Showing 210001 words to 213000 words out of 411050 words
Chapter 71 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
amma domin Allah a ɗau hakan a matsayin kaddara a cigaba da godewa Allah da ya sa har ta dawo gida lafiya ba tare da wani mummunan lamari ya auku gareta ba ,
Babu kome baiwar Allah mun gode ƙwarai Allah ya saka miki da Alheri kan yadda kika kula da ita , kema Allah ya duba miki naki iyali , Allah ya ƙara mana yawaitar irin ku cikin Al'umma masu taimako domin Allah .
Cikin jin daɗi Malama Maryam ta amsa da Ameen .
Ƴar boyayyar Ajiyar zuciya Yakaka ta sauƙe ganin yadda Alamu ke bayyanuwa yadda take zaton tsanantar lamarin nata duk bai kai haka ba ,
A hankali ta ɗora idanun ta kan Rahima wacce ita ma kallon ta take , suka haɗa ido kafin Rahimar tayi mata guntun murmushi marar sauti .
A yanzu hankalin ta ya kwanta ta kuma amince Yakaka ce da gaske ba Fatalwa ba .
Ita ma ta mayar mata da martanin Murmushin , ƙaunar junan su tamkar a jinin su take , duk da tarin abubuwan ƙi da Rahima ta san yakaka ta aikata su a yanzu , hakan bai sa ta ji kamar ta tsane ta ba .
Kalaman Prof ya sa Yakaka sake nutsuwa ta mayar da hankalin ta kan shi ,
Bisa ga doron kuskuren da kika riga kika aikata su Abubuwa biyu zuwa uku sun faru ,
Na farko labarin mutuwar ki , a gare mu tuntuni kin mutu tundaga ranar da kika gudu kika bar 'yar ki .
Na biyu shine zuwan da mutumin da ya ƙira kan sa mijin ki uban abunda kika haifa yayi ,
Na ukun su shine tafiyar sa da yayi da 'yar sa tare da auren ƙanwar ki a lokaci guda da ni da kaina nayi waliccin auren a nan falon nan na bada auren ƙanwar ki Fatima ga mijin ta uban 'yar ki na kuma ɗanka masa ita suka tafi tare ƙasar su niger tare da rikiyar Hajja me wurya .
Da ace Yakaka ta taɓa sanin yadda ciwon Ajali yake da babu shakka zata iya cewa shine ya dirar mata a lokacin saboda wani irin abu me kaifi da ta ji ya taso mata daga ƙasan mara ya zo ƙirjin ta ya tokare ta ,
Muryar ta a shiɗe ta wufto kalaman da suke kan harshen ta ta watso su ga Prof idanun ta tsaye ƙem a kan fuskar sa
Falmata ce tayi aure da Baban Mama ?
Da sake tabbatarwa Prof ya amsa mata da
Haka kalamaina ke nufi.
Abunda take jin ne ya watsu a cikin jikinta ya barbazu tamkar an watsa mata wuta kafin ya sake dunƙulewa a maƙogoran ta ya tsaya ,
Yaa Allah , Yaa Allah , Allah na tuba kar laifin da na aikata ya shafi Falmata , Allah ka dawo min da Falmata , Allah ka...
Mul-mulan hawayen da suka fara ƙwaranyowa daga idanun ta tare da fashewar ƙullutun da yake wuyan ta shi ya hana ta cigaba da magana illa kukan da ta fashe da shi marar ƙarfin sauti ,
Kuka ne irin na mutumin da ya ke a halin ɗimuwa tare da nadama kuka ne irin na ba yadda zan yi , kukan neman taimako ,
Baki ɗayan su irin kukan da take ya taɓa zukatan su ,
Musamman Malama Maryam da Rahima ,
A bangaren Prof duk da cewa ya ji tausayin ta amma ya bar ta da hakan a matsayin sakamakon laifin da ta aikata .
