Showing 150001 words to 153000 words out of 411050 words
Chapter 51 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
Bi ya dunga yi yana ganin yadda suke ƙiran juna ita da number kusan kullum sai sun yi waya , " tun wajen wata guda da ya wuce , " ji yayi idanun sa na shirin kawo hawaye , a sarari ya furta ta yaudare ni , BATA SO NA BATA TAƁA SO NA BA ,"
Jefar da wayar yayi yana barin ɗakin cikin ran sa yana tunano irin baya-baya da take yi da shi a tun haɗuwar su , yadda take janye jiki daga mu'amala da shi , yadda baya ganin fara'ar ta , bata sakin jiki tayi magana da shi , bata ɗaukar sa da wani muhimmanci ,
ashe bata son shi ne , ashe tana da wanda take so suka yi soyayya mai girma da har ta kai su ga aikata zina , ashe shiyasa take son cikin jikin ta kamar ba shege bane , soyayyar uban cikin ne ta shafi ɗan , ashe son da take yiwa wannan mutumin ya wuce son da take yiwa ƴar cikin ta tare da ƴar uwar ta ?? Tunowa yayi da kalamar ta ta ƙarshe inda tace TANA SON SU SU DUKA ," ji yayi duk wani jijiyar da ta kafa so da ƙaunar ta cikin ran shi tana tsinkewa , son ta da ƙaunar ta suna mutuwa ,"
Bai san ina yake taka ƙafafun sa ba saboda yadda zuciyar sa ta shiga ruɗani , sai tsintar kan sa yayi a tsakiyar falon Baban su ,
Ɗago kan sa professor Mustapha Dilmari yayi ya dube ɗan nasa , tashin hankali da damuwar da ya hango a fuskar ɗan nasa ya sanya shi ajiye doguwar jaridar "daily trust" ɗin da ke hannun sa ," yace da shi
Doctor yaya yarinyar nan ta sauka lafiya ?
motsa bakin sa yayi maƙogoran sa na kai kawo , ya haɗa jimlar kalmar da ta tabbatu ta fito tun daga Ƙasan ruhin sa ,
TA MUTU
innalillahi wa innaa ilaihi raji'oon , ta rasu ,? Wajen haihuwar ? Allahu Akbar , yi sauri ka sanar da jama'a a zo ayi mata sutura , ina abun da ta haifa ko tare suka tafi ,? "
An mata sutura a chan asibitin kamar yadda aka saba yiwa ƴan gudun hijira ƴan uwan ta idan sun rasu ba'a jiran mutanen su ,"ma'aikatan asibiti tare da sauran Al'ummar musulmai suke sallatar su a wuce da su makwancin su ,,"
Daga haka ya miƙe ya bar mahaifin nasa yana jero addu'o'in da ake yiwa mamata ,
Bai jin yayi kuskure akan kalmar da ya furta ga mahaifin sa , ƙwarai ta MUTU a cikin zuciyar sa kamar yadda cikin kowanne daƙika ɗaya yake sake yakice ta tare da nesanta ta da duniyar sa nisa irin na har abada ,
Shi yayi ƙarya ga mahifin sa da ƴan uwan sa , ya wanke ta ya rufa mata bargon asiri tare da kyautata mata zato da kyakkyawar niyyah, yanzu da kome ya bayyana gare shi ya fahimci wacece ita , dan haka ya sake yin wata ƙaryar da yake fatan ta zama babbar ƙarya ta ƙarshe da zai yi a rayuwar sa yayi amfani da ƙaryar ta hanyar zare ta daga rayuwar duk wani da ya shafe shi tare da shafe babin ta cikin rayuwar duk wani nasa domin ita ɗin bata chanchanta ba ...
