Showing 1 words to 3000 words out of 411050 words

Chapter 1 - MAFARI COMPLETE BOOK HAUSA NOVELS BY UMMU MUAZ.txt

10 Sep 2025

14264

[6/24, 9:46 AM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: Fikrah writers association 

*MAFARI* .....
              ( _HARGITSIN RAYUWA_ )


*Umm'muaz*

      





بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ
الرَّحِيْم.......

*In The Name Of Allah, The Beneficent, The Merciful.*

*Da Sunan Allah Mai rahama Mai Jinƙai* .

  

_MAFARI...komai yana da farko, komai yana da tushe, komai yana da asali, HARGITSIN RAYUWA kan faru cikin kankanin lokaci_ .

_Duniyar daka saba da ita zata iya birkicewa zuwa baquwa a gareka cikin kankanin lokaci._

_Tafiya mabanbanciya da sauri, a cikin kaddara da dai-daito._



              1

*SHIMFIƊA*

Ƙauyen Mairambiri , wani ƙauye ne , ko kuwa "ƙaramar Alƙarya" da yake tsakanin ƙananan  hukumomin bama da konduga, wanda suke a karkashin jahar  ( BORNO )
Mutanen garin mafi akasarin su barebari ne " kanurai", sai kuma shuwa, da fulani, tsilla-tsilla, babbar sana'ar mutanen garin shine noma, suna da makarantun primary da secondry na gomnati, sai  kuma makarantun allo da mafiya yawan yaran garin  shi suka fi zuwa ,tsiraru ne suke zuwa bokon da suke kira karatun "Malam nasara", kasancewar garin nasu yana tsakanin manyan-manyan hukumomi biyu ya sanya suke da kasuwar su a bakin babban titin da yake tsakanin garin bama da konduga" wacce take ci duk ranar Alhamis.

                       **************

Cikin wani ƙwarababben gidan kasa , wasu yara ne su uku mata,  suna cin wani zazzafan damalmalallen tuwon hatsi miyar kuka shar cikin wani tsohon kwanon da duk lamba da tsatsa suka gama munana shi , babbar baza ta wuce shekaru 16 ba ,sai ta tsakiyar me kimanin shekaru 14, sai kuma ƙaramar su me kimanin shekaru 8.

Cikin nutsuwa babbar ta ke kai lomar tuwon bakin ta bayan ta sanyawa ƙaramar su ita ma a bakin ta ,saboda zafin tuwon ta kasa sanya hannu taci ,"alama yanzu aka sauke dumamen tuwon daga wuta "duk da yanzun farar safiya ne ko 6:30am bai cika ba.

Wata doguwar mace siririya me ɗauke da wata irin farar fata sol-sol kamar ta so ta zama zabiya " Albinism" dan hasken ta yayi irin nasu, wacce da ganin ramar da take da shi na tsabar wahala da talauci ne ,tana zaune kofar wani taƙwarƙwasashiyar rumfa da alama madafi ne ganin yadda duhun wajen yafi na ko'ina a gidan, hannunta riƙe da wani jariri namiji kansa tanƙwal da aski , ta ciro yamushashen siririn maman ta tana kokarin cusawa yaron a baki shi kuma daga ya kama yayi tsotsa ɗaya-biyu yake sakewa ya cigaba da tsala kukan da yake da alamun yunwa ce ke addabar sa .

Wani baƙin dogon mutum ne, ya bullo daga bayan durkusassun ɗakunan nasu guda biyu ,hannun sa rike da babbar robar ruwa (table water ), wacce aka yanke daga wuyan ta zuwa sama gefen ta daga kasa yana ɗan ɗigar da ruwan ciki daidai inda ya ɓule aka toshe da bakar leda .

