Showing 120001 words to 123000 words out of 411050 words

Chapter 41 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14367

cikin ɗaki sai fa idan rahima ta tuno su tazo ta ishe su da surutu tare da mitar meyasa basa son fitowa cikin jama'a ," ??

   Yau ya rage saura kwanaki uku ayi ɗaurin aure kuma a yau ne za'a fara gabatar da shagulgulan bikin , inda a yau ɗin ne suke shirin yin arabs day dan haka gidan danƙam yake da ƴan mata kawayen ita amaryar da yawancin su daga nesa suke , sun yi guzurin manyan jakankunan su da suke cike da suturun su zuwa kayan kwalliyar su da takalma , dukkanin su gogaggu ne kuma wayayyu , kuma ƴaƴan manya irin ta, yawan su ya sa ɗakin ta ya gaza ɗaukar su , dan haka suka rarrabu wasun su suka samu wuri a ɗakin hafsa , da rahima , sauran ukun kuma suka sauƙa a ɗakin su yakaka ,

Tashin farko lokacin da suka shiga ɗakin da suka ga su yakaka , ɗaya daga cikin su ta tambayi zainab ɗin da ta rako su ɗakin da kan ta

    Friend Waɗannan ɗin su waye ?

Ƴan gudun hijira ne ,' ta basu amsa kai tsaye
    Yakaka ga ƙawaye na dallah ku ɗan ara musu shimfiɗun ku kafin .....
  Tun kafin ta ƙarasa babbar ƙawar ta da tun da suka shigo ɗakin take yatsina tana ƙarewa ɗakin kallo , tace
     Zee mekike nufi ? Kaddai kice min kan shimfiɗar da ƴan gudun hijira suka gama birgima zamu kwanta ? Kalan mu ɗauki wata cutar ,? Ko kuwa kwarkwata ta maƙale mana ko amosani ?
   Wata ƴar iskar dariya suka kwashe da shi ,"kai sofi baki da kyau ,kuma fa da gaskiyar ki ,"
   Ɗan murmushin ƴake zainab tayi

  Kai haba dai sofi , baki ga sun waye bane ? Ai kin ga babu alamun ƙazanta har haka tattare da su ," amma bari na samo sabbbin bedsheets idan ya so sai ayi sauya muku, sai su kuma su koma falo suna kwanciya kawai haka yayi ko ? Ta furta hakan tana mai barin ɗakin cikin sauri domun ta kawo bedsheets ɗin , har tayi nisa ta tsinkayi muryar ɗayar su tana cewa ,"
   Ki zo da germs kill/anti bacteria dan a wanke bathroom ma sosai  da kuma room freshener ,"
   Ta amsa da toh ,"tana ƙara sauri .
Sai kuwa ga ta da duk abubuwan da suka lissafa ,'
   Su kuma har lokacin suna tsaye akan kafafun su , suna hirararrakin su tare da latse-latsen waya ,

     Nan ta zube kayan a gefe ,

To wa zai gyara ɗakin ina housemaid ?

  Cikin ƙosawa zainab tace duk basu nan sun tafi kasuwa ,"

Duban ta ta mayar kan su yakaka da suke zaune daga gefen wardrobe sun yi shiru kamar ruwa ya cisu , duk suna jin maganganun su ,"

    Ke fatima tashi ki je ki wanke musu bathroom ke kuma yakaka ki sauya bedsheets ɗin tare da share musu ɗakin ya fita da kyau ki fesa turaren nan , " ta mayar da duban ta kan ƙawayen ta , muje ɗaki na kafin su gama aikin sai ku zo ku shirya , "

  Daga haka suka kama barin ɗakin suna masu cigaba da dararrakin su ,"

  Ɗan shiru ne ya ratsa ɗakin , kamar haɗin baki kowaccen su ta ce

   Bari ni zan yi aikin yakaka ke baki da lafiya ,'
  Bari ni nayi duk aiyukan falmata ke ki zauna anan ki jirani ,"
  Nan suka kama musu ƙarshe a dole falmata ta sakarwa yakaka dukkanin aiyukan ganin har ran ta ya fara ɓaci ,"

