Showing 114001 words to 117000 words out of 276165 words

Chapter 39 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

sosai tace,

"SARAUTA bana son ka sake yi min maganar yarinyar nan, kai dai ka maida hankalin ka wajen samun sauqin abinda ke damun ka, daga baya zaka ji hukuncin da mahaifin ka zai yanke akan ta,da alama kai baka san komai ba game da yarinyar da ka aura Bilkisu ta sanar dani komai kuma ta nuna min komai dan haka ni dai ban yarda da auren nan ba, ba kuma zan yarda da shi ba har gaban abada,"

Cike da tashin hankali Abdul ya kalli Innah Laminde sannan ya kalli Bilal da Sultan cikin kad'uwa yace,

"Kema ta nuna maki abinda ta tura min a wayata?"

"K'warai ta nuna min, ta kuma tabbatar min da cewa yarinyar nan karuwa ce dan...."

Cikin rintse idanu Abdul yace

"Dan Allah Innah ki daina faɗin haka, bafa da wani aka kama yarinyar nan tana zina ba, ki sake duba videon da hotunan da kyau zaki ga a wajen gyaran jiki aka yi mata su ba da sanin ta bane sharri kawai ake son a qulla mata dan kawai a raba mu, ita Bilkisun da ta turo a ina ta samu? Idan har Hadiza karuwa ce ita kuma fa?,"

Mamakin Abdul ne ya sanya Innah Laminde kasa cewa komai, kallon shi kawai take yi tana ayyanawa a ranta,

'Anya yarinyar nan haka ta bar min ɗa na kuwa bata sabauta min shi da baqin asiri ba?'

Jin kalmar shi ta qarshe ne ya sanya ta miqewa cikin ɓacin rai tace,

"Abdul baza ka yi zaman aure da Hadiza ba har abada, dole ne ka sawwaqe mata dan ba zan zauna da karuwa a matsayin suruka ta ba,idan kuwa ka qi bin umarni na  kaqi sawwaqe mata to tabbas sai dai ka nemi wata uwar amma ba Laminde ba kaji na faɗa maka,"

Cike da fushi Innah Laminde ta juya zata bar asibitin Sultan da Bilal suka hau bata hakuri amma taqi zama firrr tace tafiya gida zata yi, cikin sauri Sultan ya bi bayan ta dan ya maida ita gida.

Hankalin Abdussaboor ne yayi bala'in tashi dan jin furucin mahaifiyar shi akan auren shi da yake jin a duk sanda ya datse shi to fa kamar ya datse numfashin shi ne, Bilal ne ya dafa kafad'ar shi yace,

"Shin abinda aka tura min a wayata gaskiya ne game da Hadiza? Indai ta tabbata yarinyar nan haka take dole ne ka daure ka riqe auren nan da kyau saboda babu macen da ta fi dacewa ka aura sama da Hadiza a rayuwar ka............"

*Ko meye dalilin Bilal na faɗin haka?.....ku ci gaba da bi na dan jin yanda zata kaya...... ku qara hakuri a kai qarshen labarin dik zaren da ya qulle maku zan warware muku shi a sannu...kar ku manta sannu bata hana zuwa sai dai a jima ba aje ba.*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI


















RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨




















PAGE 44:













Ganin Sultan na wajen ne ya sanya Bilal kawar da maganar da yake so yayi wa Abdussabour,wajen zama ya samu yana yi wa Abdussabour bayanin yanda yana zaune wata No ta tura masa hotuna da videos ɗin Mommy tsirara, cikin tsananin baqin ciki da takaici Abdul yace,

"Ya qarshen No yake?"

"90 ne qarshen ta, ka san me No ne?"

