Showing 213001 words to 216000 words out of 276165 words
Chapter 72 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
sandar ke karanta mata be girgiza ta ba sai ma gaba da ta yi suka bi bayan ta,Motar Abdul ta buɗe ta faɗa gaba, Bilal yaso ya hana ta shiga gaban sai kawai ya ƙyale ta, dan baya son ma magana ta haɗa shi da ita saboda kar ya faɗi abinda zai zo ya yi daya sani daga baya.
Ko da suka je police station har gaban DPO suka je aka fara gabatar da case, daga ƙarshe ganin tana da ɗanyen goyo sai DPO ya ce zai tura su kotu direct ba sai an tsaya wani tsare ta ba.
Shi dai Bilal yana nan ya kasa ya tsare yana so a ɗauki duk matakin da ya dace kafin ma ya sanar da iyayen Abdul,dan baya son wani yace masa kar a hukunta ta akan abinda tayi saboda tana matar Yariman ƙauyen Ba Mugu.
Suna kammalawa da station ya wuce asibiti wajen Abdul,kwance ya gan shi idanun shi kulle,amma da alama ba bacci yake yi ba,zama Bilal ya yi a gaban gadon ya yi shiru dan be ma san me zai ce ba,sun jima zaune shiru kamar Abdul ba zai yi magana ba,sai Bilal yaji Abdul ya ce,
"Na gode Bilal da ka ceci rayuwa ta,ban zaci zan rayu ba a irin azaba da raɗaɗin da suka ratsa gangar jiki na,yanzu shikenan na nakasa ko Bilal? Likita yace min zai yi wahala na ƙara tashi, wace mace ce zata zauna dani a haka Bilal? Na tsani Hadiza, na tsane ta Bilal, na yi dana sanin sanin Hadiza a rayuwa ta,Bilal ba zan iya ci gaba da rayuwa da Hadiza ba,idan ta illata ni ne dan ta zauna dani ita kaɗai,to ni kuma na datse igiyar auren mu guda ukun,daga yau ni Abdussabour na datse igiyar aure na dake kan Hadiza Ɗan liti dika ukun."
"Alhamdulillahi ! Na ji daɗin wannan hukuncin da ka yanke Abdussabour,da ace baka sake ta ba ma sai na yi yanda na yi ka sake ta,Hadiza ba macen da za a haɗa zuri'a da ita bace, alhamdulillah ma da baku tara zuri'a mai yawa da ita ba,yaro ɗaya Allah ya azurta ku da shi a tare,shi kuwa yaro namiji bashi riƙon tabo kamar ƴa mace,Allah ya baka lafiya,yanzu haka ban zo nan ba sai da aka miƙa maganar ta kotu,ba zan bar yarinyar nan ta numfasa ba ba tare da an yanke mata hukuncin da ya dace da ita ba wannan alƙawari na ɗaukar wa kai na...........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 86:
Baaba ce zaune a parlour ta yi kicin-kicin da rai,fuskar ta babu alamun fara'a ko walwala a cikin ta,gefe kuwa jakar kayan ta ce a ajiye,mayafin ta ta sake gyarawa a kafad'arta sai ta tura ƙafar ta cikin takalmin roban ta mai kyau, Munir ne ya yi sallama ya shiga gidan hannun shi riƙe da wayar shi da makullin mota,tsayawa ya yi turus yana kallon Baaba da ta yi zumbur ta miƙe tsaye tana jifan shi da wani irin mugun kallo kamar wanda ya kashe mata wani nata,cikin ɓacin rai Baaba tace,
"Sannu sarkin zamba cikin aminci,kai dai Manniru baka yi halin azziƙi ba sam,zaton da nake yi maka na mutanen kirki kafff ka goge min shi a zuciya ta,haka muka yi da kai? Nace haka muka yi da kai? Rimi-rimi kuka yaudaro ni kai da uban ka da surukin ka kuka kawo ni garin nan,maida ni kuma sai ya zama aiki? Wanka dai bani ke yi wa matar ka ba uwar ka ke wanke ta ta wanke jariri,to ni zaman uban me nake yi da ba za a maida ni ɗakin miji na ba? So kuke na mutu a bariki...."