Duƙawa  yayi tare da   wanke baƙaƙen kafafuwan sa da suke sanye cikin waɗansu ratattakakkun silifa (da guntun ruwan )  ,ya ɗago tare da kallon sashin da ƴaran nan suke zaune ya ɗan ɗauki wasu daƙiƙai yana kallon su cikin nazarin yadda babbar cikin take ta ciyar da kannan nata domin ya zuwa yanzu dai su duka biyun ita take sanya hannu tana zaƙulo tuwon da ya dilmiye cikin tsululun ruwan miyar da ta haura tuwon yawa har ta shaa kansa ,tana zaƙulo shi sannan ta hura iskar bakin ta ta gutsurawa ɗayar a hannu ta sanyawa karamar sauran abakin ta ,
kuma a take ta sake mayar da hannun ta cikin kwanon da hanzari tamkar dai ita bata jin zafin tuwon .

Yakaka " _nyidin biri bun" baa ? Duwan "bii lanyen wande kausuzuin_ (yakaka ke baza ki ci abincin bane ? Kiyi sauri ki ci mu tafi kar rana ta yi ) cewar wannan mutumin ga babbar ɗiyar ta sa da ya kira da suna yakaka cikin yaren su na " _KANURI_ .

Amsa masa tayi da "toh" ,dai-dai lokacin da ta miƙe da hanzari ta zagaya ta bayan matar nan da hasken fatar su yake yanayi ɗaya da nata ,ta ɗauko wani bakikkirin ɗin tiren kwano da yayi fatsa-fatsa da lamba ta nufi fasashiyar randar su da take binne a kasa sai iya fasashen bakin ta ake gani a waje "wanda za'a iya zaton rami ne"  ta sunkuya tayi goho ta kwarfi ruwa a chan kasa ta ɗauraye farantin ,

Ta sake kwarfo wani  ruwan a cikin bulalliyar moɗar da ta sha liki da leda , cikin gudu gudu ta je ta juye tuwon a kan farantin tare da ajiye musu ruwan , har ta yunƙura ta tashi ,sai karamar ta riƙo hannun ta ,a hankali ta ɗago idanun ta ta dubi kanwar tata wacce idan aka dauke kamanni irin na jini , da kuma siraran zane ( _Shunkurai_ ) da yake kan fuskokin su guda tara-tara "wanda yake bayyanawa a sarari daga ƙabilar da suke na barebarin usul " bayan hakan kowaccen su kamannin ta daban ne ,

Babbar su tana ɗiban yanayi da uwar su "watau fara ce sol yanayin hasken mutanen da suka so zama Zabiya ( albino ) yayin da ta tsakiyar take da rangwamen hasken fata ,karamar kuwa baka ce sosai kamar mahaifin su , Da alamu dukkanin su dogaye ne samɓala-Samɓala duk da cewa suna kan shekarun kuruciya sosai "yara ne " .
Cikin yaren su  karamar ta cewa babbar ta kawo mata gurji daga gona, shafa kan ta  tayi cikin nuna kauna tace zata kawo mata daga haka ta juya ta nufi ɗakin su tare da sako wani ɗangalallen hijabi cukurkuɗaɗɗe yagagge bakikkirin da shi ta kuma zagaya bayan ɗakunan nasu ta ɗauko wani buhu da alama abubuwan bukata a gona ne a ciki.

Duk abun da ake mahaifiyar  su  tana zaune bata umm "bata a ah ,sai faman girgiza jaririn ta take da sigar lallashi "shima fari ne sol irin ta amma  ita fuskar ta babu zane irin na ƴaƴan ta ga alamu ita ba babarbari bace , kamar yadda yaran da mahaifin su kana kallon fuskar su zaka shaida yaren su .

Sun zo zasu fita ita da mahaifin su  mahaifiyar  su ta miƙe ta rako su bakin zubabbiyar katangar da baza'a  ce mutane na rayuwa cikin zagayen ta ba , a bakin labulen tsunman da aka kare wawakeken giɓin da ya kasance mashigar gidan ( ƙofa ) , ta tokare sannan ta ɗaga hannu cikin maganar kurame tana musu alamar a dawo lafiya ta hanyar jujjuya tafufukan hannun ta ( _bye-bye_ ) tare da yin gwalatu cikin maganar bebaye," wanda hakan shi yake bada tabbacin KURMA ce "kallo ta bisu da shi fuskar ta ɗauke da murmushin da sai ita kadai ta san dalilin yin sa a cikin wannan yanayin da su ke ciki" .

