Showing 78001 words to 81000 words out of 411050 words

Chapter 27 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

20057

ki ji anyi ramm da ke anyi sama da duwaiwan ki atoh , zamanin nan na yanzu ko inuwar ka baka sakankance da ita ba dan zata iya harɗewa ta shige cikin na makiyin ka idan kuka jeru, ji min duniya mai abun mamaki wai ƴan waɗannan ƙuya-ƙuyan yaran sun iya dabo-dabo da rufa-rufa , toh dan uban uban ku yau asirin ku ya tonu ,"

Duk maganganun da yake suna sauka a kunnuwan falmata wacce take duƙe a bakin fanfo da kuma yakaka wacce ta kawo kai domin shigowa ta karbi burkutu ta kaiwa abokan ciniki , dukkanin su tsam suka yi da jin kalaman ɗan liti , wannan fa shi ake kira an yanka ta tashi , take falmata ta fara yin hawaye , yayin da yakaka ta ɗaure ta cije tare da jaan ƙwanjin kare falmata ,"sai dai ayi wacce za'a yi wai bera ya zubda garin ƙyanwa ,"

Madam saly ce ta juya ga falmata bayan da ta gama jin zantukan ɗan liti ,

Kai kachalla zo nan

Sum-sum falmata ta taso tana laluben hanya ta sashin da taji tashin muryar madam saly

Haiyaratataa ni idan ba makantar taki ma ban yadda da ita ba , ni daman kullum ina shakkar waɗannan idanun naki da suke wural uwa na mujiya da tsakiyar dare ace wai bakya gani ??? Cewar ɗan liti wanda yake jijjiga ya dogare daga gefe ,"

Kai kachallah meye gaskiyar maganar da ɗan liti yake faɗa akan ka ? Tambayar da madam saly ta jefawa falmata wacce take durƙushe a gaban ta kenan , "

Madam karya yake min ni ban san kome akan abun da yake cewa ba ,"

Wata irin zaburowa ɗan liti yayi ya dako tsalle ya bangaje ƴan matan da suke tsaye daga gaban shi ,ya dire a gaban falmata ,"
Dan ubanki Alhaji basko zai miki karya ne ,? Toh idan kin ce karya ne ɗaga rigar ki aga kirjin ki , nace ɗaga rigar ki mu ga kirjin ki ƴar iska jaririyar ƴar bariki ,'
Toh kai kachalla ai sai ka cire rigar mu ga kirjin naka domin cire zargi cewar madam saly," sunkuyar da kai falmata tayi tana matsar ƙwalla
Koh kafin su farga ɗan liti yayi charaf ya kaiwa gaban rigar falmata chafka , baiyi wani jinkiri ba ya sa karfin tuwo ya balla baturan da suke jere gaban rigar , yana cewa
Dan uwar ki rigar uban waye ya saya miki ba ni ba ?? Yau sai mun ga karshen karya ,"
Da gudu yakaka ta karaso wurin ganin ana neman tozarta ƙanwar ta ayi mata tsirara cikin taron maza da mata ,"
Ƙoƙarin raba hannun ɗan liti da jikin rigar falmatan ta fara , tana cewa
Ɗan liti ka sake mata riga meye hakan ? Wai ina ruwan ka da harkar mu ,"
Wata dariya ɗan liti ya sake , kin ji koh madam saly nace kin ji koh ? Da bakin ta take ambaton ta a jinsin mata , shegu munafukai , yau me raba ni da ku sai Allah tun da kuka jawo min asara , yana gama faɗin hakan ya ingije yakaka tayi faɗuwar ƴan bori , kafin ta taso , ya sanya dukkanin karfin sa ya jijjiga falmata gami da keta mata riga , ya sanya hannayen sa duk biyu ya cisge tsunman da take ɗaure kirjin da shi ,ya murɗa hannayen ta tare da lanƙwasa su baya ya banƙaro kirjin ta gaba wanda hakan ya bayyana haliltar kirjin ta tsai a tsaye ,"

