Showing 261001 words to 264000 words out of 276165 words

Chapter 88 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

yana zargin anya ba asiri ta sake yi mishi ba kamar yanda ya ji labari a wajen Sultan bayan ta auri Malam? Cikin fitar da wata iriyar zazzafar iska daga bakin shi ya ce,

"Hadiza me yasa kike son wahal dani ne? Na zata na rufe babin ki a rayuwa ta sai kawai in sake afkawa cikin tarkon son ki a karo na biyu? Shin anya ma son ta nake yi ba wani abu nake so daga wajen ta ba?"

Rasa wanda zai kira ya sanar da shi halin da yake ciki ya yi,idan ya kira Bilal ya sanar da shi zai zama kamar cin fuska ne a wajen shi,idan ya sanar da Sultan kuma yaron zai iya tona masa asiri har mutanen gidansu su san halin da yake ciki. Hannu ya sa ya shafe zufar dake sake tsattsafo masa,salati ya hau yi ya tashi daga inda yake zaune ya buɗe fridge ya ɗauki ruwa mai sanyi ya buɗe robar ya kafa kai yana sha, be ajiye ba sai da ya ƙarar da ruwan duka. Kasa jure yanayin da yake ciki ya yi a gigice ya ɗauki wayar shi ya kira Bilal,cikin sauke numfashi mai matuƙar wahala ya ce,

"Bilal ka taimaka min a ɗaura aure na da Suhailah gobe mu haɗu a kano,Bilal ina jina kamar zan mutu a yanzu haka ka taimaka min ban san ya zan yi ba."

Wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo masa,cikin dakiya ya ƙanƙame wayar yana labartawa Bilal haɗuwar shi da Mommy,shiru Bilal ya yi kafin daga baya ya ce,

"Abdul na riga da na jima da sanin babu wata mace a cikin zuciyar ka da ta samu babban matsayi bayan mahaifiyar ka da ta wuce Hadiza,ko da sihiri ko babu sihiri Hadizar dai kake so, Alhamdulillah yanzu Hadiza ta gyara abinda ta ɓata,amma ina so in faɗa maka dik maitar ta sai Suhailah ta tare a gidan ta kafin ta samu abinda take nema a wajen ka,yanzu ka jira ina zuwa zan aiko Sultan ya kawo maka abinda zaka sha ka samu sassauci,Allah ya ƙara baka lafiya, congratulations aboki na,Allah yasa a daren ku na farko Amir ya samu ƙani ko ƙanwa."

Murmushi Abdul ya yi,sannan ya ce,

"Yanzu baka ji haushi na ba Bilal akan abinda na faɗa maka game da Hadiza? Na zaci za ka yi fushi kace kun fasa bani Suhailah shi yasa tin ɗazu na kasa kiran ka."

"Inaaa ai Suhailah da ka gani tana da ilimin addini,kuma alhamdulillahi tana aiki da shi sosai,sannan babu wanda be san labarin Hadiza ba a gidan mu,muna da yaƙinin ko bajima ko ba dad'e idan zama be ƙare ba a tsakanin ku zata dawo ɗakin ta....."

Cikin sauri Abdul ya katse Bilal da cewa,

"Tabbas na sani har yanzu ina son Hadiza,ina kuma tsananin ƙaunar ta,sannan ina son kasancewa da ita musamman a yau da ta zama silar warakata,amma Bilal har abada na haramtawa kaina Hadiza,maganar aure babu ita a tsakanin mu har abada."

Murmushi Bilal kawai ya yi,sannan ya ce,

"To Allah ya zaɓa abinda yake shine mafi alkhairi a tsakanin ku,yanzu bari na aiko Sultan ɗin ko har ka ji sauƙi?"

"Ina fa na ji sauƙi,ni dai dan Allah kar ka sanar dashi halin da nake ciki,shegen surutu ne da yaron nan,sai ya kasa ni a faranti a gidan nan kowa ya ɗauka."

Dariya suka yi kafin Bilal ya kashe waya ya kira Sultan, bayan sun gaisa ne ya sanar dashi dik abubuwan da yake so ya siyo ya kaiwa Abdul a gidan shi.