Wani irin kuka ne ya ƙwacewa Baaba,nan ta samu waje ta zauna tana rera shi kamar wadda aka yiwa wani mugun abun,dariya ce ta kama Munir amma haka ya shanye ta ya ƙarasa shiga cikin parlourn ya zauna a gefen Baaba,jakar ta ya janyo gaban shi sannan ya ce,
"Kin shirya tafiya yanzu?"
Cikin matsar ƙwalla ta d'aga kai ta kalle shi, tana so ta tabbatar da ba raina mata hankali yake so ya yi ba, dan haka tana ganin babu alamar wasa a fuskar shi ta ce,
"Na shirya mana Manniru,dan Allah ku maida ni ɗakin miji na,ni tinda aka aurar dani ina da jajayen sawu na ban taɓa yin nisa da ɗaki na ba ya wannan lokaci."
'Ikon Allah,ita wannan har yanzu tana nan da mentality'n mutanen da na rashin fita,lallai yau idan ba a maida ita ba akwai case,gashi ni kuma ina da aiki sosai a office ban san ma ya zan yi da ita ba,ya Allah ka kawo min mafita.'
Baaba ce ta ga Munir ya ƙure jakar ta da kallo yana tunani be ce mata komai ba, sai ta miƙe a fusace ta ce
"Dama na san ai ba maida ni za ka yi ba,to bari ku ji,ko mutuwa nayi anan ban yarda a binne ni anan garin ba,ku maida ni ɗakin miji na a wanke ni a can a sallace ni a garin mu,tinda kun kafe kun nace sai na zauna daku anan ɗin."
A fusace Baaba ta kama hanyar ɗakin ta tana sababi,shi dai Munir lallab'awa ya yi yaje ya ga matar shi da ɗan shi suka gaisa sannan ya leƙa wajen Ummi,sai da suka gaisa sannan Munir ya ce,
"A gaskiya Ummi a zo a maida Baaba ƙauyen su kowa ya huta tin kafin ta ja maku Allah ya isa."
"Subhanallahi Munir kana da hankali kuwa? Wanne irin ta jawo mana Allah ya isa kuma ana zaune ƙalau?"
"Ke kike zaune ƙalau da iyalan ki Ummi amma ita akan ƙaya take ta matsu ta koma garin su,yanzu zuwa na zaune na tarar da ita a parlour tana jiran na zo na maida ita garin su,saboda ta san iwar haka nake shigowa gidan kullum shi yasa ta tare ni,yau idan kika ji kalaman da ta saki zaki tabbatar da gab take da ta zabga maku Allah ya isa saboda aje ta anan da kuka yi against her will."
"Ikon Allah,to bari na yi wa Baban ku magana,ni a gani na tana nan ta huta da masifa da bala'in Innoh da yaran ta da basu ragawa kowa,sannan ko babu komai anan zata fi samun kulawa,zaman ƙauye da birni ai ba ɗaya bane."
Alhaji Baban Gida ne ya fito daga wanka ɗaure da towel a ƙugun sa ya lullub'e jikin shi da wani babban towel ɗin,waje ya samu ya zauna ya ɗauki mug ɗin da aka haɗa masa shayi ya kurɓa,sai da ya gama sha ne ya amsa gaisuwar Munir yace,
"Nima jiya na yi tunanin mayar da ita gida gaskiya,amma tinda abun ya zo da haka gobe inshaa Allahu Munir ka shirya kazo ka maida ita saboda yau ɗin nan kana da aiki da yawa da baka ƙarasa ba a office "
"To Abbah inshaa Allahu gobe zan zo na maida ta, kafin nan yau a samu ko su Anisah su kai ta a ɗan yi mata siyayyar komawa,ta haka ne zata kwantar da hankalin ta ta fahimci wannan karon da gaske maidata za a yi."
"Hakan ma shawara ce mai kyau, ohh Baaba case kenan,ita dai ta mutu a ɗakin mijin ta,to Allah yasa muyi ƙarshe mai kyau baki ɗaya."
"Amin mace ta gari,Allah ya yi miki albarka, Allah ya jiƙan iyayen ki, ina jin daɗin yanda kike son mahaifiya ta ƙwarai kike nuna damuwar ki akan ta,Allah yasa yaran mu su ji ƙan ki fiye da yanda kika yi wa naki iyayen da nawa iyayen."
