Showing 1 words to 3000 words out of 276165 words
Chapter 1 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
[09/08, 10:36 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
PAGE 1
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
(HAMIDA SANUSI AHMAD)
Shi ɗan qauyen mutum ya fi sabawa da tafiyar ƙafa abun hawa bai wani dame shi ba sosai,dan haka a duk lokacin da aka tsawwala kud'in abun hawa sai ya dab'a da qafafun shi ya je duk inda yake son zuwa. Wannan dalilin ne ya sa Ɗan liti ya zamana a kullum lallab'a sana'ar shi kawai yake yi ta kabu-kabu, dan kuwa bahaushe ya ce motsi ya fi lab'e wa,ya na ji ya na gani a rana zai saka man fetur na dubu guda amma da kyar yake haɗa ribar dubu d'aya. Wajen zaman nashi baya wuce tasha a kullum, sai dai idan ya samu kai mutane cikin gari sai ya zauna a cikin kasuwar Ba mugu ya sake bin layi har sai ya samu wanda zai sake mayarwa tashar,duk wannan zirga-zirgar da Ɗan liti yake yi ta shige da ficen fasinja dika-dika a iya qwaryar garin nasu yake yin ta baya zuwa ko ina,dan kuwa mazajen da ke yin sana'a irin tashi a wajen basu da wani yawa.
'Yan Kabu-kabun garin Ba mugu suna da tsari babu mai yi wa wani zuren layi,ko zaka kai awanni nawa zaune a wajen in har layi bai zo kan ka ba dole ka yi hakuri har ya iso kan ka. Yau tun safe da Ɗan liti ya zo wajen sana'ar tashi bai fi ɗari uku ya yi ba,gashi har rana ta take layi bai sake zagayowa kan shi ba,ya na matukar jin tsoron ya bar wajen ya shiga cikin gari ya ce zai zagaya da abun hawan nashi ya je ya K'one mai a banza. Dan haka kwance kawai yake a saman kabu-kabun nashi yana kallon sama,fuskar shi na rufe da tsohuwar hular shi da ta ji jiki,banda tinanin halin da ya baro iyalan shi a ciki a wannan lokacin babu abinda yake yi,domin kuwa ko nera bai bar musu ba ya fito. Ɗan Liti na da matan aure guda biyu,Innoh ita ce uwar gida,tana da yara uku,Sule da Hadiza wadda suke kira da momy,sai Safiyya wadda suke wa laqabi da Amirah,Yadiko Amaryar Ɗan liti kuwa na da yara biyu mace da namiji,su na Kiran macen da Siddiqa namijin kuwa Sadeeq.
Yaran Baaba wato matar yayan Ɗan liti marigayi guda uku duk sun girma sun yi aure har ma suna da manyan 'ya'ya,dan kuwa a cikin jikokin Baaba akwai sa'annin su Mommy da Amira har ma da wanda suka girme su,Yaran Abbe a gidan Ɗan liti suke da zama,saboda kasancewar mahaifin su bashi da halin riqe su a gidan haya suke mai d'aki ɗaya, sai suka yanke shawarar kawo wa Baabaa riqon su, ko ba komai sun dinga ɗebe mata kewa su taya ta ayyukan yau da kullum.
Ɗan liti ne ya sake jan hular shi ya rufe fuskar shi saboda ranar da ake kod'awa, ga qishirwa ya na ji,ya na kuma tsoron ya taɓa kud'in Jikin shi ya koma gida ya tarar da masifa da bala'in matar tashi da ba ta tausaya masa balle halin babun da yake ciki.
