Showing 189001 words to 192000 words out of 276165 words

Chapter 64 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

Billy ya tsinke, kayan ganye ne kawai ba wata tsiyar ba, amma kasancewar ta jima bata ci abinci ba sai taji daɗin ganin su.

Any ce ta ɗauki wani glass cup da yake ɗauke da wani ruwa a can ƙasan cup ɗin ba tare da Billy ta kula ba Any ta zuba mata wine a ciki,ta girgiza ta kai mata baki, sai da Billy ta kurɓa sannan Any ta bata a hannun ta, itama ta ɗauki wani glass cup ɗin ta zuba nata abun shan ta hau sha tana bin Billy da wani malalacin murmushi.

Ko minti biyu ba a cika ba hankalin Billy ya fara gushewa daga gareta,gata dai ita ce a zaune,tana ci gaba da cin abinci amma tana zaune tana jin kamar ana juya ɗakin,hannu Any ta tafa sau uku, sai ga wasu ƙattin maza guda uku sun shigo babu riga a jikin su, sanye da dogayen wanduna,biyu daga cikin su fararen fata ne, ɗaya kuma baƙar fata ne, koda mazan nan suka shigo direct wajen ɗaya Any ta nufa da gudu ta ɗane shi suka hau sumbatar junan su cikin nuna kewa da zaƙuwa.

Billy na kallon dik abinda ke faruwa amma ta kasa hanawa,wasu mazan ne suka shiga ɗakin da wasu mata guda biyu,camera ce aka dasa tare da saita ta da kyau ta yanda zata ɗauki dik abinda zai wakana a saman gadon.

Sai da suka gama saita komai sannan aka kwashe abinci da abun shan nan aka aje su gefe, Any da saurayin ta suna zaune a saman kujera suna ta zuba soyayyar su, mazan nan biyu baƙar fata ɗaya da farin fatar nan suka nufi wajen Billy dake ganin suna rabuwa mata gida huɗu.

Babu b'ata lokaci masu ɗauka suka fara aikin su, ɗakin ya yi shiru kamar masu aikin Allah'n da ba a son yin magana,kamar abun wasa matasan nan suka zage suka hau mu'amala da Billy ta dik inda suka so a jikin ta ciki har da mata biyun da aka zo dasu,sanda suka yi yunƙurin neman ta ta baya ne taso bijirewa suka tsayar da ɗaukar da suke yi suka sake banka mata magani sannan suka samu nasarar ɗaukan abinda suke so.

A wannan rana ce Billy mai harkar neman maza da mata, ta zama mai harka da maza da mata ta gaba da bayan ta,dik yanda Any ta kai ga rashin imani sai da ta tausaya wa Billy saboda yanda ta wahala a hannun matasan nan, sun jima sosai suna wahal da ita kafin su samu biyan buƙatar su su sake ta, masu ɗauka kuwa nan da nan suka hau tafi da yabawa junan su akan nasarar da suka samu,da sauri Any ta nufi Billy dake zubar da jini sosai ta bayan ta,kama ta tayi ta kai ta bathroom ta ajiye ta a saman toilet,ruwa ta haɗa mata mai zafi sosai da wasu magunguna a ciki kafin ta taimaka mata ta saka ta a ruwan,kuka sosai Billy keyi gaba ɗaya kwalliyar ta ta dame gashin idon da aka ƙara mata ɗaya ya fice,fuska tayi mata kaca-kaca,suna cikin bathroom ne aka shiga aka sake gyara masu ɗakin tare da ajiye musu abinci.

Sun jima a band'akin Any na taimaka wa Billy tana gasa mata jiki kafin tayi mata wanka su fito,wata sabuwar riga Any ta sanya wa Billy sannan ta kwantar da ita a gado ta rufe ta suka kwanta suka hau baccin gajiya.


**************************

Tin daga ranar da Abdul ya bar Maimoon a hotel ya tsere gida,bai sake ganin ta ba ko a kamfanin su,yaso ya tambayi ina take amma bakin shi ya ƙi bashi haɗin kai,dan haka sai kawai ya ci gaba da ayyukan shi kamar ma bai taɓa sanin rayuwar Maimoon ta taɓa wanzuwa ba.

