Showing 354001 words to 357000 words out of 411050 words
Chapter 119 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt
murya Maimartaba yayi kafin yace .
"Youssoufa wanne mataki kake ɗauka bissa ga waɗan da suka ha'ince ka ?
Shiru Youssouf yayi kafin yace "Ranka shi daɗe dukkanin hukuncin da ka zartar .
Shiru mai martaba yayi kafin yace " Ubangiji Mai yawan yafiya ne , yana kuma ƙaunar bayin sa masu afouwa ga junan su a duk lokacin da aka zalunce su , shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci babu wani mugun abu da zai same su, amma mugaye ba za su sami kome ba, sai wahala bayan ubangiji ya bar su da kan su , Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.
Youssoufa da yayi shiru yana sauraron sa , jin ya dakata ya sa shi ɗago kan sa a nutse
A kalaman maimartaba ya fahimci shawarar da ya ba shi cikin hikima ransa kuma ya sanyaya daga zafin da yake masa a duk lokacin da ya tuno da abunda aka masa dan haka sai yace "Nayi musu afouwa ranka shi daɗe amma ita ban iya sake riƙon Amren ta zan sauwaƙe mata daga can ta tai yankin su , mammadou kouma zan tafi mu dawo tare .
"Madallah da kai Youssoufa yadda kayi afouwa ga 'yan Adam da sunka maka ƙeta kai ma Allah shi maka afouwa bisa tarin laifukan ka .
"Amin Amin Baba .
Murmushi maimartaba yayi yana jin ƙaunar ɗan sa na kawo masa tabbas zuciyar wasu sassauƙa ce mai yawan yafiya .
"Yaushe za ka tafi Niamey domin kawo ƙarshen zaman su a magarƙama ? Ko kouwa saƙo za'a aika musu ?
"Da kaina zan je doumin na sanya hannu a takardar da zai sa a sake su sannan ita kuma zan sahale mata amre na , cikin kwanaki biyu masu zuwa zan tafi .
"Kafin tafiyar ka a sanya a tattara kayan ita wannan ɗiya a aika da su garin su , shiyar ta kouwa ni da kaina zan sa a shirya shi ga ita ɗiyar da muka amso amanar ta daga ƙasar su insha Allah ita tana cikin amintattun mu Allah ya cigaba da baku kariya baki ɗayan ku ya kuma dauwamar da zaman lafiya tare da zuri'a masu Albarka tsakanin ka da matayen ka .
Wani irin farin-ciki Youssouf ya ji yana ratsa shi jin cewa ashe Maimartaba da kan sa ya sa aka dawo da Falmata har ma kuma ga shi zai sa a shirya mata wajen zama a gidan hakan yana nufin samun 'yanci tare da tabbacin zaman sa har abada da Fatima , idan hakane yana godiya ga Allah da duk wasu hatsararruka da ya tsallaƙe tunda ya tsira da Fatima-zahra.
"Amin Nagode Nagode ranka shi daɗe Allah ya ƙara girma tare da nisan kwana .
"Allah shine abun godiya Youssoufa .
Sun jima suna tattaunawa Maimartaba yana ba shi shawarwari cikin hikima tare da yi masa nasiha har hantsi ya ɗaga lokacin zaman fada ya gabato ,
Tare suka yi karin kumallo kafin yayi bankwana da Maimartaba zuciyar sa cike taf da farin-ciki gami da nutsuwa ta musamman , tabbas wanda duk yayi dace da iyaye na ƙwarai ya samu rabi na daga nasarar rayuwar sa .
Gefe guda yana sake jin haƙaƙewa akan rabuwa da Maimounatou bayan ta amsa masa tarin tambayoyin da kullum yake bitar su cikin ransa tare da burin jin amsa daga bakin ta .
Bai koma sashin su ba sai ya zarce shiyar Hajiya Umma zuciyar sa cike da ɗokin son ganin Fuskar Falmata a hasken ranar da ta fara ɗagowa , yana da tabbacin a shiyar Hajiya Umma anan aka mata masauƙi .
Abun Mamakin da ya tarar lokacin da ya riski falon Hajiya Umma bai wuce ganin ta tare da Hajiya Mama da sauran 'yan uwan sa baki ɗaya ciki har da 'yan ɗakin Hajiya Mama duk suna karin kumallo tare da hakan sosai yake sabon lamari a wajensu baki ɗaya .
