Showing 51001 words to 54000 words out of 276165 words
Chapter 18 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
miqe ko azkar bata yi ba ta hau neman uniform ɗin ta a bakin rijiya da ta ajiye jiya, ɗauka tayi ba tare da ta buɗe su ba ta danna a bokiti ta hau jan ruwa ta zuba musu ta zuba omo ta hau wankewa, tana wankin ta ga alamar yagewa sai ta basar dan a zaton ta maimaita waje ɗaya take yi inda Ameerah ta yaga mata, bata tashi sanin b'arnar da aka yi mata ba sai da ta d'aga rigar dan tabbatar da shin anya waje ɗaya take ta wankewa kuwa?
Wani salati ta rafka a lokacin da idanun ta suka sauka akan yayyagewar da kayan nata suka yi sannan ta miqe tsaye tana sake dubawa,wandon ta d'akko ta ga shima an yaga shi kaca-kaca, se ta ajiye ta sake ɗaukan hijabin ta hawaye na zuba ta nufi d'akin Yadiko dan ta nuna mata abinda aka yi mata.
Ko da ta shiga sai ta tarar da Yadikon kwance bata tashi sallar asuba ba, sai ta yi tunanin ko dai tayi sallar komawa tayi duba da cewar bata jin daɗi,ga kuma Sadeeqa baya nan da alama ne na yana masallaci.
Komawa waje ta yi ta rasa yanda zata yi, dan ta san idan ta tada Ameerah wani rikicin ne zai b'arke da asubar nan, kuma ta yi wa Yadiko alqawarin ta dena faɗa da Ameerah,zama ta yi ta dinga rera kukan baƙin ciki tare da neman mafita dan kuwa uniform ɗin ta kenan k'walli ɗaya kamar rai.
Tana nan zaune har Baabaa ta fara fitar da kayan yin qosan ta, ta hau hidimar haɗa wuta ta ɗora mai a wuta, qamshin suyar albasa ne ya tashi Ameerah kamar wata tsohuwar mayya haka ta fito ta tsartar da yawun bakin ta sannan ta yi hamma da miqa,kallon inda Saddeqa ke zaune tana kuka ta yi,nan take ta tuna da abinda ta yi mata, murmushi tayi sannan ta wuce bakin rijiya tana waqar habaici ta ja ruwa ta zuba a buta ta wanke fuska ta kurkure baki ta fesar da ruwan a kusa da Saddeqa, da kallo Saddeqa ta bi ta tana jin wani irin zogi a zuciyar ta, ji take yi kamar ta kama Ameerah da kokowa har sai ta yi mata ligis amma ba zata yi haka ba, ta riga ta yi wa Yadiko alqawarin dena faɗa kuma ba zata karya ba.
Ameerah kuwa na gamawa ta wuce wajen Baabaa zata taya ta suya kamar yanda suka saba, sai dai tana zuwa taga fuskar Baabaa kamar hadari, ta haɗe rai ta yi kicin-kicin ko amsa gaisuwar Ameerah bata yi ba sai daga baya ta daure tace,
"Lafiya qalou na tashi, ba dan gaba haramun bace ai da ni da ku har abada, ace daga zuwan jikan nawa yaron nan rabon shi da garin nan tun yana zanen goyo ya samu kuma ya kawo ziyara abi min shi da qazafin fyad'e, Ki je can yau bana son taimakon dama can ai temaka wa kan ki kike yi da uwar ki, tinda idan na fara suya se kunci na sama da ɗari biyar kafin na gama,dan haka kama gaban ki bana son taimakon"
Wani irin baƙin ciki ne ya lullub'e Ameerah,tana so ta yi wa Baabaa rashin kunya ta kasa saboda gudun kar ta sake b'ata kan ta wajen tsohuwar,haka ta ja jiki ba k'wari ta koma d'akin su ta kwanta tana kama cikin ta dake kiran ciromawa.
Saddeqa kuwa ganin har wannan lokacin Yadiko bata fito bane ya sanya ta sake miqewa ta goge hawayen ta, Sallamar Sadeeq ce ta sa ta kalli inda yake, kallon uniform ɗin ta ya yi ya gan su a yayyage yace,
"Me nake gani haka Yah Saddeqa?"
Hawayen ta ne ya sake zubowa ta kalli bayan shi ta ga Munir tsaye sai ta kasa cewa komai ta ajiye kayan ta wuce d'akin su ta kwanta tana kuka, Munir ne ya ɗauki kayan ya gan su a yayyage, nan take zuciyar shi ta ayyana masa me ya faru, k'wafa ya yi yace,
"Da alama se na cire wa yarinyar nan Ameerah aljanun da ke saka ta yin iskancin da ta ga dama a gidan nan, dan kuwa na tabbata itace zata yi wannan wulaqancin"
"Ko shakka babu kuwa,dama basu son Yah Saddeqa tana zuwa makaranta"
"Ai kuwa sun yi qarya se dai su mutu da baqin cikin hakan"
Kayan ya kwashe ya yi waje ya bar gidan a motar shi,cikin gari ya shiga ko zai ga wanda zai nuna masa inda ake saida yadin uniform da kuma tela, zai kashe ko nawa ne dan ya samu su buɗe shago su sayar masa da yadin a d'inka mata uniform a yau.
