Showing 90001 words to 93000 words out of 411050 words

Chapter 31 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

20055

suke lumshe tana jin ta , karfin tashin ne bata da shi , wata iriyar mummunar kasala take ji tana bin duk gabobin jikin ta , ga juyawa da kan ta yake yi ɗakin kan sa juya mata yake ,"

Gefen yakaka ta dawo ta zauna , cikin ran ta tana fatan lafiya ga yakakar wacce take zaton bacci take ,"

Ko mintoci biyu basu ƙarasa ba suka ji muryar madam saly tana ɗuro musu ashar ,"
    Ni za'a kawo wa iskanci da tsaurin ido , dan uban ku ni da gidana ina cewa ku fita kuna yin biris da ni , sai kace da uwar ku muka haɗa kuɗin sayan gidan ?? To billahi minti goma yayi kaɗan zan sa a fitar min da ku bayan an chasa min ku ," yau naji jaraba da maSifa ,"

  Tana gama hanya ta fito ta durƙusa a gaban madam saly gami da fashewa da kuka ,"
    Madam dan Allah wanne laifi na miki zaki kore mu ? Ke kaɗai ce gatan mu dan Allah ki yafe min laifin da nayi miki , idan mun bar nan bamu da wurin zuwa ,"!

Ji min mayyar yarinya ? Ta ina na zama gatan ku ? Babu dangin iya babu na baba ? Na gaya miki yaks ni bana jurar asara , asara ce babba na ci da ke na ci da ɗan cikin ki ? Yo wanne aiki kike min da har ya kai na dunga ci da rai uku a biyan aikin ? Ga ki ga ƙanwar ki kuma ga ƙarin wani yanzu kin maƙalo a cikin ki ,' idan har kina son zaman gidan nan sai dai ki samo uban cikin jikin ki nayi masa lissafi kuɗin abincin ɗan sa ya lale ƙuɗi na ya biya ni sannan ,! Tab ina zan iya asara ?

Ɗa a cikin ta ? Wacce magana ce wannan madam saly take faɗi ? Ko dai kunnuwan ta sun daina ji daidai?

   Madam wane ɗa ? Ina ɗan yake ?

Yana ƙundun uwas ki yaks nace yana ƙundun uwas ki , ni zaki yiwa bariki ? Ah lalle fa gwada min firirita irin ta sabuwar karuwa ,"

Sunkui da kai yakaka tayi kan ta yana sake ƙullewa ,"

Wai zaki ki kira ɗan iskan da ya ɗirka miki cikin  ya zo ne ko kuwa kin zaɓi barin gidan ?
    Da sauri tace !
Zan kira shi madam
  Na baki nan zuwa gobe duk inda ɗan iskan yake ki nemo shi yazo ya biya kuɗin ci da ɗan tayin sa ko kuwa yasan inda zai yi da ke ,!  Madam saly ta furta hakan tana mai wucewa ta bar wurin cikin ran ta kuwa tana ayyana irin kuɗin da zata iya samu akan cikin jikin yaks domin kuwa ta san da mutum ɗaya tak yaks tayi harka , bata shakkun shi ya fara sanin yaks kuma shine uban cikin jikin ta , idan kuwa haka ne ai ita ranta ƙwal ,

tun da ta lura da samuwar cikin take farin ciki tare da ƙulla yadda zata yi wannan ciki ya buɗe mata sabuwar hanyar kama kuɗi a hannun wannan hamshaƙin attajirin da yayi mata ɓarin naira akan taraiyar sa da yaks , wanda bata tantama wani hamshaƙin attajiri ne mai muƙami , ko kuwa dai ɗan attajiran , da har yau take mamakin ina baƙauyiya kamar yaks ta samo shi ,?  shi kuma cikin jerin gogaggun matan duniya da suka dace da shi ya rasa ta zaɓa sai ya tsallako kan yaks ? Kai ita tafi danganta tarayyar sa da yaks ma da neman wani cikar burin sa na daban , wata ƙila sa'a aka bashi aka ce ya haɗa da neman kuchakar mace irin yakaka ,wata ƙila kuma wani al'amari ne mai girma ya jirkita tunanin sa da har ta kai shi ga neman yakaka , ita dai ta san ruwa bai tsami banza !

Koma meye ita gaba ta kaita !
   Harƙƴalla da irin su babbar sa'a ce .

Ko batun korar da tayi wa su yakakar , barazana ce kawai ta shirya mata domin ta zaburar ta ta nemo mutumin da ta lura a yanzu bai cikin rayuwar yakakar , da ita kuma take ganin rashin sa a matsayin wani babbar asara , dole ya dawo ya cigaba da harka da yaks ita kuma ta cigaba da samun maƙudan kuɗaɗe ta sanadin hakan ,!

