Showing 273001 words to 276000 words out of 276165 words
Chapter 92 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
sauti kafin ta ce,
"Ni ba korar ka nake yi ba,ka ga dai ba a d'aura auren nan ba fa,wannan abun da ka ke yi ba zai haifa mana ɗa mai ido ba,mu yi haƙuri mu koma ciki daga gobe jiran zai ƙare."
Sake shagwab'e mata ya yi ya ce,
"Gobe ne fa kawai,dan Allah ki ɗan yi min abun nannnn."
Zaro ido Mommy ta yi waje ta janye jikin ta daga yanayin zaman da suka yi,nan take jikin ta ya hau rawa ta fara tuna rayuwar da ta yi a baya,me yasa Abdul ke neman maida ita ruwa bayan ita a kullum neman tsari take yi da sake aikata zina? Ah zina mana tunda ba a ɗaura musu aure ba har yanzu.
Da sauri ta sanya hannu zata buɗe motar,cikin zafin nama Abdul ya riƙe mata hannu,juyawa ta yi ta sauke idanun ta a nashi,shima kallon ta yake yi da idanun shi da suka rine suka sauya kala tsabar yanda yake jin wani irin yanayi game da Mommyn,muryar ta na rawa ta kalle shi ta ce,
"Baby ka yi haƙuri ka barni na ci gaba da kare mutunci na har na tsawon awannin da ya rage mana kafin mu mallaki junan mu,ka riga ka sani kai nake so,kai zan aura,to me zai sa mu tsaya aikata abinda Allah zai yi fushi damu,mu ɓata yau saboda goben mu ta lalace? Kar ka manta muna da Amir,aikata wani abu da ya saɓawa Allah a wannan yanayin zai iya shafar rayuwar shi."
A hankali Abdul ya saki hannun ta ya jinginar da kanshi a jikin kujerar motar,cike da tausayawa halin da yake ciki Mommy ta buɗe marfin motar ta fita,duhun da ta gani ne ya bata tabbacin jimawar da suka yi a tare,godewa Allah ta yi dan kuwa ba lallai mutane su gane ta ba,cikin azama ta afka cikin gidan nasu,Abdul kuwa ya jima zaune a bayan motar kafin ya buɗe ya shiga gaba ya tada motar ya wuce gidan Sarki. Ko da ya shiga gidan ya tarar da ƴan'uwan shi da dangin mahaifin shi da na mahaifiyar shi ana ta zuba hira, mata na ganin shi suka hau guɗa suna yi masa kirarin sarauta da na angwaye,murmushin yaƙe kawai yake yi yana amsa gaisuwar su tare da gaishe da wasu da suka girme shi,Suhailah ya hango tana bin shi da kallo,murmushi ta sakar masa kafin ya yafice ta da hannu,noƙe kafaɗar ta tayi sannan ta kauda kanta daga gare shi tana murmushi. Tsaki ya ja a hankali ya wuce ɗakin shi dake gidan,gado ya faɗa ya kwanta ba tare da ya cewa Bilal da Azizah dake zaune suna hira komai ba,Bilal ne ya ce,
"Kai malam meye haka zaka faɗo ɗaki da ma'aurata a ciki babu ko sallama?"
Banza Abdul ya yi masa ya sake jan pillow ya na jan tsaki,Azizah na jin haka ta tattara kwanukan abincin da ta kaiwa Bilal zata fita,Bilal ne ya ce,
"Noor kawo masa abinci da ruwa please."
"Tom yanzu kuwa."
Fita ta yi ta bar su dan su tattauna,dan kuwa ta san yayan nata nada damuwa duba da yanda yake ta zabga tsaki. Azizah na fita Bilal ya matsawa Abdul ya sanar dashi damuwar shi,shiru ya yi ya kasa sanar da shi abinda ke ran shi,saboda nauyi da kunyar shi da ta kama shi,karshe dai ba dan yaso ba dole ya haƙura ya saki ran shi,abincin da Azizah ta kawo ya zauna yaci ya ƙoshi.
