Showing 75001 words to 78000 words out of 411050 words
Chapter 26 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
Cikin sanyin jiki falmata ta kai cinyar kazar bakin ta ta gutsuri kaɗan tana taunawa ," zaƙin kayayyakin ɗanɗano irin na alfarma tare da zaƙin naman kazar suka haɗu suka sa kunnen falmata motsi har bata san lokacin da ta cinye wacce ɗan liti ya bata ba ,
tana tanɗe baki , ɗan liti wanda suke kus-kus da wannan ɗan tsurut ɗin mutumin shi ya lura da ita ya sake fisgo ɗaya cinyar ya ɗangwala mata a hannu ,"
ungo maza cinye har ƙashin ka tauna ka haɗiye , yau ta shiga ranakun tarihi a wurin ka ɗan kachallari ,"
Miƙewa ɗan liti yayi bayan sun gama kitsa abun da suka kitsa ,"
Ɗan kachallari ni zan ɗan je na dawo nan kusa ka jira...
Koh kafin ya ƙarasa abun da yake nufin cewa falmata ta miƙe zuruf ta dangwarar da sauran naman hannun ta '',
Ah ah mu tafi tare nima zan bika ,"
Haɗa ido ɗan liti da wannan mutumin suka yi , mutumin ya yiwa ɗan liti alama da ido akan ya tafi kawai zasu yi waya ,"
Saɗaf-saɗaf ɗan liti ya fita ya jaa musu kofar wanda ƙarar rufe kofar ya sa falmata wacce take tsaye tana jiran amsar ɗan liti ta farga da barin ɗan liti wajen ,"
Kuka ta sa tare da fara taku tana nufar hanyar da ta ji motsin rufowar kofar da ɗan liti yayi lokaci ɗaya tana jera kiran sunan ɗan litin ,"
Dariya ta ji mutumin ya kwashe da ita kafin ta ji ya fara tahowa inda take yana cewa haba ɗan kyakkyawan yaro kachalla menene abun kuka yi shiru yanzu ɗan liti zai dawo aiken sa nayi , kafin ya dawo zo muyi wasa ,"kafin ta ankara ta ji ya sure ta sama yana cewa ," A ɗaga sama anyi wa wada kwace 😂 ,"
Na so na baku ya fi haka , sai dai yawan cewa kuna jira da kuke yi , yasa na dakata anan kuyi manage da wannan sai mun hadu a shafi na gaba cikin yardar Ubangiji,"
A kan karo mutunci
#umm'muaz
#vote
#comments
#share with your Family and friends[10/3, 2:42 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: *© Fikrah Writers Association*
*MAFARI*
(hargitsin rayuwa)
*Umm"mu'az*
*18*
Tuƙuru ɗan tsamurmurin mutumin nan yake son danne falmata , sai dai lamarin ya faskara domin daga ya samu nasarar cillata kan gadon kafin yayi wani yunƙuri ta zabura ta mike , babu abun da ya fi fusata shi da har ya kai shi ga danna mata cizo a kafaɗa irin ihun da ta buɗe maƙogoro tana yi tun karfin ta , wanda hakan ba karamin tada masa da hankali yayi ba sanin da yayi matar sa tana nan a sashin ta da yake maƙotan nasa , zata iya jin ihun falmata kuma duk irin manyan alfashan da yake aikatawa matar tasa bata kai ga sanin wannan mafi muni daga cikin su ba watau ,"luwaɗi," baya kuma son ta sani domin yana matuƙar son ta bai haɗa ta da kowacce mace ba cikin rayuwar sa ita take biya masa bukatar sa uwa uba ita ce silar arzikin sa tare da bazar ta yake taka rawa ," neman yara maza da basu kai ga balaga ba da yake yi a duk daren lahadi wayewar litinin wani sirri ne cikin rayuwar sa ,"
Dan haka a wannan karon cikin hakin da gajiyar kokawar da yake yi ya haifar masa , gami da tsabar mugunta ya ɗaga falmata a karo na takwas ya maka ta da kan katifar gami da sanya hannun sa ya danne mata baki , ya fara ƙokarin zare mata bujen ta da ɗaya hannun ,"
Bai ankara ba yaji ta gantsara masa wani fitinannen cizo a ɗan yatsan sa babba , wanda hakan ya sa shi sakin wani ihun azaba jin tana yunkurin gutsire mishi ɗan yatsa ,"