A hankali Rahima ta ƙarasa inda take ta sanya hannu ta dafa ta ,
Kiyi hakuri Yakaka tashi mu shiga cikin gida , ki bar kuka hakan ,
Miƙewa tayi ta fara taku ba tare da ta cewa kowa kome ba ta wuce ,
Malama Maryam ta rissina ta yiwa Prof sallama tare da shaida masa gobe da sassafe zata kama hanyar komawa gida
Godiya ya sake yi mata , suka rabu suna bin juna da kalaman fatan alheri .
Bayan fitar su bai jinkirta ba ya ɗau wayar sa ya nemo lambobin wayar Doctor Hamza ,
Fitowar sa kenan daga ICU inda ya jonawa marar lafiyar da aka ƙira shi domin ita wasu na'urai ya kuma sake duba ta sosai kasancewar ya ƙware sosai wajen gano tare da bada taimako akan cutar da take damun ta na dajin bakin mahaifa ,
Mutanen da suke ƴan uwa ga marar lafiyar suka taso caa su kusan rai shidda suna tambayar sa yanayin jikin nata ,
Nan dai ya kwantar musu da hankali tare da sanar musu da insha Allah zasu yi bakin ƙoƙarin su, su kuma su taya su da addu'a ya ratsa su ya wuce ,
Ya ji lokacin da ɗaya daga cikin su tace tunda mun ji yanayin da take ciki sai Maman Bulama ta koma gida ta yi girki ta kawo kuma ta haɗo wasu kayan da za'a iya buƙata ,
Maa ki mata bayani yadda zata gane sosai dan ke ce kika iya maganar su ta kurame ,
Da hannu suka yafito wata mata wacce take zaune a ƙasa daga gefe .
Da sauri ta taso ta ɗan russuna daga gefe ,
Maa tayi mata bayani da hannu cikin maganar kurame ,
Cikin sauri take gyaɗa kai alamun tana fahimta,
Naira ɗari biyu ta zaro daga jaka ta miƙa mata , ta sanya hanu biyu ta karɓa ,
Ta mata alamar cewa kuɗin mota ne
Ita ma ta gyaɗa kai kan cewa ta gane
Har ta juya ta sake dawowa ,
Tayi musu alamar tambaya tana nuna ɗakin da marar lafiyar ke ciki . Fuskar ta na bayyana Alhini .
Amsa maa ta bata da hannu .
Ta juya ta kama hanyar barin asibitin ,
Doctor hamza wanda ya gama amsa wayar prof da yake sanar da shi kan lalle ya zo yana son ganin sa daga zarar ya kammala abunda yake a asibitin ,
Ya mayar da wayar sa aljihu tare da juyawa da zummar komawa cikin ofishin abokin aikin sa da shi yayi ƙiran sa domin suyi sallama ya kuma gama yi masa bayani akan irin matakin da yakamata a ɗaura marar lafiya akai zuwa gwaje-gwajen da ya dace ayi mata
Ƙiris ya rage ya ci karo da matar da ta taho tana ta sauri ,
sannu Hajiya ,
Yace yana kaucewa yin karon su , a fisge ya dubi fuskar ta lokacin da take gota shi ba tare da ta amsa ban hakurin da yayi mata ba
Cak ! Ya tsaya , lokacin da kamannin ta suka yi masa yanayi da na wata da ya sani waye ?
khaalty Rahima .
Juyowa yayi da sauri da son sake ganin fuskar ta sosai , sai dai ta riga tayi nisa sai tashin hijabin ta ya ke iya gani wanda ya cika da iska saboda saurin da take zabgawa .
*****
Daga bakin ƙofar falon Yakaka ta zame ta zauna , tana wani irin kuka ciki-ciki , a halin da take jin zuciyar ta a ciki babu abunda take fata irin kome da ta ji ace a mafarki ne , bacci take yi ta yi wannan mummunan mafarkin , ta gwammaci ace ta buɗi ido ta ga kan ta a gidan samy baby , kai ta amince kome ya faru da ita , da dai dawowar ta Maiduguri ta tarar da wannan mummunan labarin da ya kassara duk wani guntun ɗoki da mararin sake ganin wani nata a duniya ,
Aure , wai Aure da Falmata da mutumin da ya yaudare ta ya cutar da ita , ya lalata mata rayuwa tare da bar mata taɓon da har abada ba zai gogu ba , ?
