Showing 213001 words to 216000 words out of 411050 words

Chapter 72 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14334

ta jikin sa , ya haɗa su ita da Mama wacce ita ma sanyin wajen ya fara damun ta duk kuwa da lodin kayan sanyin da suke naɗe da jikin ta ya rungume su ,

Cusa fuskar ta da sanyin yake shiga ta ƙofofin hancin ta tayi a jikin sa , ɗumin jikin sa ya sa ta ji sauƙin sanyin tare da yin lamo bata ko ƙwaƙƙwaran motsi .

Zaman mintoci Arba'in da biyar suka yi , lokacin da sanarwa ta karaɗe illahirin wajen ,

Would all passengers traveling to Rochester,  on flight FR3522 please have your Passport ready for boarding flight FR3522 now boarding at gate 21, Your flight is ready to Leave.

Fatima , tashi mou tafi , notre vol est prêt à partir ( jirgin mu ya fara shirin tashi ) .

  *****

Tafiyar awa guda da mintuna ishirin a sararin sama ya sada su da birnin Rochester dake babban garin New York ɗin Amurka da sanyin Asubahi ,

Bai zauna ba sai da ya yi waya a Hajiya  umma ya sanar da ita sauƙar sa lafiya , tayi masa fatan alheri , suka ajiye waya bayan ya biɗi da ta isar da sakon sauƙar sa lafiya da gaisuwa ga Maimartaba .

Yayi Niyyar ƙiran matan sa sai kuma ya fasa , da nufin sai sun cimma masauƙin su sannan .

Basu sha wani wahalan zaman jira ba suka sadu da Mr Brian ƙarƙashin hukumar asibitin Mayo da Biyamuradi ya riga ya tura musu duk wasu bayanai da ya kamata su sani game da hanyar tafiyar su tun daga Niger har zuwa saduwar su da Asibitin Mayo ,

Cikin mutuntawa bayan gaisuwar barka da zuwa Mr Brian yayi musu jagora zuwa wajen motar sa da zai ja su kai tsaye zuwa Asibitin su ,

A gajiye liƙis Falmata tayi mazauni a bayan motar hannun ta cikin na Youssouf , bayan ta zauna ,  ta kwantar da Mama a jikin ta da ita ma tayi laushi tuɓus , bakin nan tsit sai narai-narai da ido take, duk walwalar ta tayi ƙasa .

Awanni uku na gudun mota suka sada su da Mayo Clinic , asibitin da yayi suna a faɗin ƙasar Amurka da ma  duniya baki ɗaya wajen ƙwararrun likitocin da suka shafi manyan gagararrun cututtuka haɗi da ingantattun kayan aiki irin na zamani .

Doctor Williams Robert Shine ƙwararren likitan cutukan da suka shafi jini na yara da hukumar asibitin ta danƙa masa alhakin kula da lafiyar Safiyyah Youssouf Baskore .

Dan haka kai tsaye ofishin sa Mr Brian ya dangana da su , babu jinkiri suka samu iznin ganawa da shi da daman ya san da zuwan su .

Bayan sun yi taƙaitatciyar gaisuwa da harshen turancin Amurka cikin sakin fuska Doctor Williams ya nemi da su maƙala ( pilot in-ear / Ambasador,  ) ƴar na'urar da ake maƙalawa a kunne domin amfani da ita wajen fassara yare kai tsaye zuwa kunnen me sauraro cikin harshen da ya fi fahimta .

Tarin tambayoyi ne daki-daki ya dunga jero su game da matakan lafiyar Mama , Youssouf na amsa masa , lokaci zuwa lokaci yana auna Mama da na'urorin auna marasa lafiya  ,

Da hakan ya ɗauke su fiye da awanni biyu , har sai da Mama ta fara ƴan ƙananun rikici na gajiya , tana ture hannun Doctor Williams daga jikin ta fuskar ta a kwaɓe .