Girgiza kai Abdul yayi domin kuwa bai san mai No ba, amma ya tabbata ko wanene sai ya nemo shi kuma sai ya miqa shi wajen hukuma an hukunta masa shi gwargwadon abinda ya aikata na fitar da tsiraicin matar shi, Sultan ne ya ja bakin shi ya tsuke dan kuwa shima an tura masa, fad'ar an tura masan zai iya sake jefa Abdul a wani mummunan hali dan haka sai ya ɗauki plate ya zubawa Bilal abinci ya ɗauki ruwan roba ya kai masa yace,

"Yah Bilal ka ci abinci ka je gida ka kwanta ka huta ka d'ebo gajiyar hanya, ni zan kwana da Yah Abdul ɗin, ina ga dik muyi haƙuri da Maganar nan for now har Allah ya baka lafiya, dama so ake a raba ku, ni kuma a gani na tinda har kana son ta kawai ka rufa mata asiri ka riqe igiyar auren ku da kyau, wataqila za a rage samuwar irin su a society,"

Cikin ɓacin rai Abdul ya kalle shi yace,

"Wai kana nufin ka yarda da abinda ake faɗa akan Hadiza? Sharri ne fa da neman b'ata mata suna kawai, kana ganin wajen da take ka san wajen gyaran jiki ne aka samu wani marar imanin yayi mata videon, sannan...."

Bilal ne ya tari numfashin Abdul yace,

"Kaga Abdul a bar maganar kawai kamar yanda yaron nan yace,hakan shine kawai samun natsuwar ka a yanzu, ba dai kana son matar ka ba? To ai magana ta qare babu wanda zai zauna maka da ita dan haka mu rufe wannan maganar kai Sultan bani waku na wake tabahuwa nake ji,"

Abincin da Sultan ya zubawa Bilal ya miqa masa, Bilal ya Karb'a yana yi musu hira amma Sultan ne kawai ke amsa masa,Abdul kuwa ya lula duniyar tinanin rayuwar da ta tinkaro shi da wadda ya bari a baya, lallai maganar Bilal gaskiya ne, shine yafi dacewa ya auri Mommy,domin kuwa dama an faɗa abinda dik kayi sai an yi maka, dik wayon ka da zillewar ka watarana zaka girbi abinda ka shuka, to ga ranar girbi tazo masa, ranar da yayi zaton komai ya wuce har abada tinda ya dena abinda yake yi a lokacin da quruciya na jan shi,a hankali ya furta,

"Astaghfirullah wa'atubu ilaih,"

Nan take tunanin shi ya ɗauke shi ya maida shi shekaru takwas da suka gabata.

A shekarar da Abdussaboor ya kammala karatun shi a shekarar ya samu aiki saboda gata da connection da yake da shi, dik da cewa shi ɗin haziqi ne amma hazaqar shi ba ita ta bashi wannan aikin ba, idan da hazaqa na bada aiki nan take tabbas da wanda suka fishi hazaqa sun jima da zama manyan ma'aikata a qasar nan.

Cikin shekara ɗaya da fara aikin shi ya samu mahaukatan kud'in da ya sai fili da su a cikin garin kano da qauyen Ba Mugu,a haka ya ci gaba da rayuwa a gidan haya har ya samu ikon ɗora ginin gida mai ɗakuna uku da parlour biyu sai kitchen,store room da wani band'aki guda ɗaya a general parlourn gidan,gida ne mai kyau da ya amsa sunan shi gida domin kuwa ya samu zane daga k'wararrun masu zane, sannan maginan da suka yi ginin suka baiwa zanen nan haqqin sa.

Tinda ya kammala gidan ya fara kiciniyar sanya furniture a gidan wanda Sarki da kan shi ya bada tashi gudummawar saboda ganin qoqarin da Abdul ɗin ke yi birni da qauye na ganin ya samarwa kan shi muhallin, wanda a zaton su da ya kammala ginin nashi aure zai yi, sai dai bayan kammala gina gida Abdul sai ya koma tara kuɗin siyan mota mai kyau da zata dace da gayun shi da matsayin shi a wajen aikin shi da kuma nuna isa da taqamar shi na mulkin gidan su.

Dik abun nan da yake yi daga Sarki har Innah Laminde babu wanda ya taɓa yi masa maganar aure saboda ganin shi ɗin yaro ne mai hankali da hangen nesa, yana yin komai a bisa tsari da cancanta da duba buqatuwar yin hakan a gare shi,gefe ɗaya kuma basu san cewar yaron su Abdussaboor na da matsananciyar sha'awa ba ta yanda baya taɓa kwana ɗaya zuwa biyu ba tare da ya nemi wadda zata ɗebe masa kewa ba, a zahiri ko kuma ta wayar nan ta zamani har buqatar shi ta biya ya samu natsuwa.