To wai ma ina ya tafi mata da ƙanwar ta ? Kamar ta ji prof yace ya tafi da ita Ina ya kai ta ? Mutumin da ya saba yin manyan ƙarya da yaudara irin haka kome ma zai iya yi , ina suke ? Kai zata iya barin kome ya wuce ya zama ba kome ba amma banda zaman Falmata tare da wannan mayaudarin domin shi ɗin ai guba ne, dafin sa kuma ya fi na maja-ciki in yai sara .
Ɗaga sautin kukan ta tayi tunowa da ta yi da miskinancin ƙanwar ta , Wanne irin hali ta kasance a ciki lokacin da labarin mutuwar da aka ce tayi ya riske ta ? Wataƙila tundaga lokacin bata sake farin-ciki ba , yaya rayuwa ta kasance mata bayan bata nan ? Wanne irin zama take da wannan macucin mayaudarin ?
ƙwarai ta gaza a wajen bada kariya ga Falmata maimakon haka ma ta zama sila na faɗawar ta a hatsari , ƙwarai hatsari mana aure da mutumin da ba'a kai ga sanin asalin sa na haƙiƙa ba ,
A hankali Hajja ta murɗa makulli ta fito daga ɗakin da ta shige " jin tashin muryoyin su Rahima da Malama Maryam da suke faman rarrashin Yakaka , da sautin kukan ta ya karaɗe falon
Oh ni Hauwa'u naga ta kaina ! yanzu ke 'yar nan me ya miki zafi haka a duniyar nan da zaki zo ki faɗi a nan shakwaɓ , kina rusa ihu ya Amaryar da Angon ta ya mutu daren buɗan kai ?
Ganin babu wanda ya kula ta ya sa ta samu waje ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon , ta cigaba da cewa ,
Rahimatu , ince ko dai an fitar da Fatalwar ? Kar sai mutum yana ƙailula ya farka ya gan ta daf da kan sa .
Hajja dagaske Yayar Falmata ce ta dawo , Mamar Mama ashe bata mutu ba Hajja ki taya mu Murna ,
A kaikace ta dube su tana daga inda take zaune , ta gyaɗa kai .
Toh , ah lalle kun kaima Barka , 'Yar nan sannu da bayyana , kuma tsawon lokacin nan da kika shafe bakya nan dandi kike ko kuwa Da'awa ? oh duniya me abun mamaki .
Malama Maryam da take zaton Hajja ƴar uwa ce ga su Yakaka jin abunda Hajja tace ya sa tayi saurin amsawa a ƙoƙarin ta na son ganin ta wanke Yakaka tace ,
Hajiya , Yakaka yarinyar kirki ce tsawon shekarun nan ta yi su ne wajen neman ilmi , bata aikata wasu munanan aiyuka ba .
Ah to babu laifi ilmi ai abun so ne abun nema , shiyasa ma wani mawaƙi ya ƙira jahili da dattijon biri mai ɗan kwale .
Ita kuwa Falmata ,uwarɗakina duk biyu ta haɗa ga neman ilmi ga bautar ubangiji ,bautar aure , ta zama gizako katafila a gidan Babban soja , Fatima uwar Mama mata a gidan Babban Mutum ,Allah dai ya dawo mana da ku lafiya uwarɗakina .
Chak!
Yakaka ta tsayar da kukan ta , ta miƙe cikin rashin kuzari ta dawo gaban Hajja ta zauna ,
Dan Allah ki bani labarin Falmata tare da Mama , ki faɗa min a wanne hali suke ciki ? Waye yake kula da Falmata a halin Larurar ta ? Kince Falmata ta shiga makaranta ? Ta koyi karatun addini ?