Wani irin guntun salatin da ba'a ƙarasa shi ba tare da shewa da ihu sune suka cika wajen daga bakunan mata da mazan da ke wajen , cewa suke wallahi chika ce , laaah ,
A toh idan har yanzu ba'a yadda ba sai na ɗaga muku ƙasan shi ma ku gani dan gaba kar a karkace a kuma sharo wata ƙaryar ace mata-maza ce gara a ga ƙarƙashin ,
Nan dai wasu suka fara ihu suna cewa a ɗaga su gani a ɗaga su gani
Da gudu yakaka ta taso tare da yi wa falmata rumfa da jikin ta idanun ta kuwa tuni suka fara zubar ruwa , cewa take menene hakan ?dan Allah kuyi hakuri ku kƴale ta , ƙanwata miskiniya ce makauniya ce , ni ce da laifi , ni nace ta koma shigar maza , kowanne hukunci zaku yi mata ku min a madadin ta ,' tana faɗin hakan tana warware ɗankwalin kan ta tare da rufawa falmatan da take risgar kuka , cikin tsokar jikin ta take jin idanun jama'ar da suke zagaye da wajen , cikin ran ta tana jin wani irin rauni da bata taɓa jin irin sa ba tabbas an cuce ta an tazorta ta matuƙa an tsaraita ta a gaban jama'a

Yagana ma matsar ƙwallar tausayin falmata take ,

Madam saly kuwa wani malalacin kallo take bin su da shi ,"
Yanzu daman dan uwar ki yaks ƙarya kuke min ? Toh kuwa yau yau ɗin nan zaku bar min gida ƴan iska maƙaryata , da sauri yakaka ta matso gaban saly ta shiga rokon ta akan ta taimaka kar ta kore su domin basu da kowa ,"

Da ƙyar da jibin goshi larki da hema suka sanya baki wurin taya yakaka bawa madam saly hakuri saboda tausayin yaran da ya tsirga musu , bayan sun ƙora ɗan liti wanda ya zama ziga-zigi yana sake tunzura madam saly ta kori su yakaka , ya dage akan cewa turo su C.I.D aka yi wanda hakan ke ruda madam saly , sanin cewa ita ba mutum bace mai gaskiya , sanna a cewar ta kewaye take da makiya ƴan hassadar ta .

Ficewa yayi bayan ya tabbatarwa yakaka duk inda kuɗi suke ta nemo ta biya sa kayayyakin da ya sissiyawa falmata domin shi bai yin asara koh ta sisin kobo , kuma kar falmata ta sake taka ko da kofar ɗakin sa ne , idan har kuwa ya gan ta a gaban ɗakin sa babu abun da zai hana ya kirɓe ta ,'

Toh yanzu da ku ka nace kar a kore su akan ku zasu dunga kwana su biyun ? Kun san dai ku ukun ma a matse kuke tamkar kifin gongoni , cear madam saly

Da sauri yakaka wacce har lokacin rungume take da falmata da take ta faman sauke ajiyar zuci akan kukan da ta sha , tace
Ni zan dunga kwana a kan benci cikin rumfa idan ya so falmata ta kwanta tare da su a ɗakin idan kin yadda ,
Sai da madam saly ta wurga mata harara domin har yanzu tana ɗan jin haushin su
Ƙya ce haka mana dan kun samu na ƙyale ku algungumai , ni dai ku kiyaye ni kar ku bari na sake kama ku da wani laifi domin gaba ko kun fi kuturu naci sai kun bar gidan nan , tun da kin zaɓi kwanan kan benci a cikin shagon toh ke kika sani sautun mahaukaciya , duk abun da ya biyo baya ki kuka da kan ki , kar ki ce ban faɗa miki ba ,

Ba tare da fargabar kome ba yakaka ta amince da zantukan madam saly cikin ran ta tana sa mata albarka ,