"Amin ya Allah miji na gari."
Munir sai murmushi yake yana zaune yana sauraren yanda iyayen nashi ke nuna wa junan su soyayya da ƙauna ba tare da ganin sun tsufa ba,dik irin wannan kaywawan halayen dama a wajen su ya gade shi,shi yasa yake ririta Saddiqa kamar ƙwai.
Koda ya fita daga ɗakin direct ɗakin Baaba ya shiga, zaune ya ganta saman abun sallah idanu sun rine mata sun yi jawur,farar fuskar nan ta ta dik ta yamutse ta yi ja,harara ta banka masa ta kau da kai gefe, zama ya yi a gaban ta ya tanƙwashe ƙafa sannan ya ce,
"Hajiya Baaba tamu ta gargajiya,yanzu dai nazo maki da albishir mai daɗi a sakar mun fuska dan Allah,na je na lallaɓa su Abbah sun amince gobe zan maida ki ɗakin mijin ki,yau ma ba dan aiki ya yi min yawa ba da yanzu mun ɗauki hanya, ki shirya anjima su Anisah su kai ki siyayyar tsaraba,gobe da ƙarfe tara zamu tafi ƙauyen Ba Mugu inshaa Allahu."
Tinda Munir ya fara magana Baaba ke washe baki, hannu ta sa ta daki kafad'ar shi cike da murna tace,
"Ko ku fa Uhumm? A ce wai ku ɗakko ni tsofai-tsofai dani na dawo gidan yara na zauna ina da nawa ɗakin mijin ba banda shi ba? Allah ya kaimu goben da rai da lafiya, ni da an bar siyan tsarabar ma abubuwan da aka bani ma duk suna nan na kai wa yaran can su Abbe."
"Ah ah Baaba ba an yi haka ba, ki dai samu ki sake yi musu tsarabar,ƙawayen ki ma dik ki saya masu abubuwa a san kin zo Abuja gidan ɗan ki ko ba haka ba?"
"To ai shikenan, ni a shirye nake, in sun shirya su taho mu tafi."
"To ni bari na je na ci abinci na wuce na ma makara."
"Allah ya bada sa'a ya yi albarka Mannirunaaa."
Dariya Munir ya yi ya amsa da "Amin Baabataaa" sannan ya fita zuwa dinning area,abinci ya ci sosai sannan ya sake sallama da Saddiqa da babyn su Suhail ya tafi office.
Wani irin kyau Saddiqa ta ƙara yi saboda ba kaɗan ba jegon ya karɓe ta,ta cika ta zama babbar mace kamar ba ita ba,yanayin ƙirar jikin su ɗaya da Mommy,sai dai Mommy ta fi ta cika sosai da kyawun diri,ita kuma ta fi Mommy kyawun fuska da dogon gashi, yaron su da alama irin jikin baban shi ya ɗakko,wato ƙaramin jiki,amma kyawun fuskar shi dik na Saddiqa ne.
Ba ƙaramar kulawa take samu ba daga mutanen gidan gaba d'ayan su,dik wani motsi da zata yi sai ta samu mai taimaka mata,a ganin ta ma abun kamar ya yi yawa,wannan dalilin ne ya sa bata tare da kewar rashin mahaifiya,a kullum tana yi wa mahaifiyar ta addu'a da mahaifin ta sai kuma su Ummi dake kula da ita kamar su suka haife ta.
******************************
Wani irin duhu ne da d'akin mutum baya ganin koda tafin hannun sa,banda zarni da warin kashi babu abinda ke tashi a wajen,ƙarar buɗe ƙofar ɗakin ce ta sanya Sule dake ɗaure hannu da ƙafa waigawa ya kalli mai shiga ɗakin,hasken waje ne ya haske fuskar Sule har ta sanya shi kare hasken da tafin hannun shi,a tsorace na kalli leɓen Sule da ya kumbura ya yi suntum,haƙorin shi da ya karye sai ya ƙarawa fuskar shi muni ya sauya mata kamannin ta,abinci aka tura masa a irin mazubi mai soson nan na take away,cikin sauri ya ɗauki abincin ya buɗe ya hau ci kamar wanda ya yi shekaru bai gamu da hatsi ba.