Gajiya ya yi da kwanciyar ya tashi zaune tare da ɗauke hular da ya rufe fuskar shi da ita, ya na buɗe fuskar shi wasu zaratan haƙora suka bayyana a bakin shi,suna da tsahon da labb'an shi dika biyun sun kasa rufe su,haƙoran nan sun yi yallo shar da su alamun basu samun wanki, sai dai wani abun mamakin bai wuce yanda hasken fatar shi da kyawun idanu da hancin shi ke nema ya b'oye girma da munin hakorin nashi ba, Ɗan liti dattijo ne da ya kai shekaru arba'in da bakwai a duniya,rayuwar shi yake yi irin ta mutanen ƙauye, idan ya na da shi a ci a yi yanda aka so, idan bashi da shi ba wadda masifar ta da bala'in ta ya isa ya b'ata masa rai balle har ya tanka mace a yi bala'in da shi,ya na ji ana masa masifa zai toshe kunnen shi ya shura takalman shi ya bar gidan.
Da qarfi ya sauka a acab'an nashi ya nufi wajen mai Saida abinci da ke wajen, ya zaro ɗarin shi uku ya miqa mata ya ce,
"Ke bani abinci in ci kin ji? Ki cire kud'in ruwa a ciki, ba zan zauna na kashe kai na da yunwa ba,idan ban ci na koshi ba ta ya za a yi na fita neman?"
Wasu da ke gefen shi ne suka amshe maganar tashi da fad'in,
"Babu kam, ai sai uwar hanji ta ɗauka sannan za ka samu damar gudanar da sana'ar ka yanda ka ke so, musamman mu masu shiga rana,in bama koshi ai sai mu faɗi"
"Yo ni ma dai shi na gani,kafin na baro gida wannan lalatacciyar ta tsaya yi min rashin azziqin da ta saba,ita Allah ya kahye(kashe) ta sai na bata kud'in cefane ta gaji da ara min in banda mata da wulaqanci ma na bar ki ki yi sana'a a gida na amma ki qi yi min abu kyauta har sai an yi lissafi dul sanda na samu kuɗi na biya"
Malam Jibo abokin Ɗan liti ne ya watsa wake da shinkafa a bakin sa ya na taunawa ido rufe ya ce,
"Ai D'alli kai ka so,ahhh yo Kai ka so mana, ta ya ina namiji a gida na ku na sana'a gaba ɗayan ku kuma ku na samu sannan ace za a samu wata lalatacciya a cikin ku da idan ta sai maggi na dawo sai na biya ta? Ni ka ganni nan Ɗanli, Ramma bata isa ta Saida dusar awarar da take yi ba ba tare da ta cire min kamashona a ciki ba, dan haka dole ka ɗauki mataki idan ka na so a dinga girmama ka a gidan ka, har yaushe zan bari mata su susuta ni wai har mace ta shaqi kwalar riga ta ta na Kiran na bata kud'in cafane?"
K'wafa Ɗan liti ya yi da ya tuna iya shegen da matan shi da Yaran shi suke yi masa a gidan, a haka ya karɓi robar nashi abincin ya zauna a Saman benci ya na juyawa wa ya fara ci tare da ci gaba da hirar gidan shi, Jibo ne ya sake cewa,
"Ahaff ai na sani,ai tun da na ga ka kwanta a Saman acab'an ka na san ka baro su ba ko sisi kuma da alama ranar girkin 'yar kunama ne,uwar gida sarautar banza"
Dariya suka fashe da shi har da tafawa Ɗan liti ya d'aga baƙin shi sama ya saita wake da shinkafar nan ya afa sannan ya fara taunawa leb'en sa a sama haqoran kamar a buɗe suke,ya ce,
"Kai da ka san halin ta ? Ai ba sai ka faɗa ba ma,kai dai Allah ya yi mana magani halin da ƙasar nan ke ciki, Allah ya sassauta mana"
"Ameeen dai" suka amsa baki ɗayan su.
