Showing 198001 words to 201000 words out of 276165 words
Chapter 67 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
mutunci na ne? Da mutunci na ya zube a idon ƙungiyar mu da kamfanin mu gwanda na kashe ki kamar yanda na kashe Arica,ohhh ashe baki san nice na kashe ta ba ko? That is a story for another day baby,now stand up, tashi tsaye nace !"
Wata iriyar rawa jikin Billy yake yi,naman jikin ta babu inda baya cirawa saboda shiga tsananin tashin hankali,shin dama takardun da ta dinga rattaɓawa hannu babu karantawa ko gamsasshen bayani akai ashe saida kanta tayi da kanta bata sani ba? Dama Arica tsohuwar matar Any ita ta kashe ta ba mutuwa tayi saboda ciwon cancer ba kamar yanda ta faɗa? Cikin zuciyar ta ta hau ayyana,
'Dama abinda wannan matar ke son ta gargad'e ni akai kenan ban gane ba, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ni bilkisu yau na shiga uku, kwad'ayi da son zuciya da muguwar sha'awa sun kai ni gashi sun bar ni a tubalin dana sani.'
Cikin sauri Billy ta zube a gaban Any tana faɗin,
"Dan girman Allah kiyi hakuri Baby,na san ni mai laifi ce a wajen ki tinda na fara neman passport ɗina ba da izinin ki ba,na yi haka ne saboda labarin da kika bani ya taɓa zuciya ta,kewar iyaye na ce ta kama ni,ina so naje na gan su,ba hauka nake ba da zan ga dukiya irin wannan sannan na koma rayuwar talauci,labarin rashin da kika yi na iyayen kine ya tuna min da nawa, i just want to see them,dan Allah ki taimaka min,ko sau ɗaya ne na gan su,kuma ina son a cikin abinda zan dinga samu na dinga aika masu da wani abu,ke kin san ina son ki, ba zan bar ki ba saboda wani shirmen dalili,ba zan bar kuma wannan dukiyar da na ke ciki ba saboda wani dalili mara tushe."
Da fari Any ta ɗauki kalaman Billy a matsayin yaudara,amma daga ƙarshe Billy tayi amfani da ƙwarewar ta a harkar bariki da tantiranci ta yaudari Any ta bata tabbacin tafi son kuɗi da ita akan ta shiryu ta gudu ta bar ta, kewar iyayen ta kawai take yi,dan haka Any sai ta soke bindigar ta ta hau lallashin Billy tare da yi mata alƙawarin zata san yanda za a yi ko sau ɗaya ne su je Nigeria taga iyayen nata,da jin haka sai Billy ta rungume Any tana ci gaba da faranta mata ta hanyar dulmiyar dasu cikin kogin zunubi mai tsananin muni da mummunar makoma ga masu aikata shi.
Tin daga ranar Billy ta saki jikin ta da Any bata sake yi mata maganar zuwa gida ba, sai dai tana ta yi mata maganar yanda zata tura wa mahaifin ta kuɗi,a hankali Any ta buɗe wa Billy account ta zuba mata kud'ad'e masu tarin yawa a ciki,ita kuwa da wannan tayi amfani ta ci gaba da waya da mahaifin ta a boye tana aika masa da kuɗi,tin Ta Annabi na fushi da ita bata kula ta har tazo tana kula ta,watarana haka za su sha hirar su har tayi tayiwa Billy nasiha da wa'azi,wanda ke ƙara jefa Billy cikin kogin data sani bata jefa kanta a inda fitar ta zai zama sanadin mutuwar ta ba.
Ana haka watarana Any ta zo ta ɗauki Billy suka fita aiki a kamfanin su na fina-finan porn, (fina-finan batsa/blue films) tinda suka je Billy ke cikin tashin hankali,wanda da a baya ne taga irin waɗannan mazan da kanta zata kai kanta wajen su, amma a yanzu tsoron su take ji,bata son mu'amala da su, bata son su taɓa ta balle su yi amfani da jikin ta.