Loma kawai yake zubawa ko ta kan cinyar kazar dake cikin shinkafa da miyar bai bi ba,sai da ya ci fiye da rabin abincin sannan ya fashe da kuka,cikin kuka ya ce,
"Oga dan girman Allah ku min rai ku buɗe ni na fito daga ɗakin nan,ku kai ni duk inda za ku kaini amma bana son zaman nan,da na san inda gidan Hadiza yake dan uwar ta da na nuna maku shi na huta, wannan azabar ta ishe ni haka."
Kuka ya ci gaba dayi yana roƙon a fitar da shi,mamakin kafiya da taurin kai irin na Sule ne ya sanya Alhaji ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin,cikin sauri yaron Alhaji da ya kawowa Sule abinci ya matsa gefe ya bashi waje,Alhaji ne ya saka hankicin sa ya toshe hancin shi kafin ya ce,
"Kai yanzu da ka nuna mana inda Sweet H take ka gwammace ka ci gaba da azabtuwa ko?"
"Yallab'ai ai ban musa maka na gane wa kake magana akai ba ko? Ka ga kuwa ko dan azabar nan da nake ci idan na san gidan ta zan kai ku,ni tinda akai mata aure ban san inda take ba,shi wannan ƙaton ɗan daudun da kuka zo dashi rannan ai shi ya kamata ku sa a gaba ya nemo ta,gidan ta na ƙauyen mu shi kaɗai na sani ko mahaifiyar mu bata san gidan ta dake nan birni ba tinda bata taɓa zuwa ba."
"To uban me ya shigo da kai birni kake ikirarin suna kazo?"
"Alhaji ƙanwata Saddiqa dake Abuja ce ta haihu shine zan je suna daga nan na haɗu da abokai na a gaisa,idan ƙarya nake Allah ya...."
Zalɓe ne ya daka masa tsawa ya ce,
"Dalla yiwa mutane shiru."
Shiru Alhaji ya yi yana nazarin maganganun Sule,ya jima yana nazari kafin ya juya ya ce,
"Zalɓe a buɗe shi,ya yi wanka ku same ni a babban parlour."
"To Alhajin Allah an gama."
Wani irin daɗi ne ya kama Sule,alƙawari ya yi wa kan shi ko Abuja wajen abokan shi da ya yi niyyar zuwa a yi chilling ya fasa zuwa in har aka sake shi,idan kuwa ya koma ƙauye babu shi babu sake shigowa birni,zai kama kan shi ya ƙarasa rayuwar shi a ƙauyen Ba Mugu,da alama can ne yafi dacewa da shi ba zaman birni ba.
Da ƙyar Sule yake iya dirza jikin shi saboda azabar zafi da yake ji a fatar shi,ba ƙaramin duka samudawan mazajen nan suka dinga yi masa ba,wanka yake yana zubar da hawayen azaba,a haka ya gama ya sanya sabon kayan da ya siya shi da Hajiya kafin Alhaji ya kamo shi.
Tinda ya fito ya ke kallon tsaruwa da kyawun gidan,cikin zuciyar shi yake tunanin su kuwa wacce iriyar dukiya suke da ita haka? Tafe yake yana bin bayan Zalɓe har suka shiga parlourn da Alhaji yake, nan fa Sule ya sake sakin gandar leb'en shi yana ta'ajibin tsaruwar gidan,a ƙasa ya zauna ya sake gaishe da Alhaji, banza Alhaji ya yi masa ba tare da ya amsa shi ba ya ce,
"Ban fito da kai dan na ƙyale ka ka ci gaba da yawo sakaka ba, na fito da kai ne dan ka je kauyen ku ka nemo min inda Sweet H take ka sanar dani,idan ka kuskura ka ƙi sanar dani inda take zan ɗauke iyayen ka da kai kan ka na dawo da kai nan,azabar da zan sa a gana maka sai ta fi wadda ka sha a baya,ka fahimce ni da kyau ko?"
Tinda Alhaji ya fara magana Sule ke gyad'a kai alamar yana sauraron dik abinda Alhaji ke faɗi,shi dai babban burin shi bai wuce su sallame shi ya koma gida ba.
