Showing 222001 words to 225000 words out of 276165 words
Chapter 75 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
yi ɓatacciya,kaiiii subhanallahi wannan abu beyi daɗi ba sam."
Baaba na buɗe baki zata yi magana Innoh ta saki jikin ginin da take a jingine ta ƙanƙance ido sannan ta hau nuna Baaba da yatsa tana faɗin,
"Allah ka raba mu da magauta na gida da na waje,ai ke fa yanzu abun farin ciki ya same ki auren Mommy ya mace, to sai ki saka lasifika ki hau turmi ko tsani ko kuma ki bi lungu da saƙo na garin nan ki sanar da wanda be sani ba."
Cikin tsananin ɓacin rai Baaba ke bin Innoh da kallo,yau ko babu wata alaƙa a tsakanin ta da Mommy ai ba zata so auren ta ya mutu ba,to menene abun farin ciki a mutuwar auren wani? Kafin Baaba ta baiwa Innoh amsa Sule ya buɗe ɗakin shi ya fito, da ƙyar yake takawa saboda yanda jikin shi ke yi masa ciwo ko ta ina,Innoh ya kalla cike da takaici ya ce,
"Ke wai Innoh yaushe zaki gyara ne? Yaushe zaki dena ɗaukan abinda kike ji akan wani ki dage shima haka yake ji akan ki? Innoh yaushe zaki gane mu ƴaƴa ne ba wai kadara ba da zaki dinga tinƙaho damu bayan babu wata tarbiyyar arziƙi da kike bamu? Innoh anya kin san su wanene ƴaƴa kuwa? Kin san haƙƙin ƴaƴa akan uwayen su? Yana daga cikin haƙƙin mu ku sanya mu a makarantar islamiyya har ta zamani ko ku koyar damu addini a gida,ko kin san wannan halin da na shiga dik yana da nasaba da rashin ilimin addini? Innoh me yasa a kullum kike ɗora laifin gazawa akan bamu tarbiyyar da baku yi ba akan Baaba dake yi mana ƙoƙari? Ke kuma Mommy ki shige ciki ki huta zuwa gobe zamu yi magana akan wani abu muhimmi,ki sanyawa ran ki auren nan naki da ya mutu ba ƙarshen duniya bane ya zo,Allah yasa hakan shine ya fi alkhairi."
Sule na gama faɗin abinda ke ran shi ya wuce ɗaki,Baaba ma addu'a tayi akan lamarin sannan ta ce,
"Kin dai ji abubuwan da ɗan ki yace,ruwan kine ki gyara kuma ruwan ki ne ki ci gaba da tata rashin kunyar ki da kika saba,Mommy Allah ya sa hakan shine yafi zama alkhairi a rayuwar ki."
A hankali Mommy ta amsa da "Amin" sannan ta ja ƙaramin akwatin dake gabanta sannan ta wuce ɗakin su na da,tana shiga ta saki akwatin ta rushe da kuka,gani tayi komai ya sake lalacewa buhun gawayi ne ma a ɗakin a jingine,da alama Innoh ce ke saida gawayin,ga katifar ta nan jingine dik ta yi ƙura gefen ta kuwa wani abu ya gwaigwaye ta, wanda take kyautata tsammanin ɓera ne. Wani irin tsoro ne ya kama ta ta rungume jaririn ta da kyau a ƙirjin ta,yanzu a haka zata ci gaba da rayuwa anan kenan? Inaaa ba zata saɓu ba bindiga a ruwa dole ne a sama mata wajen zama mai kyau, dan kuwa ta tabbata idan ta kwana anan zata iya yin zazzaɓi.
Ƙarshe waje ta fita ta samu waje ta zauna a saman turmi tana kallon Ramma dake shirin barin gidan,dan kuwa ta kula ko dubu nawa zata bayar a matsayin kud'in niƙa babu wanda zai yi mata,tsaki Mommy ta ja dan kuwa ta san yanzu labari zai baza gari.
Naja ce ta shiga kiciniyar gyaran ɗakin kafin ta wuce gidan Kaka,dan kuwa ta san tinda mommy ta fita to fa baza ta gyara ba,ƙurar da ta dinga shaƙa ce ta sanya mata mura irin mai zubar da majinar nan,tana kammalawa tayi musu sallama zata wuce,kafin ta tafi ne ta ce wa Mommy,
"Ki kwantar da hankalin ki,idan ya san wata ai bai san wata ba,aure ne sai kin koma shi da izinin Allah, ki bari a kwana biyu abubuwa su lafa ni da kaina zan shige maki gaba ki koma ɗakin ki."