Shiru shiru Amne bata ga dawowar hamza ba da take tsumayen ganin sa tare da yakaka tayi ta ƙiran wayar sa shiru ba'a ɗauka
Ga kuma baby da take ta faman tsanyara kukan yunwa duk da cewa tun shigowar su ta ɗaura ruwan zafi ta wanke jaririyar tas ta sauya mata kaya tare da diaper a cikin kayayyakin ta da suka zo da su daga asibiti , amma daga lokacin da aka haife ta tun hantsi zuwa yanzu la'asar sakaliya dole jaririyar ta ji mummunar yunwa ,
Gefe guda ƙarin damuwar ta na ga Falmata wacce tun tana kuka ƙasa-ƙasa , zuwa yanzu kuka take riris tana ambaton sunan yakakar babu tsahirtawa , tayi rarrashin duniyar nan Falmata taƙi shiru , taƙi ci taƙi sha , sallah ma sai da tace ta tashi tayi addu'ar Allah ya sa yakaka na a halin lafiya sannan ta tashi tayi ,
Ganin dare na neman yi babu abun da zata bawa ƴar jaririyar nan ya sanya ta rufe kai ta nannaɗe jaririyar da kyau ta ɗau kuɗi mai ɗan yawa ta fita nemo mata abinda zata ciyar da ita da shi ," kasantuwar a kusa da kasuwa unguwar tasu take , dan haka bata sha wahala ba wurin samun madarar jarirai mai kyau tare da feeding bottle a ɗaya daga cikin shagunan da suke jikin kasuwa wanɗanda basu kai ga rufewa ba ta saya , ta tsallako titi zuwa gida,
Wurin da ta bar falmata nan ta tadda ta zaune kan ta haɗe da jikin bango ,
Bata bi ta kan ta ba kamar yadda falmatan ma bata nuna taji motsin ta ba , ta kwantar da jaririyar ta wanke feeding bottle ɗin ta haɗa mata madarar dai-dai yadda aka ka'idance da ruwan ɗumi , ta ɗan bar ta ta huce dai-dai yadda jariri zai iya sha ta ɗauke ta tayi bismillah , ta fara bata ,
Nan take kuwa ta kama bakin feeder tana jaa ,
Sannu sannu sai da ta sha fiye da rabi , bacci ya ɗauke ta ,
Ganin ta maida kan falmata bayan ta shinfiɗe jaririyar ,"
Tausayin falmatan ya tsarga mata , cikin ɗan zaman da tayi da yaran lokacin bikin zainab ta fahimci yadda yaran suka shaƙu da juna suke kuma ƙaunar juna tare da tattalin juna ,
Ɗan ƙaramin tsaki ta jaa lokacin da take ɗaukar wayar ta domin sake ƙiran Doctor Hamza ,
Ni ban san ina ya bar wayar ba haka , ina ta ƙira baya ɗauka ya bar mu cikin fargabar halin da yarinyar nan ke ciki bari na ƙira Rahima naji ko yana gidan ne ,"
Bugu ɗaya Rahima ta ɗauka ta ɗauka
Abnaty ina yayan ku ne ? yaya an san inda yarinyar nan ta tafi kuwa ?
Shiru Rahima tayi tana ƙoƙarin tsayar da ƙwallar idanun ta ,"
Yayan mu ya dawo tun ɗazu hankalin sa a tashe , ya shiga sashin sa ya kulle , sai yanzu da naje gurin Baba , yake sanar da ni wai ashe yakaka ɗin ta rasu ne wajen haihuwa ,"
Innalillahi wa inna ilahi raji'oon Amne ta ƙara da salati ,
Bata ce kome ba ta sauƙe wayar daga kunnen ta , tare da kai kallon ta ga falmata wacce tayi kasaƙe tana son fahimtar menene ,:
Muryar ta ƙasa tace Amne wai me Rahima tace ? Wani abu ya samu yakaka ko ? Amne Dan Allah kar ki ɓoye min ni da yakaka bama boyewa juna kome , yakaka ita ce kome na , ita ce mama na , baba na yaya ta kuma ƙawa ta meye ya same ta ? Dan Allah ku kaini na gan ta ,
ta furta hakan tana me sake fashewa da wani sabon kukan da yasa hawaye silmiyowa bisa ƙuncin ta , tana jin wani tsohon miƙi makamancin raunin da zuciyar Falmata ke ciki yana ɗanyencewa cikin nata ran , amsa kuwwar kalmai makamanta wannan da suka fito daga bakin Rahimar ta yana maimaituwa a kunnuwan ta ,"
Sai ta gaza rarrashin Falmatan .