Ta shafe fiye da mintoci biyar a durƙushe nan wurin tana tunani , sai dai duk yadda ta kai ga son fahimtar inda maganganun madam saly suka dosa ta gaza ganewa ,"
    Wanne irin ciki ? Ta san ciki ake a haifi ɗan mutum , to amma ita bata da wani sani akan yadda ake a ɗau cikin ɗan mutum ! Tasan dai sai anyi aure ake haihuwar , to ai ita bata yi auren ba ! Kuma da madam saly take cewa tana da ciki , ina cikin a jikin ta ? Cewa take cikin mata huruwa yake ya zama ƙatoto sai a haihu ,? Ita kuwa nata cikin shafal yake ,"babu ko alamun tudu ,"

Wata sabuwar tambayar ce ta kutso cikin tunanin ta , toh kuma waye baban ɗan cikin nata da madam.saly take cewa ta nemo ?
  "Bature kam silum" wani sashi na ran ta ya ayyano mata sunan sa a matsayin uban ɗan cikin ta da ake ikirarin tana da shi ,"

    Ɗan wani tattausan murmushi ya ratso tsakanin hawayen fuskar ta ya bayyana kan sa ,"
       Kome da ya dangance shi sanyata nishaɗi yake tare da farin ciki duk kuwa yadda ta kai ga shiga halin damuwa da tashin hankali ƙaunar sa daban ce cikin ran ta tafe take da wani irin kakkarfan shauƙi mai bata kuzari ,'
       Ina son ka dayawa !
ta furta hakan a sarari tana mai dafe marar ta da take ɗan yin ciwo kaɗan ,"
    Karaf kalmar ta sauka a kunnuwan falmata wacce jin wucewar madam.saly da yadda ta kaya tsakanin su da yakaka , ya sanya ta fitowa duba yakakar bayan ɗan gajeran zaman jiran shigowar ta ɗakin da tayi domin akwai tarin tambayoyin da take son yi mata ,"

Rashin shigowar yakaka da wuri ya sanya ta gaza jiran ta , sashin ran ta na fatan ba ciwo ne ya sake turnuƙe yakakar ba , sai dai kalmar da taji yakakar ta ambata a kunnuwan ta ya sanya ta sa kalmar a jerin tambayoyin da take son yi mata .

Hannu ta kai ta lalubo kafadun yakaka ta ɗora hannuwan ta duk biyu kan kafadun tana fuskantar ta ta buɗe idanun ta sosai tamkar dai tana Ganin ta ,
    Yakaka dagaske ne kina da cikin shege ? Zaki haifi yaro ba tare da kin yi aure ba irin na falta?

    A hankali ta sauke hannun falmata daga kafaɗun ta , ta rike hannayen cikin hannun ta ," tare da yin ƙasa ƙasa da muryar ta ,"
   Bani da cikin shege falmata ƙarya madam take min so kawai take ta kore mu ,!
    Ɗan jim falmata tayi cikin rashin gamsuwa ,! Kafin ta sake jefawa yakaka wata tambayar
    To waye ne naji kin ce kina son shi dayawa ? Waye shi ?
    Kallon fuskar falmatan tayi a ɗan hargitse tana jin wani yanayi cikin ran ta ,"
       Bature kam silum ! ,"yakaka ta furta hakan a ƙasan maƙoshi.
   Ɗan zaro idanu falmata tayi tamkar tana ganin ta ,"

Nduwodo bature kam silum ? Ndan shaa noum3 ? ( wanene bature kam silum aina kika san shi )
   Kaam shaa banaangndi3 .' ( mutumin da na taimakawa )

Chaaman shaa ra'amaa ? ( daman son shi kike ? )

Shii shaawa shaa rumiind3 tayd3zin zayyrod3 , ( yana da kyau baki gan shi ba ɗan gayu da shi )

Ɗan murmushi ne ya subucewa falmata wanda ya zarce zuwa dariya , cikin muryar dariyar ta ce
    Har naji ya burge ni NIMA INA SON SHI!
     Da wani irin yanayi mai daɗi yakaka ta jaa falmata cikin jikin ta tana jin yadda ƙaunar falmatan yake zagaya duk hanyoyin jinin ta , tun da daɗewa ta sani falmata mai taya ta son abun da take so ne kome lalacewar wannan abun shi yasa ƙaunar falmata ta fifita akan duk wata ƙauna da take zagaye jinin jikin ta !
      Cikin satin ta ɗan samu sauƙin walakanci tare da bautawar da madam saly take yi mata saboda kullum cikin gilla mata ƙarya take akan uban cikin jikin ta yana nan tafe , wanda har yanzu ba wai ta yadda da cewa tana da cikin bane , neman hanyar da zata sa madam saly ta haƙura ta ƙƴale ta ta cigaba da zama gidan ta take ,  duk da cewa a halin yanzu duk ta yadda ta ci abu mai ƙarni ko yaya ne sai tayi aman sa wanda yake wahalshe ta sosai , sai kuma a wasu lokutan yawu ya kan ɗan taru mata a baki ,  bayan hakan babu wani alamun ciki da ya bayyana a gare ta wanda ita a ƙaramin sanin ta zai sa ta yadda tana da cikin ,"
      Amma ba'a je ko ina ba madam saly ta farga da cewa ƙarya ce yakaka take gilla mata sumfiri-sumfiri wanda hakan ya fusata ta , ta shiga saukewa yakaka kwandunan bala'i da masifa gami da sanya ta aiki babu dare ba rana tana kuma sake tisa mata a kullum cewa gaf take da ta kore su ,

