Showing 120001 words to 123000 words out of 276165 words
Chapter 41 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
kamar madarar shanu,nan take kuwa surukan guda uku suka shiga kitchen suna aikin su cike da nishad'i da annashuwa.
Saddiqa na markad'a albasa da attaruhu a blender Baabaa na tsaye tana buga qullin qosai tana mita,
"Fisabillahi bature na kyautawa 'yan zamani kuwa jama'a? Shi yanzu jajjagen attaruhun ne sai an saka a inji ba za a ƙulƙula shi a turmi a tashi ba tsabar son jiki? Allah to ya kyauta idan kin gama ki bani abuna na zuba na hau tuya, ko tuyar ƙosan ma kuna da injin yin tane?"
Dariya Ummi da Saddiqa suka sanya, Ummi ta kalli Baabaa tace,
"Hajiya Baabaata Allah dai ya ƙaara miki lafiya da imani da nisan kwana mai albarka, Baabaa idan ina Abuja sai na dinga kewar ki,dan Allah Baabaa ki bimu mu koma tare dake,"
Murmushi Baabaa tayi dan kuwa da gaske take son Saliha surukar ta har cikin ranta, so ne na gaskiya mara algus a tsakanin su, wannan dalilin ne ya sanya surukar tata itama take son ta tsakani da Allah, cikin magana irin ta dattijan kirki Baabaa tace,
"Saliha kenan ni kaina ina so na kasance da ku a koda yaushe, dan kuwa ina alfahari da jajircewar ki wajen kula da tarbiyyar yaran ki gaba d'aya su ukun, ga kuma uwa uba yanda kike son Baban Gida kike yi masa biyayya, sai dai kashhh ba zan iya bin ku na koma Habuja da zama dindindin ba,anan garin na taso iyaye da kakanni na duka'yan nan garin ne,sannan anan garin iyaye na suka aurar dani har na hayayyafa,sannan anan garin miji na mai so na da ƙaunata ya rasu kan shi a saman cinya ta,dan haka ba zan iya tafiya na bar ɗakin aure na ba Saliha, ina fatan a dik inda mutuwa take ta riske ni a ɗakin aure na a saman gado na inda ta ɗauki miji na,"
Hawaye ne ya gangaro a idanun Baabaa na kewar mijin ta, cikin sauri Saddiqa ta durqusa a gaban ta riqe da tissue ta hau goge mata idanun ta,jikin Ummi ne yayi sanyi tace,
"Ki gafarce ni Baabaa daga yau ba zan sake roƙon ki koma Abuja da zama ba,amma inshaa Allahu jimawar da muke yi bamu zo ba daga yanzu zata kau, na gama Phd ɗina da nake yi, yara ma dik sun gama karatun sakandire shi kuma wannan kin ga ya girma har aure yayi, fatan mu suma 'yan matan Allah ya fitar musu da mijin aure na gari a yi auren su idan yaso sun ci gaba da karatun a ɗakin mijin su,"
"Yauwaa Salihatu shi yasa nake son ki, kina da fahimta, kyawun mace ta zauna a ɗakin mijin ta kar ta gusa idan ba sakin ta akai ba ta bar gidan, to mutuwa ta raba ta da gidan ta,Allah kuma ya amsa addu'ar ki Allah ya basu miji na gari mai albarka kamar Baban Gidana,"
Dariya suka yi saboda jin son kai irin na Hajiya Baabaa,a haka suna hirar su har Baabaa ta gama buga qullin ƙosai ta zuba duk abinda ya dace ta fara suyar shi a wutar da Saddiqa ta jima da kunnawa ta itace, dan kuwa Baabaa tace baza ta yi amfani da gas ba ya babbake ta, Ummi kuwa bayan ta markad'a gyaɗar ta da ginger da kaninfari kaɗan sai ta tace ruwan ta ɗora a wuta ta rufe kaɗan, sai da ya tafaso sannan ta zuba wankakkiyar farar shinkafar ta suka ci gaba da dahuwa, bata sauke ba sai da shinkafar nan ta dahu, sannan ta matsa lemon tsami kaɗan a ciki ta juya, kindirmon ta ta ɗakko ta dinga zubawa kaɗan kaɗan tana juya shi da ƙaramar mixer har sai da ya game jikin shi sosai yayi fari ƙal kamar yanda Baabaa ke son shi,banda tashin ƙamshi babu abinda yake yi, gefe ɗaya kuwa Saddiqa ce ta kashe gas dan kuwa ruwan shayin da ta ɗora ya dahu,Ummi na gama juye kunun gyaɗar ta a mazubin da take da buƙata Saddiqa ta buɗe fridge ta ɗakko ragowar farfesun naman ragon da suka ci da dare ta d'umama musu, yana gama d'umamawa ta juye a kyakkyawan mazubi ta kai parlour, a tare suka gama haɗa komai sannan suka yi hamdala tare da sakar wa da junan su murmushi suka shiga d'akunan su dan yin wanka kafin azo karyawa.
