Showing 171001 words to 174000 words out of 276165 words
Chapter 58 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
ya zille ko ruwan daya shigar dashi sha cikin gidan bai nema ba saboda tashin zuciya daya dame shi.
Yana fita sai ya buɗe shagon shi ya kunna inji,nan take masu kai cajin waya da MP tare da fitilu suka dinga sallamawa,shi kuwa da ya Karb'a yake bada lamba bayan ya manna irin lambar a jikin wayar mutum ko fitilar shi da sauran su.
Yana gamawa da saka caji ya kalli mutanen da suka rakuɓe suna jiran shi, nan take ya gane turi suka zo, murmushi yayi a ran shi yace,
'Ya kamata fa yanda ake ta ƙarawa abubuwa kuɗi a gari nima na ƙara kud'in nan, kullum siyan mai nake kamar zan sai gwal,sannan gashi ban biya kud'in injin da na sa a kawo min daga kano ba,dan haka dole na ɗan ƙara wani abu yau.''
Tsumewa yayi yace,
"To fa gaskiya kun riga da kun san cewa abubuwa sun ƙara tsada yanzu,gashi har jannareta na siya dan saka maku cajin wayoyin ku,dan haka daga yau zan yi ƙari akan kud'in caji da turi, dik film daya mai tsawo nera ɗari da hamsin, film d'aya gajere nera ɗari."
Cikin sauri wata budurwa dake wajen tana iyayi tace,
"Tabbb ai ni tinda nazo garin nan na gane kuna murza arha son ran ku, mu a can kano turi ko babba ko ƙaramin film indai irin wannan ne har ɗari uku bayarwa muke yi."
Cikin sauri Shamsu ya kalli matasa da magidantan da ke tsaye suna jira yace,
"To kun ji ba? Kun ji inda ake harikar ariziƙi, anya ni ba tattarawa zan yi ba na koma can da zama nai ta sana'a ta?"
Dariya matashiyar tayi tace,
"To ai ta can yawancin mutane suna da wayoyi andiro ba su damu da turin ba, su da kan su suke saka data su shiga su gani ko su d'akko,sai ka ga mutum a babbar riga ko a hijabi,haka zai bi dare ko rana ya kalli abunhi hankali kwance cikin rufin asiri ba sai yaje kowa ya ganhi ba,dama idan kaga masu yin turin irin mu ne marasa manyan wayoyi."
Haka suka dinga hira da yarinyar nan har ya gama sallamar mutane bata tafi ba,hira suka dinga yi har ta ƙarbi lambar wayar shi akan zai dinga tura mata ta WhatsApp,nan fa shamsu ya shiga tunanin taya take yin WhatsApp tinda ƙaramar waya gare ta, gum yayi da bakin shi bai ce komai ba,bayan tafiyar ta ne ya samu wasu mutane ƙalilan suka zo suma ya sanyawa wasun su caji,wasun su kuma yayi masu turin films,Shamsu bai tashi a shago ba sai sha daya saura na dare,kasuwa ya tafi ya samu wajen mai nama ya siyo musu na dubu ɗaya da gurasar ɗari biyar,sannan ya siya musu lemon roba ya kama hanya yayi gida.
Tinda ya shiga ya tarar da Ta Annabi zaune a bakin ƙofar d'akin ta, dan kuwa kwana biyu abinda ta tsiri yi kenan saboda idan ya dawo ya miƙa mata abinda ya siyo mata,shi kuwa koda bai yo mata nata ƙunshin ba kunya na saka shi ɗebar mata dik abin ya kawo,yau ma bayan ya gaishe ta tayi masa sannu da zuwa sai ya wuce d'aki, kwance ya tarar da Ameerah tana malelekuwa a ƙasan ledar ɗaki,gefe kuma wata baƙar leda ce take zuba yawu ciki, yana shiga ɗakin ya jawo ledar ta zuba yawu ta kalle shi cikin hawaye tana so tayi magana, cikin sauri Shamsu ya hau buɗe labulen ɗakin da window dan iska ta ratsa d'akin, muryar ta yaji tana faɗin,
"Anya shamsi kana so ka ga Annabin rahama kuwa?"