Sun dauki tsawon lokaci suna girbi cikin ƙatuwar gonar su da take wajen gari ,Suna hirar su da kana ji kasan akwai soyayya da shaƙuwa me karfi tsakanin uban da ƴar sa kafin lokacin da yakaka ta cewa mahaifin su zata je kama ruwa (Ban ɗaki )  , ta juya gami da shiga cikin dogayen shukokin masarar da suka fidda kai suna jiran girbi , tana tsugunne cikin duhun gonar ta fara jiyo kabbara tare da iface-ifacen mutane .

Ta miƙe da sauri tana sanya ɗan kanfai (wondon ta ) , lokacin da taji mahaifin ta yana kwala kiran  neman ta da sauri ta nufo wurin da taji muryar sa , ita ma ta buɗe murya tana kiran sa tare da shaida masa ta dai-dai wurin take , wata razananniyar karar da taji tare da sake kusantowar kabbara da hayaniyar mutanen nan shi ya sake sa ta ruɗe .

Duk da bata san bindiga ba a zahiri amma tasan karar nan da take ji na abu me cutarwa ne , har zuwa lokacin da taji muryar mahaifin ta cikin ƙaraji yana cewa ta kwanta kar harbin bindiga ya same ta , ai sai ta sake ruɗewa ta nufo inda ta ji muryar sa cikin gunjin kuka da kiran sunan sa .

Shi kuma jin ta nufo shi ya sanya ya miƙe daga kwanciyar da yayi dan gujewa harsashi ,ya nufi inda yake jin kukan ta cikin tsoron kar harsashi ya same ta ko kuma ƴan tawayen su ganta su harbe ta ko su tafi da ita ( kamar yadda suka samu labarin hakan na faruwa a sauran garuruwa da ƙauyukan borno *ƳAN TAWAYEN BOKO HARAM* sun addabi mutanen ƴankin arewacin nigeria musamman jahar Borno da kewayenta wanda a nan mafarin abun ya ke. ) yana miƙewa yayi taku ɗaya biyu a na uku yaji kamar wani abu me karfi ya wuce ta jikin sa ya ɗauke shi yayi jifa da shi , yaji jikin sa kamar ba nashi ba .

Dai-dai lokacin da Yakaka ta ci tintiɓe da shi da sauri ta sunkuya gami da kamo shi ihun da ya ga ta sa tare da daura hannun ta akan kirjin sa yaga ta ɗago hannun na ta face-face da jini, shi ya tabbatar masa cewa harsashi ne ya same shi ,a take ya fara salati da karanto ɗukkanin addu'o'in da suka zo kan sa a lokacin  .

Ita da kanta baza ta iya kiyasta tsawon lokacin da ta ɗauka a zaune rungume da gawar mahaifin nata , wanda tun bayan da harsashin ya same shi bai sake ko minti goma ba ya rasu . ( *Yaa Allah ya jikan dukkanin ƴan uwa musulmai da suka rasa rayukan su a sanadin annobar Boko haram Ameen* )

Tayi kuka har hawayen ta ya ƙafe har tunanin ta ya tsaya , ta gigice iyakar ɗimaucewa ,ta rasa hankalin ta a tsakiyar gonar rungume da gawar mahaifin ta wanda jinin sa ya bata mata jiki face face ,har wani wuri ya fara bushewa a hankali ta ɗaga kanta ta dubi yadda dare ya fara alamun shigowa rana ta tafi zata faɗi ga kuma  hadarin da yake haɗowa, cikin shishiƙar kuka ,jiri da tsananin galabaita ta ɗaga kan mahaifin nata da tun kafin rai ya kammala fita daga jikin sa ta ɗora kan sa a kan cinyoyin ta a gaban idanun ta ya rasu ,ita ta ke bashi kalmar shahada duk da karancin shekarun ta , cikin wani irin kuka ta sake mayar da kan nashi ta ajiye bisa cinyoyin nata tare da sake rungume gawar shi ( da ta Riga ta fara ƙandarewa ) tana wani irin shishikar kuka , ta ɗau tsawon lokaci a haka sannan ta sake ɗagowa tare da zare hijabin kan ta ,ta shimfiɗa cikin karfin zuciya ta sauke kansa a hankali daga jikin ta ta ɗora akan hijabin nata, kuma ta ɗauki lokaci tana yi masa addu'a.