Cike da jin daɗin ganin su haka a tare ya ƙarasa falon kai tsaye kusa da Hajiya Umma ya zauna , yana gaishe ta kafin ya juya ya gaishe da Hajiya Mama wacce ta amsa cikin nuna tsantsar farin-ciki kafin ta ɗora da tambayar sa ƙarfin jikin sa ? A ƙarshe ta bi shi da wata doguwar addu'ar da yasa zuciyar Hajiya Umma haske har ma ta fara samun 'yar nutsuwa akan ta karo na farko , fuskar ta ta cika da annashuwa tana amsa jerin addu'o'in da Hajiya Mama ke yi .
Da wata irin kulawa da ta zarce ƙa'ida Hajiya Mama tace
"Yarima Magajin sarki me za ka ci a zuba maka ? Da jin ɗaɗin kulawar da take masa ya ɗan yi taƙaitatcen murmushi kafin ya bata tabbacin tare da Maimartaba suka yi karin kumallo .
Wani murmushin yaƙe tayi ta jaa bakin ta tayi shiru sakamakon wata kibiyar baƙin-ciki da ta ji ta soki ran ta .
Sallamar da Hajja ta rangaɗo daga bakin ƙofa bai sa wasun su sun tsagaita daga hirar da suke ba , sai fa Youssoufa da Hajiya Mama sune suka yi hanzarin amsa Sallamar da su biyun daman kunnuwan su tarwai yake ga sauraron mai iya shigowa a dai-dai lokacin .
Daga inda Hajja ta saba tsugunnawa ta gaishe da Hajiya Umma yau ma daga nan tayi gurfano ta miƙa gaisuwar ta .
Hirarrakin su suke cigaba da yi ba wanda ya kula gaisuwar Hajja bayan ita Hajiya Umma da ta amsa sama-sama sai fa Youssoufa da ya amsa a mutunce cikin girmamawa.
Jim! Hajja tayi a zaune tana juya zancen da take tafe da shi a ran ta na rashin ganin Falmata ko sanin inda take a tun yammacin jiya .
Wanda ba ƙaramin tashin hankali ya jefa ta ba , domin kuwa ko baccin ta rabi-da-rabi tayi duk kuwa da cewa wani ɓangare na zuciyar ta na shaida mata cewa Falmatan tana tare da Youssouf ne tsakanin Mata da Miji bare ma a haɗa dai da 'ya'yan zamani.
Sai dai ganin Youssoufa a yanzu shi ɗaya ba tare da Falmatan ba ya sa taji cewa gara kawai ta tambaya domin samun tabbacin da zai bata nutsuwa dan haka ta gyara murya kafin tace "Ranka Ya dade Yarima ince dai Fatima ta kwana lafiya ? Domin kwana biyu tana fama da ciwon ƙafafu na saba mata tausa da asubar fari saboda ta ɗan ji dama-dama .
A ɗan jahilce Youssouf yake kallon Hajja kafin yace "Hajja ina itta Fatima ta fita da safe hakka ita da bata cika lafiya ba ?
Kalaman sa sun zo dai-dai da bugawar zuciyar Hajja a take ta ji wani tashin hankali mai girma yana durfafar ta cikin ruɗewa tace "ha'a ? Ai tun jiya bayan ta shigo nan domin taryar ka bata sake komawa ɗakin da aka mana masauƙi ba , ban sake ganin ta ba , yau Fatima bata kwana a ɗakin da aka sauƙe mu ba , ban kuma san inda take ba .
Hajja ta ƙare zancen da baza hannuwan ta biyu cikin tashin hankali.
"que de diable racontes-tu ? Youssouf ya furta hakan cikin ƙaraji tare da miƙewa akan ƙafafun sa da hakan ya jaa hankalin duk sauran mutanen dake wajen bayan Hajiya Mama da daman tuni take sauraron bayanan Hajja .
Muryasa cikin tashin hankali ya cigaba da cewa "Hajja wanne zance ne wannan ? Ina Fatima ta kwana ? Tare da wa aka gan su sun fita ina kuma suka tafi ?