Washegari da safe dangin Mommy suka je gidan ta suka sake gyara mata shi tsab,kowa sai son barka yake yi domin babu abinda Abdul bai saka mata ba a cikin gidan. Dan haka basu wani jima ba suka ɗunguma suka koma gidan Ɗan Liti da mata ke taron yini,dafadikan shinkafa aka dafa da ta ji kayan lambu da nama,wasu na ta tsincewa saboda rashin sabawa da cin ganyayyaki a shinkafa. Ruwa kuwa pure water sai ya zamo kamar wani zam-zam a gare su. Amarya da sauran ƴan'uwanta da suke a matsayin ƙawayen ta na can gidan Alhaji Baban Gida sun sha gayu ana ta kaiwa da komowa. Da misalin ƙarfe biyu na rana bayan an idar da sallahr Juma'a aka ɗaura auren Hadiza da Abdussabour a karo na biyu,bisa sadaki nera na dukan nera har dubu ɗari da hamsin,mutane sai ƙananun maganganu ake yi akan yawan kud'in da Abdul ya bayar a matsayin sadakin bazawara.
Tinda aka ɗaura auren Abdul ke ɗauke da mabayyanin farin ciki,sai gaisawa yake da mutane ya na yi musu godiya Maestro cinematography na biye da shi yana ɗaukan shi da mutanensa video saboda tarihi. Gefe ya samu suna tsaye shi da Bilal da Sultan da wasu cousins ɗin shi ya kira Mommy a waya,hayaniyar su Ameerah bai bari ta ji ba,dan haka sai da ya jera mata missed calls biyar sannan ta ɗauki wayar,cikin wata iriyar murya ya ce,
"Halalina kina lafiya?"
Baki Mommy ta damƙe tana dariya ƙasa-ƙasa ba tare da ta ce komai ba,wani irin farin ciki take ji wanda ko a auren su na farko bata ji irin shi ba,muryar Abdul ta jiyo yana faɗin,
"Alhamdulillah Baby an ɗaura auren mu,kin zama mallaki na a karo na biyu,wanda nake fatan mutuwa ce zata sake raba mu."
Cike da farin ciki Mommy ta ce,
'Alhamdulillah Baby Allah ya bamu zaman lafiya,Allah ya baka ikon tsaida adalci a tsakanin mu."
Ihu su Ameerah suka sanya Saddiqa dake tsaye tana yiwa Mommy video ta hau rera waƙa tana faɗin,
"Alhamdulillahi ta zama matar Abdul,ta zama d'akko riga,ta zama,ta zama ɗakko wando,ta zama,ta zamma miƙo buta."
Gaba ɗaya sai ɗakin ya ɗauki waƙar,har Abdul ya kashe wayar yana dariya basu dena ba,Mommy kuwa kukan farin ciki ta fashe da shi,cikin zuciyar ta take jin ko yanzu rai ya bar gangar jikin ta ta cika burin ta,sallamar Tsahare da su Mero ce ta katse ihu da murnar da su Ameerah ke ta yi, Mommy na ganin Tsahare ta tashi tana share hawaye ta isa gare ta ta rungume ta, cike da murna ta ce,
"Iya sai yanzu kuka zo? Ina su Binta? Me yasa baki zo min dasu ba?"
"Humm baban su ne ya hana, muma da ƙyar ya barmu muka zo,kin san halin shi da kulle."
"Hakane kam,na ko gode da ya barmin ke kika zo,Hajiya Mero babu magana,Asabe barkan ku da zuwa bismillah ku zauna."
Bayan sun zauna ne suka hau gaisawa,Ameerah ce ta yatsina fuska ta kalli Mero ta ɗauke kai,Mero ma dake mace ce mai tsiwa sai ta yatsina baki ta kauda kai daga kallon Ameerah,Saddiqa ce ta tashi ta kawo musu abinci,sun jima a gidan kafin su yi sallama tare da fatan alkhairi,Mommy bata barsu haka ba sai da ta sa aka ɗebar masu kayan biki mai yawa sannan ta ce su gaida yaran.
Amarya da ƙawayen ta basu bar gidan Alhaji Baban Gida ba sai da yamma sannan suka wuce gidan Ɗan liti,Saddiqa kuwa da misalin ƙarfe biyar suka yiwa kowa sallama suka tafi Abuja ita da Munir ta jirgi.
Suhailah ma motar su Bilal tabi suka koma da yamma bayan ta yiwa Abdul da Mommy fatan alkhairi,zuciyar ta cike da matsanancin kishin da ta yi namijin ƙoƙari wajen danne shi suka bar garin,daga dangin Abdul har na Mommy sun jinjinawa Suhailah saboda ƙoƙarin kwantar da hankalin ta da na mijin ta da ta yi,babu wanda zai ce ga kalma ɗaya ko wani aikin rashin arziƙi ko rashin mutunci da ta yi kafin bikin da bayan biki,Abdul kanshi ya yaba mata,kuma ya ɗaukar mata alƙawarin tsaida adalci a tsakanin su kafin su tafi.