  Bata ɗau lokaci ba ta gama , zuwa tayi ta kama hannun falmatan zo muje mu faɗa musu mun gama sai mu samu wurin zama ko ta waje ne mu zauna ,"
    Sama-sama zainab ɗin ta amsa musu lokacin da suke sanar da ita sun gyara ɗakin ,' saboda hayaniyar ƙawayen ta da ta cika ɗakin ,"

   Nan suka kamo da baya tare da kama hanyar barin falon , kichiɓus suka yi da hafsa tare da wata ƙanwar baban su da ta titsiye ta tana mitar ta ƙira mata hamza ya zo ya ƙaro musu ma'aikata ,'domin aikin yayi yawa yafi ƙarfin ƴan aiki huɗu baza su iya bada abunda suke so ba ,"

    Wayar ta sa taƙi shiga ga alama a kashe take watakila yana kan aiki ne ,"
    Auntie hajja wayar ta sa bata shiga , amma ga waɗannan su biyun su ma ƴan gudun hijira ne kawai aje da su wajen da ake aikin su kama , kafin a ƙaro wasun ,"  ta furta hakan tana mai nuna mata su yakaka da suke ƙarasowa wurin ,'
     Kallon su tayi sama-da-ƙasa , kafin ta ce
   Toh su zo mu je ,"

Ku bita zaku je wurin aiki , ta furta musu hakan tana mai shigewa cikin falon ba tare da ta ko sake waiwayo su ba ,'

    Jikin su ba ƙwari suka bi bayan wacce aka ce su bitan , har zuwa wani faffaɗan fili da yake ta chan baya ƙarshen gidan , inda aka kafa babbar rumfa aka kakkafa manyan murhu da takwane , gefe guda ga manya-manyan kasko da aka cika shi fal da mai ana suyar dubulan da alkaki , ga kuma manyan daruna an cika su fal da ruwan narkakken sugar ,"

aiki dai kacha-kacha ta ko'ina , da kallo yakaka ta bi hamshaƙan matan su kusan rai shida da suke tsaitsaye akan aikin , daga wuya zuwa kunne da hannuwan su sai ƙyallin gwalagwalai suke , yayin da daga sun buɗe baki hasken haƙoran gwal da suka yi ado da su a hakoran su yake ɗauke ido ,"

ko alama hannun su bai taɓa aikin ba , illa wasu jikkatattun manya mata su huɗu da suke yin duk wasu aiyukan wajen suna ta faman kai kawo ,"
      Ga wasu masu aikin biyu ƴan mata an ƙaro su ,"
   Cewar wacce suka biyo ɗin ,'
   Waɗannan ai yara ne wane aikin kirki zasu yi da ya wuce wanke wanke da aike ? Inji ɗaya daga cikin matan ,"
  
   Ko shi ɗin ma dai su yi , ai kuma zasu iya irin su soya abubuwa ma , "

   Ke babbar ki zauna anan ki cigaba da suyar dubulan ɗin nan , ƙaramar kuma ga wanke wanken abubuwan da aka yi ƙwabin fulawar a ciki ki wanke ki kawo mana zamu sake yin amfani da su , cewar ɗays daga cikin ƴan aikin ,'

  Cikin ƙasƙantar da kai suka haɗa baki wurin amsawa da toh ,' aiki ba sabon abu bane a wurin su , kuma basu jin tsoron aiki kome yawan sa ,"

  Yakaka ta kama hannun falmata ta kaita wurin da aka tara wanke wanken manyan darunan silver da farantan silver manya da a zahiri sun fi ƙarfin hannun falmata ,
     Ga bakin fanfo falmata ta sanya mata bakin tiyo ɗin da yake zubar ruwa akan hannun ta , kuma ga omo ga soso , ki wanke da kyau kin ji ?idan kin gama ki min magana kar ki taso ke ɗaya kin ga gurin akwai murhu ,!
    Toh yakaka