Watsa hannuwa biyu Hajja ta kuma yi kafin tace "Allahu shi ya barwa kan sa sani ni dai ba shakka ban san inda ta tafi ba .
Cikin nutsuwa Hajiya Umma da zuwa lokacin ta ji abunda Hajja take cewa ta dubi Youssouf "Mene ne ya faru ?
Ta tambaye shi , wani ɗan taku ɗaya biyu yayi kafin yace "Fatima, elle est partie, elle est perdue.
"comme quoi ? Ubbo ta furta hakan tana tsare Hajja da ido kafin ta ɗora da cewa "kuma sai dai idan da kan ta ta tai wani wuri .
Hajiya Mama ta muskuɗa tare da cewa "wai meye ya faru ? Wace ce Fatima ?
Damuwa na bayyana a fuskar Hajiya Umma tace "ɗiyar Nigeria da Youssoufa ke amre ita ce ta ba'a gan ta ba .
Salatin da Hajiya Mama tayi ya sake dilmiyar da Hajja da Youssouf cikin ƙarin wata damuwar kafin tace "to ina ta tafi ? An kuma duba ko'ina ba'a gan ta ba ? Bai fa kamata a zauna ba a yi oumarni maza a fantsama neman ta cikin gida ba'a rasa inda tayi ba.
Kafin a ɗau wani lokaci baki ɗaya bayu masu ɗauke da alhakin tsaron gidan sun fatsama neman Falmata lungu da saƙo na gidan ƙarƙashin umarnin Biyamuradi .
Kasa zama Youssouf yayi ya kama hanyar komawa sashin sa zuciyar sa cike da fatan zuwa ya tarar da ita a inda jiya ta shiga ta ɓuya .
A bakin ƙofar sashin suka ci karo da Siyama wacce ta ci kwalliya cikin riga da zani na wani sassalkan leshi sai zuba ƙamshi take fatar ta na ƙyalli .
Da fara'a ta tare shi zuciyar ta da koyaushe ke kwaɗayin ganin sa tana cika da farin-ciki .
Sai dai ga mamakin ta bai ko saurare ta ba ya wuce ta da sassarfa da alamun rashin nutsuwa a tare da shi .
Da sauri ta taka ta bi bayan shi bayan ta ɗauki Yumna da tasan ba zata iya sauri ba .
"Baban Yumna lafiya kouwa ? Me yake faruwa na gan ka haka hankali tashe ?
"Wai Fatima-zahra ta ɓace tun jiya ba'a gan ta ba .
Ya furta hakan lokacin da yake ƙarasawa gaban bishiyoyin da a jiya ta ɓuya bayan su , bai jinkirta ba ya tsallaka bayan bishiyoyin yana ƙiran sunan ta da wani irin sauti .
Sasakai! Siyama tayi tana cikin yanayi mai kama da almara wai Fatima ta ɓata shi kuma Youssouf ya zo neman ta nan bayan shukoki anya Youssoufa ba matsala ya samu cikin ƙwaƙwalwar sa ba ? idan ba haka ba me zai kawo Fatiman nan bayan shuke-shuke'?
Haka ya gaji da bankaɗa ganye ya fito jikin sa duk ya ɗau ƙura idanun sa sun yi jawur .
"Baban Yumna Fatima kake nema anan kuma ?
Cikin duƙusasshiyar murya yayi mata nuni da wajen yana cewa "anan jiya mun ka shiga ɗaki mun ka bar ta, kafin zouwan ki ina tare da itta a can
Ya ƙarasa zancen da nuna mata bakin barandar sa kafin ya ɗora da cigaba da cewa " Ina Fatima zata sake tafiya ta bar ni ?
Kamar ruwa ya cinye ta Siyama tayi shiru , zuwa yanzu ta fahimci abunda yake nufi da neman ta anan ashe ma jiya sun haɗu har sun gana? Ita har sokuwar zuciyar ta ke kambama ta a matsayin wacce ta fara kasancewa da Youssouf ɗin a jiya ashe hasashen ta bai zama gaskiya ba koyaushe alfarmar Fatima take ci daga wurin sa muddin ta samu cikakkiyar kulawar sa to Fatima ce ta mata tubalin ginuwar farin-ciki da nishaɗin sa .