Bayan wasu awanni Sultan ya isa gidan Abdul da lemon tsami da na zaƙi,har da jar kanwa,shi dai mamakin abinda Abdul zai yi dasu ya sanya shi ƙin tafiya bayan ya bada aiken,hira ya hau yiwa Abdul dake ta tsiyayar da zufa duk sanyin fankar dake kaɗawa a parlourn,ƙarshe da ya gaji da surutun Sultan sai ya kora shi ya rufe gidan shi,daga nan ya wuce kitchen ya haɗa lemon tsami da na zaƙi ya matse a waje ɗaya dan ya ji dad'in sha, gefe ɗaya kuma kanwa ya jiƙa daban ya kafa kai ya shanye ta tas,yana gama sha ya ɗauki cup ɗin da ya matse lemon nan ya shanye shi shima. Ɗaki ya koma ya cire kayan shi ya ɗaura towel ya faɗa wanka,sai da ya jima yana wanka da ruwa mai sanyi kafin ya fito cike da kwanciyar hankali a tattare da shi,a hankali ya furta,

"Alhamdulillah ! Allah na gode maka da ka fitar dani daga wannan musibar da na afka,Allah na gode maka da ka bani ikon tsare dokokin ka ban afkawa zinar da matasa ke yi da hannayen su ba domin biyawa kawunan su buƙata,lallai Allah kaine ke shiryar da dik wanda ka so,Allah ka ƙara shiryar dani,dole ne na gujewa haɗuwa da Hadiza idan ina so na zauna lafiya,idan ta kama ma na bar garin nan ne a gobe bari shi zan yi tinda na wadata su da duk abinda suke buƙata na biki."

A gida ya yi sallar la'asar ya samu waje ya kwanta yana hutawa,bacci ne mai daɗi ya ɗauke shi a wajen har Sultan ya kawo masa abinci be sani ba.

Ta ɓangaren Mommy kuwa tinda ta isa gida ta sauya tunani akan sake auren Abdussaboor,ta sanyawa ranta ko soyayyar shi zata yi ajalin ta gwanda ta bar duniyar da ta sake auren shi. Jikin ta babu kuzari sam haka ta dinga aikace-aikace a gidan,tana gama girkin dare ta yi wanka ta shige ɗakin ta,Sule ta roƙa ya kula da Innoh dan bata da ƙarfin ɗaukar jikin ta ma balle ta ɗaga Innoh.

Da daddare Ɗan Liti ya dawo musu da karas me yawa ya sa Sadeeq ya wanke aka raba aka baiwa kowa nashi,kallon karas ɗin ta dinga yi tana tina yanda Abdul ke yaba miyar ta idan ta yanka masa karas a ciki ya naɗi kayan ƙamshi da ɗanɗano a jikin shi,murmushi tayi mai ciwo ta sa hannu ta share hawayen da ya zuba a kuncin ta,cikin sassanyar murya ta ce,

"Na haƙura da kai Abdussaboor Allah ya baku zaman lafiya da sabuwar amaryar ka,na barwa Allah komai ya yi min zaɓin alkhairi a rayuwa ta,haka ƙaddarar mu ta zo dole ne mu rungume ta,na san ka dena so na,dan haka nima dole na baiwa zuciya ta haƙuri akan ka."

Kuka ne ya ci ƙarfin ta ta kwantar da kanta a saman pillow ta dinga rera shi a hankali. Sallamar Sadeeq ce ta tashe ta babu shiri tana share hawayen ta,cikin mutuwar jiki ya miƙa mata wayar shi ya ce,

"Yah Saddiqa ce take son ku gaisa,wai ta kirawo ki bata samu ba."

Nan take ta tina yau gaba ɗaya bata saka wayar ta a caji ba,waje ta samu ta zauna da kyau kafin ta karb'i wayar,sai da ta daidaita muryar ta sannan ta amsa sallamar Saddiqa,shiru Saddiqa ta yi kafin ta ce,

'Yah Mommy lafiya kike kuwa na ji muryar ki haka? Ko kina damuwa ne akan rashin lafiyar Innoh?'

Wasu zafafan hawaye ne suka soma tsere daga idanun Mommy zuwa kuncin ta,cikin rawar murya da fashewa da kuka ta ce,

"Na cuci kaina da kaina Saddiqa, ina son Abdul son da ban taɓa yiwa wani namiji ba a duniya,na zalince ki na samu soyayyar shi ta hanyar sihiri a baya,gashi yanzu ko kallo ban ishe shi ba,ba nice a gaban shi ba Saddiqa aure zai yi da ƙanwar Bilal a cikin satin nan."