Dik wani shirye-shirye da ya kamata ayi mata kafin gabatar da wannan shiri an yi mata,magunguna da ƙwayoyin da suka saba dirka mata suka bata tasha tayi tatul,nan da nan taji babu abinda take buƙata da ya wuce ta ganta tare da waɗannan mazajen tare da matan dake nasu shirin dan gabatar da film ɗin nasu,cikin abinda bai fi minti biyar ba aka fara ɗaukan film ɗin,sun jima suna yi kafin su kammala su sallami mutanen wajen su wuce gida.
Tinda suka koma gida take fama da ciwon jiki,dik jikin ta ciwo yake yi mata saboda aikatuwar da tayi,Any ce ta zage ta taimaka mata wajen yi mata wanka da ruwa mai zafi,sannan ta yi mata tausa da mayukan dake cire gajiya,bayan ta gama mata ne ta ci abinci tabi lafiyar gado,tinda ta kwanta take fatan bacci ya ɗauke ta,amma ta kasa,idanun ta sun bushe sun ƙeƙashe,banda tinanin mafita babu abinda take yi,shin me zata yi ne Allah ya dube ta da idanun rahama ya kub'utar da ita daga hannun waɗannan mutanen? Kamar wadda tayi tambaya aka bata amsa sai taji zuciyar ta ta raya mata,
'Sallah ! Yaushe rabon ki da ki ɗora goshin ki a ƙasa? Yaushe rabon ki da ki amsa sunan ke musulma ce ta ayyukan ki? Ki koma ga Allah ki nemi gafarar shi,tabbas shi mai yawan gafara ne, kuma mai karb'ar tuban bayin shi ne,zai yafe maki kuma zai kuɓutar dake daga hannun waɗannan mutanen komai daren daɗewa.'
Hawaye ne ya zubo mata mai masifar zafi,cikin sauri ta sanya hannun ta ta share shi,tashi tayi ta shiga banɗaki ta yi wankan tsarki sannan ta d'aura towel ta fito,kayan ta ta hau bincikawa anan ta shiga tashin hankali,gaba ɗaya babu hijabi ko mayafi,babu doguwar riga irin tamu ta musulmai ko ɗaya,kuka ta fashe dashi sannan ta hau faɗin,
"Allah na tuba, Allah ka gafarta min ba dan hali na ba Allah, Allah kai ne al-wadud kuma al'afuwwu,Allah ka so ni ka yi min afuwar laifuka na."
Tana gama addu'ar nan ta samu wata riga da wando da suke rufe ko ina na jikin ta ta sanya,hula ta nema ta saka ta samu waje a ɗakin ta hau yin sallolin da ita kanta bata san adadin su ba.
Any ce ta farka ta ganta a wannan yanayin sai ta murza ido, ta sake murzawa, wayar ta ta jawo ta duba time,gani tayi asuba ta kusa, sai kawai ta koma ta kwanta ta ci gaba da baccin ta,ita kanta ta san bata kyautawa da rashin sallar da take yi,a cikin zuciyar ta ta ƙudirta zata gyara ko ba yau ba.
Billy kuwa bata tashi daga wajen ba sai da ta duba lokaci taga lokacin sallah yayi, sannan ta yi sallar asuba ta tashi ta kwanta,ba jimawa kuwa bacci mai cike da ni'ima da mafarkai barkatai da ta kasa tantance su ya ɗauke ta.
**********************
Yau sati ɗaya kenan ake neman inda Sule ya shiga ba a samu ba,magana har ta fara baza gari Sulen gidan Ɗan liti ya ɓace,Ɗan liti tin da ya dawo aka gama sunan yaron Ameerah ya ji labarin ɓatan Sule sai bai baiwa abun mahimmanci ba,ranar da ya cika sati ɗaya cif bai dawo bane ya tafi tasha wajen abokan kasuwancin shi ya labarta musu abinda ke faruwa,nan fa aka hau bashi shawarwari, ciki har da masu cewa ya kai maganar wajen malamai a yi masa duba,ita ce hanya mafi sauki da zai gano inda Sule yake.
Ɗan liti tin yana ɗaukan maganar ɓatan sule abun wasa har abu ya kai shi ga kwantawa jinyar kwana biyu,likita Mommy ta ɗauka tin daga kano tayi masa kud'in mota aka bashi masauki a gidan sarki yaje ya duba Ɗan liti,Saddiqa dake can Abuja ma hankalin ta ya tashi saboda ɓatan Yah Sule.