Baabaa ce ta kyab'e baki tace,
"Yo ba dole na koma gida na ba nima tinda ina da nawa d'akin mijin? ita surukar tawa ta wuce d'akin su ita da nata mijin, ita waccan ta shiga ɗakin jikan nawa an barni ni ɗaya a parlour ya munafukar tsohuwar da taje gulma gidan surukai,"
Tana gama faɗin haka ta wuce d'akin ta dake cikin gidan, d'akin nata yafi kowanne d'aki girma a gidan, kayan da aka ƙawata d'akin kaɗai zai sa mutum ya gane lallai wannan na uwar mai gida ne, dan kuwa komai na more rayuwar dattijo an saka a ciki, matsala ɗaya aka samu daga wajen Baabaa domin kuwa dik wannan kayan more rayuwar Baabaa bata da buqatar su acewar ta, ita dai fatan ta ta koma ɗakin da tayi rayuwa da mijin ta ta zauna har ta Allah ta kasance.
Saddiqa ta jima a tsaye tana kallon Munir dake ta baccin gajiyar abubuwan da suka faru a jiya, da kuma hana idon shi bacci da yayi saboda an haɗa su d'aki ɗaya da matar da ya sha warning akan ta, idan sun san basu son komai ya shiga tsakanin shi da matar shi me yasa suka turo ta d'akin shi? Murmushi tayi da ta tuna kalaman shi na daren jiya,
'Babu abinda zan ce da Allah nidai da ya wuce godiya Saddiqa,saboda ya bani duk wani abu da nake so a rayuwa ta, ciki kuwa har da wanda nake so na ci gaba da rayuwa da ita har a aljannah, Saddiqa ina son ki, Ina ƙaunar ki,dan Allah ki so ni kamar yanda nake son ki kin ji?'
Band'aki ta faɗa tana rufe fuskar ta kamar a lokacin yake sanar da ita abinda ke cikin zuciyar shi game da ita, tana shiga Munir da ya jima da farkawa tin shigar ta d'akin yaga yanda take qare masa kallo sai ya tsaya yaƙi motsawa kar ya katse mata hanzari.
Cike da murmushi ya sauka daga gadon ya isa bakin ƙofar band'akin ya hau k'wank'wasawa dan tsokana yana faɗin,
"Ki yi sauri ki fito ko na shigo brush nake so nayi ina jin yunwa,"
Cike da matsanancin tashin hankali Saddiqa ta hau watsa ruwan da ta tara a pampo a cikin wani bokitin roba, tana gamawa ta sanya kayan ta ta buɗe qofa zata fito kanta a qasa saboda kunya da tsoron kar ya shiga band'akin tana tsaka da wanka, tsaye ta gan shi yana jiran ta ta fito, ƙura mata ido yayi yana kallon ta, hannu ya d'aga kamar zai taɓa ta, tayi saurin kaucewa ta bar bakin ƙofar band'akin, murmushi yayi sannan ya shige band'akin dan gabatar da uzirin shi.