Da ɗaya hannun sa yayi amfani wajen kai mata maruka da duka ta ko'ina amma falmata ko gizau taƙi sakin ɗan yatsan da zuwa yanzu take jin gishiri-gishiri a bakin ta da ta tabbatar jinin sa ne ," ƙara nutsa haƙoran ta tayi da ya sanya shi ba shiri ya daina dukan ta ya koma roko cikin kuka akan ta sakar masa yatsa ,"
Bata sakar masa da yatsan ba sai da ta tabbatar ta jikkata shi ta inda ko ta sake shi jinyar raunin da tayi masa zai fara sannan ta sakar masa yatsan ta miƙe da sauri tana tofar da jinin da ya zuba mata cikin baki,"
Tana sakin sa ya tashi da gudu ya buɗe kofar banɗaki da yake cikin ɗakin ,'
Tana jin tashin muryar sa tare da ihu lokacin da ya buɗe fanfo yana wanke yatsan ,"
Bin bango ta fara yi da lalube tana neman hanyar fita duk kayan jikin ta sun yamutse , tsumman da take ɗaure kirjin ta da shi ya zazzago wanda hakan ya bawa kirjin ta damar tasowa ,
Sai dai duk yadda ta kai ga lalubawa ta gaza gano kofar bare ta buɗe ta sai kewayawa take yi cikin hawayen tausayin kai da take yi ," makanta mutuwar tsaye ,"
Ido jawur ya fito ya tsaya ta bayan ta yana kallon ta cikin ran sa yana aiyana irin azabar da zai ganawa yaron nan a daren yau ,"
Cigaba yayi da naɗe hannun sa da Bandage yana kallon yadda take ta laluben bango , chak ya tsaya da abun da yake lokacin da idanun sa suka fara bayyana masa ainahin surar ta ta ƴa mace ,'
Sosai ya ƙura mata ido yana kare mata kallo daga sama har ƙasa domin tabbatarwa ,"
Wata chafka yayi mata tare da haɗa ta da bango yana mai ɗaura hannayen sa akan kirjin ta ,
Zabura tayi ta angaje shi baya,
Dan ubanki daman ke mace ce ??
Shine aka kawo min ke a matsayin namiji ??
Kika bani wahala irin wannan har da yi min rauni ? ashe ma ungulu da kan zabo ce ? Me zanyi da macen titi ? Kuma ma ƙwaila ?
Dan uban ki yau zaki yabawa aya zaƙin ta , sai na wassafa ki ta yadda gaba baza ki sake yadda ayi haɗin baki da ke ba , ƴar yarinya da ke amma har kin san ta kan bariki , kin san yadda ake maguɗi ,
Bugun kofar falon da aka Fara yi da karfi shi ya sa shi dakatawa da maganar da yake yi ,tare da yin kasaƙe domin sauraro , ai kuwa ya tsinkayo muryar matar sa tana danna masa kira tare da cigaba da bugun kofar , wani irin zillo yayi cikin taraddadin riskar falmata da zata yi cikin ɗakin sa ,'
Diri-diri yayi yana neman abun yi ba tare da ya lura da falmata wacce ta fara kokarin kintsa kanta ta cikin shigar ta na maza ba,
Bugun yana tsananta tare da ƙarin fargabar sa juyowa yayi da nufin chafkar falmata ya tura ta cikin wardrobe Ya kulle domin ya san muddin matar sa tayi ido hudu da budurwa a ɗaƙin sa da daren nan kome zai faɗa mata baza ta yadda ba , bai kuma san wanne irin mataki zata ɗauka akan sa ba , da ya san ba mai sauki bane domin ya san kalar kishin ta na masifa dan haka ya gama yanke shawarar ko ta halin ƙaƙa sai ya rufawa kan sa asiri ko da kuwa zai kashe falmata ne,
Sai dai ga mamakin sa shirye ya ga falmatan tsaf yaro namiji kamar dai yadda ɗan liti ya kawo masa ita , wanda ya tabbatar a kallo ɗaya baza'a taba gane falmata ƴar budurwa bace ,
Wani ɗan sanyin daɗi ya ji cikin ransa ,
Dan haka ya matso kusa da falmatan
Dan uban ki ga mata ta ta zo tana buga min kofa , idan kika yadda kika yi wani abun da ya sa ta gane ke mace ce sai na kashe ki kin ji ko baki ji ba ??