Daga haka ta je ta kama aikin da ita ma aka sa ta ,

   Yakaka ta kama wannan aikin ta gama ta hau wancen , falmata tayi wanke wanke ta ƙara , har yamma suna wannan wurin , nan suka ci abincin rana da yin sallolin , gajiya tilis sun yi ta musamman ma yakaka da bayan ta ya riƙe ƙam , 'kawai karfin hali take amma a zahiri aikin yayi mata yawa , ' daga inda suke suna jiyo yadda ƙidan wakokin larabawa suke tashi ta cikin gida tare da tsinkayo hayaniyar jama'ah ,"

  Karfe biyar aka sake kawo wani aikin wanda girki ne za'ayi na abincin dare a ainahin babban kitchen ɗin gidan , nan aka bar su yakaka suyi zaman gadi a wurin tare da ƙarasa tsoma sauran dubbulun da alkakin a ruwan sugar kafin a zo a juye su a ma'adanai a killace su,

Har karfe takwas na dare suna wajen ,  zuwa lokacin hayaniya ta ɗan ragu a gidan ,saboda ɗaukewar kiɗa , sai dai shewa da dararrakin jama'a , falmata har ta fara gyanyaɗi saboda tsabar gajiya ,"babu abun da take so irin ta ji ta kwance bisa ƴar katifar ta amma ta san yau kam babu damar hawa wannan katifar ,

Chan sai ga hamshaƙan matan nan sun zo tare da wasu mata da alama su ma ma'aikata ne , nan suka ce su juye kome a manyan robobin tara ruwa , bayan sun sallami su yakaka babu ko sannu bare nagode , ! To meye ƴan aiki ne fa ? !

  A gajiye liƙis suke cire takun kafafun su , duk sun yi laushi ,' ko magana sun gaza yi da juna burin kowaccen su ta samu muhallin ajiye haƙarƙarin ta
    Tun daga bullowar su farfajiyar gidan hasken da yake wadace gal a wurin ya haske fuskokin su , babbar mashigar kofar gidan a buɗe take motoci sai kai kawo suke ,

Sun kawo tsakiyar farfajiyar kusa da ƴar hanyar da zata sada su da cikin sashin kwanan su , ya sanyo kan motar sa cikin gidan ,' idanun sa suka sauka a kan su , me suke yi a nan da daren nan wajen karfe tara ? Da sauri ya ajiye motar sa a mazaunin ta ya fito dags cikin motar yana bin su da kallo nan ya hango yadda suke duk a hargitse , kasan zanin falmata duk a jiƙe ,"
   Ya taka da niyyar bin su , sai wasu ƴan uwan su mata su kusan rai biyar suka kutso kai cikin gidan , suna hango shi kuwa suka nufo shi suna gaishe shi tare da tsokanar shi kasantuwar su abokan wasa , nan dai dole suka tsayar da shi da ƴar hirar su ta zumunci ,
  Zuwa lokacin da suka wuce su yakaka sun riga sun shige sun ɓacewa ganin sa ,

   Shiru yayi a tsaye yana sake tunano yanayin da ya gan su ciki , " ba dai aiki aka sanya su ba ? Ya tambayi kan sa ,"
     Nufar sashin sa yayi yana haɗa kamannin da ya gan su ciki da wanda yanzu ya ga yaran matan nan ƴan uwan sa a ciki , hakan ya tuno masa da abunda baki ɗaya ya manta "watau yiwa su yakaka ɗinkin fitar biki," al'amura sun haɗu sun chakuɗe masa , yanzu haka fita zai sake yi domin yana so ya ƙarasa shirye-shiryen kome kafin jibi da tawagar masu neman auren zasu iso daga garin abuja ," a ɗaura a basu matar su juya da ita bayan anyi walima ," sauran bukukuwan chan a abuja zasu ƙarasa bikin irin na su na soji ,"