K'wank'wasa ƙofar d'akin nasu aka yi, cikin sauri Saddiqa ta isa bakin ƙofar ta buɗe Ummi ta gani riqe da leda irin mai hasken nan da kaya a ciki tana miƙo mata,
"Ga wannan ki sauya dan na san baki da kaya anan zuwa anjima sai kuje ke da mijin ki ku ɗebo kayan ki da kike da buƙata kafin Abbah ya gama yanke hukuncin abinda ya dace muyi kuma,"
"To Ummi na gode Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata,"
"Ameeen ya Allah Saddiqa,"
Ummi na tafiya Munir ya fito daga bathroom,ko magana Saddiqa bata yi masa ba ta faɗa band'akin ta sauya kayan jikin ta, riga ce doguwa kalar ruwan zuma mai haske,ko da ta fito Munir kafe ta yayi da idanun shi masu rikitar da ita a dik sanda yake yi mata wannan kallon da bata saba gani a idanun shi ba, cikin wata murya mai taushi yace mata,
"Wife kin yi kyau sosai masha Allah, da alama shigar dogayen riguna za a dinga yi min a cikin gida, idan za a fita kuma a sanya ƙaaaton hijabi har ƙasa da niƙabi,"
"Dik abinda kake so shi za a yi maka a gidan ka Husband,"
Tana faɗin haka ta bar ɗakin cike da jin nauyin shi, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar Munir har bai san sanda ya fara taka rawar murna ba daga ƙarshe ya bi bayan ta dan su je su karya.
Zaune suka tarar da Baabaa har ta kusan cinye nata abincin, tana ganin Saddiqa ta zauna tana gaishe da Abbah da ke kurb'ar kunu yana santi tace,
"Ina kika baro min jika na ko ke kaɗai ce me cikin cin abinci?"
Sadeeq dake murmushi tinda yayar shi ta fito ne ya fashe da dariyar jin abinda Baabaa tace,Munir kuwa da ya qaraso zai zauna a kujerar dining table ne yace,
"Ah ah fa Baabaa kar ki takura wa Mata ta, kuma naga idan taci ai kamar naci ne ko?"
Salati Baabaa ta saki tana kama baki, ta kalli Abbah da Ummi dake yi musu dariya tace,
"Inyeee kun ji yaro wai har yayi auren da zai nuna min iyaka ta,"
Ɗan haɗe fuska Abbah yayi cikin wasa yace
"Manniru ka kiyaye ni fa,"
"Tuba nake yi Abbah, barka da safiya,"
"Ba haushe yace da yawan faɗa gwara yawan gaisuwa ko? Lafiya ƙalau alhamdulillah,yauwa ɗazu muna hanyar dawowa daga masallaci nace maka kuje ku ɗebo kayan Saddiqa ko? A bari sai zuwa yamma bana so kuma idan kun je ku kula kowa a tsaya hayaniya,idan naji an yi faɗa Munir kai zan hukunta domin kowa ya san Saddiqa ba mai rikici bace ba,"
"Inshaa Allahu Abbah babu abinda zai faru sai alkhairi,"
"To Allah yasa,"
"Abbah to ya maganar jarabawar ta ta? Ni fa ina ganin mu koma can ta yi kawai,"
"Idan aka koma can sai dai ta bari wata shekarar ta rubuta kenan,ina ganin kawai ku zauna anan mu zamu koma gobe har da Sadeeq sai a samar masa da wata makarantar a can amma fa idan Baba Ɗanli ya amince,ita kuma idan ta kammala jarabawar sai ku taho Abujan, Baabaa hakan yayi kuwa?"
Abbah ya faɗa yana kallon Baabaa da ta kammala cin abincin ta ta miqe zata koma parlour ta zauna, cikin fara'a da jin daɗin yanda rayuwar Saddiqan ta ta haskaka cikin lokaci qanqani tace,
"K'warai da gaske hakan yayi,Allah yasa ta rubuta jarabawar cikin nasara daga nan ta zama likita kamar yanda Yadikon ta ke fata,"
K'walla ce ta taru a idanun Saddiqa ta sunkuyar da kan ta qasa,tabbas tayi kewar Yadikon ta sosai daurewa kawai take yi dan kar ta d'aga hankalin mutanen dake yi mata alkhairi,Munir ne ya kalle ta cike da so da qauna da tausayawa yace,
"Da yardar Allah sai Saddiqa ta zama babbar consultant a kuma babban asibitin tarayya ta Abuja,"
"Allah ya amince Manniru da kuwa nayi farin cikin da ban taɓa yin irin shi ba, Allah ka bani tsawon rai mai albarka naga wannan ranar,"
"Ameeen ya Allah,"
Haka suka ci gaba da cin abinci suna hira gwanin sha'awa kafin daga baya su kammala Saddiqa ta kwashe dik abinda aka b'ata ta tafi wanke-wanke.