Suna nan zaune wata matashiyar yarinya ta zo ɗauke da akwatin ta, ta tsaya a gefen inda su Ɗan liti ke zama, kalle -kalle take yi alamar ta na neman wanda zai shigar da ita cikin gari zuwan ta kenan daga birni, fito/fed'uwa shugaban su Ɗan liti ya yi wa Ɗan litin da ke kan layi,sannan cikin d'aga murya ya ce,
"D'alli zagayen ka ne wannan fa"
Da sauri ya washe baki ya tashi ya isa gaban acab'an shi ya hau ya ja shi zuwa gaban ta ya kafe shi, daga baya ya sauka ya nufe ta ya na goge hannun shi da ya ke cin abinci da shi a Jikin rigar shi, ita ma murmushi ta yi sannan ta saki akwatin ta da wata jaka da ta riqo a hannun ta,shi kuma ya hau babur ɗin shi sannan ya ajiye kayan a inda suka dace tare da karkata mata yanda za ta iya hawa babur ɗin,d'afal kuwa ta d'afe babur ya danna horn ya ɗauki hanyar shiga cikin ƙauyen nasu.
Tun a hanya matashiyar ta d'akko wayar ta ko tsoron fad'uwa ko a warce mata bata ji ta hau yi wa hanyar video ta na haɗawa da fuskar ta,cikin d'aga murya yanda zata ji shi Ɗan liti ya ce,
"Wai ni kuwa na ce ba Balki bace 'yar gidan mai dusa?"
Yatsuna fuska wadda aka kira da Balkin ta yi irin na 'yan gayun da ke ji da kan su, sannan ta ce,
"Eh Baba ni ce, amma dan Allah ka daina kira na da Balki, Billy 'yar gidan sanator za ka ce,gaba ɗaya birni da Sunan aka sanni,"
"Tohhh ! Allah sarki Billish"
Nan da nan ran Billy ya ɓaci ta harari keyar shi, da ba dan mahaifin kawar ta bane da ta faɗa masa bakar magana, cikin ran ta ta ke fad'in;
'Ta yaya dama za ka iya fad'ar suna na da wannan galli gatson naka?'
A haka suka qarasa qofar gidan su Balki wadda ta maida kanta Billy a birni saboda tsabar qaryar da ta ɗora wa kan ta, kud'in shi ta d'akko ta bashi, ta ɗauki akwatin ta ta yi gaba ta na ce masa,
"Na gode Baba ka riƙe canjin a gaida qawa ta a ce mata na shigo gari"
Cike da farin ciki Ɗan liti ya hau sanya mata albarka, ya na godiya ya buga babur ɗin shi ya wuce gida dan ya kai masu na cefanen rana tunda ya samu kyautar dubu guda ɗaya.
A soron gidan shi ya kafe babur ɗin shi bayan ya tsugunna dan d'aure shi da makullin saboda satar babur da ake yi abun har ya yi yawa a wannan lokacin, tun daga nan inda yake tsugunne ya ke jiyo yanda Baaba ke faɗa ita da Innoh wadda bata ganin tsufa da girman Baaba sam in ta so zuba mata rashin mutunci. A gaggauce ya gama daure babur ɗin shi ya afka gidan fakam-fakam da ƴar sharar rigar shi fara da ta rine ta koma ruwan ƙasa,cikin yanayi na gajiyawa da halin su ya ce,
"To bismillahi ! Ku wai ba ku gajiya da tsattsagar juna ne kamar wasu kaji? Ku duba baiwar Allah'n can shiru ba ruwan ta ta na harkokin gaban ta, amma ku kun saka juna a gaba da ci mutunci sai kace ku ne kishiyoyin,dan Allah ku dinga raga wa juna,"
Nan da nan idanun Baaba suka kawo ruwa ta fyace majina ta kalli Ɗan liti ta ce;
"Ina fa za ta raga min? In kaga ta raga min to ai Delu ce ta dawo duniya ta yi mata barazanar tsinuwa,(Mahaifiyar Innoh kenan)"
"To ka dai ji da kunnen ka Malam,a gaban ka ta zagi uwa ta da ke kwance a kabari shekara da shekaru"
"Dan Allah ku tsahirta min ku yi min bayanin me ya janyo wannan fad'an yau kuma har ake ambatar mamatan da ke ƙasa shekara da shekaru"
Da sauri Baaba ta karɓe maganar dan bata so Innoh ta riga ta faɗin me ya faru,kasancewar ta mai mita ne ya sa tinda suka fara faɗan duk wanda ya shiga gidan yaro da babba sai ta bashi labarin abinda ya faru tsakanin ta da Innoh. Cikin kuka Baaba ta ce,
