Showing 18001 words to 21000 words out of 276165 words

Chapter 7 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

cikin gaggawa,tana idarwa ta kalli Saddiqa ta ce,

"To qanwa ta a yafi juna ni fa yau zan tafi kano,zani neman kuɗi a sanya ni a addu'a Allah ya bani su masu yawa Allah ya sa daga can na samo mijin nuna wa sa'a na kece raini,ga d'akin nan a yi ta ibada Allah ya sada mu da alheri"

Cike da mamaki Saddiqa ta miqe tsaye, kawai sai ta ji idanun ta sun ciko da k'walla, ko da dai ba wani shiri suke yi ba sosai da yayarta ta amma ta na son ta sosai, ta na son 'yan uwan nata matuqa gaya sune kawai suke kyarar ta da gudun ta,cikin murya mai rawa Saddiqa ta ce,

"Yanzu idan kin tafi sai yaushe kuma? Dan Allah Yah Mommy kar ki dinga dad'ewa baki dawo ba kamar yanda Yah Balki ta gidan me dusa take yi,Yah Mommy zan yi kewar ki da yawa"

Wani irin abu Mommy ta ji ya narkar da zuciyarta game da saddiqa a yau kaɗai a rayuwar ta tun bayan da aka haifi Saddiqar, tun saddiqa na yarinya Mommy ta yi son ta sosai domin kuwa ta girme ta sosai, tashin su da fara zama 'yammata ne ta fara kyarar yarinyar saboda ta kula da yanda take da iyayin son yi mata nasiha akan duk abinda taga ta na aikatawa mara kyau (girman kai kenan, ba wai mutum ya dinga ganin yafi kowa ba shine girman kai, ah ah mutum ya qi karb'ar gyara daga wanda yake ganin be kai ya yi masa gyaran ba shi ake kira da girman kai a musulunci). Da sauri mommy ta ɗauke kan ta daga barin kallon Saddiqa da ke matsar k'walla ta na ta yi mata addu'a da fatan alkhairi tare da roqon ta kar ta dinga jimawa bata dawo sun ganta ba.

Wajen da Ameerah ke kwance kamar gawa Mommyn ta nufa ta sami qafarta ta shalla mata wani mugun duka dan ta san idan zata shekara kiran sunan ta ko tashin ta a hankali ba zata tashi ba, ba ma za ta san ana yi ba, ai kuwa da alama wannan mugun dukan ya shigi Ameerah a hargitse ta farka ta na kara hannyenta gaban fuskar ta kamar wata k'aura ta na fad'in,

"Waye ya kawo min farmaki? Waye nan ke mommy d'akko adda b'arayi sun shigo"

Harara Mommy ta banka mata duk da cewa har wannan lokacin idanun Ameerah a rufe suke ba gani za ta yi ba, cikin hargowa ta sake shurin ta da qafa ta ce,

"Ke banza ni ce nan ba b'arayi ba,ki tashi mu yi sallama lokaci na tafiya zan wuce a yafi juna"

Nan take Ameerah ta wartsake dan kuwa ta san da zancen tafiyar, cikin goge wani shafcecen yawun bacci da ya yanko a gefen bakin ta ta ce wa Mommy,

"Kai haba da asubar nan zaku tafi kamar wanda ake korar ku? Ina laifi ku bari azahar ta yi? To Allah ya kiyaye kin barmin jakar can taki na dinga amfani da ita?"

"Eh na bar maku komai ke da Saddiqa ku raba duk abinda ban ɗauka ba,se watarana"

Fita ta tashi yi Saddiqa ta tafi da gudu ta rungume ta ta fashe da kuka, bata janye ta ba a jikin ta sai da ta ɗan jima ta na kuka sannan ta janye ta ta ce,

"Meye haka kamar wadda in na tafi na tafi kenan? Ku kula da kan ku sai na dawo,"