Bayan wata biyu Abdul ya baro gida lafiya, cike da so da ƙaunar da Mommy ta cika shi da su ya shiga kamfanin su,tsaye yaga abokan aikin shi suna alhini da jimamin wani abun da ya kasa gane menene shi,wajen da ya gansu tsaye ya nufa ya yi musu sallama,nan fa suka hau gaisawa da juna sannan ya kalli Bilal dake sake jinjina kai yace,

"Man,wai me ya faru ne naji ana ta salati da jimami?"

"Humm ba zaka yarda ba aboki na, wai kasan ashe yarinyar nan Maimoon cikin shege tayi a zaman ta a wajen nan? Yanzu haka tana can asibiti tayi ɓari ko in ce ta zubar da cikin, wai saboda ta tsani uban cikin,ka duba min shiririta da shirmen banza na yaran yanzu fa? Bata son shi ta sakar masa jiki har yayi lalata da ita? A gaskiya tarbiyya ta taɓarɓare a wannan zamanin da muke ciki."

Tinda Bilal ya fara yi wa Abdul bayani gaban shi ke tsananin bugawa da fad'uwa,cikin ƙarfin hali ya daure ya furta,

"Ba kaɗan ba aboki na,fatan mu kawai shine Allah ya shirya mana zuri'a,Allah ya shirya mu ya kare mu daga yin aikin dana sani, and thank god she is still alive bata wuce ba daga wajen zubar da cikin."

"Shine ai, yanzu da ta mutu fa? Me zata cewa Allah? Yanzu haka iyayen ta wai sun ce ta koma gida,babu ita babu bokon bada ita ubanta zai yi sadaka, dan Allah me yafi wannan wulaƙanci da ƙasƙanci, ki ɓata shekaru masu yawa kina karatun boko rana ɗaya ki zama macen sadaka?"

"Babu kam, Allah ya kyauta, bari na ƙarasa ciki."

Jiki babu ƙwari Abdul ya isa office ɗin shi,jakar shi ya ajiye a saman table ɗin shi ya hau yawo cike da matsananciyar damuwa.

"Tabbas a waccan ranar ban yi amfani da kariya ba(condom) ina kyautata zato shi yasa ta samu ciki,ni ne namiji na farko da na fara sanin ta a matsayin ƴa mace, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,yanzu kenan da bata zubar da cikin ba sai a kawo min ɗan gaba da fatiha da salatin Annabi a matsayin dan shege na?"

Motsin mutane ya fara ji kowa na shiga office ɗin shi yana rufe ƙofa,nan take ya maida hankalin shi jikin shi ya samu waje ya zauna, hamdala ya dinga jerawa da Allah ya kawo masa komai cikin rufin asiri babu wanda ya san me ya aikata.

"Yanzu asiri na ya rufu kenan ko akwai sauran matsala a gaba?"

Tambayar da ya jefawa kan shi kenan,wadda kafin ya samo amsar tane wayar shi ta hau ruri,cikin sauri ya ɗauki wayar ya kara a kunnen shi,cike da farin ciki ya hau hamdala tare da faɗin,

"Gani nan zuwa Aunty Naja, Allah ya saka da alkhairi,gani nan zuwa yanzun nan, akwai abinda kuke da buƙata ne?"

Shiru yayi yana sake sauraren Aunty Naja kafin daga baya ya furta,

"To gani nan zuwa, a yi mata sannu dan Allah kafin na iso,Allah ya raya shi bisa tafarkin addinin islama."

Cike da murna da zumud'i Abdul ya kulle office ɗin shi ya nufi ofishin Bilal..........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI













RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨















PAGE 77:











Bilal na tsaka da ayyukan shi ya ji an buɗe ƙofar office ɗin shi da ƙarfi an shiga, cikin hanzari ya ɗaga kan shi sama yana kallon wanda ya shigar masa office babu neman izini,ido huɗu suka yi da Abdussaboor dake cikin tsananin farin ciki, da sauri Bilal ya miƙe tsaye ya nufi abokin nashi,Abdul na isa ya rungume Bilal yana faɗin,

"Alhamdulillahi Bilal ka zama Baba, Allah ya sauki Hadiza lafiya, Mai martaba yayi takwara inshaa Allahu."

Da sauri Bilal ya cire Abdul daga jikin shi cikin murna ya furta,

"What ! Kana nufin Hadiza ta haihu? Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi,Allah ya raya mana lil Takawa da imani,Allah yayi masa albarka,Ubangiji Allah ya kare shi daga sharrin wannan zamani da muke ciki,Allah ya kare shi daga zina ya sa musulunci da musulmai su amfana da rayuwar shi."