Hawaye Mommy ta share kafin tace,
"To Aunty Naja na gode da kulawar da kika bani kamar ke kika haife ni,Allah ya saka da alkhairi,dan Allah muje na baki ɗan wani abu ki kai wa Kaka."
Ɗaki suka koma Mommy ta bada sabuwar atampa da kuɗi tace a kaiwa Kaka,sannan ta baiwa Naja itama atampa da shadda guda ɗaya, godiya tayi mata kafin ta wuce.
Ganin ɗakin ya sha gyara dai-dai misali ne ya sanya Mommy zama gefen katifa tana kafe ɗan ta da kallo tana jinjina ikon Allah.
Da dare bayan Ɗan liti ya dawo ya kira Mommy da Innoh,nan fa Mommy ta zauna ta basu labarin kafff abinda ya faru, faɗa sosai Ɗan Liti ya dinga yi mata,kafin ya ce,
"Malam Jibo ne ya fara sanar dani maganar sakin ai,wai Ramma ce shima ta kira shi take faɗa masa,yanzu fisabillahi Uwata kin kyauta kenan? Allah ya ɗaukaka ki kina gidan hutu ki dawo nan?"
Tura baki Mommy tayi kafin tace,
"Ni dai Baba ku dena ganin laifi na,taya za ai ya jajiɓo aure ina matar shi yaƙi sanar dani?"
"Ni dai a bar wannan maganar,idan ana tado ta zuciya ta bugawa take da ƙarfi."
Sallamar Ameerah ce ta katse masu hirar su,cikin hauragiya da hargowa ta hau masifa tana zagin Abdul tare da aibata shi da dangin su,sai da ta gama zibar gadon rashin mutunci kafin ta gaida iyayen nata,zama suka yi suka ci gaba da tattauna lamarin kafin ta leƙa ɗakin Sule ta yi masa ya jiki, bayan ta fito ko wajen Baaba da ta dawo bata leƙa ba balle ta gaishe ta tayi wa su Innoh sallama ta wuce,su kansu babu wanda ya yi azancin yace ta je ta gaishe da Baabaan.
**************************
Dik wani plan da ya kamata Any da Hisbah da kuma Jami'an tsaro su haɗa sun gama haɗawa, Billy na can kwance a asibiti domin kuwa ƙurajen bakin ta sun fito har a gaban ta,likita bai hana ta amfani da magungunan da ta zo dasu ba saboda suna da kyau da inganci,ruwa aka sanya mata tare da ɗura masu alluran da ke ɗauke da strong antibiotics a ciki,bacci mai daɗi ne ya ɗauke ta wanda ta jima ƙwarai bata samu irin shi ba,a nan Any ta bar ta ta wuce gida dan ta shirya ta sanar da Alhaji zuwan su Nigeri.
Cike da farin ciki Alhaji yace,
"Welcome back my dear,akwai fa kaya a ƙasa masu kyau,ba ƙaramin kaya za mu ja ba mutuniyas,yaushe zaki shigo?"
"Gaskiya sai na huta,babyna bata da lafiya yanzu haka tana asibiti a kwance,nima zuwa nayi na yi wanka na huta sannan na koma wajen ta."
"Ayyaa Allah ya sawaƙe."
"Amin,ina ga mu bari zuwa jibi da misalin 12 na dare sai mu haɗu a club ɗin ka ka nuna min kayan ko?"
"Hakan ma ya yi, brohhh sai kin gan su, tsala-tsala da su, na tabbata sai kin zaɓi wata a cikin su ko hutawar sati ne kiyi da ita."
"Hhhhh to shikenan ba wahala sai mun sake waya,"
Suna gama waya Any ta kira shugaban ƴan sanda ta sanar da shi abinda suka tattauna da Alhaji sannan ta ƙara da cewa,
"Maga ta gaskiya sai kun ƙara Jami'an tsaro, kuma ya zamana kuna da kayan aiki sosai,idan ba haka ba Alhaji da mutanen sa za su iya samun nasara akan ku,yana da mazaje zarata sun kai ashirin ko sama da haka dake aiki a ƙarƙashin shi, kuma dikkanin su suna da makamai kamar yanda na sanar daku tin fari,dan haka dole sai anyi shiri sosai,saboda kar azo ana ɓatacciya suyi galaba akan ku."