A mamakance ya juya ya kalle ta tare da kama ƙugu yana son jin me ya aikata me muni haka ake masa irin wannan maganar,cikin kuka tace,
"Yo ai dole na tambaye ka ko kana son ganin Annabin rahama shamsu, fisabillahi kana ganin halin da nake ciki kayi min alƙawarin kawo min abinda zan ci amma shiru,nan nan na fita wajen Ummah nace ta sammin abinci idan sun dafa amma haka ta hana ni wai me yasa ba zan rage son jiki ba na girka namu,ai kowacce mace a gidan mijin ta ita ke hidima dashi, ka fita daga ƙarƙashin ta dan haka ba abinda zata sammini,ina ji ina gani suka shige da abincin su d'aki ita da su Fadila yawu nata zuba min, ga yunwa ga ƙwadayi ina ji,yau ko zaman gidan haya muke da Ummah ai sai haka."
Majina ta sharce ta ƙyalla ido akan ledar hannun shi ta sake marairacewa dan ya yarda da maganganun ta,cikin ran shamsu sam bai ji daɗin abinda aka yi wa Ameerah ba,tinanin miƙa mata ledar hannun shi yayi dan taci naman ta ƙoshi,sai dai wata zuciyar na tuna masa tayaya zasu sa abu a gaba shi da matar shi su cinye ya hana mahaifiyar shi? A baya yana yo musu nasu ƙunshin amma Ameerah tayi kutun-kutun da kirsa da kisisina ta hana kuma sam bai fahimci makircin ta ba, yanzu ya koma siyo musu su kaɗai sai dai su ɗebar musu tana so shima ta hana da makirci.
Sassauta fuska Shamsu yayi ya zauna yace,
"Kiyi haƙuri,ni idan na samu ma yanda nake so barin gidan zamu yi,ko mu kama haya ko na fara gini a filin da Baba ya bani."
"Au da kana ma da fili shine baka taɓa faɗa min ba?"
"Yanzu ba gashi dalili yayi kin sani ba? Ina da fili ina da gona dik shekara ana ara ana noma a bani wani abu."
Shiruuu Ameerah tayi na ɗan wani lokaci, zuciyar ta na raya mata a yanzu ta miƙa wuya ɗari bisa ɗari zata yi zaman Aure da Shamsu da zuciya ɗaya tinda dai-dai gwargwado yana da kadara.
Hira Ameerah ta dinga jan shi da ita har suka cinye nama da gurasa ba tare da Shamsu ya kula ba,suna gamawa yace,
"Gaskiya dole ne kiyi wanka kafin mu kwanta,kin ji yanda kike tashi kuwa? Daurewa kawai nake ina cin abicin nan."
"Shamsu ba zaka gane halin da nake ciki bane,tinda cikin nan ba a jikin ka yake ba,ni ko warin sabulu bana so,bana son ƙamshin komai saboda yawan haraswa."
"Ikon Allah, to yanzu bari na jiƙa maki toka a ruwa na tace miki kiyi wankan da ita sai ki d'auraye jiki da ruwa me kyau idan kin gama."
"Ashe shamsu haka ka tsane ni ban sani ba? Wanka da toka se kace wata kifi?"
"To Ameerah ya kike so nayi ne dan Allah? Yanda fa kike jin haraswa idan kin shaƙi ƙamshi ni kuma ina jin haraswa idan na ji wannan ɗoyin na tashi."
Kuka sosai Ameerah ta fashe dashi ta tashi cikin fushi da borin kunya ta fita, zaune ta tarar da Ta Annabi ta cika tayi fammm, dan kuwa kusan dik abinda suka tattauna ta ji shi sarai a kunnen ta, kasancewar ƙofar su Ameerah buɗe take,ita kuma tinda shamsu ya dawo take zaune a wajen tana jiran a miƙo mata nata kason ta tanɗe ta koma ɗaki,cikin ɓata rai Ameerah ta wuce ta ɗauki bokiti ta d'ebi ruwa a rijiya ta ɗauki sabulun wanki ta shiga bayi, ita da kanta da ta zo cire rigar ta ta shaƙi warin hammatar da take yi sai da taji kamar zata yi amai,da sauri ta ƙarasa cirewa ta ja iska mai tsawo sannan ta hau wanka,tasss ta dirje jikin ta ta d'aura alwala ta koma ɗaki.