Addu'o'in da Bilal ya dinga jerowa jinjirin ne suka sanya Abdul kukan farin ciki sosai, tabbas duk duniya bashi da aboki sama da Bilal,ya zame masa kamar ɗan uwan shi na jini,yana jin Bilal a ran shi kamar yanda yake jin Sultan,ta wani ɓangaren ma zai iya cewa yafi haka,nan take shima ya tsugunna a wajen yayi sujjada domin godewa Allah,yana ɗagowa ya ɗaga hannayen shi sama yana kallon gabas,cikin zuciyar shi yake faɗin,

'Ya Allah ka gafarta min manya da ƙananan zunubai na, Allah na roƙe ka ka kare min zuri'a ta daga aikata kwatankwacin abinda na aikata a rayuwa ta,Allah nayi alƙawari daga rana mai kamar ta yau ba zan sake kusantar zina ba, balle har na aikata ta, Allah ka gafarta min, Allah na tuba, Allah na tuba Allah na gode maka da dikkan ni'imomin ka a gare ni...'

Kukan da Abdul keyi ne ya baiwa Bilal mamaki,da sauri ya isa gaban shi ya ce,

"Man wannan kukan naka yayi yawa,tashi zaka yi mu je muga jinjiri ai,ka dai san bata da kowa anan garin,ni daga yau ma na dena jin haushin ta,za mu dinga gaisawa ba dan halin ta ba,Allah ya ƙwato mata Bilal,tashi mu tafi mu ga kyautar da Allah yayi mana,a gaskiya nima auren nan zan zo nayi."

Abdul kuwa hawayen shi ya fara gogewa sannan ya kama hannun Bilal ya miƙe tsaye, makullin office da waya Bilal ya ɗauka suka fita,Abdul ma office ɗin shi ya koma ya ɗauki abinda yake da buƙata ya isa office ɗin shugaban su ya sanar da maganar haihuwar da aka yi masa tare da neman izinin tafiya wajen iyalin shi, taya shi murna shugaban nasu yayi tare da yi wa jariri da mahaifiyar shi addu'a sannan ya bashi damar tafiya.

Ko da ya fito ya tarar da Bilal dik ya kwazawa abokan aikin su maganar haihuwar,nan fa suka dinga yiwa Abdul ɗin barka da fatan alkhairi,cike da farin ciki yake amsa su kafin suyi musu sallama su wuce asibiti.

A hanya Abdul ya tsaya yayi wa su Mommy siyayyar abinda za su ci, da ruwan sha,tare da duk wani tarkacen da yake tunanin za su buƙata,cike da farin ciki suka isa asibitin,suna zuwa ya sa waya ya kira Aunty Naja ta sanar dashi ɗakin da suke, babu ɓata lokaci suka nufi hanyar ɗakin,suna zuwa suka tarar da Hadiza kwance tana bacci, kan nan babu kitso dik ta baza shi, hula Naja tayi ƙoƙarin saka mata amma dik da haka sai da gashin ta ya fito saboda babu kitso,Babyn Naja ta d'akko ta miƙa wa Abdul sai ya yi mata nuni da Bilal ya ce,

"A fara baiwa Uban ɗa ya ɗauki abun shi kafin mu sa albarka."

Bilal yaji daɗin karar da Abdul yayi masa,dan haka yana karɓar yaro ya hau jero masa kiran sallah a kunnuwan shi dama da hagu, addu'o'i ya dinga yi masa masu matuƙar amfani wanda idan Allah ya amsa yaro zai tashi abun so abun kwatance a cikin al'umma,banda fara'a babu abinda Bilal da Naja ke yi saboda jin daɗin irin addu'o'in da Bilal ke zubawa yaron,sai da ya gama sannan ya miƙa wa Abdussabour yaro ya koma gefe yana neman wayar Sultan.

Bilal ne ya fara sanar da Sultan samun ƙaruwar da aka yi, cikin farin ciki kuwa Sultan dake zaune a parlourn Innah Laminde yana cin abincin rana ya fita tsakar gida da sauri ya sanar da iyayen nashi maganar haihuwar Mommy, hamdala suka dinga yi tare da addu'ar Allah ya baiwa Mommy lafiyar shayarwa.

Nan da nan su Azizah da Hafsat suka fara maganar tafiya suna, tare da fatan Allah yasa yaro yaci sunan mahaifin su,Innah Laminde kanta bakin ta yaƙi rufuwa saboda farin ciki.