Wanene Alhaji basko ?? Aina kika san shi ? meye haɗin ki da shi ? Kuma ta yaya yasan cewa ke mace ce ??
Su ne tambayoyin da yakaka ta jerowa falmata lokacin da take taya ta shiryawa cikin ɗaya daga cikin kayan da take warewa take ajiyewa falmatan su ,

Ba tare da jinkirin kome ba falmata ta fayyace mata kome ,

Hawaye ne yake sauka bisa kumatun ta , meyasa mutanen duniya suke son zukatan su ?meyasa taimako domin Allah yayi ƙaranci meyasa zalunci ya yawaita , meyasa fasikanci ya zama mahaɗin rayuwar mafi yawan mutane ,??? Meyasa meyasa ? Ji tayi tsanar dukkanin mutanen da suke kewaye da duniyar ta ya kama ta idan aka ɗauke ƙanwar ta ,'
Nan gaba kar ki sake yadda da kowa falmata , idan na ce kowa ina nufin kowa ,! Kin ji ko ?
Ba tare da falmata ta hakiƙance da inda kalaman yakaka suka dosa ba ta amsa mata da toh ,"

Daga ranar yakaka ta koma kwanan cikin rumfar da suke sana'ar su ciki , yayin da idan kafafu sun yanke a wurin kamar sha biyun dare sun riga sun gama sana'ar su, zuwa lokacin duk ƴan iskan sun watse wasu sun shige ɗakunan su tare da abokan iskancin su sai ta haɗa teburan da suke gaban kujerun , guda huɗu ta shimfiɗa zanin ta akai tayi matashi da hannunwan ta tare da rufuwa da wani zanin , sai tayi baccin ta ba tare da tsoron duhu da shirun da wajen yayi ba ko kuma tsoron ƴan iskan da ka iya kawo mata farmaƙi , wurin kwanan ta na cikin ɗakin kuwa ta barwa falmata ,

A haka kwanaki suka fara miƙawa har yau da ake kwana na uku da faruwar lamarin falmata ta gagara sakewa dan kuwa tuƙuru ƴan matan gidan suke tsokanar ta , har suna cisge mata ɗan kwali , suna faɗin ta koma shigar maza ta fi yi mata kyau , da hakan ba ƙaramin sanya ta takaici yake ba , sai dai tayi matuƙar koƙari wajen boye damuwar ta domin kar ta jefa yakaka cikin damuwa ita ma , duk wani abun da idon ƴakakar bai gani ba game da tozarcin da ake yi mata bata faɗa mata .

Juyi yake ta yi akan katifar sa kaɗan-kaɗan yana jin wani sabon yanayi da ya fara ziyartar sa a tun lokacin da agogon wayar sa ya nuna masa sha biyun dare cib wanda a lokacin yana kan computer sa yana wani aiki sai dai wannan yanayi da ya fara ji yana taso masa ya sa shi rufe computer tare da wani irin bingirewa akan katifar sa tamkar dai an tunkuɗa shi ,'
daran ranar ya zo dai-dai da cikar sa shekaru talatin cif a lissafin watanni turawa ,

Miƙewa yake so yayi ya fita ya ɗauro alwala , domin ya samu damar raya ƙarshen daren da ibada Kamar yadda yake aikata hakan jifa-jifa , sai dai ga mamakin sa ya kasa tashi , haka yake jin sa kamar an ɗaure shi ko kuma an aza masa wani abu mai nawi an danne shi , yana jin sa a wani yanayi mai cike da fargaba da tsoro zuciyar sa na wani irin bugu , yana jin sa ɗan mitsitsi kuma sakayau tamkar ba shi ba , shi ya san ba bacci yake ba ba kuma a farke yake ba sannan ba mafarki yake yi ba , yana jin sa kawai a wata duniya ta daban , duk yadda ya so yayi addu'a ya kasa ,