Sannan a daren na yau yana so ƙwarai ya je yaga mahaifitar sa a unguwar da tayi bigire,'

Duk yadda za'a yi dai goben zai samu ya saya musu kayan fitar bikin ko da ready made ne saboda lokacin yin ɗinki ya ƙure ,"  da wannan tunanin ya ƙarasa shigewa sashin sa ,'

Su yakaka a cike suka tarad da falon duk kuwa da girman sa ,"yaran mata ne masu aure da marasa aure birjik a falon su da ƴaƴan su ,kowacce tana wace wance ," kaf ɗin su dangin juna ne , saboda ta bangaren mahaifin su manyan gida ne kuma shahararrun masu kuɗi kaf garin ansa kakan su wanda ya haifi baban su ,'

Kamar jiran shigowar su hafsa take wacce take tsaye suna magana da wata ƙawar su ," tace
   Yauwa yakaka dan Allah ɗauki Mopper nan ki goge duk illahirin cikin falon nan saboda akwai ruwa-ruwa kar a tattaka a faɗi ,"

  Cikin juriya yakaka ta amsa
   toh anti hafsa ,
Tas ta goge faffaɗan tiles ɗin ta ɗauraye mopper ta ajiye , ta dawo inda ta bar falmata a tsaye ,daga bakin kofa ,

  Falmata zo muje ki gani na gano mana wurin kwana ,"

Wata ƴar siririyar hanya ta kai su da take bangaren hagu na falon da wata ƴar kofa ɗaya jal ta karfe , ta tsakanin karafunan kofar yakaka ta hango step ɗin bene , da yayi sama wanda a duk zaman ta a gidan kusan watanni biyu bata san cewa akwai bene ba ta cikin falon ,"

Kinga sai muyi kwanciyar mu anan tunda babu kowa , koh ?

********

Daidai da rana guda bai taɓa mantawa da ƙanƙanuwar yarinyar da ya lalatawa rayuwa ba , kullum sake ganin laifin kan sa yake a duk lokacin da yayi hasashen irin halin da ya bar ta da wanda a yanzu zata iya kasancewa a ciki ya kan shiga zullumin da yake kai ga hana shi walwala ,,

Yayi nadama marar iyaka da ta sa har yau yana laluben neman sanin haƙiƙanin abunda ya same shi a wancen lokacin da har ya aikata abunda ko a mafarkin sa bai taɓa nuna masa shi youssouf zai aikata ba ,' idan akwai abunda yake bashi mamaki da sanya shi hamdala bai wuce wucewar wannan lamarin ko kuwa yace warkewar ciwon da ya kai shi ga aikata mummunan aikin ba , tun daga ranar da ya bar ta bai sake jin son kasancewa da wata mace a irin wannan yanayin ba , ya koma youssouf ɗin sa da ya san kan sa ,"

Ko ruwan burkutu yanzu ba sosai ya cika neman ta ba , sai jifa jifa jarabar sa da burkutun ya ragu da kusan kaso shidda cikin goma , kuma a lokuta da dama ko giyar company ma ya samu ya ɗan kurɓa yana jin kwaɗayin sa da barasar ya kau ,

Bulayin neman abunda zai sa shi ya goge laifin sa ko kuwa ya gyara barnan da yayi a wurin yarinyar , ya sanya shi ɗaukar tsawon lokaci bai sake waiwayar ta ba duk da cewa sau da dama a farkon rabuwar su ya sha ganin kiran ta ta layin da ya saya mata , kafin daga baya ya daina ganin kiran ,

  Ya shiga damuwa da har ya sashi fara neman layin nata sai dai amsa guda yake samu kullum daga computer shine wayar tata a kashe take ," meya same ta ? Wane hali take ciki ? Wacce irin rayuwa take yi ?? Bai sani ba !