Ta ƙasan ido hajja take duban Yakaka ,
Falmata da Mama suna nan sumul-luwai ƙalau , ƙarƙashin kulawar jigon da ya tallafi rayuwar su , sai girma suke yi suna bunƙasa , karatu arabi da boko kullum cikin yin sa suke , yanzu haka ma yau kwanakin su shidda da tafiya ƙasar Amurka can turai ince ko kina jin sunan ƙasar ?
Hawayen dake fuskar ta basu bushe ba ta kamar yadda bata janye rinannun idanun ta daga kan fuskar Hajja ba , tace
Falmata bata kasance ba cikin damuwa ? Bata shan wahalar kome , babu me zaluntar ta ko cin zarafin ta ?
Buɗe baki Hajja tayi da sigar mamaki
Ah kinji min kiɗifi ? To wa kuwa zai zalince ta tana tare da mijinta adali gamjigo , wacce damuwa zata kasance a ciki bayan yana kyautayin ta tare da kyautatawa , ke 'yar nan raba mu da mugun fata ,
Ɗan karyar da kai Yakaka tayi fuskar ta ta ɗan washe kaɗan daga damuwar da take bayyane ,
Falmata ta girma sosai ko Hajja ?
Ɗan tsinken tsintsiyar da hajja ta ɗauka a ƙasa ta kai bakin ta tana saƙace hakori ,
Idan kika ce girma ma ai kin ɓata bakin ki , ta cika tayi fam , ɓul-ɓul da ita kamar kazar gidan gona , ta fiki kome-da-kome , 'yar nan hutun gidan miji fa aka ce miki ?
Ƴar ajiyar zuciya Yakaka ta sauƙe tana Miƙewa tsaye , kaso biyar cikin ɗari na daga halin da ta tsinci kan ta ciki ya sauƙa ,duk da cewa baƙin-cikin da yayi mata tsaye a rai yana nan bai gusa ba amma jin lafiyar su ya rage mata matsananciyar damuwar da ta tsincin kan ta a ciki dalilin rashin ganin su ,
Rahima ki ba mu masauƙi ni da Ummi .
Ta furta hakan tana ɗora ganin ta ga Rahima ,
To Yakaka Bismillah ku shigo .
Da kallo Hajja ta bi su tana nazari , duk da cewa ta ji daɗin dawowar Yakaka cikin ran ta , amma bata so zuwan nata a dai-dai wannan lokacin ba domin ko kusa Allah ya sani baza ta so rabuwar Falmata da Youssouf ba wanda ita Hajja ta riga ta san ko wanene Youssouf Abdul-azizou Baskore ,
ta san matsayin sa na Yarima ɗan sarki da kasancewar sa Babban soja. Ta san abubuwa masu ɗan yawa akan sa wanda tsawon lokaci ta ɗauka tana bincike a kan sa sannu-sannu batare da shi kan sa ya sani ba , ta kuma cigaba da taya shi boye ko shi wanene agare su ita da Falmata duk da cewa ita ta sani , abunda take da yaƙini akan sa shine rana na nan zuwa da zai bayyana kan sa da kan sa .
A ganin ta Youssouf yafi dacewa da Falmata , sannan muddin aka raba auren su a wannan gaɓar an cutar da Falmata cuta kuwa me tarin yawa duba da yadda ta rungumi Mama ba tare da ta taɓa cin moriyar auren ba ko na lokaci guda tsawon shekun tayi ta yi su ne wajen kula da Mama da hidimar ta da jinyar ta ,
duk kuwa da miskinancin ta , karon farko yakama ta samu tubarrakin da ke cikin aure sannan kuma Yakaka ta kauda kai ta haƙurewa Falmata Youssouf su cigaba da zaman auren su idan ya so ita ta nemi wani mijin ta aura ,
Wannan dalilin ya sa Hajja ta ƙudurci niyyar toshe duk wata hanya da Yakaka zata iya bi ta iya raunata auren Falmata duk kuwa da cewa bata hango alamun hakan daga gareta ba domin ko Youssouf ɗin bata ji ta gwada ambatar sa ba , amma ko ma dai menene dole ta bada kariya ga auren Yarima Youssouf da Musaƙa Falmata.