Washegari
Bayan fitowar doctor Hamza daga masallacin sallar asubah kai tsaye sashin mahaifin sa ya shigo kamar yadda ya saba , kan shi a ƙasa suka gaisa da mahaifin sa wanda yake nazarin ɗan nasa ba tun yau ba ya fahimci akwai wata ɓoyayyar manufa a zuciyar ɗan nasa game da yarinyar ya bari ne yaga iya gudun ruwan sa , amma tundaga yadda ya ɗau komen su da muhimmanci ya fahimci yana da ra'ayi akan ɗayar su ,"
Tausayin sa ya ji mutuwar yarinya da irin birkicewar da yayi ya sashi fahimtar wataƙila ita zuciyar sa ke ra'ayi
Addu'a ya sake yi masa sannan ya ɗora da tambayar sa ina ƴar uwar ta ?
Nan yayi shiru ,
Kafin yace
Suna gidan Amne ita da jaririyar da uwar ta bari ,
Nan take fuskar professor ya sauya
Gidan Amina ?
Me kuma ya kai su gidan Amina ?
Na kai su ne wai dan ta kula da su musamman ma jaririyar .
Ita Amina MACE ɗin ce za'a bawa kulawa tare da tarbiyyar yara mata har biyu ? ? To ban amince ba maza idan gari ya gama haske kaje ka zo da su , tunda ka kawo yaran nan gidan nan ikon su ya bar hannun ka ya dawo ƙarƙashi na , ni nake da ikon kulawa da su , nima ina ƙwaɗayin samun ladan rikon marayu da marasa galihu , kan Ji na ko ?
Toh Baba
Ya amsa yana jin wani sabon tirniƙin ɓacin rai na taso masa sam sam baya son wani abu ya sake haɗa shi da kome ƙanƙantar abu wanda ya shafi yarinyar nan , daren jiya kwana yayi bai yi bacci ba saboda yadda ran sa yake ƙuna game da abun da yarinyar tayi masa , juyi ya dunga yi yana mamakin halin MACE ,
Shi a son ran sa ya bar su a chan wajen Amne ɗin lokaci lokaci yana zuwa yana kai mata abunda zasu buƙata domin a zahiri shi fatima da jaririyar ma bai son ganin su ," gani yake ita ma ƙanwar tata ta san kome tare suka haɗa baki , " shi yanzu ya bar ganin ƙanƙantar su tare da musu kallon matausaya ," ya tsinke akan lamarin MATA
Ba yadda ya iya haka ya shirya kafin ya wuce aiki yaje gidan Amnen inda ya tadda ta tana yiwa baby wanka jikin ta duk a sanyaye ta kwana da zancen mutuwar yakaka sosai yarinyar ta shiga ran ta saboda yanayin kamanni sosai da take da ƙanwar ta Rahima ,
Bai yadda ya ɗora idon sa kan jaririyar ba suka gaisa da Amne tana sake jajanta mutuwar yakaka tare da yi mata addu'a ta ɗora da tambayar sa aina aka yi jana'iza
Kaucewar tambayar yayi ta hanyar cewa ina ita ƙanwar tata ??
Tana wanka tun jiya take abu ɗaya ,"kuka ," kuma har zuwa yanzu bata kai ga sanin mutuwar ƴar uwar ta ta ba , ban ma san wanne irin hali zata iya shiga ba idan ta samu labari ," sai dai ka san hanyar da zaka bi ka kwantar mata da hankali kafin ka sanar mata da mutuwar nan
Cikin ƙagauta Hamza yace
Wane rarrashi Amne kowa ai zai mutu ki gaya mata kawai yayar ta mutu , kuma ki bata baby ta zo mu koma gida Baba ya ce na mayar su gida ...