(Qalubale a gare ku iyaye, dik natsuwa da hankalin ɗan ku yana da sha'awa a cikin halittar shi take, dan haka kar ku sake ku kauda kai akan wannan bangaren wajen kula da tarbiyyar yaran ku maza da mata)

A cikin shekaru huɗu Abdussabour ya gama gina gidajen shi na cikin garin Kano da na qauyen Ba Mugu, sannan ya sayi mota mai azabar kyau da tsada, kuɗi ne suke ci gaba da shigo masa ko ta ina saboda aikin shi da yake yi ba dare ba rana, ganin yanda ya zama busy ne ya sanya Sarki qara ganin bari ya kyale ɗan nashi har sai ya bijiro masa da zancen yana son yayi aure, idan yaso sai a yi a wuce wajen, dan kuwa ya kula a yanzu bashi da lokacin kanshi ma balle na mace, neman kuɗi kawai ya sanya a gaba, nan kuwa bai sani bane da zarar ya gama da aikin shi yake wucewa joint ɗin da yake samun macen da zata ɗebe masa kewar gajiyar aikin da ya sha da rana.

(Wannan shine dalilin da yasa maza komai gajiyar da suka yi a waje idan dare yayi suke buqatar matan su a kusa da su, dan haka dik kamun kan yaron ku iyaye idan ya kai minzalin aure kar ku yi qasa a guiwa wajen tirsasa shi ya yi aure, ko ku taya shi neman matar da zai aura, ko ku bashi dama da 'yancin nema da kan shi)

A kwana a tashi Abdul na neman matan banza yana kaiwa gidan shi ya hole da su ba tare da sanin iyayen shi ba balle dangin shi,a haka har ya haɗu da Bilal dan garin Bauchin Yakubu,Bilal mutum ne mai rawar kai da wayewa tare da ɗaukan wanka na garari, dik da cewa Abdul sama yake dashi a wajen aiki hakan be hana su yin abota ba,qarshe Abdul ya gane Bilal a gidan haya yake da zama, dik qarshen wata biyu ko uku yake zuwa gidan su ganin iyayen shi.

Watarana suna zaune a masallaci an idar da sallar magrib bayan sun tashi daga aiki, suna fitowa zasu tafi gida Abdussabour ya kirawo Bilal yayi masa tayin komawa gidan shi da zama idan babu damuwa,bayan 'yar jayya da Bilal yayi akan kar ya takura wa Abdul ɗin,daga qarshe dai ya amince ya koma gidan Abdul da zama.

A hankali Bilal ya fara gano muguwar dabi'ar Abdul ta neman matan banza da dare, hakan kuwa yayi masifar d'aga hankalin Bilal da sanya shi a cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali har ta kai ya dena cin abinci sosai, baya kuma yiwa Abdul magana daga sallama da gaisuwa shikenan, a wajen aiki kowa yayi harkar gaban sa idan an tashi kafin Abdul yace wa Bilal yaje su tafi Bilal ya wuce, ko kuma ya boye a wani wajen sai Abdul ya tafi ya fito ya b'ata lokaci a waje kafin ya koma gida.

Ana haka watarana Abdul ya ritsa Bilal a gida da tambayar dalilin sauyawar halayyar shi da nesanta kanshi da shi Abdul ɗin, bud'ar bakin Bilal sai yace,

'Ka yi hakuri idan nesanta kaina da kai da nayi yana yi maka ciwo, amma zan yi mamaki ace baka san halayyar da kake yi ta neman mata tana nesanta ka bane da Ubangijin da ya halicce ka,ya kaji yanzu a ranka da nake gudun ka?'