Zuwa lokacin da ya samar da abun da yake ganin zai taimaka mishi gurin gyaro ɓarnar da yayi , kuma sai yanayin aiki ya tsaida shi ,tare da sake yin nisa da inda take , amma ya ƙudurce ba zai bar kasar ba har sai ya gyaro barnar da yayi ta hanyar da shi yake ganin ya dace ,"

Dan haka da yanzu ya samu damar da zai iya fita daga wajen aikin ya taka zuwa cikin garin da take , domin a jiya da suka yi waya da tafeeda ya sanar da shi cewa ya shigo ƙasar nigeria a halin yanzu yana abuja , '

biyamuradin ya tabbatar masa da cewa zai halarci wurin ɗaurin auren , aina za'a yi bikin ɗaurin auren ? Amsar da ya bashi faɗuwa ce ta zo dai-dai da zama domin ya tabbatar masa da auran a jahar borno za'a ɗaura shi cikin birnin na maiduguri ,"

shikenan ma ba sai na zo har abuja ba , zan tsumaye ku cikin birnin maiduguri domun ai cikin garin nai bigire ," amsar da youssouf ya bawa tafeeda kenan !

Washegari , tun sassafe aka kaɗa kan su yakaka zuwa wurin aiki , ba'a ko bar su sun karya ba , sune shara wanke-wanke goge-goge basu nan basu chan , sai misalin sha ɗayan rana aikin ya dan tsahirta musu , suka shigo gidan suna rarrakaɓewa saboda kallon hadarin kaji da ake bin su da shi ,

Wanka suke so suyi su sauya kaya domin rabon su da wanka tun shekaran jiya , amma ko da suka shiga ɗakin da yake a zaman nasu , kawayen zainab da suke ta faman harƙƴallar su a ɗakin wasu na wanka wasu na karin kumallo koro su suka yi basu ko saurari zantukan da suke da nufin faɗi ba ,

haka suka fito jiki a sanyaye suka dawo bakin kofa suka rakaɓe ,"

Suna nan tsaye ya danno kan sa cikin sashin , yayi wankan sa fes cikin wani brown ɗin yadi mai shara-shara , sosai kayan suka ƙarbi kalar fatar jikin sa mai ɗan haske kaɗan ,

Akan su ya fara ɗora ido ,"

Me kuke anan fatima ?
Ya na gan ku haka wani iri ?
Anyi muku wani abu ne ?
Kun kuwa ci abinci ?

Ƙwallar da tuntuni take taruwa a idanun falmata suka tsiyayo ," lokacin da take saita idanun ta a sashin da ta ji tashin muryar sa

Mun ci abinci yaya dakta , kuma ba'a mana kome ba , cikin ne babu wurin zama sosai shiyasa muke tsaye anan 'yakaka ta amsa masa ,

Wanne irin babu wurin zama ?ba ga ɗakin ku ba ku shiga ciki kuyi zaman ku mana ko kun fi son zaman parlour  ne??

Wannan Karon falmata ce tayi karaf ta amsa
    Ai ƙawayen auntie zainab sun cika ɗakin , korar mu ma suka yi da muka shiga muna son muyi wanka mu chanja kayan mu ," ta furta hakan tana turo ɗan ƙaramin bakin ta bayan ta kumbura kumatu ,"irin su da ɗakin su ɗin nan," ( su falmata samun sarari tusar asuba )

  Da kallon nazari yake bin su , yana ƙoƙarin boye ɓacin ran sa a gaban su kan abunda aka musu ,

To wai ya na gan ku kun yi datti haka ,? Ba dai aiki kika je kina ta faman yi ba a wannan yanayin da kike ciki ?

   Tun jiya muke aiki yaya dakta yanzu ma muka gama na safe , cewar falmata , irin su a dole ga garkuwar su ,( ja'ira falmata an samu wuri )

Gabaɗaya bacin ran da yake ji ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login