Haka ya shafe tsawon awannin karshen daren har zuwa lokacin da alarm ɗin da ya saita a wayar sa ya fara rangwaɗo sautin kiran sallah cikin zazzaƙar muryar balarabe , wanda cikin ikon Allah ya ji cimak wannan nawin da yake ji ya hana shi motsi , babu shi tamkar dai an sauka a kan sa , da gudu ya miƙe tsaye , jikin sa ya jiƙe sharaf da gumi , wannan tsoron da yake ji ya kau , sai dai har yanzu ɗan sauyin da yake ji a jikin sa yana nan , amma cikin ran sa sai ya dangan ta hakan da zamantowar sa cikakken ɗa namiji lafiyayye da ya kai minzalin da ya kamata ya buƙaci mace , duk da cewa shi youssouf ba manemin mata bane , bai taɓa zina ba , bai taɓa kusantar kowacce mace ba duk yadda ya kai ga cuɗanya da matan bariki matan banza , shi mutum ne mai tsantsani ta wannan fannin ,
Da sauri ya ɓude ruwan leda ya juye cikin ɗan bokatin da yake yin amfani da shi wurin yin wanka , ya cika shi taf da ruwa gami da sunkuta ya fito daga tantin sa zuwa ɗan bayan gidan da aka samar masa na wucin gadi wanda yake mallakin sa shi ɗaya ,'

Ruwan na da sanyi sosai dan haka yayi tunanin zai taimaka wurin kawar masa da yanayin da yake ji a jikin sa , sai dai ga mamakin sa daga lokacin da ruwan ya sauka akan fatar jikin sa , ya ji tamkar an ƙara masa masifa ne domin gaba ɗaya tsikar jikin sa tashi tayi da ya sa dukkanin wasu jijiyoyi na jikin sai da suka taurara tare da fitowa baro-baro ,wani irin ƙullewa ya ji marar sa tayi ,

Ba shiri ya sanya tufafin sa gami da ɗauro alwala ya dawo cikin tantin sa , a daddafe ya idar da sallah saboda yadda marar sa take tamkewa tana sakewa ,

Kwanciya rub da ciki yayi bayan ya sanya ɗaya hannun sa ya riƙe marar sa ,tun da yake bai taɓa tsintar kansa cikin wani hali makamancin wannan ba, a hankali ya fara jin ciwon marar yana raguwa , wani ɗan daddaɗan bacci yana fisgar sa a sakamakon lafawa da ciwon yayi tare da daɗin ƴar sassayan iskar asuba da take shigowa ta tsakankanin rumfar tantin sa ,,'

Bacci yake yi sosai da bai samu irin sa ba duk tsawon daren jiya , kafin sautin kiran wayar sa ya tashe shi , miƙa hannu yayi ya jawo wayar tare da miƙewa zaune saboda sautin kiran ya bayyana masa girma tare da muhimmancin mai kiran na sa

Allô mama oui meilleur sava,?

Daga chan ta amsa masa sava bien yaro na ya kwanan ka ? Da dama kou ?
Ɗan jim yayi yana son faɗa mata yadda yake jin jikin sa saboda ya saba bayyana mata duk wata damuwar sa , sai dai kuma yanayin da yake jin yayi masa nawin faɗi a kan harshe musamman ma ga mahaifiyar sa *

Daga bangaren ta kuwa zuciyar ta ce ta buga a sakamakon tunowa da mummunan mafarkin da tayi akan sa asubahin daren jiya da ya haddasa mata rashin nutsuwa , da ya sa tun asubah take neman layukan sa domin ta ji lafiyar sa kou ta samu kwanciyar rai amma rashin kyaun hanyoyin sadarwa ya sa sai yanzu da safe ta cimma nasarar samun sa a wayar ,"