Washington DC
Sauƙar tsakar dare jirgin su ya yi a Harabar tashi da sauƙar jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa dake Washington DC, ( Ronald Reagan Washington National Airport )
Muryar chief flight attendant da ta zagaya cikin jirgin shi ya tada Falmata daga baccin da ya ɗan dauke ta ,
Good evening Ladies and gentlemen we have landed at DCA airport in Washington DC, where the local time is 2 :30 and the temperature is 6°. We hope you have enjoyed your flight with Turkish Airlines this evening and wish you a very safe journey to your final destination .
Bonsoir Mesdames et Messieurs, nous avons atterri à l'aéroport DCA de Washington DC, où l'heure locale est de 2h30 et la température de 6 °. Nous espérons que vous avez apprécié votre vol avec Turkish Airlines ce soir et nous vous souhaitons un voyage très sûr jusqu'à votre destination finale .
matsanancin sanyin da ya ratsa ƙasusuwan Falmata lokacin da suke tako matakalar jirgin a yayin fitowa da bata taɓa jin makamancin sa ba , shi ya sa ta sake shigewa cikin jikin youssouf da yake ɗauke da Mama bisa kafaɗar sa wacce take baccin ta naɗe cikin nannauyan bargo .
Sake kusantata da jikin sa yayi , yana gyara kwanciyar Mama , ya ce
il fait extrêmement froid ( yanayin da akwai tsananin sanyi )
Bayan sun bi duk tsare-tsaren da yake dole a yi su a airport yayin da aka shiga ƙasar Amurka a farko, kama daga kan yin hoton yatsu zuwa hoton fuska da sauran su , zuwa lokacin da jakankunan su suka zo hannun su
Youssouf ya ɗau Babbar jakar kayan su ba domin ya so ba ya danƙawa Falmata Ƙananun jakankunan guda biyu a hannun ta da basu wani cika nawi ba, ƴar tafiya kaɗan suka yi suka samu wajen zama a cikin airport ɗin,
Cikin sauri ya buɗe jakar kayan sa bayan ya ɗora mama a kan ƙafafun sa wacce ta farka tana ta kalle-kallen baƙon gurin da haske ya wadata shi tamkar tsakar rana.
Babbar rigar sanyin sa ya zaro daga ciki jakar shi doguwa ce har ƙauri mai buɗaɗɗan gaba da turawan ƙasar Amurka ke ƙiran ta ( tribal oversized Cardigan sweater )
Fatima sa rigar sanyi , kadda hunturu shi yi miki lahani ,
Ya furta hakan lokacin da ya zagaya mata rigar da jikin ta ya taya ta sawa , hijabin kan ta ya gyara mata , ya zarce da riko hannuwanta biyu da suka ɗau sanyi , ya haɗa tafukan su waje ɗaya , bayan ya kusanci jikin ta sosai ,
Tsananin sanyin ya yi mata yawa da ya sa take jin sa har cikin cikin ta , jikin ta sai karkarwar yake , idanun ta da basu cika lafiya ba suka fara tara ruwan hawaye ,
Lura da hakan da youssouf yayi ya sanya shi rankwafo da kan sa saitin kunnuwan ta ,
Fatima na biɗo miki , café kafin zouwan notre prochain vol ? ( kafin zuwan jirgin mu na gaba ? )
Muryar ta na ɗan karkarwa tace
Har yanzu zamu sake tafiya wani waje ? Akwai sanyi dayawa anan , bana son sanyi ina da cutar wahalar numfashi .
Je sais Fatima que vous allez passer à notre destination finale d'ici 1 heure , ( Na sani Fatima zamu tafi zuwa matsayar mu nan da awa guda )
Shiru tayi ta sunkui da kai .
Hannun sa ya kai ya ƙarasa jawo