Kwance ta ga shamsu yana chatting, yana ganin ta yayi saurin kife wayar yana zare ido alamun rashin gaskiya sun bayyana,cike da mamaki tace,
"Yau kuma dan na kama ka kana kallon abun duniya shine ka tsorata? Bari nayi sallah nazo mu gani tare maye a ciki?"
Dariya tayi ta tada sallah, cikin abinda bai fi minti uku ba ta idar da magariba da isha'in da ta haɗe waje ɗaya, tana idarwa shamsu yayi saurin kashe data ya shiga wajen films ɗin da suka zame musu jiki wajen kallon su,sun jima suna kallo kafin daga baya su ajiye wayar su kashe fitila, tankad'a ni waje shamsu yayi ya rufe musu ƙofar su yace ɗaukan rahoton ya isa haka.
Bayan wata uku.............
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 69:
Fuskar shi mutuk yake d'aura agogon hannun shi tare da gyara zaman wuyan rigar shi a kafaɗun shi,cikin sauri ta fito sanye da atampa ɗinkin doguwar riga da hijabi iya guiwar ta,hannun ta riƙe yake da ƙaramar jaka,takalmin ta baƙi flat ta ƙarasa sanyawa ta kalle shi tace,
"Dan Allah ka kaini gidan Ummi na yi kewar su,"
Cikin wani irin yanayin da ta kasa fassarawa ya kalle ta yayi gaba, shiru tayi riƙe da jakarta ta turo baki gaba tace,
"In taho?"
Ɗan guntun tsaki ya ja kafin yace,
"Kiyi sauri kar ki ɓata min lokaci."
Da gudu tabi bayan shi tana murna, a zafafe ya kalle ta yace,
"Gudun na menene? Ohhh so kike kiyi gudu wani tsautsayin ya same ki ki samu abun da kike so ko? To ki buɗe kunnen ki da kyau kiji Saddiqa, akan cikin nan sai na soke komawar ki makaranta sokewa ta har abada,ai ba jahila bace ke balle kice rashin ilimi zai zame maki tawaya, wuce muje idan zaki je."
Hawaye ta fara zubarwa masu mugun zafi, cikin kuka ta kalle shi kamar zata yi magana, sai ta fasa,gaba tayi ya bi bayan ta ya kulle gidan, a jikin motar shi ya same ta tsaye tana sharar hawaye,tsananin tausayin tane ya kama shi, amma haka ya ɗauke kan shi ya shige motar shi ya tada ta, cikin sauri itama ta buɗe ta shiga ta zauna tana ci gaba da share hawaye,kallon ta yayi cikin sassauta murya ba dan ya dena fushin da yake yi ba yace,
"Ki dena yi min kuka tinda ba dukan ki nayi ba ko zagin ki,idan kuma kuka zaki yi na ajiye ki anjima na aiko a kai ki wajen su Anisan."
Da sauri ta hau goge hawayen ta tana bin shi da kallon mamaki,dama wai Munir ya iya fushi haka? Idan wani yace mata Munir ɗin ta zai yi fushi da ita har na tsawon kwana ɗaya ba zata yarda ba, wai sai gashi yau Munir ke fushi da ita har na tsawon sati guda currr babu ɗaga ƙafa,lallai dik wanda ya ɗauka a gidan aure soyayya kawai za a yi ta ci babu irin wannan tsarabe-tsaraben na rashin jituwa tsakanin ma'aurata to fa tabbas ya d'akkowa kan shi dala babu gammo.
Har suka isa gidan Ummi tana tunani bata san sun isa ba,mai gadi ne ya gaishe ta sannan ta yi saurin fitowa daga duniyar da ta lula ta kalle shi tana sake gaida shi cikin girmamawa, a parking space ya ajiye motar tashi ya kashe yayi ficewar shi ba tare da ya jira ta fito ba,jiki babu ƙwari ta buɗe ɓangaren da take ciki ta fita tabi bayan shi.
Zaune ta ganshi yana gaishe da Ummi su Anisa na gaida shi, kallon Saddiqa Ummi tayi tana murmushi tace,
"Oyoyo oyoyo mu daughter,wa ya taɓa min ke ne na gan ki haka kamar kin yi kuka?"
