baki kamar yana ganin ta tace "Na fasa yin Appel vidéo ɗin da kai .
****
Duk da cewa tafiyar bata yiwa Siyama armashin da ta so ba amma hakan bai guntule mata jin daɗi da ɗokin ta ba sai hira take yi masa wani ya amsa wani kuwa yayi shiru yana shafe-shafen waya da sarai ta lura da wacce yake faman ƙira Fatima ce .
Ko da suka isa jahar Tahoua da gefen Azahar a share a tsaftace suka tarar da gidan dan haka aikin da tayi ba mai yawa bane ba illa kayayyakin su da tayi musu ma'ajiya a muhallin da ya dace ta sake yin wasu 'yan gyararraki da ba'a rasa ba.
Kafin ta gama wani Soja da yake hidima da gidan ya zo da cefene dan haka kai tsaye ta shiga kitchen duk da cewa ba sabon ta bane yin girki amma bata gagara iyawa ba dai-dai gwargwado ta zage-damtse dan farantawa Mijin ta tayi girki mai kyau da daɗi Yumna na taya ta da ɓarna .
Youssouf kuwa tunda suka zo da aka sauƙe su shi wucewa direba yayi da shi can babban ofishin su inda zasu yi wata ganawa shi da abokan aikin sa .
Ba shi ya samu damar komawa gidan ba sai bayan isha'i lokacin da ya shiga gidan tsit babu motsin kome sai na na'urori.
bai tarar da Siyama a falon ba sai fa wani daddaɗan ƙamshi da ya shaƙa wanda take ya tado masa da tunanin Fatiman sa domin kuwa ƙamshin irin nata ne a duk inda tayi bigire nan yake jin irin ƙamshin kewar ta mai yawa ya ji tana bin jikin sa , tunda suka taho yake son ya ji lafiyar ta amma taƙi ɗaukar wayar a ƙarshe ma ta kashe ta baki ɗaya kuma tunda ta kashe bata kunna ba .
Zama yayi akan kujerar falon yana sunce igiyoyin takalman sa , bai ji tahowar ta ba sai sauƙar kyakkyawan hannun ta da yasha adon ƙunshi ya gani ta ajiye akan hannun sa ta karɓe kunce takalmin da ya fara .
Sakar mata yayi yana bin jikin ta da kallo da ta sha ado da wata bugaggiyar shadda Boo ɗinkin bubu tayi ɗaurin ɗankwali mai ban sha'awa jelunan kitson ta da ta haɗa ta tufke ta haɗe cikin ƙaton ribbon ya taimaka wajen ɗago da ɗaurin daga ƙasa sai ya zauna ɗas a kan ta kamar hula .
"Siyama ma'abociyar kwalliya ce , daga can ƙasan ran sa ya aiyana haka .
Yana kallon ta har ta gama ta ɗago fuskar ta da bata cika fente-fente ba tana masa murmushi ta ce "Bienvenue mon amour et comment va le travail? Sannu.
Fuskar sa a sake da taƙaitatcen murmushi yace "ke za'a wa Sannu Maman Yumna da hidmar gida da kaɗaici , ɗakin taro mun ka hige sai yanzou munka kai ga hittowa.
bata amsa ba ta miƙe da ɗan murmushi a fuskar ta ta wuce ɗaki daga can ta haɗa masa ruwan wanka .
Ya shiga yayi bayan ya gama ya sako ƙananun kaya da basu cika nawi ba a jikin sa ya fito
Daga nan abinci ta kawo suka ci tare bayan sun gama ta tattara wajen ta dawo ta zauna daga gefen sa suna kallon TV tare duk da dai ita ba wani jin daɗin kallon take ba saboda tashar labarai ne shi yake ganin kayan sa .
Lokacin da ta ga ya ɗau waya sa sai da zuciyar ta ta doka tana satar kallon sa ta ga ya fara ƙira bugu ɗaya biyu , daga can ta ji computer na sanar da shi wayar a kashe take chajin wayar sa ya duba ya ga saura kadan ta mutu dan haka kawai sai ya kashe wayar ya sa a chaji
yana jin duk babu daɗi "meyasa Fatima za ta masa wannan horon ?
"Biyamuradi
Ta ƙira sunan shi
Da ido ya amsa mata yana kallon ta .
Murmushin yaƙe tayi kafin ta ce "tunda muka zo nayi ta neman wayar ƙamnata a kashe wayar....
Kafin ta ƙarasa Youssouf ya amsa mata fuskar sa na bayyana damuwa "nima itta nake ta ƙira amma ta kar wayar ko mai yassa tayi hakan ?
"Watakila batta so ta tsare ma aiki ne , Siyama ta amsa masa tana ɗan nazarin sa ta ɗora da cewa
"Amma ko za ka gouda kiran Hajja ne saboda a san halin da ta yini ciki.
"Hakka ya kamata, Amma itta telephoné na babu wutta cikin ta.
"Bari na ƙira ta da telephoné na sai ta sada mu da itta
Bugu ɗaya Hajja ta ɗau wayar ta tana ɗan gigin bacci tace "hallo waye anan ?
Daga can Siyama ta amsa mata tana jin muryar ta ta watsake suka gaisa faran-faran ta ɗora da faɗa mata dalilin ƙiran nan take Hajja ta yunƙura ta fita daga ɗakin ta ta nufi ɗakin Falmata cewa take "kada ma ki katse ƙiran ai yanzu zan kai mata idon ta biyu dan ban jima ba ma da barin ɗakin nata bayan mun gama hira .