Da misalin 9:59pm dangin ango suka je suka ɗauki amaryar su kamar yanda al'adar ƙauyen take. Tinda suka kai amarya basu wani jima ba Ta Annabi ta sa kowa ya tattara nashi ya nashi suka bar amarya ita ɗaya daga ita sai halin ta.
Bayan tafiyar su Mommy sai ta buɗe fuskar ta dan taga ya ɗakin yake,mamaki ne ya kamata da taga an sauya komai na ɗakin ba kamar yanda suke a da ba,hamdala ta dinga yi a ranta tana jin wani irin farin cikin da bata ji ba a auren su na farko. Abdul bai shiga gidan ba sai goma da rabi na dare,hannun shi ɗauke da manyan ledoji guda uku,ba tare da jin nauyi ko kunya ba Mommy ta yafa mayafin ta da kyau a kanta ta miƙe ta isa gaban shi ta karɓi ledojin suka ƙarasa bakin gado suka zauna a tare,tin kafin ta karasa ajiye ledojin Abdul ya rungume ta tsam a jikin shi yana sauke ajiyar zuciya kamar wani jaririn da ya yi kewar mahaifiyar shi,cikin matsanancin farin ciki murya na rawa ya ce,
"Alhamdulillah ya Allah na gode maka da ka saukar da ƙaddarar da ta rabani da wannan baiwa taka,sannan ka saukar da ƙaddarar da ta sake haɗamu a inuwa ɗaya,Allah kasa babu wata mummunar ƙaddarar da zata sake raba tsakanin mu har abada sai mutuwa ."
A hankali Mommy da hawayen farin ciki ke kwaranya a idanun ta ta furta,
"Amin ya Allah,tabbas kai ɗin ƙaddara ta ce,ina son ka Abdussabour,ina matuƙar ƙaunar ka,Allah ya barmin kai na yi ta son ka ina jin daɗi a raina."
Rabata da jikin shi ya yi suna fuskantar juna ya ce,
"Ni ma kece ƙaddarata Hadiza, ina son ki,ina ƙaunar ki,Allah kar ya kawo dalilin da zai sa na dena son ki,saboda idan haka ta kasance zuciya ta zata yi babban rashi,gangar jiki na zai zamo kamar mutum-mutumi."
Murmushi suka sakarwa junan su kafin Abdul ya fara isar mata da saƙon dake neman rikita mata nutsuwar ta,cikin sauri ta zame jikin ta,murya na rawa Abdul ya ce,
"Ina zaki je kuma? Jiya kin ƙi yi min abinda zaki faranta min kin ce na bari sai yau,yanzu kuma kina ƙoƙarin ture ni."
Murmushi Mommy ta yi ta kama leɓen shi da ya tura kamar irin na yaran nan masu rikici ta ce,
"Babyyyy jiyan ma na hana kane saboda ba halalin ka bace ni,amma yau babu abinda zai rabani da kai sai bacci,ina so mu gabatar da Sunnar Annabin rahama ne kafin na faranta maka,domin mun cancanci mu nuna farin cikin mu da godiya ga Allah a wannan daren mai dimbin tarihi."
Tashi ya yi tsaye ya sumbaci kuncin ta kafin ya fita ba tare da ya ce mata komai ba,yana fita ta gane ɗayan ɗakin ya tafi,dan haka sai ta tashi ta shiga banɗakin ta ta yi tsarki ta yi alwala sannan ta fito ta sanya musu abun sallah,sallah suka tada suka yi kafin Abdul ya dafa kanta ya yi mata addu'a,ledar da ya shiga da ita ya ja gaban ta ya buɗe musu gasasshiyar kaza da Azizah ta gasa musu kafin su tafi a cikin coil paper a cikin garwashin da akai girki a gidan nasu,daga nan ya buɗe ledar fruits da ya siyo a kasuwa da lemo da madara sai ruwan roba.
Zama suka yi suka ci suka ƙoshi suna ta hira,suna kammalawa Mommy ta tashi ta gyara wajen, sannan ta ce masa,
"Bari naje na wanke baki na nayi shirin bacci,ya kamata ka kira Suhailah ka ji sun isa gida lafiya?"