'Kar ki damu,kedai ki ci gaba da updating ɗin mu akan dik abinda ke faruwa kawai.'
Sallama suka yi Any ta shiga banɗaki domin yin wanka,madubin jikin bango dake a cikin band'akin nata ta kalla,ganin ta tayi kamar namiji,nan take ta tina da rayuwarta ta baya,a baya bata da suturar da ta wuce riga da zani na atampa,sai kuma dogayen riguna na atampa,ko materials ko kuma shadda,kullum idan zata fita kuwa sanye take da hijabi da jiƙabi,me ya sami wannan halittar dake tsaye a gaban ta har ta manta Allah? Me yasa ta san halal da haram amma take takewa? Ina zata kai zunubin da ta ɗauka a baya?
"Anya Allah zai gafarta min kuwa? I killed Arica....i killed her, matan da na yi sanadiyyar shigar su bariki fa? Matan da suka rasa rayukan su ta sanadiyyata fa? Anya zan samu rahamar Allah kuwa?"
Kuka ne ya ƙwacewa Any nan ta durƙusa a ƙasan band'akin nata da yake wanke fesss saboda gyaran da yasha kafin su iso daga masu aiki,kuka ta dunƙule waje ɗaya tana ci gaba da rizga kamar zata shiɗe,a hankali ta tsaya saboda yanda ta ji zuciyar ta na maimaita mata ayar,
'Lataknaɗu min rahmatillah..........innallha yaghfiruddhunuba jami'a.'
Idan hakane tuba ya kamata ta yi tayi har sai Allah ya yafe mata kawai,jiki babu ƙwari ta miƙe ta cire kayan ta dan ta yi wanka, dik wani tattoo da ta zana sai da ta sa hannu tana shafashi,yanzu idan taje lahira Allah be yafe mata ba ko a iya tattoo ɗin nan fa sai ta ji jiki tinda Allah ya haramta.
Wanka tayi da kyar ta ɗaura alwalar da ta manta yaushe rabon da ta yi ta,tana kammalawa ta fito d'aure da towel,idanun ta sun kumbura saboda kukan da tasha,muryar ta kuwa ko fita bata yi a haka ta fita ta kirawo mai aikin ta,tana zuwa tace,
"Zulfa bani aron hijabin ki,zan baki kuɗi gobe ki je kasuwa ki ɗinko min guda ashirin nawa,sannan a d'inka wa bab..ammm Bilkisu guda ashirin,manya muke so ba ƙanana ba please."
Mamaki ne ya kusa kashe wadda aka kirawo da Zulfa,amma sai ta shanye mamakin ta,domin kuwa bata da damar sanar da kowa tinda bata iya magana,haka nan ta taso tin tana ƙarama dik abinda za a ce zata ji, amma baza ta iya magana na,hijabin ta ta koma ta d'akkowa Any mai kyau,ta feshe shi da turare ta kawo mata, Karb'a tayi ta koma sama ta sanya kayan ta sannan ta hau sallah,ta jima tana sallolin da ita kanta bata san adadin su ba,tana idarwa ta zauna ta dinga istighfari babu ƙaƙƙautawa,yi take yi amma gani take kamar ba karɓuwa ma za su yi ba,a haka ta miƙe ta fita ta karɓi abincin da aka girkawa Billy ta wuce asibiti,ko da ta fita sanye da Hijabi masu aikin ta sun zaci Zulfa ce, sai da ta kunna mota ta shiga sannan suka gane ashe fa Any ce da gaske, wasun su dariya suka dinga yi dan sun san tabbas akwai wata tsiyar da take ƙullawa wasu.
A haka ta fita tana kallon dik abinda suke yi,murmushi tayi sannan ta bar unguwar domin zuwa asibiti wajen babyn ta auuu ƙawar ta......lols
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 90:
Daga yanayin kwanciyar Billy a saman gadon asibitin Any ta gane me ya faru,ji tayi hawayen tausayin Billy na zuba daga idanun ta,itace sanadin shigar Billy wannan tashin hankalin da damuwar,gashi yanzu tana shan azaba kala-kala saboda ita.