Kukan da Mommy ke yi har tsakar gida ana ji,bata damu da wanda zai ji ta ba babban burin ta shine ta cire damuwar dake danƙare da zuciyar ta a wannan lokacin. Cike da tausayawa Saddiqa ta ce,

'Yah Mommy dan Allah calm down ok? Tin farko Allah bai nufa Abdul zai zama mijina ba,Yah Munir shine zaɓi na,kuma alhamdulillahi na aure shi ina zaune lafiya da ni da shi da iyayen shi,kinga kenan u don't owe me any apology,Allah ya nufa kece zaki zama uwar ɗan shi tilo Amir,dan haka ki kwantar da hankalin ki,zan ci gaba da taya ki addu'a Allah ya yi maki zaɓin alkhairi.'

"A yau na sake tabbatar da ana gadon kyakkyawan hali,domin kuwa Saddiqa kin yi gadon hali me kyau a wajen Yadiko,Allah ya yi miki albarka ya jiƙan Yadiko,ina son ki ƙanwata kin sa baƙin cikin dake danƙare a raina ya ragu sosai,sai nake ji na kamar na sauke wani ƙaton dutse da ya danne zuciya ta."

Murmushi Saddiqa ta yi sannan ta ce,

'Ga ɗan ki nan ya fara iya surutu,amma fa ba a gane abinda yake cewa sai dai ya cika mana kunne da ihu.'

"Ina Baban nawa yake? Bani shi mu gaisa."

Hira Mommy ta dinga yiwa yaron kamar yana ganewa kafin daga baya suyi sallama da ƙanwar tata da take jin ƙaunar ta na ratsa ko ina na jikin ta. Murmushi tayi da ta tina Ameerah,da ita ta sanarwa halin da take ciki balbale ta zata yi da masifa sannan ta cusawa Abdul ashar har sai zuciyar ta ta yi sanyi,dariya ta saki tana jin ƙaunar ƙannen nata a ranta.

Sadeeq ne ya sake yin sallama ya karb'i wayar shi ya fita,Hadiza na nan kwance tana tinani Ɗan Liti ya aika kiran ta, Sadeeq na shiga ɗakin ta sakar masa murmushi ta ce,

"Ƙani na ko dai hira kake so mu yi da kai ne yau?"

Murmushi ya sakar mata cike da sakin jikin shi da ita ya ce,

"Zan so hakan Yah Mommy,amma Baba ya riga ni,shi yace na kira masa ke yanzu haka."

"Ok to next time zan gayyace ka hira,amma fita zamu yi mu zaga garin Ba Mugu a ƙafa mu sha iskar maraice da kai,ka amince?"

Cike da murna Sadeeq ya ce,

"Na amince Yah Mommy."

Tashi tayi ta maida doguwar rigar da ta sanya da rana ta nufi ɗakin Innoh,tana shiga ta tarar da Innoh a tsaye da ƙafafun ta tana takawa daga farkon bangon ɗakin zuwa bakin ƙofa,dariya suke ta yi ita da Ɗan Liti suna hira gwanin ban sha'awa,rungume Innoh Mommy ta yi ta ce,

"Alhamdulillah Innoh yaushe kika fara takawa ke kaɗai ban sani ba? Baaba ! Baaba zo ki ga ikon Allah !"

Cikin abinda bai kai minti uku ba Baaba ta bayyana a ɗakin,murna kowa ya hau yi saboda ganin Innoh na takawa da kanta,Sule ma dake waya da yarinyar da yake so ya aura sai da ya katse ya kutsa d'akin dan ganin abinda ake yiwa murna,yana yin arba da Innoh na takawa sai ya hau murna shima, a hankali Innoh ta samu gefen gadon ta ta zauna,cikin tsananin farin ciki ta kalli Baaba dake kukan murna ta ce,

"Yaya mai zuciyar zinare kenan,dik ɗawainiya da kulawar da kike yi dani ina gani kuma ina ji,me yasa Yaya kika ci gaba da kula dani bayan kin san yanda na tsane ki nake yi maki rashin kunya?"

"To yanzu ba gashi kin warke ba mu ɗora daga inda muka tsaya? Innoh idan babu tsiwar ki a gidannan ai gidan ba zai yi armashi ba,ranar da kika faɗa cikin wannan mawuyacin halin kasa bacci nayi...."