Ƙarshe dai Abdul ne ya kai magana gidan redio da talabijin aka bada cigiyar Sule,Mommy kullum kukan ta da damuwar ta bai wuce sai da Sule yaje suna wajen ta sannan ya ɓace ba, ai da can yana shiga kano lafiya ya koma lafiya,me ya faru wannan karon aka rasa shi?
*********************
Hajiya K'waisa na zaune a parlour abun duniya ya bi ya ishe ta saboda barazanar da take samu ta wajen Alhaji akan ya nemo masa Mommy,gefe ɗaya kuma ga Sam da ya juya masa baya,hawaye ne suka zubo masa yasa hannu ya share su,Sallau ne ya shiga ya kai masa smoothy dan kuwa yanzu ya dena cin kowanne irin abinci sai wannan,saboda samun sauƙin wahalar da yake sha idan yaje zagawa.
Tausayin K'waisa ne ya sanya Sallau zama a ƙasa yace,
"Hajiya dan Allah ki dena kukan nan,idan ina ganin hawayen ki zuciya ta na karye wa,"
Ajiyar zuciya K'waisa ya sauke kafin ya sauke tagumin da ya zabga ya ce,
"Humm Sallau ai dole na zabga tagumi tinda ni na gayyato shi da kai na,kana ji kana gani wancan ɗan tijaran tsohon shegen da yazo shekaran jiya ya ƙare min tanadi,yace dole na fito masa da Sweet H,ni yanzu ina zan ganta? Me kama da ita ma ban gani ba balle ita, ya yake so nayi da rai na? Ga matsalar Samuel da ta sako ni a gaba,ya manta halacci da soyayyar da na yi masa a rayuwa,saboda shi bana bin kowa,na kame kai na na ce shi kaɗai nake so,sai yanzu na gane wautar da na tafka,tin ciwon nan yana kaɗan idan zan je asibiti baya raka ni,sai dai ma ya bar ƙasar ko yace naje zai biyo baya na, da na ji sauƙi zai dawo ya sake rarake min baya ya gudu ya bar ni da jinya,yanzu gashi ya yi min muguwar illa ya dena zuwa, ko kasan wai yau ni K'waisan alheri ne zai kira baby baby ya ƙi ɗaukan waya ta? Ko kasan jiya da na kirawo shi wani ne ya amsa wayar yake faɗan wai babyn shi na bacci a dena kira sai ya farka?"
Kuka sosai K'waisa yake yi,damuwa da tashin hankali sun haɗu sun yi masa yawa,Sallau zama ya yi yana lallashin K'waisa tare da ɗaukar masa alƙawarin dik inda Mommy take sai ya taimaka masa ya samo masa ita...........o......"[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 81:
Tin daren ranar asabar ɗin da Ummi tayo waya daga Abuja ta sanar da haiwar Saddiqa ake fama da Baaba akan ta yarda ta je suna ta ƙi sam,an kaɗa ta dambu taliya taƙi yarda tace Allah ya raya abinda aka samu ita dai babu inda zata je ta bar ɗakin mijin ta,wannan dalilin ne ya sanya Alhaji Baban Gida ya haɗa baki da Ɗan liti akan su ce mata shi zai kai ta Abujar a motar shi, sannan ana gama suna a ranar za su dawo tare,dan haka tana iya tattaro dik wanda take so taje da shi a tafi gaba ɗaya.
Baaba na jin haka sai hankalin ta ya kwanta,tinda a ranar za a je a ranar kuma za a dawo babu matsala,shiri ta fara yi sosai cike da farin ciki,da daddare tana zaune ita da Sadeeq dake murna zai je yaga Yah Saddiqan shi da babyn da ta haifa musu ta kalli Sadeeq ɗin ta ce,
"Ka ga abun Allah ko? Na gama haɗa mata kafff kayan gara na uwa da ake yi da niyyar Abbee da Shalele su kai se gashi ashe ma ni zan kai da hannu na."
"Da alama kina yin auren ne da wannan mai gidan naki shi yasa,to ke yanzu Baaba da kika dage sai an tafi da Aunty Shalele ba tace mijin ta ba zai bari ba? Shi fa yace ya gaji da yawon suna da bikin nan da take yawan zuwa,ki ɗauki Aunty Abbe ku tafi kawai abun ku."