Sannan ta mike a zabure ta juya cikin hanzari ta nufi hanyar gidan su domin ta sanar tana tafe tana waiwayen duhun ciyawar da ta riga ta kare gawar mahaifin nata , har dai  ta zura da gudu tana kuka tana sharar hawayen ta.

Birki ta jaa tare da rage takun tafiyar ta lokacin da ta bullo bakin hanya , hakan yana da nasaba da guje guje gami da iface-iface da ƙarar harbe-harben da take ji yana tashi daga ainahin cikin ƙauyen nasu , kowa ta nufa da gudu domin ta tsaida shi tayi tambayar me ke faruwa sai taga an bangaje ta an wuce da gudu wasu na kuka wasu na salati da addu'o'i wasu kuwa kana ganin su ma kasan gudun ceton rayukan su suke domin dai duk sun kukkuje sun ji munanan raunika ,amma ahaka suke gudu suna barin ainahin cikin ƙauyen nasu zuwa cikin gonaki da daji.

A hankali ta ɗaga kanta sama tana iya hango yadda sararin samaniyar ƙauyen nasu ya tuniƙe da hayaki har ma tana iya hango harshen wuta da yayi tsiri yake toroƙo a wasu sashi na cikin garin, nan take wani irin tsoro da tashin hankali ya mamaye zuciyar ta tunowa da mahaifiyar da kannen ta da tayi suna cikin ƙauyen nasu ,da yanzu take hango tarwatsewar sa da mummunan bala'in da ya fada musu .

Cikin karfin zuciya ta yunƙura da gudu ta nufi hanyar gidan su , tana ta cin gware da karo da mutanen da suke gudu daga cikin garin( amma ko kula bata yi  ba) zuwa lokacin da ta ji carafa an kama hannun ta da karfi an fusgo ta, da sauri ta waiwaya tana fatan  ko ɗaya daga cikin ƴan gidan su ne "mamar su ko ƙannen ta.

Amma sai taga modu ne saurayin da unguwar su ɗaya ɗan maƙotan su ne , cikin sauri ta dawo da baya tare da rike hannayen sa biyu tana haki ,fuskar ta ɗauke da matsanancin tashin hankali take tambayar sa ina mamar ta ina kannen ta ? Amma maimakon ya bata amsa sai taga yana jaan ta da gudu su koma hanyar da ta bullo , da karfi ta fisge hannun ta tare da yi ma sa tsawa tana sake maimaita tambayar ta "Modu nda mamanyi nda kiramiyanyi " ?

Yakaka  yanzu ba lokacin tambaya bane domin rayukan mu suna cikin haɗari , ban san inda suke ba , ki zo mu gudu yagana, kashe mutane ƴan tawayen *BOKO HARAM*  suke sun yanka babanmu ,da yaa bakura sun tafi da Fannah da yaakori "(kannen sa) " maman mu ban san inda take ba ita da sauran kannen  mu ,sun ƙona gidan mu da gidan ku da ....

Tunda ya fara nisa cikin bayanin sa ta daina fahimtar me yake cewa , zuciyar ta ta tafi ga tunanin me yake faruwa da su ne ?, ta yaya zata rasa kowa da kome nata a yini ɗaya ? Baban ta ya mutu , bata san inda mahaifiyar ta da kannen ta suke ba a mace suke ko a raye ? Ina zata je ? Bata da kowa bata san kowa ba bata taba zuwa ko'ina ba babu inda ta sani bayan ƙauyen su , a hankali ta juya tana nufar cikin garin su hanyar unguwar su cikin ran ta tana aiyanawa gwara ita ma a kashe ta gwara ta mutu .

Bata da karfin jiki da na zuciyar tunkarar wannan sabuwar rayuwar da take tunkaro ta wacce bata hango kome a cikin ta ba sai tarin tashin hankali wuya da wahala ,maraici da rashin madafa .