Waje ta samu ta ajiye abincin sannan ta zauna a kujerar dake kusa da gadon da Billy ke kwance a galabaice,bacci take yi amma se sambatu take yi,kasa kunne Any tayi dan ta ji me Billyn ke faɗi,sai ta ji tana cewa,
"Ummah yaushe zaki zo? Na tuba na dena abinda nake yi mara kyau..... Ummah dan Allah ku zo kar na mutu ban gan ku ba."
Ire-iren kalaman dake ta fita daga bakin Billy kenan,wanda ya yi matuƙar karya zuciyar Any ta zauna a wajen ta dinga kuka,tinawa da mahaifiyar ta da mahaifin ta da suka yi ƙoƙari tuƙuru wajen bata tarbiyya mai kyau ya taimaka wajen shigar ta matsanancin tashin hankali,akwai hisabi a tsakanin yara da iyayen su,cikin wata iriyar murya Any ta ce,
"Ni dai na san wuta zan je kawai, saboda haƙƙoƙin mutanen da ke kaina suna da yawa,ya Allah ka nuna min hanyar tuba da zata wanke zunubai na gaba ɗaya,na shiga uku ni Anam ina zan saka kai na? Rayuwa ta ta munana,na tabbata iyaye na ba za su yi alfahari dani ba a ranar gobe ƙiyama,na tabbata Annabin rahama zai yi Allah wadai da samuwata a cikin al'ummar shi ranar gobe ƙiyama, innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,ya Allah ka gafarta min, Allah ka shiga lamari na ba zan iya ɗaukan wannan zunuban da na kwasowa kaina ba suna da yawa, Allah ka kula min dasu ka sauke min su."
A cikin wannan mawuyacin halin matan da hukumar hisbah ta wakilta suna kula da shige da ficen Any da Billy suka tadda Anyn,wata baiwar Allah ce ta ɗago ta daga durƙushen da tayi a ƙasa tana kuka tana sambatu,rungume ta tayi tana jin yanda ƙwalla ta cika mata ido saboda tausayin Any,cikin murya mai taushi ta ce,
"Tabbas irin wannan tuban naki kowanne musulmin da yake aikata saɓo ya kamata ya yi,da kin san ladan da Allah ke baiwa irin wanda suka yi wannan tuban naki da kin yi farin ciki,inshaa Allahu tsoron da kike ji Allah zai maki maganin shi,ke dai kawai ki dage ki ci gaba da neman gafarar Allah,sannan ki dage iyakar iyawar ki ki nesanta kan ki daga wannan zunuban da kika yi a baya."
"Ta yaya zan goge zunuban da na ɗauka bayan website gare mu na musamman da muke watsa videos da pictures na batsa? Ta yaya zan goge zunubai na bayan muna ɗaukar nauyin matasa su dinga yaɗa hotuna da videos ɗin batsa tare da rubuce-rubucen batsa da yaruka daban-daban,akwai gudummawa mai girma da na bayar wajen lalacewar tarbiyyar wasu al'ummar,kina zaton Allah zai yafe min dika wannan zunuban? Na san Allah mai rahama ne,kuma shi mai afuwa ne,amma zunubin da na aikata ya shafi bayin shi,ba iya tsakani na da shi bane subhanahu wata'ala,ya zan yi dan Allah malama...ki nuna min hanya na ɓata."
Gaba ɗaya d'akin kukan tausayin Any suke yi,dan kuwa sun kula the more suna bata haƙuri the more tana sake tono laifukan da ta aikata tana jin cewa Allah ba zai yafe mata ba,dan haka wannan aikin mataimakiyar kwamanda ne ba nasu bane,ita ce kawai zata iya lallashi da kuma nusar da Any mahimmancin tuba da kuma rahamar da Allah ya tanadarwa dik wanda ya yi shi,dan haka sai kawai suka ci gaba da bata baki da ƙudirin za su sanar da mataimakiyar kwamanda abinda ke faruwa, su kuma su suka san abinda za su tsara domin su baiwa Any ƙwarin guiwa akan tuban da tayi.