Nan take ya tuna da Suhailah,sai ya ji rashin kyautawa akan rashin kiran ta da baiyi ba,cikin sauri ya ɗauki wayar shi ya fita daga ɗakin,ɗayan ɗakin ya je ya kira Suhailah,ta jima tana ringing bata ɗauka ba har daga karshe ta mutu, sake kira ya yi,bata ɗauka ba,ƙarshe sai ya yi mata message mai daɗi da sanyaya zuciya,ya ɗan tsaya ya ji ko zata kira shi,shiru bata kira ba bata yi masa reply ba,sake kiranta ya yi har ya cire rai zata ɗauka,ya kai hannu zai kashe kiran kenan ya ga ta ɗauka,cikin sauri ya kara wayar a kunnen shi tare da yi mata sallama,amsawa tayi tana ta ƙoƙarin danne kishin dake nuƙurƙusar zuciyar ta,a hankali Abdul ya ce mata,
"My Suhailah na yi kewar ki da ƙamshin ki yau sosai,kin min rowar ganin ki,babu komai zan dawo ne zaki yi min bayanin guduna da kika yi yau,kun isa gida lafiya?"
Murmushi ta yi dan kuwa sai taji damuwar da take ciki ta ragu sosai,a hankali ta ce,
"Eh mun isa lafiya ƙalau ina ma gidan Yah Bilal,zan yi weekend anan,ranar lahadi da yamma zan koma gida saboda fita aiki.
"Da kyau my love ! hakan ma ya yi,saboda bana son ki zauna ke kaɗai bana nan kar ki yi kewa ta da yawa,ina son ki my Suhailah,ki yi bacci mai daɗi kin ji? Allah ya yi miki albarka akan namijin ƙoƙarin da kika yi,sai dai har yanzu ina da ƙorafin ƙin bari na na ganki sosai da kika yi yau."
Murmushi ta sake yi na jin matuƙar daɗin kalaman shi kafin ta ce,
"Mun fa yi sallama ko ka manta ne?"
"Ai ban gaji da kallon ki ba,kin ga kyam da kika yi ne?"
"Kar ka damu,idan ka dawo za ka ganni har sai ka gaji"
Tana faɗin haka ta kashe wayar ta gaba ɗaya ta kwanta tana murmushi,saɓanin da da take cikin ƙunci da zubar hawaye,Azizah ta ji daɗin ganin farin cikin ta,dan haka sai ta taƙaita yi mata hira ta gudu wajen mijin ta.
A can ɗakin Mommy kuwa ko kaɗan daɗewar shi be tada hankalin ta ba,dan tasan idan ita ce tana iya jan hirar ma fiye da haka,koda ya koma ɗakin yana shirin bata haƙuri ta jashi jikin ta ta haɗe tazarar dake tsakanin su,ina ganin haka na ce to dama kinibini ya kawo ni gidan amare.
Tin daga wannan daren mai albarka Hadiza da Abdul suka ɗinke suka dawo kamar sabbin ma'auratan da basu taɓa aure ba saboda tsananin soyayyar da suke zubawa. Yana gama kwanakin da ya dace ya yi mata suka je gidan Sarki ta ɗakko Amir da kayan shi ya koma wajen ta da zama,Abdul kuma ya wuce kano saboda komawa bakin aikin shi.
********************
Bayan shekara biyar....
Abubuwa na farin ciki da baƙin ciki sun faru,ciki kuwa harda sake haihuwar yarinya budurwa da Mommy ta yi mai sunan Innah Laminde wato Zainab suna kiran yarinyar da Amirah,Azizah ta haifi takwaran mahaifin Bilal sannan daga baya ta haifi Salma,Sai Ameerah da ta haifi yara biyu mace da namiji,a shekarar da Saddiqa ta kammala karatun ta na zama cikakkiyar likitar fata wato Dermatologist a shekarar ta haifi yaran ta biyu maza kyawawa,wanda sune ƴan biyu da aka fara yi a kaf zuri'ar GIDAN ƊAN LITI. Sule ya auri wata yarinya ɗalibar shi,suna nan zaune a GIDAN ƊAN LITI a daƙin Yadikon Sule,sai ya keɓance wajen shi ya ƙara mata ɗaki da makewayi da madafi,Saddiqa ta matsa masa akan ya karkaɗe takardun shi zata ɗauki nauyin karatun shi ya koma makaranta dan samun ci gaba a rayuwar shi.