Saddiqa na jin haka ta ɓare baki tin ƙarfin ta tana kuka irin na shagwab'ar nan da bata san ta iya shi bama ta tafi da sauri ta faɗa jikin Ummi,baki Munir ya sake yana binta da kallo dan ya kula so take ta ƙulla masa wata ƙullakiyar, cikin sauri Ummi da su Anisah suka tare ta suka kama ta suka zaunar da ita a kujerar da Ummi ta tashi akai suna tambayar ta lafiya take kuka?
Ummi ce ta ga Munir na sanɗa zai bar parlourn cikin haɗe fuska tace,
"Zo nan Munir ! Ina zaka je? Me kayi mata take cikin damuwa bayan kasan condition ɗin da take ciki bata buƙatar damuwa?"
Sosa kai yayi ya koma da baya ya coge a jikin kujera bai ce komai ba, shi fa bai so abun ya kai haka ba, so yayi ya ɗan hora ta ta yanda gobe baza ta sake nuna tafi son karatun boko sama da haihuwa dashi ba,sai gashi yarinyar ta kasa jure ɗan fushin da yake yi tana neman ja masa faɗa wajen Ummi dake da mita.
Cikin kuka suka ji Saddiqa na faɗin,
"Ummi ki bashi haƙuri yayi fushi dani sosai,ya dena yin hira dani komai nayi faɗa yake yi min,ko nayi dai-dai ko banyi dai-dai ba faɗa yake yi min."
Kama ƙugu Ummi tayi tana binshi da kallo, Anisah ma kallon shi take tana tura baki tare da lallashin Saddiqa,zama yayi yana hararar Saddiqa yace,
"Ai sai ki sanar da ita me kika yi last week ko?"
Sunne kai tayi ƙasa tana marairacewa,yana ganin haka ya saki murmushi sannan yace,
"Ummi gata nan ta faɗa maki me tayi da kanta, idan kuma baza ki iya ba bari ni na sawwaƙe maki jin kunya,cewa tayi bata son haɗa zuri'a dani."
Cikin sauri Saddiqa ta kyab'e baki tana kuka tana shura ƙafa dan kuwa yayi mata ƙarya ita ba haka suka yi ba, mamaki ne ya kama Ummi ta maida kallon ta kan Saddiqa da alamar tambaya a kan fuskar ta,da sauri Saddiqa tace
"Ummi ba fa haka muka yi dashi ba,shine fa yayi min alƙawarin zan ci gaba da karatu Ummi, kawai wai daga kaini asibiti last week suka ce wai ina da...uhummm..inaa da....uhummm wai ciki gare ni...kuma Ummi shi yace zai kaini makaranta, shikenan wai dan nayi kuka nace ina alƙawarin da yayi min to shine yake ta min faɗa har da ture ni ƙasa na faɗiiiiii."
Ta ƙarasa maganar ta tana rushewa da kuka, murmushi Ummi tayi sannan tace,
"To ai Saddiqa tin wata biyu da suka gabata na san kina ɗauke da juna biyu, shi yasa kika ga na ninka kulawar da nake baki, kune dai baku gane hakan ba kasancewar dikan ku baku da experience akai,kai kuma menene abun yin fushi har haka? Ai is normal ta nuna ɓacin ran ta kai kuma sai ka lallashe ta ka bata baki, tinda koni dama ba zan so ta fara zuwa makaranta ba tare da ta yi haihuwa ko guda ɗaya bace duba da irin karatun da take so tayi,idan kika yi haihuwa ɗaya sai kuje asibiti a duba tsarin iyali mara cutarwa sai ku fara yin shi,ni a gani na hakan shine zai fi muku, kai koda amfani da condom ne ya kama kuyi sai kuyi,saboda dai ku samu maslaha,yaro ko yarinya ko yara idan an haife su ana iya kawo min su nan raino i will be more than happy to help,me nake yi?"