Bata ankara ba ta ga ya sake wuce ta yayi hanyar fita daga sashin nasu , da sassarfa ta bi bayan sa .
Bayan kamar awa biyu labarin ɓatan Falmata ya fara zagaye masarautar bayan shafe fiye da awa guda da bayun gidan suka yi suna neman ta a cikin gidan amma ko wanda yace ya gan ta ma ba'a samu ba bayan masu gadin shiyar Youssoufa da suka bada tabbacin shigar ta da fitar ta daga sashin .
Zaman dirshan Youssoufa yayi a falon Hajiya Umma yana jin wani irin bugu da ya wuce ƙima da zuciyar sa ke yi .
Hajja kuwa zuwa lokacin ta fara sharar hawaye da gefen mayafin ta .
Ubbo wacce take cike da takaicin damuwar da ɗan uwan ta yake shiga ta sanadin Falmata tace
"To wai za ta ɓata ne ? Sai dai idan da ƙafafun ta ta fice doumin kouwa ai hakan bai zama sabon abu ba wajen ta .
Kallon ta Youssouf yayi zai ce wani abu Hafsatouwa wacce ita ce ƙarshen dawowa daga neman Falmata da aka fantsama su tayi gurfano a gaban su hannun ta riƙe da cukurkuɗaɗɗen Mayafi.
Da hannu biyu ta miƙawa Youssoufa kafin ta ɗora da cewa " wannan mayafin can wajen ƙofar fita gida ta ɓangaren kudu na tsinto shi wanda kuma nayi hasashen ya.....
Miƙewar da Youssouf yayi riƙe da mayafin ya sa ta yin shiru duk suka zuba masa ido .
Yana riƙe da mayafin ya kai shi ga hancin sa yana shinshinawa kafin ya ɗago kan sa da wani irin sauti yace "lalle wannan shine Mayafin da ta rufu da shi a jiya .
Ita ma Hajja gyaɗa kai tayi cike da tabbatarwa tace "ƙwarai wannan mayafin Fatima ne to ita tana ina ?
Muryar Hajiya Mama da ta ratso wajen ta katse musu hanzari inda take cewa "wannan alama ce da take nuna yarinyar nan an fita da ita daga gidan nan ne ta ƙarfin tsiya kuma babu makawa sace ta aka yi .
Wani ƙaƙƙarfan kuka Hajja ta sa wanda ya ratsa zuciyar Youssouf ya tarwatsa duk wata nutsuwa da ta masa saura .
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon yanzu wanne azzalumin ne ya ɗauke yarinyar nan a wannan yanayin da take ciki na shiga uku ni hauwa'u 'yar mutane ta ɓata a hannun mu .
Hajja ta furta hakan tana rufe fuskar ta da mayafin ta ta shiga rera kuka .
Shigowar Babbar jakadiya yasa kallon su ya koma kan ta , saƙon Maimartaba ta isar inda take shaida musu kan cewa baki ɗaya yana neman su a shiyar sa a yanzu-yanzu da gaugawa.
Ba a ɗau lokaci ba dukkanin su daga kan Hajiya Umma , Hajiya Mama da su Ubbo duk suka cika falon Maimartaba suka yi zaune suna sauraron sa .
Bayan duk sun nutsu yace "wani labari ya zo mana Fada kan cewa wannan ɗiya ta Nigeria ta ɓata a cikin gidan nan yaya gaskiyar lamarin yake ?
Shiru duk suka yi kafin Hajiya Umma tace "Hakane ran ka ya dade amma duk cikin mu babu wanda yake da masaniya kan haƙiƙanin yaya lamarin ya kasance domin ba'a gan ta a gida ba ba'a ga kuma wanda ya ce ya ga ficewar ta ba .
"Rashin tsaro a gidan har ya zama haka da za'a nemi mutum sukutum a rasa ?
Maimartaba ya furta haka da bayyanuwar matsanancin ɓacin-rai a fuskar sa .
A hankali Ubbo tace "Ranka ya dade Allah ya daɗa maka nisan kwana ka cigaba da jagorar mu ni nafi tunanin Yarinyar nan ba ɓata tayi ba sai dai tafiya tayi da kan ta kamar yadda ta taɓa yi daga Niamey zuwa ƙasar su dan...