Daga yakaka har falmata hankulan su a tashe yake akan tsangwamar da madam saly take yi musu , ita yakaka bata san wata hanya da zata bi ta nemo youssouf ba baya ga lambar wayar sa wacce ita kuma tun kwanaki biyar da suka wuce da madam saly ta turke ta ta sa ta kira lambar sa ƙwaya ɗaya jal da yake kiran ta da ita a lokacin da suke tare , sai dai kiran farko da tayi da ya shiga , har ta gama ƙara ba'a ɗauka ba , to tun daga sannan ko ta kira lambar bata tafiya , daga tayi alamun ta shiga sai ta katse , ga alama an datse hanyar shigar kiran daga computer.

Gaba ɗaya sun fara lalacewa kasantuwar su duk biyun ba ma'abota son tashin hankali bane daɗi da ƙarin tsoron madam saly da suke yi kamar me ,!

Allah Allah yakaka take yi samy baby ta dawo , ko zata ɗan samu sa'ida da wurin fakewa , bakin cikin ta ɗaya akan bacewar ƴar takaddar da samy baby ta zana mata lambar wayar rta bisa ,ta nemi ƴar takaddar ta rasa sama ko ƙasa babu , tafi zaton a tun ranar da ta bata ta yar ba tare da sani ba ,

a haka kwanaki suka tura , zuwa lokacin da lamura suka fara tsananta gare su , laulayi tuƙuru ya sako yakaka a gaba , kome ta ci amai take ,bata da abun so da kuma yake ƙwantar mata da hankali irin ƙamshin turaren youssouf da yake manne da jikin kuɗin sa na Niger da kuma agogon sa,  duk dare da su take ƙwaƙume cikin zanen rufuwar ta , idan ba haka ba babu ita ba bacci , ɗan ƙaramin hoton fuskar sa ya zamar mata abu ɗebe kewa a duk lokacin da ta ji son sa ya mintsine ta !

ga aikin da madam saly ta walle ta ce bata janyen shi daga kan ta a wai domin tana laulayin shegen cikin ta , a cewar ta ma ita ake ƙwara , kullum cikin zagi da aibata yakaka take da munanan kalamai iri-iri a duk lokacin da taji tana amai ,"

A halin yanzu duk wani mai shigowa cikin gidan ya san yakaka tayi ciki , ciki kuwa har da ƙawar ta da suka zo gari tare yagana , wacce tun daga lokacin da ta ji da kunnen ta yakaka tana da cikin shege , ta janye mata , magana ta kirki bata haɗa su , haka yakakar zata yi ta bin ta tana so ta bata dama suyi magana amma fir yagana ta juya mata baya taƙi kula ta , ɓaro-ɓaro take nuna ita fa kƴamar ta take yi , da har ta kai a wani yammaci ta gaggasawa yakakar magana ta kuma nemi da ta fice a harkar ta ita ba karuwa bace mai abun kunya irin ta ,"

   a ranar kusan raba dare yakaka tayi tana kuka a cikin zanin rufuwar ta bisa teburin kwanan ta , ji take gaba ɗaya ta muzanta domin a zuwa yanzu ta fara amincewa da tana ɗauke da cikin shege a jikin ta ,"

Sannu sannu rayuwa tayi wahala da tsanani ga yakaka da falmata , domin kuwa a halin yanzu haka suke wuni jibge a gefen ɗakunan gidan cikin yunwa da ƙishirwa , saboda yakaka bata iya yin aikin dalilin rashin lafiya , amai da take ta faman yi ya ƙarar da ruwan jikin ta ga kuma ba abincin kirki wanda hakan ya sa gaba ɗaya jikin ta ya shika yayi yaushi idanun ta har kore-kore suke , babu mai kula ta sai ƙanwar ta wacce ita ma yawan tashi ta zo wurin yakaka idan taji tana amai ko kuma idan tana buƙatar ruwan da take shan sa take dawo da shi , ko kuma ta kawo mata abincin ta da ba iya ci take ba , wannan zirga-zirgar da take yi ya jaa madam saly tace ta dakatar da ita daga yi mata wanke wanken da take yi a cewar ta baza ta yadda falmata ta dunga gwamutsa mata aikin wanke wanke da wankin amai ba ," ta maye guraben su da wasu fallallun ƴan mata biyu , a cewar ta tun da sun zame mata ƙarfan ƙafa , baza su bar gidan ba to su nemi abincin su wurin kwana kuwa su tsaya daga tsakar gidan zuwa cikin rumfa ,"