Ganin yanda su Mommy da Saddiqa suka rungumi juna abun sai ya burge Ameerah dan su a garin nan ba su wani saba haka ba, sabon abu ne ma a wajen su wannan rungume-rungumen,tafiya ta yi da azamar ta zata rungumi Mommy, Mommy ta ji wani mugun warin yawun bacci ya dake ta, da gudu ta yi waje ta na dakatar da Ameerah,

"K'wal uba ! Ameerah kin ji bakin ki kuwa? Waiii hyadda kenan,ki wa Allah kar ki goga min wannan buhun warin na shiga kano a kasa shaqa ta"

Wani takaici ne ya kama Ameerah ta hau masifa da rashin kunya kala-kala, dan ita bakin ta baya shiru sam, suna nan tsaye Billy ta shigo sanye da wani riga da wando masu mugun kyau da matse jiki, sai wani siririn mayafi da ta yafa ta ɗauki irin pillown nan da ake sawa a wuya idan an shiga jirgi ko mota, kan ta ɗauke da gingimemen headphone kalar kayan ta wato dark pink and light pink, takalman qafarta kuwa farare ne fatt sau ciki sai zabga qamshi take yi, cikin yanga da sauya maganar da basu taɓa ji ta yi irin ta ba suka ji ta ce,

"Mommy please ki yi sauri mana mu wuce driver guda Hajiya ta aiko mana daga kano dan ya maida mu, kuma ta yi haka ne kawai saboda ke kin ga be kamata mu barshi ya yi ta jira ba ko?"

Da sauri Mommy ta nufi d'akin Yadiko dan ta taso Ɗan liti su yi sallama, ta na isa kuwa ta k'wank'wasa qauren d'akin Yadiko ta yi mata gyaran murya alamar sallah take yi, qara k'wank'wasawa ta yi ba jimawa Ɗan litin ya amsa tare da yunk'urawa ya tashi ya sanya kaya a jikin shi da kyau ya fita, a bakin qofa ya coge ya na kallon Billy da ta ci uban wando a matse kamar su ce wayyoo Allah a cire mu mun takura,maida kallon shi ya yi wajen Mommy ya ganta sanye da kayan mutunci sai ya ce,

"To kuje lafiya ku dawo lafiya da arziki mai yawa, amma ban yarda ki dawo min da irin waccan shigar karuwan ba"

A hankali yake magana yanda daga shi sai Mommyn ne za su ji, d'aga kai ta yi ta juya zata fita Yadiko ta fito ta miqa mata leda mai cike da quli-quli mai sugar da kayan qamshi da take siyarwa ta ce,

"Allah ya kiyaye ya sa ki je a sa'a Allah ya yi maki tsari da haram komai yawan ta ya haɗa ki da halal komai qanqantar ta, Allah ya kare ki daga sharrin dake cikin zamanin nan ya fito maki da miji na gari mai albarka"

Innoh ce ta iso sajen ta na hamma ta na gyara d'aurin qirjin ta tare da tsirtar da yawu sannan ta ce,

"Ba amin ba, ji min wata iriyar addu'a dan Allah malam,wannan ai mugunta ce, idan zaki yi mata addu'a Allah ya bata miji na gari da dukiya me yawa ki yi mata idan ba za ki yi ba ki ja bakin ki ki yi shiru dan Allah"

Baki Yadiko ta sake dan bata ga laifin da ta aikata ba a addu'ar ta,cikin d'akin ta ta koma ta hau azkar ɗin ta na bayan sallar farilla da bata yi ba ta na yi ta na tuna yanda ta ga idanun Saddiqanta alamar ta sha kuka wanda ta tabbata na rabuwa da Mommy ne, murmushi kawai ta yi da ta tuna yanda Mommyn ta kula da Saddiqa lokacin ta na qarama kafin su girma amma daga baya komai ya sauya, addu'ar alkhairi ta yi musu ta rufe shafin tunanin su gaba ɗaya.