"Wata rana mu na nan zaune da ku za ku ji Innoh ta ce na zagi sarkin garin nan a zo har gida a d'aure ni a Kai kurkuku,yau tin da ka fita na d'akko goro na ina gyarawa ban kula kowa ba gudun tashin hankali,kawai sai ga wannan yarinyar Ramma qawar Innoh ta shigo ta na duba tsabar ido na ta na fad'in na yi gulmar ta tsofai-tsofai da ni,rantsuwar duniya yarinyar nan ta ce ni ce munafuka,bayan tafiyar ta ne na je qofar Innoh na buga ta fito ashe matar nan idon ta biyu ta na ji ana tsigale ni bata yi magana ba,nan take na tuna ni da ita mu ka yi maganar Ramma ya aka yi Ramma ta sani? Ka ga kenan Innoh ce munafukar da ta kai mata zance ko? To fa shine daga na yi magana ina so Innoh ta faɗi gaskiya wai bud'ar bakin ta ko tsufa na bata duba ba ta kira ni da alkafidaru qunjin guiwa(almasifatu qurjin guiwa)"
Baabaa ta ƙarasa maganar ta cikin fashewa da kuka,tagumi Ɗan liti ya zabga ya na bin Baabaa da kallo wadda ke zuba kuka tun ƙarfin ta,dan tinda ta fara bashi labarin ya gano Innoh ta sake yiwa Baaba rashin kunyar da ta saba.
Rayuwar gidan shi ta zame masa tamkar wata mummunar qaddara, kowa da inda ya sa gaba, shi kan shi watarana rasa ina ya dosa ya ke yi,dan kuwa shi mutum ne da ba za a kira shi da mutumin kirki ba, sannan ba za a kira shi da na banza ba, lokaci d'aya Ɗan liti zai yi maka abun masu hankali da kirki tare da mutunci, wani lokacin kuma zai juye ya yi maka aikin qattan qauye irin marasa kirkin nan wanda ba su san ciwon kan su ba, dan haka gidan shi rayuwa kawai ake zabgawa kowa da inda ya dosa.
Hakuri ya baiwa Baaba a matsayin ta na matar wan shi kuma ko babu komai duk ta girme su sosai kusan ma shi a wajen ta ya taso tun yayan shi na raye ita ta raine shi, nan da nan kuwa 'Yar kunamar tashi ta ɗana qarin ta ta na so ta yi harbi, cikin washe haƙoran shi ya kashe mata ido ɗaya,sannan ya riqe aljihun shi, ya na yin hakan ta gane akwai kuɗi a wajen shi, dan haka sai ta sunne kai ta na murmushi tare da fad'in,
"Malam kenan ai sai ka yi bayani tun wuri"
Baabaa na jin haka ta juyo ta na tambayar,
"Wanne bayani zai yi kuma? Kar dai a danne min hakki na dan ba yafewa na yi ba, ah toh ! ka tabbata ka ja mata kunne ta dena zuwa ta na haɗa ni faɗa da ƙananan yara ana zuwa har gida ana ci min mutunci to ka ji, in ba haka ba na yi waya can gidan Baban Gida a maida ni Habuja da zama, ai ni na qi zama da su dama saboda sabon da na yi da ɗakin miji na,amma ba dan haka ba ai da na fi ƙarfin Babar yarinya ma ba yarinya ba, da har za a zo gida a zage ni ana ce min munafuka, na yi magana a kira ni da alkafidaru qunjin guiwa "
Kowa ya bar tsakar gidan an bar Baaba na mita ita kaɗai ba tare da ta san sanda suka shige d'aki suka bar ta a wajen ba,Innoh na can ta karɓe ɗari bakwai a hannun Ɗan Liti ta ce ai ita ke da girki dole a bata kuɗi mai yawa,in ya so ya ba wa Yadiko nera ɗari ya riqe ɗari biyu, ba yanda ya iya haka ya fito daga d'akin ya na qunquni dan kar ta ji sabon bala'i ya tashi, d'akin Yadiko ya leqa ya ganta zaune da Littafin hisnul muslim ta na koya wa Saddiqa, baki ya washe sosai ya ce,
"Allahu Akbar ! Daɗi na dake Yadikon Sule akwai ki da imani da sanin ya kamata, waɗancan kajin na can na tsattsagar juna ki na nan kin koma ga mahaliccin ki,Allah dai ya yi miki albarka, ga wannan a sai omo,yau kasuwar dai sai godiya"
Karb'a ta yi cike da murmushi ta yi masa godiya tare da fatan Allah ya sa idan ya koma a samu abinda ya fi haka, Saddiqa ce ta gaishe shi ya amsa cikin sakewar fuska sannan ya fita.