Cike da jin kunya da gane inda maganar Bilal ta dosa Abdul yace,

'Ina jin babu daɗi a raina, sai nake ganin kamar na yi maka wani laifi ne babba da ya sa kake nesanta kanka dani,'

'To mu 'Yan Adam ma kenan Abdul,kamar yanda na nesanta kaina da kai haka ubangiji ya nesanta da kai har se sanda ka tuba ka dena aikata zina sannan zai kusanta da kai, sannan kamar yanda kake ji a ranka ka yi min laifi ne ya sanya ni nesanta kaina da kai to ya kamata ka dinga ji a ranka cewa neman matan nan da kake yi kana saɓawa Allah, kana fusata shi, idan ya fusata ka san me zai yi maka? Ya baka kuɗi, ya baka gida,ya baka abun hawa, ya baka rai, ya baka lafiya, to me kake nema? Ka tsaya ka bauta masa shi d'ayan ne kake ganin ba zaka iya ba sai ka yi ta saɓa masa da babban zunubin da da an kirawo shirka saɓawa iyaye sai an ce zina? Habaa Abdul nayi zaton ka girmi wannan level ɗin shashancin ashe....'

Cike da jin kunyar Bilal Abdul ya tari numfashin shi da cewa,

'Ya isa haka Bilal, na gode sosai da tunatarwar ka a gare ni, tabbas sai yau na fahimci nasihar da mai martaba yake yi min a fakaice, me yasa bai fito fili yayi min nasiha da faɗa sosai yanda kayi min ba? A kullum sai dai ya dinga cewa idan Allah ya baiwa matasa kuɗi su ji tsoron Allah su kashe su ta hanya mai kyau kar su b'arnatar,Bilal wannan dalilin ne ya sanya nake yawan taimaka wa marasa shi,nake kyautatawa iyaye na sosai suke sanya min albarka, a gani na neman matan da nake yi ba wata matsala bace kawai kauda sha'awa ne kafin nayi aure,tinda ai kowa nada sha'awar,'

(Da damar matasa idan suka samu kuɗi basu da aure, to fa ba a raba su da d'aya daga cikin abubuwan nan, shaye-shaye,neman mata,caca da sauran abubuwa na sab'on Allah, dan haka da ka kula Allah ya ɗaukaka ɗan ka maza ka ja shi a jiki ka nuna masa hanyar da zai bi, ba zaka samu damar jan d'an ka a jiki ba har sai ka bashi tarbiyyar da zaka iya juya shi ko bayan ya girma)

Nan dai Bilal yayi tayi wa Abdul nasiha da nuna masa haramcin yin zina har ya samu maganganun sa suka yi tasiri a zuciyar shi yayi alqawarin ba zai sake ba.

Bayan shekara ɗaya da daina neman matan da Abdul yake yi, ya koma ga Allah rayuwar shi ta koma daga ibada sai aikin shi, kyautatawa iyayen sa da mutanen da Allah ya sa suna da rabon ya taimaka musu, sai kuma da dare idan ya dawo gida sai ya shiga social media ya shiga facbook ya ga me duniya take ciki, daga nan ya koma shiga Instagram da sauran social media platforms, a hankali shaid'an da shaid'anun mata suka fara jan ra'ayin shi har yake chatting da matan Facebook dake nuna suna son shi, dan kuwa hoton shi ne da ya ɗauka a wani companyn qarafa da suka je Abuja wani aiki a profile ɗin shi,a haka Abdul ya gane soyayyar social media da daɗin da take da ita, dan kuwa yana samun biyan buqata sosai kuma daga nan yake aikawa dik yarinyar da ta gamsar da shi kuɗi ko nawa ta buqata baya jin shakkar yin hakan.

Dik wannan abun da yake yi Bilal bai sani ba, dan kuwa bai taɓa bada wata qofar da zai gane abinda yake aikatawar ba, tinda kowa da d'akin shi da band'akin shi a cikin d'akin.

Ana haka ya haɗu da wata yarinya kyakkyawa a Facebook mai suna Salwahlove,tinda ya haɗu da Yarinyar nan ta ɗauke hankalin shi ya daina mu'amala da kowacce yarinya sai ita, qarshe dai sai da ya zamana har da rana sai Salwa ta sanya Abdul keb'e kan shi a wani wajen su sha soyayyar su,dik yanda taso su haɗu yaqi yarda gudun kar Bilal ya gane wa'azin shi yaa rushe yayi sabon d'ori.