Abdussaboor da kanshi ya kira mahaifin shi ya sanar da shi yayi takwara, addu'o'i mai martaba ya dinga zubawa jinjiri da shi kanshi Abdul ɗin da Mommy,godiya yayi masa kafin ya kashe ya nemo wayar Innoh,sai a lokacin ne Naja tace,

"Kaga ka fini tunani ko? Ni fa gaba ɗaya kaina ya kulle ban yi tunanin sanar da su bama,"

"Farin ciki ne ya jawo hakan ba komai ba, da alama kina yi da wannan sabon mai gidan naki."

Sanda Abdul ya sanar da Ɗan liti samun ƙaruwar da aka yi,sai yaji ɗan liti ya fashe da dariya yana sanar da abokan sana'ar shi a tashar da yake,kafin daga baya yayi wa jinjiri addu'a,bayan sun kammala waya da Ɗan liti sai ya kirawo Innoh ya sanar da ita haihuwar, guɗa ta rabka sannan ƙit ta kashe waya,mamaki ne ya sanya shi bin wayar da kallo,cikin murmushi ya ce,

"Wato a duniya kowa da yanda yake nuna farin cikin shi."

Innoh kuwa na kashe waya ta ɓaɓɓaka da ƙyar ta na tafe tana muskuta mazaunai ta isa tsakar gida, turmi ta ɗauka da taɓarya ta hau daka tana waƙar farin ciki tana sanar da mutanen gida da maƙota haihuwar Mommy a waƙen ta, nan da nan kuwa Baabaa da Shalele da ta kawo mata ziyara suka fito suna murna suma, hararar Baabaa Innoh tayi ƙasa-ƙasa a ranta tana ayyana,

'Munafukar tsohuwa, wannan farin cikin daga jin shi kasan ba har ranta take yi ba, ba dan wannan ragowar iskokan ba ai yau mai raba ni da ke sai Allah.'

Cikin shewa Innoh ta ce,

"Alhamdulillahi Hadizatuna ta zama uwar sarakai,bari muje mu fara shirin tafiya suna birni,bana naga munafikin ƙarmadasshen tsohon da zai hana ni zuwa birnin ai."

Cikin wani irin mugun kallo Shalelen Baabaa ta kalli Innoh,kafin tayi magana Innoh ta sanya sauri suɓur-suɓur ta shige ɗaki tana ci gaba da habaici, har shalele tayi nufin binta har uwar ɗaka taji da wa take Baabaa ta hana ta,cikin fara'a Baabaa ta ce,

"Habawaa Shalelena, ke yanzu ai yaci ace kin saba da halin waccan ƴar kunamar,idan bata saida hali a guri ba wa zai saida? Muje ciki Allah ya raya,idan tana so ma ta tafi amurka ƙarewar zuwa birni."

Babu jimawa maƙota suka dinga shiga gidan suna taya Innoh murnar samun ƙaruwar da aka yi,zama tayi ta dinga zabga ƙarya da ƙarairayi game da haihuwar kamar a gaban ta akai komai, kud'in da aka biya a asibitin da Hadizan ta ta haihu kuwa ta yanko ya kusa miliyan,mutane kuwa sai jinjina lamarin suke yi suna faɗin,

"Ai ayi mafiyin haka ma,yaron dake taimakon talakawa da dukiyar shi, ai iyalin shi ya yi masu mafiyin abinda yake wa wasu."

Da yamma liss Innoh ta kira layin Ɗan liti ta sanar dashi ita fa zata shirya ta tafi birni wajen Mommy,cikin farin ciki Ɗan liti yace,

"Ban ƙi zuwan ki birni ba Innoh,amma ki jinkirta na samu wasu ƴan kuɗi na aiko maki,kafin nan kafin suna sai ki daka mata yaji da ɗan abubuwan da ake yi na al'ada ki tafi mata da shi,idan kin tashi komai biyu zaki raba,kin dai ga Ameerah ma na hanya,tinda al'ada ce tace ayi hakan gwanda muyi kar ya zama abun gori."

Har tayi nufin zazzaga masa rashin mutunci sannan ta kafe sai ta tafi,sai taji ya kirawo kalmar gori,nan take ta natsu,dik da ba haka ranta yaso ba, taso ta tafi da wuri, ƴan kajin nan da gashin da ake ci na jego a ci da ita,cikin tsuke fuska tace,

"To ta yaya zaka turo kuɗi bayan baka nan?"