*********************
Da misalin biyu na rana aka sallamo Abdul daga asibiti, zaune suke a gaban Mai martaba a cikin turakar shi, Innah Laminde na zaune a gefen mijin ta Bilal da Abdul na gaban su sun duqar da kai kamar marasa gaskiya.
Cikin in ina Bilal ya qarasa zayyane wa Innah Laminde kafff abinda Mai Martaba ya umarce shi da ya sanar da ita game da rayuwar Abdul ta baya, domin a ganin shi akwai abinda Abdul ya b'oye bai sanar dashi ba a wancan lokacin shi yasa ya roqi Bilal da kar ya b'oye musu komai, sai dai basu sani ba Bilal ya b'oye abubuwa da yawa badan ace Mai Martaba ya san su ba ba zai gane ba, cikin murmushi irin na manya Mai Martaba yace,
"Lallai Bilal kana son wannan abokin naka shi yasa kake rufa masa asiri, to babu damuwa Allah ya bar qauna domin shi ya yi muku albarka,tabbas kai ɗin aboki ne na gari wanda kowanne iyaye za su so ace irin ka na tare da ɗan su, mun gode maka sosai a bisa nusar da shi Babana da ka dinga yi a lokacin da ya kauce hanya ya manta da tarbiyyar da muka bashi, ya manta da cewar idan kai bawa baka ganin ubangijin ka ido da ido, to shi ubangiji yana kallon ka, kallo irin wanda yake har zuciya, dan kuwa ya san me kake saqawa a ran ka mai kyau ko mara kyau.
Dan haka ke yanzu kiyi haƙuri ki daina kukan da kike yi, kin ji dai dik abinda ya faru, dan haka mu ɗauki ƙaddarar da ta sanya Abdul auren Hadiza ya tare da matar shi idan ya tashi komawa aiki ya ɗauke ta su tare a waje ɗaya bana son ya qara zama babu mata tinda yanzu yayi auren,Allah ya sanya albarka ya kare dikkan abun qi,Allah kuma ya kawo wa malam Bilal tashi matar ta gari ko?"
Murmushi Bilal yayi ya sunkuyar da kai qasa sosai cike da girmamawa, Innah Laminde kuwa hawaye take ta sharewa tana kallon Abdussabour dan kuwa bata taɓa zaton irin rayuwar da ya aikata a baya zata bibiye shi ba, lallai abinda ya aikata yayi muni,da k'yar ta buɗe baki ta iya cewa,
"Allah ya sanya albarka,"
"Ameen"
Suka amsa da shi kafin daga baya Mai Martaba ya sallami Abdul da Bilal su wuce d'akin Abdul ɗin,bayan fitar su Sarki yayi wa Innah Laminde nasiha sosai ya bata haƙuri sannan yace a sanar da mata da dare suje su ɗauki amarya a kai ta d'akin ta idan yaso an yi walima dan taya su murnar aure.
********************
Mommy da Ameerah ne suka shirya dan tafiya Saloon ɗin cikin kasuwa dan a wanke musu kai a zana musu qunshi, sun shirya cikin manyan hijabai Mommy har da sanya tsohon niƙabin ta ta rufe fuskar ta, kuɗi ta ɗauka sosai suka bar gidan dan kayan matan da Naja ta kai mata basu yi mata ba,tana so ta siyo wani da kanta.
Suna fita Innoh ta afka d'akin Yadiko tana so tayi bincike a kayan Mommy, sai dai kashh tana shiga taga Mommy ta sanya wa akwatin ta kwad'o ta rufe shi, dukan akwatin tayi da ƙafa ta hau masifa,
"Kaiii wannan yarinya an yi marowaciyar masifa, yanzu fisabillahi menene na rufe akwati da kwad'o? "
Har za ta fita ta koma da baya ta hau lalube d'akin Yadikon, ba tare da ta ji Sallamar su ba taga an ɗaga labule a daidai lokacin da take ɗaga katifar Yadikon........