Da wani irin sauti saɓanin wanda aka saba amfani da shi a masarauta yayin da ake gaban sarki Hajja tace " 'Yar nan wannan zancen naki ba gaskiya bane muddin kuma ya zama gaskiya to kune sanadi , saboda abubuwan da kuke yiwa yarinyar nan na tozarci kaɗai ya isa yasa ta zuciya ta bar gidan nan haba mana shin shi talaka ba mutum bane ? Ko kuwa laifin tayi domin ta auri ɗan uwan ku ? Fatima baiwar Allah yarinya ce ƙarama da take da larura wanda idan har baku gwada mata ƙauna ba bai kuwa dace ace kuna tozarta ta ba yanzu me za'a ce ga iyayen ta da kuka yi sanadiyar da ta gudu ba'a san halin da take ciki ba ?..... kasa cigaba tayi da magana saboda kukan da ya ci ƙarfin ta
Hajiya Umma ta yunƙuro zata yi magana da hannu Maimartaba ya dakatar da ita .
"Me yake Faruwa a gidan da ni ban kai ga sani ba ? Waye yake tozarta Al'umma ciki har ma da mutanen da suke amintattun mu da muka amso amarnar su daga hannun mutanen su ?
Shiru aka yi babu mai tsaurin idon iya amsawa .
Kamar daga sama Muryar Youssouf ta ratso wajen inda yake cewa " Fatima ba gudu tayi ba babu makawa ɗauke ta aka yi ..
Ya ɗan jinkirta lokacin da idanun kowa ya dawo kan shi zuciyar Hajiya Mama ta fara sauya ƙarfin bugu tana dik-dik-dirim-dim.
"Wa kake tunanin ya ɗauke ta ?
Maimartaba ya furta haka cike da nazarin sa ,
Shiru yayi da yasa gumi ya shiga zarya ta cikin rigar Hajiya Mama .
"Maimounatou .
Ya furta hakan da tasowar matsanancin ɓacin rai a muryar sa , ya cigaba da cewa
"Maimounatou ita ta sanya a zo a ɗauke Fatima domin cikar burin ta ta wani fanni sai dai a wannan karon ba zan kyale ta ba dole ne na gwada mata ainashin ɗabi'ar da na ɗau shekaru a wajen koyar ta cikin aikina na na soji .
Muryar Hajiya Mama ita ta ratso wajen cike da wani boyayyen farin-ciki a sautin ta tace " Yarima ni da kaina tunanin da ya fara zowar min kenan ba shakka wannan ɗiyar ta Agades ita ta sanya anka ɗauke wannan yarinya ta ƙwarai kuma dole ayi hanzarin ɗaukar mataki akan haka.
Shiru Maimartaba yayi cikin son yin nazari sai dai hayaniyar da ta fara tashi a tsakanin iyalan sa da duk suka aminta da cewa Maimounatou ce ta tura aka sace Falmata duk kuwa da babu hujja ɗaya da aka samu wanda yake bada tabbaci ga hakan ya dukusar da hanzarin sa musamman lokacin da Youssouf ya miƙe a safure ya taho gaban shi yayi gurfano .
"Ranka shi daɗe zan tai Niamey yanzu zan tai na tadda Maimounatou ta faɗa min ina ta kai iyalina ?
"Youssoufa ka nutsu wannan batu ne da yake buƙatar nutsuwa da tsawaita bincike , ina maka oumarni da ka jinkirta hanzarin da kake yi har a ƙarƙare bincike a samu madogara .
Da kyar Maimartaba ya shawo kan hayaniyar su bayan ya tabbatar da za'a tsananta bincike kafin tunkarar koma waye da aka samu shaidar yana da hannu a ɓatan Falmata
Bayan fitar su daga Sashin Maimartaba Hajiya Mama bata koma sashin Hajiya Umma ba kai tsaye sashin ta ta koma ba tare da ta zauna cikin 'ya'yan ta da suke ta hira kan batun ɓacewar Matar Youssouf da wasu daga ciki ma daɗin lamarin suke ji saboda ta riga ta gina ƙaƙƙarfar ƙiyayya tsakanin su da Youssouf da duk wani abu na bakin-ciki da zai faru da shi su murna suke yi .
Can ƙuryar ɗakin ta