Kuka ne ya ci ƙarfin Baaba,Ɗan Liti ne ya ce,

"Dan Allah ku dena koke-koken nan haka,mu godewa Allah da sauƙi ya samu."

Innoh ce ta share hawayen ta tace,

"Na gode Yaya,na gode wa duk wanda ya bani gudummawar kulawa har Allah ya bani lafiya,Mommy Allah ya yi miki albarka ya baki miji na gari,ban taɓa zaton zan tashi ba,na yanke tsammanin ba zan sake moruwa ba koda na rayu,Mommy ina son ki samu farin ciki mai ɗorewa a rayuwar ki,Allah yasa idan kin samu miji anan gaba ya zama mijin ki har a aljannah,Yaya ki gafarce ni,daga yau ba zan sake yi maki musu ba, balle har in faɗa maki baƙar magana."

Ranar a ɗakin Innoh aka dasa hirar dare har sai da kowa ya fara jin bacci sannan suka barta ta kwanta itama dan ta huta.

Washegari da sassafe Abdul ya bar ƙauyen Ba Mugu ba tare da sanin kowa ba,tinda ya tafi zuciyar shi ke ganin kamar ya baro wani abu mai mahimmanci a can,a haka ya daure ya koma bakin aikin shi dan ya ɗebe wa kanshi kewa da yawan tinani. Yana cikin wannan yanayin kwanakin ɗaurin auren shi da Suhailah suka gabato, Sultan da dangin mahaifin shi da za su tafi garin Bauchi dan ɗaurin auren su Abdul, tin da asubar fari suka baro ƙauyen Ba Mugu suka shiga Kano,a cikin motoci uku suka tafi garin Bauchin Yakubu.

Suna isa Bilal ya tare su ya kai su masaukin baƙin da aka tanada domin su. Gaba ɗaya tunanin Abdul ya tattara ya koma ranar ɗaurin auren shi da Hadiza da aka ɗaura a fadar mahaifin shi ba tare da an shiryawa hakan ba. A hankali ya tambayi kanshi,

"Shin me yasa nake tuna aure na da Hadiza kamar ita kaɗai ce matar da na taɓa aura a duniya?"
 
Zuciyar shi ce ta bashi amsa da,

'Saboda har yanzu Hadiza kaɗai ka ke so,itace macen da kayi rayuwar soyayya da nishad'i da ita.'

Lumshe idanun shi ya yi tare da lafewa a kan gado,ya ce,

"Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir."

Tinda ya yi wannan addu'ar sai ya samu natsuwar zuciya,ya tattara dikkan lamuran shi ya miƙa su zuwa ga Allah,dan ya san hakan shine kawai mafita a cikin halin da yake ciki.

Washegari da safe da bidirin ɗaurin auren Suhailah da Abdussaboor aka tashi a garin Bauchi a unguwar dumi. Ango da ƙanin ango tare da babban abokin ango kuma yayan amarya sun sha shadda fara tasss mai farin aiki a jiki,hatta da hulunan da suka sanya iri ɗaya ne, Maestro cinematography suka ɗakko yake ta aikin ɗaukan su videon ɗaurin aure,inda bayan an ɗaura aure suna da walima da za a gudanar,wanda duk shi suke son ya ɗaukar masu video da hotunan auren nasu. A wajen Suhailah suka samu labarin shi dan kuwa shi ya yi aikin Video ɗin bikin aminiyar ta dake Yola,videos ɗin da pictures ɗin sun fito fess kamar an saka a computer tsabar haɗuwa,shi yasa itama ta yi booking ɗin shi ta biya masa kud'in mota ya isa har garin bauchin dan ya gwangwaje nasu auren da basirar shi......
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨









PAGE 106:






Da misalin ƙarfe biyu na dare Abdussaboor ne ya sauka daga saman gado fuskar shi na ɗauke da wani irin murmushi mai ƙayatarwa. Farin cikin da ya tsinci kanshi a ciki a wannan dare ba zai taɓa misaltuwa ba,bai taɓa zaton zai samu lafiya cikakkiya ba bayan abinda ya faru da shi a baya,juyawa ya yi a hankali yana kallon yanda Suhailah ta dunƙule waje ɗaya tana bacci,har a wannan lokacin ajiyar zuciya take saukewa. A hankali ya tashi daga gadon ya taka zuwa bathroom,alwala ya yi sannan ya yi wanka ya sake yin brush ya fito.