Cikin sauri falmata take gyaɗa kan ta tana gwalalo ido jin kalmar kisa daga bakin sa wanda azabar da ya gana mata a cikin mintuna da suke ƙasa da talatin ya sa ta tabbatar tsaf zai iya sheƙe ta har lahira ,"
Ungo nan ya watso mata kayan sa masu datti da ya ciro su daga loƙo ,
ki riƙe su a matsayin garƙuwar ki da zata fidda ki gidan nan lafiya
Da gudu ya fita ya buɗewa matar sa da take tsaye daga bakin kofa tana ƙuta , tare da mamakin meye yake yi haka a ciki da bai jin bugun kofa kuma ta kira wayar sa bai ɗauka ba , ita ba kome ya kawo ta ba illah ihun da ta tsinkayo daga sashin nasa ," ta ɗaga hannu da nufin sake buga kofar ,karaf ya buɗo kofar
Yanayin fuskar sa kawai ta duba ta san ba lafiya ba , lafiya kuwa baban sadiq?
ta tambaye shi ,
Subahananlahi ta furta hakan tana mai riko hannun sa da ta gani naɗe da bandage kafin ta ja shi ciki tana tambayar sa cikin tashin hankali akan meye ya same shi , ' shi kuwa sai faman yamutsa fuska yake cikin alamun nuna jin zafin ciwon ,"
Kwantar da hankalin ki my dear ɗan ciwo na ji da wuƙa ,ya furta hakan yana me satar kallon kofar ɗakin sa cikin ransa yana zagin falmata akan me ta tsaya yi masa kuma cikin ɗaki ?
Fitowar falmata rungume da kayan da ta naɗe su da kƴar cikin daya daga cikin rigunan nasa , shi ya maida hankalin matar sa kan falmata ,'
Bin falmatar tayi da kallo lokacin da ta ga ta doshi jikin bango gadan-gadan tana shirin cin karo ,"
Kai yaro kai kuma daga ina da daren nan ?
Chak falmata ta tsaya lokacin da ta ji kafar ta ta zunguri garu ,
Juyawa tayi ga mijin ta wanda yayi kicin-kicin da fuska ,
Baban sadiq kana ganin yaron da nake gani koh dai gamo nayi ?
Cikin bagararwa yace wane irin gamo kuma bilkisu ? Yaro ne ya shigo karɓan kayan wanki ,?
Kayan wanki kuma ? A daren nan ?
Kuma naga kai kake kai kayan ka laundry da kan ka yaushe kuma ka koma bawa masu wanki , ? Tukun ma yaron baya gani ne naga yana bulunbutuwa ?