"Ni fa ina ga ma cikin satin nan zan dawo gida,wahala an sha ta iya wahala Innoh,amma yanzu na gane kan gari,da yardar Allah idan na dawo zaki yi farin ciki."

Sakin ranta tayi kaɗan suka ci gaba da hira yana bata labarin gwagwarmayar da ya sha da farkon zuwan shi,kafin daga baya Allah ya haɗa shi da wani mutumin kirkin bakano ya yi masa jagora game da yanda zai samu ci gaba shima.

A haka Innoh ta hakura da shirye-shiryen tafiya ta fara shirin haɗawa Mommy garar haihuwa,da dare da Sule ya dawo ta sanar da shi ya yi murna sosai shima, sannan yace da shi za a je suna,dan kuwa sau biyu kawai ya taɓa zuwa gidan Hadizan tinda suka koma birni.

Bayan kwana biyar da haihuwar Mommy Ameerah ma ta haihu lafiya,nan da nan labarin haihuwar Ameeran Shamsu mai Turi ya yaɗu a cikin garin Ba Mugu,mutane sun taya su farin ciki sosai, Innoh ta samu ta leƙa su sau ɗaya, daga nan bata sake komawa ba, zuciyar ta gaba ɗaya ta tattara ta yi kano.

Sanda labari ya riski Kaka Ameerah ta haihu sai tayi tattaki har gidan su Shamsu ta roƙi arzikin su basu Ameerah tayi wankan gida tinda haihuwar fari ce,babu musu ko ɓata lokaci iyayen shamsu da shi kanshi Shamsun suka amince, tinda dama haka al'adar su tace, cikin daren Kaka ta taimaka wa Ameerah suka haɗa kayan jinjiri wanda shamsu yayi matuƙar ƙoƙarin siyan dik abinda ake da buƙata dai-dai ƙarfin shi,suna kammala shiri Shamsu ya kirawo adaidaita sahu ya ɗauke su sai gidan Ɗan liti.

Ko da Kaka da Ameerah suka shiga gidan sun tarar da Innoh ta gama raba yajin da ta niƙa da rana ta dake shi da kayan ƙamshi da daddawa da kayan ɗanɗano,kallon Kaka da Ameerah tayi wadda ke rungume da jinjirin ta,cikin mamaki da faɗuwar gaba ta ce,

"Goggo lafiya na gan ku cikin wannan talatainin daren da kaya niƙi-niƙi haka? Allah dai yasa ba sakin...."

"Dakata min mai fatan tsiya kawai,ina sane da dik iya shegen da kike aikatawa a gidan nan Innoh,rashin lafiyar danake yi ke taka min burki wajen zuwa na ci maki mutunci,ke yanzu idan aka ce ki je gidan Hadiza sai kije dik da kin san Naja na can? Ita kuma wannan fa? Wa zai yi mata wankan jego kenan?"

Sule ne ya fito daga ɗakin shi ya karb'i yaron Ameerah dake tsaye tana jin takaicin yanda Innoh ke nuna banbanci a tsakanin ta da Mommy,cikin kame-kame Innoh tace,

"Wanne munafukin ne ya sanar dake zani kano Goggo? Ni babu inda zani,na dai so zuwa da amma tinda Naja ta tafi ma na cire rai da zuwan,bismillah shiga ciki ki zauna bari na kammala raba kayan garar nan."

Kaka bata sake bi ta kan Innoh ba ta kalli Sule tace,

"Baabar Abbe na nan ne na ji wajen ta shiru kamar babu kowa? Bari na je mu gaisa nazo ka raka ni gida."

Ɗakin Baabaa ta nufa ta ƙwanƙwasa ƙyaure,Baaba ce ta yi gyaran murya da alama ko sallar isha'i take yi ko jan carbi,dan kuwa idan Baabaa na jan casbahar ta bata magana sai ta kai aya,ko da Kaka ta d'aga labule sai ta tarar da Baabaa na shafa addu'a tana faɗin,

"Lale maraba da Goggon Naja, bismillah shigo ina ɗan lazimi ne,"

"Allah sarki,ai na ɗakko muku ƴar ku ne da kuka barta a gidan surukai ta haihu,shine nace bari na leƙo mu gaisa kafin na wuce,ya haƙurin halayyar Innoh kuma?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login