Bayan ya tattara bayanan cikin na'ura mai ƙwaƙwalwa dake gaban sa kan teburi ,

Ya musu iznin tafiya masauƙin su su huta zuwa gobe da zai sake ganin su ,

Wanda ya kawo su shi ya yi musu jagora zuwa masauƙin nasu da bashi da nisa sosai da cikin asibitin tafiyar mintoci basu wuce goma ba a mota , a tafiyar ƙafa zai kai mintoci ishirin da ɗoriya ,

Tun gabannin zuwan su da kwanaki biyar youssouf ya samu nasarar kama hayar ɗan madai-daicin gida na tsawon watanni huɗu a Lofts Apartment, dake 1st St SW.

Bakin wata ƴar ƙaramar ƙofa ya dakata da su , bayan youssouf ya sauƙe musu jakankunan su da ke bayan motar , Mr Brian ya miƙe masa ƴan mukullin gidan tare da shaida masa daga yanzu shi aikin sa ya ƙare idan suna buƙatar wani taimako akwai ma'aika na musamman da zasu zo waɗanda aikin su ne kulawa da su da lura da masauƙin su .


Bayan tafiyar Mr Brian , Youssouf ya kama hannu Falmata da Mama suka ƙarasa gaban ƴar ƙaramat ƙofar gidan tare da sanya ɗan makulli ya buɗe .

Sai da ya zaunar da su a cikin falo
sannan ya fita ya shigo musu da kayan su cikin sauri-sauri saboda tsananin sanyin da ke akwai duk kuwa da cewa rana ta take tsaka misalin sha biyu na rana agogon can .

Ɗan madai-daicin falon ya bi da kallo wanda yake tsare tsaf babu wasu tarkace illa kujeru da ƴan tebura sai Tv da kayan kallo daga gefe , tare da kan Tarho ajiye bisa ɗan teburi  , ko'ina a share a goge tamkar da ɗai ba'a taɓa rayuwa a gidan ba .

Idanun sa ne suka sauƙa akan Fireplace ( ɗan wajen da ake tanada domin hura wutar ɗumama ɗaki ) da sauri ya ƙarasa wajen cikin zuciyar sa yana hamdala , ya harhaɗa ƴan kututturan itatuwan ( ironwood ) da ya tarar a wajen da basu cika yawa ba , ya ɗau poker tare da cinna wuta a jikin itatuwan  ,

Hannun ta ya riƙo ya kawo ta gaban wutar ya ajiye ta ya ɗau mama ya ɗora bisa cinyar sa , suka yi shiru suna  ƴan kara hannuwan su ɗumin wutar na ratsa su , suna jin yadda jijiyoyin jikin su ke warwarewa , jinin jikin su na gudana .

Fatima muyi sallah sai na fita ga wajen gari na biɗɗo mana kayan cimaka da amfanin gida ,

To ,

Ta amsa tana miƙewa riƙe da hannun Mama

Hannun ta ya riƙo suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunan biyu da suke manne da juna , ɗan madaidaicin gado ne  a ɗakin na kwanciyar mutum biyu da yake shimfiɗe da rigar katifa sai matasan kai biyu, gefe kwabar kaya ce ,

ɗan ƙaramin agogo bisa teburin gefen gado shine abu na ƙarshe da yake girke cikin ɗakin

Gaba kaɗan daga fuskar gadon banɗaki ne wanda ake iya hango kome dake cikin sa ( mai murfin gilashi ) da a turance ake kiran sa da ( Framless Glass shower Door )

Tare suka shiga banɗakin ya gwada mata wajen alwala .

Bi yayi ya dudduba tsarin gidan da bashi da girma sai tsaruwa ɗan cas da shi kamar a ɗauke , bayan ɗakuna biyun da suke falon akwai kitchen da ke ɗauke da ƴan abubuwan buƙata da ya zama dole a kitchen , cikin kitchen ɗin anyi killatatcen guri domin cin abinci ,

Sai ƙaramin laundry dake ɗauke da na'urar wanke kaya .

Daga haka babu kome a gidan sai fa shinfiɗaɗɗen Hardwood floor ruwan zuma da ya malale ko wanne lungu da saƙo na gidan .