Har ya kai soron gidan nashi ya buɗe acab'an shi ya haye zai tada ya tuna ya yi mantuwa, da sauri ya kashe acab'an ya shiga gidan nashi ya na kwala mata kira kamar zai tsaga gidan....
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA HAERMEEBRAEH
PAGE 2:
K'yauren d'akin 'yammatan gidan ya daka da k'arfi ya na masifa, hakan da ya yi ne ya sanya Mommy saurin kife k'wabirar wayarta,tare da saurin jan zani ta lullub'e Jikin ta, kafin ta ƙarasa tashi daga yaloluwar katifar tata mai ɗauke da k'ullin kaya wanda take amfani da shi a matsayin matashin kai.
Rigarta ta 'yan kwallon k'afa mai ɗauke da Sunan wani shahararren ɗan k'wallon ƙafa na k'etare ta zira a jikin ta ta gyara d'aurin zanin ta sannan ta fita tsakar gidan ta jingine a jikin k'ofar dakin nasu ta ce,
"Gani maye ka ke kirana a hargitse haka Baba?"
Kallon ta Ɗan liti ya yi daga sama har ƙasa, kanta babu kitso ta gaba an saka kumfar lux ya kwanta gwanin sha'awa ta baya ya zama diddiga saboda yawan kwantawa akan shi da take yi duk ya danqare, Mommy na kama sosai da Ɗan liti sai dai kasancewar ta mace haƙoran ta basu kai na shi girma ba kuma labb'an ta na iya rufe su,amma kyawun manyan idanun ta da girar ta tare da hasken fatar su iri ɗaya ne da na Baban nata,k'ank'ance ido ta yi sannan ta ce,
"Ni baba ka kirawo ni baka ce min komai ba ka tsaya ka na ƙare wa halitta ta kallo, daɗin abun dai da kai nake kama, ba ka isa zagin haƙora na ba kamar yanda sauran mutane ke yi , alqur'an kana zagi na ka san dawa nai kama ah toh"
"Ka ji min ja'irar yarinya,wani abu ki ka ji na ce? Na ce wani abu ki ka ji na ce? Kin wani fito ido ya maki fici-fici kamar mara gaskiya kin jingina da jikin gini kamar sa'an ki ne ya kira ki,to wai ma uwar me ki ke yi a d'aki tun d'azu baki amsa min kira na ba? Momy ban hana ki maqalewa a jikin waya ba?"
Kame-kame ta fara yi ta na sosa cinyayyen gashin kan ta, sai kuma ta kauda maganar shi cikin sauri da cewa,
"Baba ka san maganar ci gaba da karatu na da na yi maka ɗin nannn? To na samu wadda zata taimaka min na koma birni da zama na ci gaba da karatun a kyauta babu ko sisin ka"
"Kwarankwatsa tarnatsa ba Zaki je makarantar gaba da sakandare ba na faɗa maki,ke ba ki jin kunya ne mommy kaff sa'annin ki sun yi aure daga mai yara biyu sai uku amma ke ki na gida kullum riƙe da shegiyar waya ki na latse-latse? To ba inda za ki je wani karatu"
Dire-dire ta fara yi ta na kuka, gaba ɗaya ta wage bakin nan har a na hango dasashin ta duka,cikin kuka ta ce,
"To shi zuwa