Akwatin shi Zalɓe ya wurga masa sannan ya damƙi hannun shi ya ɗaure masa idanu da wani farin ƙyalle,tankaɗa ƙeyar shi ya yi suka fara tafiya,sun jima suna tafiya kafin Sule yaji an wurga shi cikin mota shi da akwatin shi,gyara zaman shi ya yi da kyau yana hamdala a cikin ran shi,sai da mazajen suka gama hirar da za su yi sannan suka tada motar suka fige ta.
Sule na nan zaune yana ayyana abubuwa da dama cikin ran shi yaji an taka wani wawan burki,motar na gama tsayawa aka buɗe inda yake aka damƙi hannun shi da kayan shi aka wurga su waje,ƙarar tashin motar da kurar da ta buɗe Sule ne ya bashi tabbacin su Zalɓe sun wuce, cikin sauri ya kunce idanun shi ya hau juye-juye,gaba ɗaya bai gane wajen da yake ba tinda dama shi baƙo ne a garin, dan haka cikin sauri ya buɗe akwatin shi ya ɗakko wayar shi,ganin ta ya yi a kashe alamar babu caji,maida ita ya yi aljihun shi ya miƙe tsaye ya fara tafiya, mutanen da suka ga abinda ya faru ne suka ƙaraso wajen shi da sauri suna tambayar shi ko lafiya? cikin ƙwalla Sule ya ce,
"Kidinafin d'ina suka yi,dan Allah ku taimaka min na koma ƙauyen mu bani da ko sisi a jiki na."
Salati mutane suka hau yi kowa na tofa albarkacin bakin shi, da ƙyar aka haɗawa Sule dubu biyu da ɗari takwas,godiya ya dinga yi musu,tambayar su inda zai samu tashar mota ya yi,wani bawan Allah me machine irin lifan ɗin nan yace,
"Yanzu haka ta wajen zan wuce,hau na ajiye ka."
"Na gode,na gode bayin Allah, Allah ya raba ku da shiga tashin hankalin da na shiga a rayuwa ta."
Cike da tausayawa suka taimaka masa ya haye machine, ko ina na jikin shi ciwo yake yi masa,ganin haka ne ya sa mutumin rage gudu suka tafi a hankali har suka isa tasha,ko da suka je tasha babu motar da zata tafi garin Ba Mugu sai can kauyen dake gaba da garin nasu,Sule bai ɓata lokaci ba wajen afkawa motar ya ce,
"Ranka ya dad'e ni dai ku kai ni ko ƙauyen dake gaba da wannan ne, fatana shine kawai naga na bar garin nan."
"Baka da matsala kawo haƙƙin inji."
"Nawa ne?"
"Ɗaya da biyar zaka kawo,ka rubuta sunan ka da lambar wayar ɗan uwa anan."
Babu ɓata lokaci Sule ya yi dik abinda aka buƙata, ana samun cikon mutum huɗun da suka rage mota ta tashi suka kama hanya.
*****************************
Hannun su sarƙafe da na juna suke fitowa daga airport,fuskar Billy sanye take da face Mask,kanta lullub'e da wani ɗankwali fari tasss mai jefi-jefin pink ɗin flower,dogon wandan dake jikin ta ya kama shape ɗin ta ya yi cif kamar a jikin ta aka ɗinka mata shi, Any kuwa Sanye take da suit farare tass kanta babu ɗanƙwali sai aski da aka yi mata tsakiyar kanta da gashi,kunnen ta sanye suke da wasu ɗankunnen diamond sai ɗaukan idanu suke yi,wuyan ta kuwa zagaye yake da sarƙar ɗan kunnen siririya mai ado da ƙaton dutsen diamond a jiki,manyan zobunan hannun ta da abun hannun da ta sanya ne suke nuni da zaman ta mace.
Drivern ta ta hango yana tsaye yana jiran su,hannun ta mai janye da akwatin su ta miƙa masa sannan ta riƙe hannun Billy da kyau suka taka zuwa inda motar su take.
Ajiyar zuciya Any ta sauke dan kuwa a gajiye take saboda dik ita ta gama yi musu dik abinda ya dace a yi kafin a fito daga cikin airport ɗin,sai da suka fito daga airport suka kama hanyar gidan Any dake GRA a cikin garin kano kawai