"Yo ai magana ta ƙare tinda na masa waya da magariba nace tayi zaman ta Ɗanli zai kai ni har Habujar,ba se ya kwaɗa ta ya cinye ba,masifaffen banza kawai."
Dariya Sadeeq ya yi sannan ya tashi ya ɗauki singiletin shi da ya gama ninkewa ya zuba su a akwatin shi ya zuge,Baaba ma ƙarasa haɗe babban buhun da ta cika da kayan garar da za ta kai wa Saddiqa tayi,suka yi wa juna sai da safe ta shige ɗaki ta kwanta.
A dai-dai wannan lokacin da Baaba da Sadeeq ke shirin zuwa Abuja uwar gayya Innoh na can na masifar babu inda Ɗan Liti zai kai su Baaba a mota,idan suna son zuwa Abujar su hau ta haka su tafi,dik yanda Ɗan Liti yake ta ƙoƙarin yi mata bayani ta ƙi fahimtar shi,wani irin kishi da baƙin ciki ne yake nuƙurƙusar zuciyar ta,jin kunnen ta taji irin maƙudan kuɗin da Alhajin ya aiko wa Ɗan liti wai a sha mai dasu a hanya,dan haka ta ci alwashin babu inda zai je sai dai ya zauna su cinye kud'in,ko da Ɗan liti ya gaji da yi wa Innoh bayani sai kawai ya ƙyale ta ya juya mata baya ya kulle yana jiran bacci ya ɗauke shi,tafiya dai babu fashi in dai Allah ya tashe shi da ran shi da lafiyar shi,ganin abinda Ɗan Liti ya yi ne ya baiwa Innoh tabbacin sai fa yaje kenan,kuka ta fashe dashi tana faɗin,
"Da yake su masu kuɗi ne ai gashi zaka je Abujar wajen sunan ƴar ka,amma nan nan Mommy ta haihu kaje ne? Kuma kana cikin garin kanon baka nemi gidan ta kaje ba,ga Sulena ya ɓata yau sati uku kenan babu amon shi balle bayanin inda yake,amma dake abun bai dame ka ba shine za ka tafi Abuja, to Allah ya bada sa'a."
Banza ya yi mata ya hau munsharin ƙarya dan kawai ta zaci ya yi bacci ta dena mitar da take yi masa akai,da ƙyar ya samu ta hakura ta muskuta mazaunan ta ta kwanta tana jan majina kamar wata yarinyar goye har bacci ya ɗauke ta.
Ameerah kuwa tinda taji za a je sunan taji kwad'ayin zuwa,sai dai ta san babu yanda za a yi taje tinda itama jegon take yi,ita gaba ɗaya zaman gidan ma ya ishe ta,dik abinda shamsu ya kawo mata na ƙwalama akan idon Innoh,bata jin nauyi ko kunya sai an raba da ita ko an ɗebar mata ta lasa ko babu yawa,yaron ta da yaci sunan Mai Dusa wato Abubakar ta ja gaban ta,kallon shi tayi taga yanda yake kama da su ita da shamsu sai dai ya ɗakko farar fatar ta sak,murmushi tayi sannan ta sake rungume jinjirin a ƙirjin ta,a hankali ta furta,
"Ohhh rayuwa kenan,wani baya haihuwar ɗan wani, sai yanzu na gane tin asali ba son Yah Munir nake yi ba,haushin yanda yake baiwa Saddiqa mahimmanci ne ya sa na kafe nake ganin kamar ina son shi,dik da dai na san ƙamshin shi da gashin kan shi sun ja ra'ayi na a wancan lokacin,amma a yanzu ne na san menene so,ina son ka Shamsu na Allah ya barmu tare har a aljannah."
Murmushi ta sake yi ta rungume jinjirin ta dake bacci sannan ta sumbace shi,wayar ta ta lalubo ta kunna ta danna wa shamsu kira dan taji muryar shi ta rage kewa,cikin rashin sa'a kuwa da ta kira taji alamun waya yake yi,cikin sauri ta cire wayar a kunnen ta tare da dire jinjirin ta a gefen ta ta miƙe tsaye,sake kiran shi tayi aka tabbatar mata da cewa mamallakin wayar yana amfani da abar shi a dai-dai wannan lokacin,wani ashar Ameerah ta lailaya ta saki.