Kunya ce ta kama Saddiqa sosai kanta manne da ƙirjin Anisah take sauraron Ummi, shi kuwa Munir sai yanzu ya fuskanci kuskuren shi, cikin sanyin jiki ya kalli Saddiqa wadda taƙi ɗago kanta,shima maida kanshi yayi ƙasa yana kallon wayar shi,Ummi ce tace,
"Dan haka daga yau bana son na sake jin wai ana fushi har na kwana ɗaya ma ba a daidaita ba balle na sati, ita mace ƴar lallashi ce, wadda ma ba ayi mata alƙawarin karatu ba aka ce tana da ciki reaction ɗin farko sai ya baka takaici kafin ta dawo tana ririta cikin kamar ƙwai, dan haka kar ka takura mata, ba kowanne ciki bane da an ce an same shi ake farin ciki da farko, wani sai daga baya ake nuna masa tsantsar soyayya da kulawa, ka lallashe ta ka bata hakuri yanzun nan,Anisah ku muje ciki."
Waje suka basu, Saddiqa sai shan majina take tana wani tura baki,Munir na ganin kowa ya tafi sai ya tashi ya shammace ta ya sumbace ta har sai da taji iska na neman yi mata kaɗan,tin tana ture shi har sai da ta kasa ture shi ta miƙa kai, a hankali ya janye ya kalle ta ya raɗa mata wata magana, cikin sauri ta kalli hanyar da su Ummi suka bi tana dariya ƙasa-ƙasa tare da kulle fuskar ta da tafukan hannayen ta,hannun ta ya kama suka bar gidan suna dariya, aikin da Munir bai je ba kenan a wannan ranar saboda da gaske yake son wanke laifin shi a wajen Saddiqan shi.
Washegari da safe haka suka tashi cikin farin ciki, dika aikin gidan shi yayi, hatta da girkin safe shi ya dafa musu indomie da k'wai ya haɗa musu shayin da yaji kayan ƙamshi irin wanda Ummi ta haɗa wa Saddiqa.
A baki ya dinga bata bayan tayi wanka ta sanya wata rigar sanyi mai dogon hannu da dogon wando siriri da ya kama ta a kowacce kwana ta jikin ta da ta dace,kanta Munir ya kalla yace,
"Baby ya kamata Anisah ta kai ki inda ake yi musu kitso a taimaka wa kan nan,masha Allah gashin ki na da kyau na tabbata idan aka zana masa kitso ba ƙaramin kyau zai ƙara ba."
"Dik yanda kace haka za a yi Rouh."
Wayar shi ce ta fara ringing a saman kujerar dake parlour,da sauri ya bar dinning area ya d'akko ya amsa,gaishe da Ummi yayi cike da jin nauyin ta, bayan ta amsa tace,
"Idan ka gama lallashin kazo ka karb'ar mata jakar ta da wayar ta tin jiya Baabaa ke kiran ta."
A hankali ya furta,
"Ummi dan Allah kiyi haƙu...."
Kashe wayar Ummi tayi tana murmushi ta bar shi da jin nauyin ta, wajen Saddiqa ya koma ya kama ƙugu yana kallon ta yana gimtse dariya yace,
"To kin ji saƙon Ummi dai, tace ki je ki ɗauki wayar ki da kika bar mata a gidan ta kika bi miji,ni dai babu ruwa na dan ba zan iya komawa gidan nan ba nan kusa saboda kunya nake ji."
Wata iriyar kunya da nauyin Ummi ne suka mamaye Saddiqa tana jin ta kamar tana gaban Ummi,cikin yin ƙwalƙwal da idanu kamar na mai shirin tsaga kuka tace,
"Masoyi dan Allah ka taimake ni idan ka fita office ka ɗakko min kaji tinda hanyar kace? Kaga bani da cikakkiyar lafiya a jiki na jiri ma nake ji."
"Ai kuwa zaki warware ko wayar ki ta tabbata a can ni babu ruwa na ke da Ummi."
Dariya ya dinga yi mata har sai da yaga tana shirin yin kuka sannan ya ƙyale ta ya kirawo mata Baabaa dan su gaisa, tinda ance tana ta kiran wayar ta,bata wani jima tana ringing ba aka amsa,muryar Sadeeq Munir yaji, cikin fara'a yace,
"Aboki na yane? Ashe kai ne kake kiran matata da sassafe haka?"
Murmushi Sadeeq yayi yace,
'Lafiya ƙalou alhamdulillahi,na kira ne dama mu gaisa kuma naji bata ɗauka ba, kwana biyu Baabaa na yawan zancen ta,shine nace bari na kira dik sai mu gaisa.'
"Allah sarki gata