Bagarar da sauran tambayoyin ta yayi ya bata amsar tambayar ta ta karshe almajiri ne kuma makaho ," nuna masa hanyar fita daga falon , ya saki ƴar wata ƙarar da ke bayyana azabar da hannun sa yake yi ,da hakan ya tilasta bilkisu ta bar sauran tambayoyin ta tare da watsar da wasi-wasin da ya fara zuwar mata na ganin yaro a turakar maigidan nata har uwar ɗaki da dare ,'
Ta kama hannun falmata wacce tun da a garin neman hanya ta bige ɗan yatsan ta da kafar kujera ta raƙube ta tsaya daga wajen tana sauraran duk maganganun su ,cikin ranta ta gudurta muddin ta ga matar nan zata zalunce ta , zata fyaɗe mata biri har wutsiya ta faɗa mata gaskiyar zancen , idan ya so shi mijin nata ya kashe ta a gaban matar ta sa kamar yadda ya ce ,"
Ga hanya nan ka miƙe nan kar kayi kwana ,'
Ɗan turus tayi cikin kokonton
Kai yaro !
Chak falmata ta tsaya wacce har ta fara taku cikin sauri tare da hamdalar kubutar da ita da Allah yayi daga hannun wannan azzalumin mutumin da bata kai ga sanin sunan sa ba ,"
Waye ya kawo ka ? Ina nufin tare da wa kuka shigo gidan ?
Unn'umm'un tare tare da alhajin muka shigo shi ya kawo ni ," cikin inda-inda kalaman suke fitowa daga bakin falmata ,'
Shikenan tafi,"
Babu ko waiwaye falmata ta miƙa hanya , bata yi wata tafiya mai nisa ba ta fara tsinkayo tashin muryar ɗan liti da yake hira da wani , yana ta faman sheƙa dariya cikin salon maganar sa ," wata irin tsanar sa ta taso ta maƙure ta ," macuci azzalumi ta ambata a ranta ,'
Hangon ta da ɗan liti yayi ya sa shi miƙewa daga inda yake zaune akan bencin mai gadi suna hirar su ta duniya domin zamu ce ta tadda muje mu ,( yaƙin ruwa ya ci sakaina ,) shi ma maigadin tsohon ɗan iska ne wanda duniya ta gama kare masa ba tare da ya farga ba , duk wasu tsiyatakun da ubangidan sa yake yi ya sani , ya kuma san ɗan liti kawalin ubangidan sa ne , dan kuwa duk lokacin da ɗan litin ya shiga da yaron da ya kawo , nan yake zama a wurin sa yayi jiran fitowar yaron ,'
A ah kaga ɗan kachallarin Alhaji har ka fito ? Iyeeh har da kaya haka alhajin ya baka ,?? Inji dai baka yi masa gardama ba ?? Ka saki jiki ka ci tsokokin nama ka kora da ruwan tatattun ƴaƴan itatuwa yadda ya kamata ? Toh albishirin ka ɗan kachallari ? Kafin ka ce goro kawo kayan na riƙe maka ya furta hakan yana mai karɓe kayan hannun falmata ,"
Sati mai zuwa iwar haka kana nan na sake kawo ka ka dangwali arziki kayi buroshi da zuƙa-zuƙan cinyoyin kaza ɗan kachallari fiye da yadda kayi a yau,'
Ni bazan sake zuwa ba , bazan sake bin ka ba , ka maida ni gida ,' falmata ta furta hakan tana me rushewa da kuka
Wata ƴar iskar dariya ɗan liti ya kwashe da ita da ya sa falmata ƙaro sautin kukan ta wanda yake tabbatarwa da ɗan liti aikin gama ya gama a tunanin sa ,'