Da hakan suka amince domin kuwa basu da wata mafaka bayan nan ɗin yini suke bin inuwar gaban ɗakuna da baccon kayan su da shi ma aka wurgo musu abun su kan su , 

babu mai lura da su , sai idan falmata taji yunwa na neman galabaitar da su ta daidaici lokacin kammala cin abinci ta lallaɓa zuwa bakin  makwarari inda take ɗan tattaro musu guntattakin abinci da ƙanzo-ƙanzo da a yawan lokuta ita ɗaya take ci domin yakaka ko son kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci ,"

Idan dare yayi kuma su koma cikin rumfa su kwana bisa tebura.

Falmata ta so ta fara fita bara sai dai rashin ɗan jagora ya hana ta , tayi yunƙurin neman taimakon yagana akan ta dunga kai ta bakin hanya wurin barar ta amma sai yakaka ta hana ta yiwa yaganar magana ,"

a cikin wannan halin na tsanani suka shafe fiye da sati uku suna watangaririya cikin rashin galihu , tare da yunwa da kirshirwa , 

kwatsam rana ɗaya sai ga samy baby ta dawo bayan ta shafe kusan watanni biyu da ƴan kai bata nan ,  nan ta tarar da yakaka cikin mummunan yanayin mutu Kwakwai rai kwakwai , ba shiri ta kwashe su zuwa wani ɗan jeka na yi kan asibiti mai zaman kan sa ,"

Nan aka shiga bata taimakon gaggawa , har jini aka ƙara mata leda ɗaya bayan ruwa da tarin allurai da ta sha ,

Ba ƙaramin faɗa likitan yayi ba da yadda aka bar yarinya ƙarama da ciki jikin ta cikin irin wannan mummunan yanayi , har ma ya nemi da ya ga mijin ta domin su gargaɗe shi
    sororo samy baby tayi tana kallon likitan , kafin ta buɗe baki tace
    ciki fa likita ? Waye ke da cikin ?

Ita marar lafiyar da kika kawo/ƙanwar ta ki
  kina nufin baki san tana ɗauke da ciki ba har na tsawon sati goma sha biyar da kwanaki shidda ? ?
   Goge gumin da ya tsatsafo mata a goshi tayi ,"
    Ban sani ba likita kasan bama tare jiya na dawo daga tafiƴa , ta furta hakan cikin rashim sanin takamaimai amsar bayarwa , cikin sanyin jiki ta miƙe ta fito daga ofishin likitan bayan ya sake jaddada mata lalle ta nemo mijin yakaka !
wai yaks ke da cikin??har na tsawon watanni kusan huɗu , wannan wanne irin ɓata wasa ne yaks take son yi masu ? Ita da ta je abuja ta ga yadda alhazan birni ke rububin ƙananun ƴan mata irin yaks , har tayi mata sha'awar samun irin wannan damar ta dawo da niyyar ta sake wanke ta ta shigar da ita  aJi na musamman ta samu ilmin bariki yadda zata ci ribar sa  su wuce abuja tare ,"

ta huce takaicin duniya ", hatta waɗanda suka raɓe ta ma su huta , amma shi ne dan rashin sa"a zata zauna da ciki a jikin ta har tsawon wannan lokacin , waye ya gaya mata ana haɗa harkar bariki da jego da rainon ƴaƴa ?

Ya zama dole a fidda cikin nan muddin tana so tafiyar ta tayi kyau !

BAYAN SATI ƊAYA .

Jikin yakaka yayi kyau ta murmure babu laifi duk da cewa shi laulayi bashi da wani magani takamaimai amma dai ta samu farfaɗowa daga halin galabaitar da ta shiga , sai ɗan abun da ba'a rasa ba na daga larurar masu ɗauke da ƙaramin ciki , kamar kasala , tashin zuciya , yawu da sauran su .

dan haka yau likitan ke sallamar ta bayan ya kafa mata dokokin kula da kan ta da lafiyar jaririn cikin ta , ya kuma sake jaddada mata da ta fara zuwa awu cikin wata mai kamawa ,"

Yakaka wacce zuwa yanzu ta amince tabbas tana ɗauke da ciki a jikin ta domin kuwa ga cikin ya ɗan fara tasowa kuma kaɗan kaɗan tana ɗan jin taurin sa yana dunƙulewa guri guda ,"
   Cikin ladabi ta amsawa likitan tare da sake jero kalaman godiya tana mai satar kallon samy baby wacce tayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login