Mota ce mai kyau ta zo ɗaukan su gaba ɗayan ta baqin gilasai gare ta kamar ta masu kidimashin, (kidnapping) haka su Mommy suka shige drivern da ke tuqa motar ya ja suka bar qofar gidan, ko da Saddiqa ta juya zata koma ciki dan yin sallar asuba dan kuwa har an riga an yi bata samu ta yi ba ita, sai ta ga bata ga Ameerah ba a masu raka Mommyn kad'a kai ta yi ta shige ciki dan kuwa a tunanin ta yau tunda dai tafiya Mommyn zata yi tafiyar da bata taɓa irin ta ba ko wani a gidan nasu ai ya kamata ta je su raka ta tunda har sule sai da ya fito.

Bayan tafiyar mommy ne da kamar awa guda Baaba ta fito suyar qosai Ameerah ta tafi taya ta ko sallah bata yi ba kamar koda yaushe, suna cikin aikin saida qosai ne Ameerah ta nisa ta ce,

"Ohhh ko su Mommy sun isa yanzu kuwa ko suna can suna tafiya a wannan luqeqiyar motar sai Allah,ai Baaba baki ga motar da Mommy da Balki suka shiga ba yanda ki ka san jirgi haka motar take"

"Keee 'yannan jirgin ki ka taɓa gani ko me? Sannan gidan uwar wa Mommyn za ta je har ta shiga mota ban sani ba ina gidan nan?"

"Ai baki sani ba dama ? Ba a faɗa maki Mommy za ta tafi kano aikatau ba? "

Wani salati Baabaa ta saki sai da ta firgita yaron da ke kusa da ita zai miqa mata kud'in k'osai kamar zai faɗa cikin mai Ameerah ta yi sauri ta tare shi, kuka Baaba ta fashe da shi har da majina ta miqe ta tafi cikin gidan ta na surutai, a tsakar gida ta tadda Ɗan liti ya na miqa wa Yadiko kuɗin cefane Innoh na qulla qullin alale ta na waqe-waqen habaici da neman fitina, ganin Baaba afujajan ta na rusa kuka ne ya sanya Ɗan liti da Yadiko yin kan ta da sauri dan su ji bahasin kukan nata,cikin tsananin kuka ta ce,

"Allah ya jiqan malam, Allah ya lullub'e shi da rahamar shi a kabarin sa, Ɗan liti ka kiyayi zubar hawaye na kar ka sa ya jiqa kabarin miji na a can barzahu yana zaman zaman sa,"

"Me ya faru kike irin waɗannan maganganun ne Baaba?"

"Yo ba dole na yi irin waɗannan maganganun ba, yarinyar nan Mommy na ga dai ba Innoh ce kaɗai uwar ta ba a gidan nan balle ace 'yar tsamar da ke tsakanina da uwar ta zata iya hanawa a sanar da ni zata bar gari ta tafi har kano aikatau ba tare da an sanar dani ba ,"

Ajiyar zuciya suka sauke gaba ɗaya Ɗan liti da Yadiko dan jin ba wani mummunan abu bane ya faru, kafin su yi magana Innoh ta fashe da dariya sannan ta ce,

"Ai baki yi kuka ba ma Yaya sai sanda ki ka ga ana hyigowa da jarakunan alheri da buhunan dukiya gidan nan,ko kuwa kina tunanin 'ya'yan ki ne kawai suke da ikon yin azziqi su dinga sammana ana yi mana wulakanci da gori?"

Cikin ɓacin rai Baaba ta kalli Innoh ta kanne Idon ta ɗaya me ciwo ta goge bakin ta da ya ji farin goro ya yi jawur tace,

"Ki kiyaye ni Innoh ba dake nake yi ba, da wanda na isa da shi da shi nake yi, ai na gan ki kina qullin alalar wahalar ki ban kula ki ba, dan nasan ke ba hankali ki ka cika ba kin kuma raina ni"

"Ai bansan mahaukatan sun zama biyu ba, to Allah ya bamu lafiya"

Ta na fad'ar haka ta juya ta na waqe-waqen habaici wa Baaba ta ci gaba da abinda take yi, abinda take yi ba qaramin qona zuciyar Baabaa yake yi ba, amma haka ta hakura ta shanye ta saurari ban hakurin da Ɗan liti yake yi mata ta ce,

"Babu komai, ai ni kam yanzu an nuna min iyakata a gidan nan,Allah ya kai su lafiya"

Ta na fad'ar haka ta koma kan suyar k'osan ta da ta baro, Ameerah ta saida na saidawa ta ci na ci ta bar na bari.