Ƙarar faɗuwa da suka ji shi yasa Amne fitowa da gudu bayan ta shinfiɗe jaririyar ,
Doctor hamza ko gizau bai yi ba hasalima tun tsayuwar falmata a gun ya gan ta , yi yayi kamar bai gan ta ba , da hikimar sa na son fahimtar ko falmatan ta san kome da ya faru ?
Ganin yaƙi fitowa yasa Amne kwala masa ƙira ,"
Ka fito ka ga abun da yarinyar nan take yi , kar ita ma ta mutu ," tace da shi cikin ɗaga murya
Shi da kan sa ya tsorata ya kuma ji tausayin yarinyar lokacin da ya fahimci ciwon ta na asthma ne ya tashi , gaba ɗaya numfashin ta ya siƙe yana neman ɗaukewa bata cikin hayyacin ta ,
Da taimakon Allah da dabarun sa na likita , numfashin ta ya dawo ,
Zumbur ta miƙe zaune tare da kufcewa daga riƙon da Amne ta mata , lalube take tare da faɗin
Ina yaya daktan , ina kake yaya dakta , Dan Allah Dan Allah ka kai ni wajen Yakaka , naji kun ce wai Ta mutu , wai yaya ta ta mutu , ai wasa kake ko ? Yakaka tana gida ko ? Yaya za'a yi yakaka ta mutu ta bar ni ? Alhalin ta san bani da kowa sai ita , bani da ƙarfi kun gani fa ni miskiniya ce Dan Allah kar ku min irin wannan wasan ,"
Yaya dakta ka min magana mana , tace haka lokacin da ta samu nasarar chafko rigar sa ta rike tamau ,
Yaya dakta Dan Allah
Ta sake cewa muryar ta tana wani irin harɗewa ,
Ji yayi wani mugun tausayin ta ya rufe shi yaji ina ma bai ambaci kalmar mutuwa ba , cikin ƙwarar makafin idanun ta da suks firfito suka sauya launi tamkar ba nata ba yake iya hango irin firgici tare da azabar da zuciyar ta ke ciki ,
Kukan da baby ta tsanyara shi yasa ta yunƙura da gudu tayi sashin da taji tashin muryar jaririyar , kafin su taro ta har ta faɗa ɗakin kasantuwar ɗakin da ɗan zurfi ya sa ta faɗa ciki sakamakon jefa ƙafar da tayi nan take ta gurɗe ta tafi ta faɗi , bata haƙura ba ta rarrafa da gudu sashin da take jin kukan jaririyar
dai-dai da shigowar su
da lalube ta ɗauke ta ta riƙe ta gam a cikin jikin ta , "
Idan ni bakwa tausayi na Dan Allah ku ji tausayin jaririyar nan ku kai ta wajen maman ta ni da yakaka mun yi Alƙawari zamu haife ta mu rene ta mu biyu mu bata kulawa mu biyu ,
Meyasa yanzu zaku ce Yakaka ta mutu ? WAYE NI DA BABY IDAN BA YAKAKA ? WAYE ZAI KULA DA MU ?
ALLAH shine zai kula da ku Fatima , Amne ta ce tana sharar ƙwallar tausayin yaran , shi da kan sa hamza idanun sa sun kaɗa , tsanar yakaka na sake taso masa ,"
Wani irin kuka falmata take har tana tsuma ,"
Baba , Mama , yaana , Bulama Yakaka duk kun mutu ? Kun mutu kun bar ni ni kaɗai ? Ni meyasa ban mutu ba nima ??