Suhailah kuwa na ɗauke da ƙaramin cikin da bata san dashi ba har sai da ta kwanta ciwo aka kaita asibiti,gwajin farko aka gano tana da ciki har na tsawon watanni uku,sai ta fara rikici tana shagwab'a tare da kiran bata so,nan take Abdul ya ɓata rai ya ɗakko wayar shi ya ce
"To bari na sanar da su Mama abinda kika ce,Allah ya yi mana kyauta su Amirah za su yi lil brother ko sister ke kuma kin ce baki so."
Da sauri ta rike wayar tana bashi hakuri. Bayan sun koma gida da sati biyu kuma ta fara jin wata iriyar soyayyar cikin na ratsa ta,har tazo ta fi Abdul so da zumud'i akan cikin ma.
Ta ɓangaren k'waisan Alheri kuwa likafa ta ci gaba ya buɗe gidan abinci mai suna HALAL RESTAURANCE a unguwar Jambulo,ya ɗauki masu aiki dake taya shi girke-girke da miƙa abinci,da wannan sana'ar ya sai gida da machine ɗin shi mai kyau. Suna nan suna ci gaba da zumunci shi da Sallau,duk ranar Juma'a kuma yana zuwa gidan yari ya kaiwa Alhaji abinci,ba dan komai ba sai dan zaman tare da ya taɓa haɗa su a baya.
*******************
Wani babban ɗakin taro ne dake cikin Bayero University Kano cike da mata danƙam suna sauraron wata baiwar Allah da ke zuba bayani,ina karasa shiga wajen na ga Billy riƙe da abun magana tana faɗin,
"....Dan haka ƴan'uwana mata ina yi maku nasiha da ku ji tsoron Allah,ina son wannan labarin da na baku na rayuwar mu da ni da ƴar'uwata da muka yi a baya ya zame maku babban darasin da zaku gina rayuwar ku akan tafarkin musulunci,domin bariki ta yi min mummunan tabon da ba zai taɓa gogewa ba,sannan ta sa na rasa ƴan'uwana,da garin mu da duk wani wanda ya sanni, tunda babu mai son a gammu tare dashi,ba komai ya kawo haka ba sai mummunan tabon da na yi wa kaina,jinyar da na yi kuwa kaɗai ta ishi mutum ya ji tsoron faɗawa halaka da saɓon Allah,mu yi ƙoƙari iyakar iyawar mu muyi amfani da social media ta hanya mai kyau,hanyar da zata yi sanadiyyar shigar mu aljannah,ba wuta ba,mu gujewa zinar da ake aikatawa ta cikin wayoyin nan na zamani,saboda tana kai mu ga aikata zinar zahiri,anan zan tsaya saboda lokaci da ake nuna min,ina yi muku fatan alkhairi Allah ya tsare mana imanin mu."
Abun magana ta miƙa ta sauka a hankali sanye da dogon hijabin ta da ya rufe cikin da take ɗauke da shi,fuskar ta rufe take kiruf da niƙabi,ta samu gefen da Anam take zaune ta zauna itama.
Bayan an kammala taron ne ta shiga mota Any ta sauke ta a gida,daga nan Any sai ta tuƙa motar ta wuce shagon su da customers ke ta yi mata waya da messages suna jiran ta,tana isa bakin shagon taga dandazon mutanen dake jiran ta,sai kawai ta godewa Allah a ran ta sannan ta ce,
"Tabbas duk wanda ya yi haƙuri a rayuwa ya bi Allah,to Allah zai azurta shi da halal daga ƙarshe,wanda ya yi gaggawa ya bi hanyar shaiɗan to zai samu duniya ƙarshe ta barshi cikin wuya,ko ban yi aure ba ina godewa Allah da ya bani abinda zai riƙe mutunci na,na yarda da Allah na san komai lokaci ne."
Fita tayi ta faɗa shagon nasu ta fara sallamar mutane,fuskar ta ɗauke da mabayyanin farin ciki.
Rayuwar GIDAN ƊAN LITI ta ƙayatu ta kuma kyautatu,zaman Baaba da Innoh zama ne na mutunci da mutunta juna,Ɗan liti ya bayar da motar shi haya ana fitar da shi kullum,shi kuwa Saddiqa ta yi amfani da albashin ta da taimakon da Munir ya bata ta buɗe masa shagon saida kayan gyaran mota da saida baƙin mai,a duk sanda sadeeq bashi da lecture yana zama da Ɗan Liti a