Yaro na yi min magana mana hankalina ya tashi ,

Da sauri ya katse ta ," da dama umma ya ɗaura da tambayar ta ina merama ? Ta amsa masa da lafiya take , "
Cigaba tayi da tambayar sa lamuran da suke gudana daga wurin sa , yana bata cikakkun amsoshin da suka gaza wurin gamsar da ita , zuciyar ta ta gaza nutsuwa duk lokacin da ta tuno da mafarkin da tayi sai ta ji bata son ta daina jin sa a waya , inda da hali so take ya kasance a idanun ta cikin waɗannan kwanakin dan tana jin kamar wani abu marar daɗi zai faru da su,

duk da ta san sau dayawa mafarki bai zama gaskiya a mafi yawan lokuta daga shaiɗan yake , kuma ita bata da ikon kare kan ta ma bare wanin ta , ta san ko da agaban idanun ta yake , bata isa ta bashi kariya ba , illah addu'ar ta da ka iya yin tasiri akan ko ma menene , kuma duk nisan tazarar da ke tsakanin su ta san addu'ar zata isar masa ,

sanin da tayi youssouf ba sosai sosai yake tsayuwa yayi addu'a ba , shi dai mai tsayar da ibadun sa na farillah ne , bayan su sauran lokutan sa ƙorafi yake aiki ya cinye su ,wanda ita kuma hakan bai mata daɗi , ta san duk wata nasar da kariya daga wurin ubangiji ake samun su ,

dan haka a yanzu ma sai ta sake tunasasshe sa game da girman addu'a inda shi kuma ya tabbatar mata da yana yi ,'
Sallama yake shirin yi mata , sai kalaman ta suka katse shi ,"Tu es notre lumière, notre joie, et pour toi nous donnerons le meilleur. En te souhaitant une vie abondante et en bonne santé.Joyeux anniversaire mon fils!,' Allah shi yi maka Albarka shi kare ka du inda kake yaro na ,
Murmushi ne ya suɓce masa halin da ya wayi gari cikin sa ya sa ya ma mance da yau take ranar zagayowar haihuwar sa kalaman ta na yanxu suka suka tunassashe sa,'amsa ya maida mata cikin tsantsar ƙaunar ta da yake ji cikin ran sa ," merci mama je t'aime,"
Daga bangaren ta ajiyar zuciya ta sauke bayan kammala wayar su , babu laifi ta ɗan samu nutsuwar zuciya , sai dai ta kuɗurce a ran ta zata ƙara ƙaimi wurin neman kariyar ubangiji akan ta da ƴaƴan ta , daga makiyan su da ta san suna kewaye da su ,
Juyowar da zata yi domin nufin ta shiga ɗaki ta fara sallar walha , idanun ta suka sauka akan hajiya uwa wacce take yi mata wani irin hargitsattsen murmushin da baza ta iya hasashen nufin sa ba , bata san lokacin da ta wanzu a wurin ba domin baya ta bawa kofar shigowa falon nata na ciki ,

Tsawon zaman su baza ta iya tuna rana ta karshe da hajiya saratu ta tako kafafun ta sashin ta ba , basa shiga sassan juna iyakacin su , su haɗu a bangaren mai martaba idan haɗuwar ta kama dole , ko kuwa wurin gaishe da hajiya uwa ,'

Sannan tayi mamakin ganin ta ita ɗaya kai tsaye har cikin bigiren ta da sai an nemi iznin ta kafin a shigo ,' a sanin ta tare da tawagar ta hajiya saratun zata iso kuma karƙashin jagorancin shugabar bayi ta bangaren ta ,'

Da kallo ta bita lokacin da take yi wa kan ta mazauni akan shimfiɗar alfarma da ta tashi daga kan ta yanzu ,'
Hala uwargidan mai martaba sarauniya tayi mamakin wanzuwa ta gaba gare ta a yau ,? Shi yassa aka gaza wurin taryaa ta kamar yadda ya kamaace ni ,

Fuskar ta babu walwala ta ce ,"
Ban yi mamakin zouwar ki nan ba saratu , shin ƙaƙa za'ai mamakin wanzuwar macce a kowanne bangare cikin gidan amren ta ? Sannun ki da isowa ina

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login