Ɗaya ɗakin ya shiga wanda ya tarar da shi ya ɗara wancen a girma haka ma kayan ciki sun fi na wancen girma sannan a cikin sa akwai ɗan ƙaramin fireplace da babu a ɗayan ɗakin ,

Cikin sauri ya shiga banɗaki domin yin uzurin sa , abunda ya ba shi mamaki tare da yi masa daɗi a lokaci guda bai wuce ganin Falmata da ta gama ɗaura Alwala tar a gaban shi ba tamkar suna banɗakin tare , nan ya fahimci banɗakin ɗaya ne me ƙofa biyu a tsakanin ɗakuna biyu da ake ƙiran irin sa da ( jack and jill bathroom )  sai dai wannan akwai gilashi a tsakanin su ,

Ya ji ɗaɗin ganin banɗakin a haka ba dan kome ba sai dan sake samun kusanci da ita a matsayin ta na mai laruri a kuma baƙon guri da bata kai ga haddace tsarin sa ba bare ta iya yin gaban kan ta a yayin mu'amalar cikin gida .

***

Baban Mama .

Ta ƙira sunan sa cikin sanyin Muryar ta lokacin da ta gama sallolin ta tana son fitowa daga ɗakin ta gaza gano ƙofar , ga sanyi da take ji yana daɗa ruɗa ta , gami da sasuƙaƙƙar yunwar da ta fara gallabar ƴan hanjin ta ,

Da sauri ya taso, kasantuwar daman hankalin sa na gare ta , ya fito zuwa ɗakin riƙe da Mama wacce take sanya ƴan ƙafafun ta a duk inda ya ajiye nasa ,

Yana tura ƙofar cikin rashin sani tana tsaye a wajen ƙofar ta ɗan daki fuskar ta ,

Ashih

Ta furta tana murza goshin ta  ,

Da sauri ya saki hannun Mama ya ƙarasa gami da tallafo ta jikin sa ya riƙo ƙugun ta ya ɗora tafin sa akan goshin ta yana murzawa a hankali

Je suis désolé Fatima,  ban san kina kussa ba , akwai zafi ? T'ai-je blessé ?

A hankali ta zame jikin ta ,

Ban ji ciwo ba , ka kaini wajen wuta na ji ɗumi nan akwai sanyi ,

Bai zauna a gaban Fireplace ɗin ba ,  yana tsaye akan ƙafar sa ya zura hannayen sa biyu cikin aljihun sweater dake jikin sa ya ce

Fatima zani dubo wajen gari ku zauna nan kadda ki tashi , bani jinkirtawa zan dawo , me kuke so daga abinci ?

Papa abinci j'ai faim aussi ,

Mama ta furta haka tana shirin fashewa da kuka ,

Mama kai ni wajen jakar kayan mu akwai Tourte à la viande,( meat pie )  samosa , sai mu ci mu sha ruwa ko ?

Eh mama , papa ka kawo jakkar mu  ,

Bayan ya miƙo mata jakar kayan ta , ta ciro ƙunshin meat pie da samosa,  da suke nade cikin takarda ,

Ƴar ajiyar zuciya yayi yana juyawa kan ƙafafun sa ,

Taku biyu yayi ya ji ta ƙira sunan sa ,

Baban Mama , ka tsaya ka ci abinci .

Kallon ta yayi ya ga ita ma bata kai ga fara cin abincin ba , sai Mama ta danƙawa meat pie babba ɗaya ,

Ku ci abinci Fatima idan na dawo zan ci rabo na ,

Bata amsa ba ya juya domin ya ƙagauta da ya tafi sanin da yayi idan yammaci tayi sanyin na iya ƙaruwa , 

Baban mama

Ta sake ƙiran sa

Fatima

ya ce yana juyowa gami da ɗora idanun sa kan fuskar ta ,

Sunkui da kai tayi , da zata iya hana shi fita zata yi ya bar su su kaɗai .

Ka dawo da wuri ,

Shiru tayi tana jiran amsar sa .

Da shi kuma ya ji kalmar ta ɗarsu a ran sa da wani irin yanayi da ya sanya shi murmusawa yana cigaba da kallon fuskar ta daga inda yake tsaye ,

Saboda-saboda nan baƙon waje ne ba mu san kowa ba , kar ka daɗe ko Mama zata nemi wani abu.

je serai bientôt de retour Fatima.
   Yace yana ƙarasa barin falon ya fita gami da rufo musu ƙofar .