Sai da ya shafa mai sannan ya fesa turarukan shi masu tsananin ƙamshi da tsada sannan ya sanya farar jallabiya da dogon wandon ta a jikin shi,carpet ɗin sallah ya shimfiɗa a ƙasa tare da tada sallah dan godewa Allah akan ni'imomin da ya azurta shi da su da ba zai iya lissafawa ba. Suhailah kuwa na ganin ya tada sallah ta miƙe a hankali ta taka da ƙyar ta shige band'aki,ruwa ta tara a kwamin wanka sannan ta shiga ta gasa jikin ta da kyau,duk yanda taso ta ji haushin Abdussabour kasawa ta yi,ƙarshe ma samun kanta tayi tana sakin murmushin jin daɗi dik da baƙar wuyar da ta sha a hannun sa. Ashe ba zaman haƙuri zata yi a gidan miji ba kamar yanda ake ta bata haƙuri? Ashe ya ji sauƙi shine bai sanar da su ba ya shammace ta? Cikin zuciyarta ta yi hamdala ta fita daga kwamin wankan sannan ta tsiyaye ruwan da ta zauna a ciki ta haɗa wani ta yi wanka ta fito daure da towel a jikin ta. Har a wannan lokacin Abdussabour na nan duƙe yana sujjada wanda da alama ya jima a hakan,wucewa tayi cikin sanɗa ta sanya kaya a jikin ta sannan itama ta shimfiɗa abun sallah ta gabatar da nafila raka'a biyu,tana idarwa ta yi addu'a ta koma saman gado ta yi addu'ar bacci ta kulle idanun ta,babu jimawa bacci mai daɗi ya ɗauke ta.

Abdul kuwa bai tashi daga wajen ba har sai da aka yi sallar asuba sannan ya tashi Suhailah shi kuma ya wuce masallaci.


*****************************

Bayan shekara biyu da auren Abdul Innah Laminde ta kira shi ta shawarce shi da ya ɗauki ɗan shi ya maida shi gaban shi,tinda ko babu komai yanzu Amir ya ɗan yi wayo,idan yana gaban mahaifin shi zai rage kewar rashin shi a tare da shi,idan yaso lokaci bayan lokaci sai a dinga kawo shi hutu wajen Hadiza. Abdul ya yi na'am da wannan shawarar amma sai ya ce,

"Innah ina ganin a bani nan da kwana biyu mu yi shawara da Suhailah,kinga tana zuwa asibiti kar a kawo shi ya zamana yana zama babu cikakkiyar kulawa."

"Wannan wace iriyar magana kake yi ne Abdul? Dan tana aiki a asibiti shikenan ba za a kawo yaro gidan uban shi ba? Inda Allah ya bata haihuwa da wuri yanzu ai da nata take reno ko? To bana son shirmen banza dole ta san yanda zata yi da yaro idan an dawo da shi gidan ubansa."

Shiru Abdul ya yi kafin ya sassauta murya ya ce,

"Dan Allah Innah ki fahimce ni,ba haka nake nufi ba,ke da kan ki kin san idan aka kawo yaron nan yanzu wahala kawai zai sha,dama ya ɗan tasa ne ya kai na sakawa a makaranta sai....."

"Shekara ukun ne be kai na sakawa a makaranta ba? Ina ce anan birnin kuna da makarantun yara kamar shi? To ku saka shi ya yi karatun shima mana ba shikenan ba."

A sanyaye Abdul ya ce,

"To Innah inshaa Allahu idan na shigo wannan satin zan karɓe shi, a gaishe da mutanen gida na gode."

Tinda ya gama waya da Innah Laminde yake cikin tsananin damuwa,domin kuwa ya san halin Suhailah,bata da matsala ko ta wanne ɓangare tana kula da shi,matsalar ta ɗaya shine rashin son haihuwa. Ita a yanda ma ya fuskanta reno ne gaba ɗaya bata so,dik ilimin da take da shi na addini bai hana ta ɗaukan ra'ayin riƙau ta ɗorawa kanta ba na ƙin haihuwa da renon yara,akwai sanda suka taɓa samun matsala da ita a lokacin da ya gano tana shan maganin planning,da ƙyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login