Sun jima sosai a wajen kafin su tafi su bar Any na baiwa Billy faten dankalin turawan da ba a sanya masa komai ba face gishiri da mai kaɗan sai butter da hanta,ta samu ta ci kaɗan ta koma ta kwanta tana numfarfashi,wajen da aka yi mata aiki a bayan ta ciwo yake yi mata mai tsanani,cikin hawaye ta ce,
"Dan Allah Anam ki taimaka ki kirawo min iyaye na muyi sallama,na tabbata mutuwa zan yi ba zan yi rayuwa mai tsawo ba,ni kaɗai na san azabar danake sha a baya na,ga fuska ta ta daure da zafin ciwo,ji nake yi kamar zan yi hauka saboda azaba."
Hawaye ne suka zubowa Any ta ce,
"Inshaa Allahu ba zaki mutu ba Billy,gobe zan je garin ku ni da Man mu ɗakko iyayen ki su gan ki,sai dai ina tsoron su gan ki cikin wannan yanayin ba za su ji daɗi ba,da kin yi hakuri ba za ki wuce sati ɗaya ba komai zai dawo normal,idan yaso sai a sanar dasu daga baya,ni kaina ba dan ina kula da wajen ba da na tabbata dole sai an yi min irin naki,to dake mun riga mun san illar dake tattare da hakan mu bamu barin ƙazantar da ake zubawa ta zauna mana,shi yasa kusan koda yaushe kike gani naje asibiti,dan Allah Bilkisu ki yafe min,ki yafe min dik abinda nayi maki a rayuwar da muka yi a baya,idan baki yafe min ba bana jin zan samu rahamar Allah,kin yarda dani,kin aminta dani,ni kuma na ci amanar ki."
A hankali Billy dake kuka ta ce,
"Shiii kar ki yi kuka Anam,ko kina da laifi nawa laifin yafi naki yawa,son kuɗi da son abun duniya sune suka jawo na faɗa wannan halin da nake ciki,ni mace ce mai tsananin son abun duniya,ni kaina ina da ƙudirin cutar da ke tin a ranar da kika min tayin aure,na so na cutar dake na gudu da dukiyar ki sai kuma nayi rashin sa'a ashe kin fini bala'i."
Dariya tayi a cikin kuka a dai-dai wannan lokacin,Any ma murmushi tayi sannan ta shafa kan Billy tace,
"Kina nufin kin yafe min kenan?"
D'aga kai Billy tayi tana lumshe ido hawaye na zuba ta furta,
"Na yafe maki dik abinda kika yi min,ina neman gafarar Allah nima ya yafe min,Allah na tuba Allah ka gafarta min ba zan sake aikata abinda ka hana ba sai bisa kuskure ko rashin sani,Allah ka yafe min domin rahamar ka da ta yawaita ta ke lulluɓe dikkan bayin ka,abu ɗaya nake so kiyi min idan zai samu."
Cikin sauri Any ta matsa kusa da gadon da Billy ke kwance sannan ta ce,
"Menene abinda kike so nayi maki? Fad'e shi ko menene zan yi maki indai ina da iko akai"
"Kina da iko akai Any,sai dai yin hakan zai iya taɓa dukiyar ki da dik abinda kika mallaka, wataƙila ma ki samu barazana akan rayuwar ki daga abokan huld'ar ki."
"Bilkisu sanar dani ko menene zan yi maki shi,ban damu da dik wani abu da zai same ni ba as long as zan faranta maki."
"Ina son ki goge dika videos ɗin mu dake kan web ɗin ku."
Murmushi Any tayi tace,
"Kar ki damu, yanzu haka kafin na fito na baiwa wani guy aikin yin hakan a can new york yake da zama,hacker ne na gaske,idan aka yi nasara ya yi hacking web ɗin zai goge komai ta yanda ba za su iya maidawa ba, zai sakar masu virus a jiki ta yanda sai dai su rufe shi gaba ɗaya su buɗe wani idan suna so,tinda dama da shawarata aka buɗe to dole na sa a rufe,channel ɗin mu kuwa yanzu zan goge ta na sauke komai,inshaa Allahu zamu sake buɗe sabuwa wadda zamu dinga ɗora abubuwa na faɗakarwa saboda wanda suke da irin halayyar mu su hankalta kar su jefa kan su a wahala kamar yanda muka yi."
"Thank you so much,Allah ya sa ya samu nasarar yin hakan."
"Amin ya Allah,ki kwanta ki huta,bari na kirawo nurse ta yi maki alluran da aka ce za a yi maki da ƙarfe goma,