*Dan Allah kuyi min haƙuri saboda ji na shiru da kuke yi kwana biyu,abubuwa ne suka yi yawa wallahi. Ina yi wa kowa fatan alkhairi...yau Wattpad taqi hausa na fara rubutu sai da nayi mai yawa ya goge, har na yi zuciya nace ba zan sake ba amma ina tunano yanda kuke qaunar littafin nan dai na daure. Son so fisabillah mutanen Hajiya Baabaa😂*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 47:
"Uhummm ai tinda na ga babu ke a cikin waccan hayaniyar ta ƙofar gida na san bakya kusa, sai dai ban taɓa zaton na taddake a irin wannan halin ba, to yanzu da kike bincike ɗakin mamaciya me kike nema? Ko kin zo satar abinda ba zaki kai shekara ɗari kina mora ba tinda kema dole taki mutuwar zata ɗauke ki a lokacin da baki gama jin daɗin duniyar ba?"
Haɗe fuska Innoh tayi sosai ta qanqance ido ta ɗakko kud'in da ke ƙasan katifar tace,
"Kin ga Yaya ki fita a ido na na rufe, da kike maganar sata ai kema kin san ban yo gadon ta ba, sai dai ki tambayi 'yar so ina ta samu wannan maƙudan kuɗaɗen har take ajiyewa a ƙasan gadon ta,"
A wannan karon dole Baabaa tayi shiru, domin kuwa ita da kan ta za ta so sanin inda Saddiqa ta samu kuɗi masu yawa haka kafin ta zargi Innoh da binciken d'akin mamaciya ba a sanya ta ba,cikin d'aure fuska Baabaa ta kalli Saddiqa dake tsaye a gefen ta kai duƙe idanun ta na zubar da ƙwalla tace,
"Ina jiran jin bayanin inda kika samu kuɗi masu yawa haka Saddiqa, kar kuma kiyi min ƙarya dan ba halin ki bane,"
"Baabaa Yah Munir ne ya bani su tin zuwan da yayi na farko,sai wanda Yadiko ta b'oye na ribar sana'ar ta,kuma ni ban taɓa amfani da kuɗin da Yah Munir ya bani bane saboda Yadiko ta gargad'e ni akan amfani da kuɗin samari, tace dik rintsi duk wuya kar na zaƙe akan cin kuɗin samari domin watarana dole ne su fanshe kuɗin su, zata iya yuwuwa su fanshe da jiki na tin kafin su aure ni, amma idan ya tabbata namiji aure na zai yi to bayan ya aure ni ya kashe min ko nawa ne babu damuwa, ni kuma nayi-nayi na ƙi karɓar kuɗin a lokacin da ya bani amma ya dage sai da na karɓa, shi yasa na ajiye ban taɓa ba,"
Cike da tausayawa Baabaa ke kallon Saddiqa,a hankali ta kama kafaɗar ta tace,
"Haba Saddiqa ! Munniru ai ɗan uwan ki ne me yasa baki yi amfani da kuɗin da ya baki ba? Da kina da waɗannan kuɗin kuka dinga zama da yunwa ke da ɗan uwan ki da rana ko da dare? Yanzu gasu nan me zaki yi dasu bayan baki more su ba a lokacin da kika fi tsananin buƙatar su?"
"Ku dena wannan wasan kwaikwayon dallah malamai, ni da kaina na san yunwa na iya jefa mutum aikata zina da sata dan ya samu abinda zai ci, waya sani ma ko...."
Cikin tsawa Baabaa tace,
"Kar ki kuskura ki danganta zuri'ar Yadiko da sata ko zina,dan kuwa basu sha a mama ba, ke da kan ki sai dai son zuciya ya hana ki fad'ar gaskiya, amma kafin ki samu yarinya mai kamun kai da natsuwar wannan a kaf garin nan sai kin jima kina nema,ke matsa ki baiwa mutane waje ina ruwan wani ma da zarge-zargen ki na iska da wofi? Yarinya dai alhamdulillah yanda kika so ta lalace Allah ya tsare ta bata bi maza ba dan su ciyar da ita,yanda kika so ta zamo mai halin ɓera bata yi ba,sai aka barki da mai halin ɓera a ɗakin ki, domin Ameerah ba barin ki tayi da ɗauke-ɗauke ba balle ni da ta