Tun daga ranar Baaba ta qullaci abinda Innoh ta yi mata a rai.


****************************

Su kuwa kanawan dabo suna shiga cikin motar nan bayan an rufe Billy ta d'afe bawan Allahn nan suka hau sumbatar juna kamar za su cinye junan su, da kyar Billy ta kwace kanta daga wajen shi suna maida numfashi da sauri da sauri ta ce masa,

"Baby take it easy now, baka ga ba mu kaɗai bane akwai qawata a motar?"

Juyawa ya yi ya na sosa kai ya ce wa Mommy,

"Qawar mu a yi hakuri da mu please na kasa daurewa ne, na yi kewar babyn tawa ne da yawa shi yasa"

Yaqe Mommy ta yi a cikin facemask ɗin ta wanda da ace babu shi yaga wannan gayaunar haqoran nata tabbas da sai ya jinjina wa halittar da Allah ya yi mata, ta saman fuskarta kuwa kyakkyawar yarinya ya gani mai ɗauke da jiki irin na 'yan hutu,dan haka sai ya sake saita madubin motar tashi da kyau ya na hango ta, Billy ce ta zira hannu ta qasan shi ta gasa masa mintsini sannan ta lume a kujerar gaba ta na zabga masa harara,ganin hakan da ta yi ne ya sanya shi saurin maida madubin motar yanda yake suka kama hanya suka tafi.

Tafe suke Mommy na kallon ikon Allah dan kuwa yau ce rana ta farko da ta taɓa barin qauyen nasu bata taɓa sanin haka hanya take ba, har a wannan lokacin akwai sauran korayen ganye sharrr a hanya kasancewar damina bata wani jima da fita ba, haka ta dinga ganin suna wuce kogi manya da qanana abun na bata sha'awa ta na jin haushin rashin jimawar da ta yi bata lallab'a su Ɗan liti sun barta zuwa birni ba.

A haka sukai ta tafiya sai da suka yi awa ɗaya da rabi kafin ta fara ganin gidaje na siminti ta rabu da ganin gidajen qasa da qauyuka,cikin tafiyar da bata fi qarin minti talatin ba suka shiga garin kano.

Anan ne fa Mommy ta kusan kwaye facemask ɗin ta dan sai ta ji kamar ya rage mata ganin hanya,sai da suka shiga gari sosai Billy ta kwanta jikin saurayin ta sosai ta na shafa shi ta ce,

"Man ka kai mu wajen da na ce ka kai mu kafin mu isa gida kaaa jiii"

Ɗan haɗe gira ya yi sannan yace mata,

"Habaa babyna kin fa san yanda na yi bala'in kewar ki amma ba zaki bari mu je gida ba kai tsaye sai mun yi biye-biye? Ki bari mana anjima da dare sai na kai ku"

"Dan Allah baby ka kai mu yanzu is very important mu je yanzu dan ka san idan muka je gida Hajiya k'waisa ba barin mu fita zata yi da wuri ba"

"I will do anything for you my baby,kin san ina son ki ko?"

D'aga masa kai ta yi ta hau shafa hannun sa a haka ya sauya akalar tuqin motar shi suka sake nausawa wata duniyar da ke cikin garin na Kanon dabo..............
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: *GIDAN ƊAN LITI*










RUBUTAWA:HAMIDA SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAEH)








PAGE 8:









Tinda saurayin Billy da ta yi ƙarya tace driver ne ya sauya hanya Mommy ke sake ware idanu ta na kallon yanda cikin garin kano yake, ji take yi kan ta kamar yana juya mata saboda ganin cikowar mutane kala-kala,ta ga farare ta ga baqaqe sannan ta ga dogayen mutane da gajeru har da wadanni,wasu ma in ta kalle su sai ta ga kamar ba mutane ba tsabar yanayin halittar su ko dan tsakanin kyawun su ko kuma munin su,ga masu kuɗi nan kaca-kaca a cikin luntsuma-luntsuman motoci, sannan ga talakawa nan suna yawo da qafafun su, sai kuma jama'ar da suke a tsaka tsakiya wasu a adaidaita sahu wasu a motocin su masu sauqin kuɗi, sannan wasu kuma a babura, ta na kallon wani bawan Allah fari tass a babur ɗin shi sai mahaifin ta Ɗan liti ya faɗo mata a rai,tsaki ta ɗan ja dan tunawa da tayi bashi da waya da ta yi,yanzu da yana da waya balle ta kira ta sanar da shi ta iso lafiya, masu tura abubuwan sana'o'in su ta gani suna ta turawa hankali kwance basu ko tsoron motocin dake sharara gudu,ga almajirai nan a saman tituna suna bara jinsin maza da mata yara da manya wasu ma kamar matan aure dan kuwa ga goyon su nan a bayan su,can kuma idon ta ya hango mata masu saida pure water da chocolates da fruits sai ratsa tsakanin motoci suke yi suna talla ko a jikin su.

Ta na nan tana tunani ta ga sojoji a bakin wani gate, cikin ta ne ya bada wata iriyar qara nan take zufa ta karyo mata duk kuwa da sanyin ACn motar da ke bugawa,turanci taji saurayin Billy na yi a cikin abinda ta tsinta ta ji yana fad'in zai d'akko wani ɗan uwan sa ne a ciki,nan dai ya kammala abinda zai yi suka shige ciki, cikin rawar murya ta ce musu,

"Balki ina ne nan kuka kawo ni na ga sojoji da bindiga ni Hadiza kuma wa za ku d'akko?"

Gimtse dariyar ta Billy ta yi ta ce,

"Idan mun shiga zaki gani, ba dai ke kin ce kin ji kin gani ba sai kin zo kano aikatau? To idanun ki zasu sha kallo yau Mommy, and kar ki sake kira na da Balki ki kira ni da Billy idan baza ki iya ba ki ce Billisious"

Nan da nan Mommy ta kwaye facemask ta fara zubo da ruwan hawaye ta ce,

"Billy ki wa Allah ki faɗa min me muka zo yi anan kada wasan da ki ke yi min ya kashe ni dan kuwa ji na nake yi kamar na haɗiyi zuciya na mutu"

"Kin ga shikenan kin hutar da sojoji nuna maki kuskuren biyo ni da ki ka yi"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una na hyiga uku ni mommy na kawo kaina gidan halaka gidan bala'i da masifa,sai da Yadiko tace kar a barni na zo amma muka dage sai na zo gashi nan yanzu zan mutu a banza ban yi aure ba balle na ga k'wai na"

Saurayin Billy ne cikin dariya ya kalli Mommy ba facemask ya ce,

"Waiii gayauna sunan wani ai dole a dinga saya baki, Baby dan Allah ki bar yi mata irin wannan wasan ki duba ki ga yanda 'yar mutane ta yi jawur kamar an kara ta a rana ko an mulke ta da barkono?"

Dariya sosai Billy ta dinga yi ta juya ta daki Mommy a cinya sannan ta ce,

"Shege na qauye sai tsoron ɗan sanda,duk ina iskancin naki yake Mommy? Dalla share hawayen ki, karb'i nan ki gyara ki shafa powder wajen wata harkar arziqi na kawo mu, kuma nan ba wajen sojoji bane, tun bayan da muka wuce wadancan na gate ɗin kin sake ganin wasu ne? Nan wajen saukar jirgi da tashin shi ne wato airport ,wata yawa nake so na kare a TikTok da IG account ɗina, na ce na je kano wajen grandma d'ina ina so su ganni zan koma Abuja ne ta jirgi kin gane?"

Wata wawuyar ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan ta maida facemask ɗin ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login