"Da uwar wa shamsi ke waya a daren nan? Ƙarfe sha biyu na dare saura minti takwas fa, tabdijam lallai za a yi ruwan masifa da bala'i a garin Ba Mugu."
Tini bacci ya ƙaurcewa idanun Ameerah da kishi ke narkar da zuciyar ta, zama tayi a katifa tana hawaye,cikin kuka tace,
"Sai da zuciya ta ta kamu da son ka zaka fara tsalle-tsalle shamsu? Ni dai a gaskiya gobe zan koma ɗaki na,dan banga amfanin da zaman nan yake yi min ba a gidan nan,tinda har yanzu ni ke yi wa yaro wanka idan Baaba bata yi masa ba,ɗaki sai na share watarana ma Innoh tace na haɗa da tsakar gida, haka ake jegon? Masu jego ba lallaɓa su ake yi ba a basu cima mai kyau dan su maida abinda suka rasa a jikin su wajen haihuwa? To a gaskiya ni dai gobe zan koma d'aki na."
Zama tayi ta rubuta wa Shamsu message ta tura masa, Shamsu na can na waya da budurwar shi da yayi a shagon shi na turi,ƙarar shigar message ɗin ya tsaida shi daga abubuwan da yake yi dan biyawa kan shi buƙata, a hankali ya zare wayar ya sanya ta a handsfree saboda ya dinga jin me budurwar tashi take faɗa,karanta message ɗin ya yi a cikin zuciyar shi kamar haka,
'Idan baka zo da adaidaita sahu ba gobe da safe ka ɗauke ni ka maida ni ɗaki na ba zan je gidan Goggon ka na sanar musu abinda ya faru a daren mu na farko,kuma ko da wacce shegiya kake waya ka yi mata albishir da ajalin ta ya gabato ta zaɓi maƙabartar da za a binne ta'
Cikin sauri Shamsu ya daƙile wayar da suke ya hau waige-waige,nan take ya nemi wutar sha'awar da ta kunno masa kai ya rasa ta,sai da ya tabbatar da Ameerah fa bata ganin shi da dikkan alamu kira tayi taji busy shi yasa ta faɗi haka,zama yayi a bakin gado yana maida kayan shi a jikin shi,wayar ta ya kira ya ji ta a kashe, cike da damuwa ya ja tsaki ya ce,
"Kaiiii amma yarinyar nan Ameerah bata yi ba,sai da na d'akko hanya ana zuba min kalamai masu rikita kwanya ta rusa komai,ita bata iya yanda zata sama wa mutum natsuwa ba,ta kuma hana wasu su jiyar da ni daɗi,yanzu dole goben na je na d'akko ta kafin tayi min bankaɗa."
Tsaki ya ja ya ƙarasa gyara zariyar wandonsa sannan ya haye gado ya kwanta,ya jima sosai kafin bacci ya ɗauke shi. Be jima da fara baccin ba wayar shi ta hau ruri,cikin magagin bacci ya amsa tare da faɗin,
"Ameerah goben fa zan zo na ɗauko ki,ni bana son fitina dan Allah,kuma da kike cewa zaki je ki tona abinda ya faru a daren mu na farko,ai idan asiri na ya buɗe kema naki ba rufuwa zai yi ba,dan haka ki dena yi min barazanar banza."
'Yah Shamsu Bilkisu ce fa,ya mai jegon da Babana?'
Da sauri Shamsu ya buɗe ido ya na kallon wayar,lambobin da bai saba gani ba ya gani a jiki,cikin rawar murya yace
"Baiwar Allah ke wacece? Kuma wannan wacce iriyar lambar waya ce? Me ya sami Bilkin"
'Yah Shamsu nice Bilkisu, wannan No ƙasar waje ce shi yasa ka ganta a haka, na kira ne nayi maka barka akan haihuwar da aka yi mana, ina yawan ganin posting ɗin ka a Facebook ai,na jima ina so na kira ka