Shiru tayi ta kasa cin wani abincin kirki duk kuwa da yunwar da take ji , tana jin kan ta a nesa sosai da ƙasar ta ta haihuwa kewar Nahiyar ta Al'ummar ta , Yaren ta ƴan Ƙasar ta na taso mata , yanayin tsananin sanyin Nahiyar  nan sam bai mata daɗi ba , yayi yawa . Ta gwammaci rana irin na Nahiyar ta ,( Africa ) " Tabbas kowa ya bar gida  ?

Zaman jiran awowi uku da lokaci ya  kai gefen la'asar ,nisan sa ya kai na kwanaki uku a wajen Falmata ,

Ta sauya salon tagumi ya fi iri takwas , Mama kuwa baccin ta take hankali kwance bisa jikin mamar ta ,

Ƙarar buɗe ƙofa ya sanya ta ɗago kai gami da maida hankalin ta kachokam kan ƙofar da fatan jin tashin muryar sa ,

Sallamar sa ya sa fara'ar da bata da masaniya daga inda ta ɓullo bayyana kan fuskar ta ,

ya shigo da kayayyaki niƙi-niƙi a hannun sa , bakin sa na amsa gaisuwar barka da dawowa da take jera masa ,

Fita yayi tare da sake shigowa da wasu kayan a jakankunan takarda , bayan ya sallami me taxi da ya kawo shi ya rufe ƙofar tare da ƙarasowa kan kujera ya zauna daga gefen ta.

Ɗaya daga cikin jakar kayan ya jawo , ya ciro safar hannu sun kai saiti takwas , haka ma na ƙafa ,a jiye su a gefe ya cigaba da zaro manya-manyan rigunan sanyi sun kai guda shida na mata masu launika daban-daban ƙaurara masu inganci

Fatima sauya wannan chandail ɗin da wannan Le pull ta fi nawi ,

Ta sauya rigar jikin ta da wata lallusar rigar sanyin da aka yi ta da fatar dabbar cikin ƙanƙara ( Bear ) me ɗauke da launin fari da baƙi , da ta kawo mata iya guiwar ta , zame hijabin kan ta yayi ya ɗora mata hular sanyi da take mahaɗin rigar , ya zarce da riƙo hannayen ta ya zira mata safar hannu ,

Sauƙa yayi bisa guiwowin sa bayan ya kamo tafukan ƙafar ta ya fara ƙoƙarin saka mata safa ,

Cikin sanyin murya ta ce

Baban Mama zan iya sakawa , tare da kai hannun ta ta sauƙe akan na shi hannun da yake sanyi ƙalau saboda yawon da yayi a waje .

Muryar shi a ƙasa ya ce .

Zan saka miki Fatima hakkin ki ne na kula da ke .

A hankali ta ɗauke hannun ta , ya ɗago ƙafar ta ya ɗora bisa cinyar sa cikin sannu kan hankali ya sanya mata safar ,

Nagode ta furta

A wani irin yanayi na jin tsantsar kusanci da shi ta tsinci kan ta da bata taɓa jin irin sa ba , wani shauƙi me daɗi ya fara ɗibar ta .

vous êtes belle ( kin yi kyau )

Ta tsinci muryar sa

Ɗan murmusawa tayi duk da bata ganin sa ta ji tashin muryar sa ya maida mata da martanin murmushin ta ,

Bayan tarin suturun da ya sayo musu da fiye da rabin su suke masu nawi ( kayan sanyi ) takalma da sauran suturu , da bargunan rufuwa .

ya sayo kayan abinci da fiye da rabin su na cikin gongoni ,da kwalaye ne irin wanda yake hasashen zasu iya ci musamman ma Falmata ( shi ai ya saba fita ƙasashen ƙetere ya saba da irin cimakar su)  Mama kuwa ya sayo mata kunun yara dai-dai shekarun ta da yake tsammanin zata so shi kasancewar ta ma'abociyar shan kunu .