Kiyi haƙuri Fatimah kowanne me rai zai mutu lokacin sa kowa yake jira , kiyi musu addu' a
Kawo baby na shirya ta ku tafi ," Amne ta furta hakan tana mai ƙoƙarin amsar jaririyar ,
Wani irin janyewa Falmata tayi da ƙarfi ta sake ƙanƙame yarinyar ,"
Ki bar min ita kar kowa ya taɓa ta bani da kome bani da kowa sai ita , ita ma haka , ita ce jini na kaɗai a duniya ita ce ƴar uwa ta madadin dangina gaba ɗaya , ita ce HASKEN da zan iya gani da ido na , kar kowa ya taɓa ta , kar kowa ya taɓa ta , kar kowa ya taɓa ta , ta dunga maimaitawa kamar bata cikin hankalin ta ,
Da ƙyar ta yadda Amne ta sanyawa babyn diaper tare da kayan sanyi tana riƙe a hannun ta ,
Wani irin yanayi take ciki , kamar ɗaukewar ruwan sama hawayen fuskar ta suka tsaya , ta kuma haɗe labban ta wuri guda bata cewa ƙala , sai ajiyar zuciya da take akai akai , lokaci zuwa lokaci laɓɓan ta na motsawa ,"
A haka suka fito Amne ta kama ta ta sanyata a mota tana rungume da jaririyar da ruwan ɗumi ya ratsa ta take ta baccin ta kasantuwar tun farar safe Amne ta cika mata ciki taf da madara ,"
Motar su tana tsayuwa Rahima wacce daman tana dakon jiran zuwan su , ta fito da gudun ta tana kuka ta rungume Falmata ,
Wacce take ƙiƙam bata kuka kuma bata ce ƙala ba , "
Sashin Baba ya kai ta , ta ɗurkusa guiwar ta biyu a ƙasa tana rungume da baby ,
Muryar ta chan ciki ta gaishe shi kan ta a sunkuye , ta'aziyya yayi mata kafin ya ɗora mata da nasihu , " a ƙarshe ya ɗora da shaida mata cewa ",Hajja mai wurya," dattijuwar dake yi masa girki ita zata cigaba da kulawa da jaririyar har zuwa lokacin da zata yi ƙwarai , bata ce kome ba kan ta a ƙasa ,
Rahima ƙarbo jaririya ki kawo ta nayi mata huɗubha , wanne suna kike so a sa mata ??
Zare jaririyar Rahima tayi ta miƙewa baban su ,"
Ya sake maimaitawa wanne suna kike son a sa mata ,
YAKAKA ," tace da shi a taƙaice
Jimm yayi yana mai maida duban sa ga hamza , "
Wannan ba suna mai asali bane ki faɗi wani sunan Fatima ," Baba yace da ita ,"
YAKAKA , ta sake maimaitawa hawaye na kwararowa daga idanun ta ,
Shikenan za'a mata laƙabi da Yakaka, .
a take yayi wa jaririya huɗubha ya miƙawa rahima ta mayar ta hannun yakaka ,"
Suka miƙe suna barin falon ,
Abuja Nigeria
Ƙarfe shidda na yamma su Yakaka suka samu isa garin Abuja ," gajiya da ciwon kai da ciwon ciki irin na ssbuwar haihuwa, zazzabi tare da dumuwar da take cinkushe cikin zuciyar Yakaka suka haɗu suka yi ligi-ligi da ita , , ta zama marar lafiya sosai sai numfarfashi take , bata ko iya buɗe idanun ta sosai ,
Unguwar "Gwarimpsamy baby tayiwa tsinke , tana shiga unguwar bata yi nisa ba tayi parking a bakin wani ɗan madai-daicin gida mai ɗauke da ƙaramar ƙofa da ɗan madaidaiciyar ƙofar shigar da mota da mota ɗaya zata iya shigewa ," fita tayi ta sanya ɗan mukulli ta buɗe ƴar ƙaramar ƙofar ta shiga ta ciki ta buɗo ƴar babbar ta dawo ta tada motar tare da sanya shigar da motar cikin gidan , bayan ta kashe motar ta zagayo gami da bude ƙofar bangaren da yakaka take ta taimaka mata ta fito , "
Da kyar ta iya sanyo ƙafafun ta waje sakamakon