Tsawon dare falmata bata yi wani baccin kirki ba daga ta fara baccin zata ji ƙarar marukan da mutumin nan ya dunga yi mata , cikin ranta tana sake tsorata da mutane gaba ɗaya , abun da ta fahimta a ɗan ƙarancin shekarun ta shine mutane basu da kirki mafi yawan su azzalumai ne tana mace bata huta ba ta zama namiji ma bata tsira ba , sai dai cikin ran ta tayi niyyar boyewa yakaka abun da ya faru da ita domin ta huttashe ta shiga damuwa a dalilin ta , tasan daga lokacin da yakaka ta ji abun da ya faru baza ta sake samun nutsuwa ba har sai ta samo hanyar da take ganin ta bada kariya a gare ta , kwatankwacin wacce ta baro su daga sansanin su , a gare ta samun kwanciyar hankali tare da walwalar da take tsinkayowa daga muryar yakaka yafi mata kome , baza ta so tayi wani abu da zai Wargaza mata farinciki ba , hakan ya sa da a halin yanzun yakaka ta takura ta faɗa mata abun da ya sa ta kuka , taƙi bayyana mata haƙiƙanin gaskiya ta danganta kukan ta da tuno da mahaifan su da tayi ,
Kwanaki biyun da suka biyo baya sun yi su ne cikin takura , ita yakaka al'adar da take yi ita ta hana ta sakewa a matsayin ta na sabon shiga , dan haka duk a takure take jin kan ta gani take kamar kowa ya san halin da take ciki duk kuwa da cewa dai-dai gwargawdo samy baby ta wayar mata da kai tare da saya mata sabbin pad da pants,kuma zuwa yau da take kwanaki biyar da fara yi , ya fara jaa baya, ita kuwa falmata fargabar da take danƙare cikin ran ta akan irin matakin da ɗan liti zai ɗauka akan ta ne a lokacin da mutumin da ya kai ta wajen sa ya tabbatar masa da cewa ita mace ce ,
Sai dai a yau da ake kwana biyar da faruwar lamarin ta ɗan samu nutsuwar zuciya ganin har yau bata ji ko ganin wani sauyin da yake nuna mutumin nan ya gayawa ɗan liti wani zance ba, dan haka ta sake suka yi hirar su ita da yakaka da yagana waɗanda suke ɗan zagayowa su taya ta wanke-wanke , walwalar ta ta sauya zuwa taraddadi ne lokacin da ta ji muryar ɗan liti yana dannanawa madam saly kira ,
ahayye nanayee madam saly fito, fito , fito ki ji sabon bayani abun mamaki ciyawa da cin doki ,wai kamar mu a garin nan za'a nunawa barikanci , za'a yi mana ungulu da kan zabo ,? Chafɗijam , inji masu iya magana suka ce bar ganin ƙanƙantar allura karfe ce , yekuwa jama'a ku hallaro ku ji abun al'ajabi ango ya kwana da ƙunzugu ,
Da ɗai-ɗaya hankali mutanen wurin ya fara dawowa kan sa saboda tsabar ƙwarmaton sa hatta masu cinikin madam saly da suke cikin rumfa sai da suka ji yo shi wasu ma har suka tsallako suka zo ganin dal ,"
Liti yaya ne ? Yaya ne ?ya da irin wannan kiran haka ? Ta samu ne ? Ko kuwa ta guntso ne zata fesar , ? Kunne na tarwai ina jin ka bamu mu sha ," cewar madam saly wacce take ƙarasowa wurin tare da wasu daga cikin ƴan aikin gidan ,"
To wallahi yaran nan yaks da ƙawar ta tare da munafiki koh munafukar ƙanwar ta zan ce ? Yo abun ne ya sauya , ninke mu baibai suka yi suka buga mana stamp ɗin sakarkaru na gaya miki, "
Wani banzan kallo madam saly take sakar masa kafin ta jaa ɗan guntun tsaki ,
Ban gane ba ? Daman akan waɗannan yaran kake kwalla wa jama'a kira har da yekuwa ? , kai dai Allah wadaran ka dan liti
Tsiya ta da ke wutar ciki madam saly , toh na rantse da Allah kachalla dai mace ce , macen ma luntsumemiya kuma nunanniya , shine dan iskanci da kuturun munafurci yaran nan suka ce wani wai namiji ne , aradun Allah ma ni ban yadda da su ba idan ba turo su ɗaukar rohoto aka yi ba , atoh ki dai bincika ki kuma san abun da kike ciki kar sai kin baje kafafu