Da karfi modu yake kwala mata kira yana so ta dawo su tafi domin shi yaga irin bala'in da bata gani ba da yake cikin garin wanda mutuwa ce murarar ta , mutuwar ma ta walakanci wanda aka harbe da bindiga ya mutu shi ya ji daɗi akan waɗan da aka kwantar aka yi wa yankan rago da waɗan da aka sanya wa wuta suka kone kurmus ,da waɗan da aka jefawa bom yayi kaca-kaca da su .

Dan haka ya kasa bin ta ya taro ta "duk da cewa akwai boyayyar soyayyar Yakaka cikin ransa wanda bai kai ga bayyana ta ba" amma baya jin matakin son da yake yi mata ya kai wanda yake yiwa ransa da rayuwar sa baya jin zai iya salwantar da ran sa domin taya ta neman iyayen ta, dan haka ya sake juyawa da gudun gaske yayi gaba ba tare da ya sake waiwayar ta ba ,

Cikin rashin sanin inda take sanya kafafun take tafiya kunnuwan ta sun toshe daga jin hayaniyar da ta cika duniya, tunanin ta ya bar gangar jikin ta ta yadda har bata jin turewa da bangajewar da mutane suke mata , wanda yawancin su daga unguwannin da suke ƙasa da tasu unguwar  suke fitowa wanda a halin yanzu ƴan tawayen  suke far musu ,.baza ta ce ta yaya aka yi ba kawai taga kanta ne a gaban rugujajjen ƙonannen gidan nasu da har yanzu ta wasu wuraren wutar bata gama mutuwa ba domin tana iya hango hayakin da ya ke turnuke da gidan .

Da gudu ta taka ta shiga gidan tana kwalla kiran "mama "yaana "falmata " shiru taji babu motsin kowa , cikin tashin hankali take kallon tsakar gidan nasu da yake a hargitse kamar sansanin yaƙi , kome baya muhallin sa duk da daman su basu da kome a cikin gidan nasu sai tsumokarai da ƴan tsofaffin kayan aikin su na gida wanda su ma a halin yanzu duk a ƙone suke idan ka dauke randar su da take binne cikin ƙasa da gudu ta nufi ɗakin su duk da hayakin da take hangowa cikin ɗakin ta saman sa wanda rufin zanar ya riga ya cinye ,ya zama saman a buɗe yake wayam, hakan bai hana ta cusa kanta cikin ɗakin ba babu  kome cikin ɗaƙin sai burbuɗin tokar wutar da ta gama cinyewa , bakikkirin hayaƙin ma daga kan guntun kayan su ne da ya gama ƙonewa ba jimawa yake tashi .

Durƙushewa tayi ta saki wani irin kuka da yake fita daga karƙashin zuciyar ta ,kukan maraicin da ya same ta a rana daya , kukan rasa komen ta da tayi , kukan sabuwar Rayuwar da take fuskanta  .

Ta ɗauki tsawon lokaci tana kukan nan har zuwa lokacin da ta fahimci hayaniyar da ta cika garin nasu ta fara raguwa sai tsilla tsilla take jiyo ihu da wucewar mutane a guje , har zuwa lokacin da ta tabbatar dare yayi , ganin duhun da ya mamaye sararin samaniya , da sauri ta miƙe tunowa da tayi bata yi sallar azahar, la'asar, da magarib ba ta kuma tabbatar lokacin isha'i ya yi tana son yin addu'a ta sani bata da kowa bata da kome a yanzu sai Allah dan haka gun shi zata kai kukan ta .

Tana fitowa tsakar gidan ta rasa abun da zata yi alwala da shi ,( sakamakon duhun da ya mamaye tsakar gidan, ) da taimakon hasken walƙiyar da take ta haske sararin samaniya, ta hango wani bakin kwanon da duk wuta ta kone sa wanda  ada shine kwanon da suke ji da shi duk gidan kuma shine kwanon cin abincin baban su .

Da gudu ta karasa ta ɗauki kwanon ta rungume tare da fashewa da kukan tuno mahaifin ta da gawar sa take can a cikin gona bai samu ko darajar suturtawa a kai sa makwancin sa ba .

Bayan ta share hawayen ta takarasa tare da buɗe

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login