Sai turarurruka da sabulai da sauran ƙananun abubuwan buƙatu na gida , sai kuma itacen wutar ɗumama ɗaki da ya ƙaro musu ,

Shi ya ajiye kome a muhallan da suka dace da hakan ya ɗauke shi har lokacin da duhun dare ya fara shigowa da yake hasashen magariba ta kawo jiki  , ya duba lokacin sallah ta yanar gizo ( online prayer timetable  )  ya ga cewa lokacin sallah yayi .

Bayan sun idar da sallar magarib da kan sa ya shiga kitchen domin samar musu da abunda za su ci ,

Elbow macaroni ya tafasa musu , tare da ƴar miyar da ya soya ta sama-sama bayan ya haɗa kifin gongoni da zallar tsokar nama na gongoni a ciki , nan take kitchen ɗin ya ɗau ƙamshin girkin maza .

Shi ya zuba musu a plate guda me ɗan girma suka ci tare baki ɗayan su .

Bayan sun sallaci isha' zaman shiru ne ya ratsa tsakanin su , saboda rashin sabo da yin hira da juna ,

Miƙewa yayi ya ɗauki mama wacce ta sake komawa baccin gajiya ,

Fatima tasso ku tai ku kwanta ke ma kiyi bacci dare ya yi da akwai gajiya ga jikkin mou .

Babu musu ta miƙe ya kama hannun ta zuwa ɗakin da yake mafi girma , bayan ya zaunar ta bakin gado  ya kwantar da mama daga tsakiyar gadon ya miƙe tare da ƙarasawa gaban fireplace ya kunna musu wuta

Ɗaya daga cikin bargon da ya kawo ya ɗauka ya rufa musu ,

Ki yi mouku du'a Fatima bonne nuit et fait de beaux rêves ,

gyaɗa kai tayi

Kan sofa ɗaya jal da take ɗakin ya koma ya kwanta tare da rufuwa da bargo  bakin sa ɗauke da addu'o'in neman tsari daga abun cutarwar da daren ke ɗauke da shi .

****

Iskar da take kaɗawa da ƙarfi tare da sauƙar dusar ƙanƙara suka sa birnin na Rochester ɗaukar matsanancin sanyin da ya sa baƙi ire-iren su Falmata gaza samun nutsuwar bacci saboda tun baccin farko da ya ɗan ɗauke ta da bai kai ko'ina ba ta farka saboda matsanancin sanyin da yake ratsa ɓargon jikin ta ,

Motsi ta sake yi a hankali gudun tada Mama wacce ga alama ita sanyin bai dame ta har sosai ba ko kuwa dan ta nitse ne cikin kayayyakin sanyi da bargo ?

sake tattakewa tayi a cikin bargon tana jin yadda ƙofofin hancin ta ke toshewa .

Biyamuradi da duk motsin da take yi a kunnen sa , ya buɗe kan sa daga cikin bargon sa , tare da miƙewa ya zauna ,

Ta hasken ƙwan fitilar gefen gado da bata cika haske ba ya hango yadda ta cure tana rawar sanyi ,

Kumama ce , bata son sanyi
ya kitsima haka cikin ran sa  ,

Miƙewa yayi ɗauke da bargon sa ya ƙaraso bakin gadon

Falmata wacce tayi lamo tana saurarar takun ƙafar sa cikin ran ta tana kitsimawa ,

Ashe shima ya kasa bacci ,?  Haba me ake da wannan irin sanyi kamar cikin firiji ?

Zuciyarta ta buga ɗas 

Lokacin ta ji hawowar sa kan gadon , bata yi aune ba ta ji kwanciyar sa ta bayan ta , hannuwan sa ya kai ya zagaye ta da su , ya zarce da sake matso da mama jikin Falmata ,

ya yi amfani da hannun sa guda wajen sake rufa musu bargo .

Lamo tayi tana shaƙar ƙamshin turaren jikin sa , bata ce kome ba kamar yadda shi ma bai ce ƙala ba ,

Sannu kan hankali ɗumin numfashin su ya gauraya tare da taimakon ɗumin jikin su da yake ratsowa ta cikin suturun jikin su, tsanani sanyin da suke ji ya ragu , bacci mai daɗi da nutsuwa ya yi awon gaba da su baki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login