"Hello Maman Yumna da fatan kun isa lafiya ? daga can Falmata da ta karbi wayar ta furta
Shiru ta ji anyi "Hello ta sake cewa.
Daga can ɓangaren da tunda ta ɗaga wayar Siyama ta miƙawa Youssoufa
"Fatima .
Sautin sa ya doki dodon kunnen ta da yasa ta runtse Ido tana jin yadda gangar jikin ta ke sauyawa daga jin amon sa .
"Fatima me yassa kin ka kashe min waya unn ?
Shiru ta sake yi tana jin sa ya cigaba da cewa "kin sa na shigga damouwa , kar ki sake min ya hakka kin ji kou ?
"Fatima
"Mon bébé kina ji na ?
Sautin kukan ta ya ba shi tabbacin tana jin sa runtse ido yayi yana jin ciwon kukan nata ya fahimci Fatima tana da zafin kishi sosai da sosai da shi a ganin sa ba kome ya kawo hakan ba illa tsananin son da take masa.
Ajiyar zuciya yayi daga ƙasan ran sa ya fara harhaɗo kalaman da zai rarrashe zuciyar ta take cike da ƙaunar sa.
****
Bayan Awa Ɗaya da Rabi:
Rarrashi ya rikiɗe ya koma hira mai cike da raha da ƙaunar juna daga ƙarshe ma suka koma video call kamar ba sa rabu ba kafin daga ƙarshe ya sake wani rarrashin kafin su yi Sallama da alƙawarin gobe za ta gan shi a vidieo call a dai-dai wannan lokacin
Zuciyoyin Su cike da nishaɗi da begen juna suka yi Sallama bayan sun aikawa da juna Sumba ta iska .
Sai bayan da ya sauƙe wayar ya lura da yadda dare ya shiga wajen shaɗaya da rabi na dare.
Yawo yayi da idanun sa a falon sai dai ko alamun wacce yake dubawa bai gani ba , haka kawai ya ji wani irin yanayi na bin jikin sa yana ganin rashin kyautawa kan abunda yayi musamman da ya tuno da cewa da fa wayar ta su ka sha hira shi da Fatima , "anya kana adalci ? Zuciyar sa ta ƙwanƙwashe shi.
Cikin rashin kuzari ya miƙe bayan ya kashe kayan kallon ya rufe ko'ina ya nufi ɗakin baccin su '
A hankali ya turo ƙofar cike da son kiyayewa kada ya tada su a baccin da yake hasashen suna tsaka da yin sa .
Da shigar sa yayi turus kafin ya ɗan yi duru-duru saboda ido huɗu da suka yi shi da Siyama wacce take zaune daga ƙasa ta tasa laptop a gaba da alama karatu take yi .
Murmushin da ta jefe shi da shi lokacin da take zare gilashin idanun ta bai taimaka ba ko kaɗan wajen rage masa yanayin da yake ji a dai-dai lokacin da shi kan sa ya gaza fahimtar ainashin wanne irin yanayi ne ? .
"Ya Fatima da Bébé ? Duk suna lahia kou.?
"Suna lafiya , ya amsa mata kafin ya zauna daga kan kujera ɗaya tal da take ɗakin yana ɗan sosa ƙeya .
"Siyama .
Ya ƙira sunan ta yana kallon ta .
Cikin nutsuwa ta ɗago kan ta ba tare da ta amsa ba
Da taimakon hasken ɗakin ya iya hango yadda launin idanun ta suka sauya su ka yi jaa kaɗan .
"Ba kiyi bacci ba har yanzou ?
Ya tambaye ta .
Wani irin murmushi mai ciwo tayi tana kawar da kan ta , muryar ta babu ƙarfi sosai ta ce " Ban yi bacci ba Biyamuradi ina jiran ka shiggo muyi Sallama.
"Siyama
Ya sake ƙiran sunan ta bai jira amsawar ta ba yace .
"Duk lokacin da kin ka ji bacci kiyi ko da ina gidan ko bana nan ba sai kin jira mun yi sallama ba...''
"Saboda me ? Ta katse shi da wata irin muryar da take tsakanin harshe da wuyan ta
Kallon sa tayi ta ga yadda ya ke duban ta da rauni a cikin idanun sa , kafin ta ɗora da cewa .
"Saboda baka sona ? Baka ƙamna ta ? Baka amre ni domin so ba ? Ni matar cushe ce gare ka ?
"Siya...
Da sauri ta katse shi lokacin da ruwan hawayen ta ke sauƙa yana ɗiga ta cigaba da cewa
"Laifi zuciya ta tayi a doumin ta so ka ? Ko kouwa ni nayi laifi da na kassa jumriya akan ƙamnar ka har dai nayi kafiya kan Amren ka ? Da ka ke gwadan rashin ƙamna a fili kake watsi da sha'anin da duk ya shafe ni ?
Tasowa yayi ya dawo gaban ta ya zauna yana jin girman laifin sa na masa lulluɓi tunda ya kai girman da har ta kai yau Siyama ta ɗaga Muryar ta .
Hannuwan ta da suka ɗau sanyi ya riƙe yana lalubo kalmomin da ya musu ajiya mai nisa da basa taso da kan su sai fa akan wacce aka yi ajiyar su a domin ta yau so yake ya ƙalato su ya yiwa Siyama kyautar su wataƙila sa wanke mata zuciya su samar mata da nutsuwa a cikin hakan babu laifi domin ita ma ta cancanta.
"viens chérie yaya ki ke faɗin hakka ? Me yassa za ki ce bani ƙamnar ki ? Bani ƙamnar