A kwana a tashi Abdul da Salwa sun kai watanni huɗu suna soyayya Kwatsam sai Salwa ta fara turo masa hotunan sassan jikin ta, daga qarshe shima ta dinga hilatar shi har ya fara tura mata nashi, cikin rashin dabara da wayo Abdul idan ya tashi zai tura kafff jikin shi, ita kuma dake mai wayo ce sai ta tura iyakar qirjin ta ko gaban ta ko wani sashe na jikin ta, bata taɓa nuna masa hoton ta ba gaba ɗaya tsirara,sannan bata yarda da video call ko voice call kawai a yi chatting.

Watarana Bilal da Abdul na zaune a parlour sun yi order ɗin abincin dare, sai mai abici ya kawo ya buga qofa, kasancewar Abdul na zaune kusa da qofa sai ya miqe yace Bilal yayi zaman shi bari yaje ya dawo, Abdul na fita gate ɗin gidan dan karɓo abinci Salwa ta hau kiran shi a waya, ko da Bilal ya leqa sai yaga an rubuta Salwahlove a jikin sunan, Murmushi kawai yayi ba tare da ya ce komai ba sai ya ɗauka yana ɗauka sai yaji an kashe wayar,a zaton shi ma katsewa wayar tayi, yana ajiye wayar Abdul ya shigo, cike da shaqiyanci irin na abokai Bilal yace,

'Aunty Salwa ta kira ka yanzun nan,amma ina ɗauka dan na ji muryar mai sa'ar da ta sace zuciyar ka har ka qi sanar dani, sai naji ta katse,'

Murmushi Abdul yayi yace,

'Ba katsewa kiran yayi ba haka take da kunya, tinda muke da ita tsawon watanni ban taɓa jin muryar ta ba sai dai muyi chatting,yanzu haka kiran da ka gani sanar dani take yi lokacin tane yanzu,'

'Tooo ikon Allah, ai kuwa yau sai dai tayi haƙuri, nima ina buqatar lokacin ka, mun jima bamu zauna haka mun yi hira ba, ashe ita ce ke janye ka,'

Nan da nan kuwa Abdussabour ya sanya wayar shi a silent suka hau hira suna cin abincin su da aka kawo musu,a can facbook kuwa Salwah ta cika tayi famm da baqin ciki da damuwar rashin Abdul domin kuwa ta qudirta a ranta yaune wa'adin soyayyar qaryar su zata qare bayan ta amshi wasu manyan kuɗi a wajen Abdul ɗin.

Abdul kuwa bayan sun gama cin abinci da hira da Bilal sai kowa ya tafi makwancin shi, suna komawa d'akunan su Abdul ya kunna data ya hau Facebook dan ya lallashi abar qaunar shi Salwa, yana shiga yayi mummunan gamo da saqon da ya rikita ƙwaƙwalwa da ruhin shi har ya kasa kwanciya ya fito zuwa d'akin Bilal a kid'ime.

Bugu ɗaya yayi wa qofar d'akin Bilal ɗin Bilal ya fito sanye da gajeran wando da singileti yace,

'Lafiya kake min irin wannan bugun qofar kamar zaka balle ta? Meya fa...'

Maganar shi ce ta katse bayan kiran wayar Abdul da aka yi, cikin hanzari Bilal ya kafe shi da ido yana son sanin abinda ke faruwa,Abdul ne ya amsa wayar ya sanya ta a handsfree nan take muryar gardin qato ta fara magana,

'Baby ya baka turo min kud'in da na tambaya ba? Ko baka gane me magana bane? Salwa ce faaaa, dan Allah ka turo min kud'in na gaji da ganin ka ina so na sauya sheqa na koma wajen wani sabon jinin,'

'Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,dama Salwah ba mace bace namiji ne?'

Abdul da Bilal suka faɗa a tare, nan take abubuwan da suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login