Sadeeq na shiga d'aki sai ya ji gaban shi ya yi wata iriyar mummunar fad'uwa sakamakon ganin Yadiko a kwance a yanda ya barta, cikin sanyin jiki ya isa gaban ta ya taɓa ta a karo na biyu tin kafin ya tafi masallaci.
Ji ya yi tayi shiru bata amsa shi ba kuma bata juyo ba, hannun shi yaji ya fara rawa cikin sanyin jiki ya juyo da ita sai kuwa yaga ta biyo shi gaba ɗayan ta idanun ta kulle babu numfashi a jikin ta,da qarfin gaske ya furta,
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un Yadiko ! Yadiko ki tashi ki yi sallar asuba lokaci ya yi fa, Yadiko ! Yadiko ! Baabaaaa ! Yah Saddeqa Yadiko bata motsi !"
Cike da tashin hankali yaron ke kiraye-kirayen sunayen mutanen gidan, a guje Saddeqa ta shiga d'akin ta duqa saitin fuskar Yadiko sai ta ji babu numfashi sam a tattare da ita, wani irin kuka ta saki mara sauti, nan take Sadeeq ya fita da gudu ko zai ga Munir ya taimaka musu ya kai musu Yadiko asibiti, saidai yana fita ya tarar da babu Munir babu motar shi, a guje ya wuce wajen Baabaa yana kuka yace,
"Baabaa ki taimaka ki kirawo mana Yah Munir a waya yazo ya kai Yadiko asibiti bata motsi, bata numfashi"
A zabure Baabaa ta miqe ta hau lalubar lalitar ta, nan take ta zaro waya ta miqa masa tace,
"Gashi nan kira shi ya zo ni ba iyawa na yi ba, bari naje na ga Yadikon Sulen"
Baabaa na shiga d'akin ta daskare a tsaye sakamakon mugun gamon da ta yi..................
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 19:
Ganin halin da Yadiko ke ciki shi ya firgita Baabaa dan kuwa ba yau ya san mutuwa ba,a saman cinyoyin ta mijin ta ya rasu,nan take ta ji rasuwar shi ta dawo mata sabuwa,da azama ta isa gaban Saddeqa da ke ta qoqarin tashin Yadiko da ta riga mu gidan gaskiya, cikin kuka Baabaa tace,
"Allahu akbar ! Yadikon Sule Allah ya sada mu dake a darissalami, Allah ya yi miki Rahama ya sa aljannah ta zama gidan ki na karshe, yarinyar kirki mai ladabi da biyayya, Allah ya sa halayen ki na gari su zame maki abokan rakiya kabari, kaico ! Mutuwa mai raba tsakanin masoya,Allah ya haɗa ki da Annabin Rahama,"
Kallon ta kawai Saddeqa take yi hawaye na zuba a kuncin ta, ta kasa cewa komai, saboda ta kasa gasgata kunnuwan ta akan abinda take ji daga bakin Baabaa, shin da gaske ne Yadikon ta da suka gama cin tuwon dare tare jiya-jiya ta rasu? Da gaske ne Yadikon ta aminiyar ta masoyiyarta ta rasu? Shin da gaske ne ba zata sake ji ko ganin Yadikon ta ba? Me yasa Yadiko zata tafi ta bar su a lokacin da suke da tsananin buqatar ta? Cikin wani irin kuka mai tsuma zuciya Saddeqa ta kwanta a cikin Yadiko sannan tace,
"Na zata kin ji sauqi Yadiko na zaki iya kaiwa safiya mu kai ki asibiti,Baba ya yi min alqawarin da safe zai kai ki asibiti da kud'in shi, me yasa ki ka mutu Yadiko? Abinda aka faɗa akai na k'arya ne ba gaskiya bane, na ɗauka kin yarda da ni, na ɗauka kin amince ba zan aikata abinda aka yi min sharri akai ba,me yasa baƙin cikin abinda ban aikata ba zai yi sanadiyyar rayuwar ki?"
Munir da ya dawo gidan a cikin tsananin damuwa ne ya tarar da Saddeqa na irin wannan kalaman masu ratsa zuciya, sai kawai ya ji ba zai iya jurewa ba, da sauri ya fita waje yana share hawaye, Sadeeq ya gani a jikin gini ya kifa kan shi da bango yana wani irin kuka, nan take ya ji qauna da tausayin yaron sun ninku a zuciyar shi, hannu ya sa ya ja yaron jikin shi ya rungume shi,Sadeeq na kuka Munir na hawaye, Ɗan liti ne ya shigo ya na gyara rigar shi yace,
"Ke Saddeqa maza fito kije ki taimaka wa Yadikon Sule a kai ta asibi...... Ku lafiya kuke ta koke-koke kamar gidan mutuwa? Kai Manniru meye haka da girman ka yaro na kuka makon ka lallashe shi koma me akai masa sai ka qwaqume shi ku yi ta sharar hawaye tare? Me yake faruwa a gidan da safiyar nan ta ilahi?"
Baabaa ce ta fita daga d'akin tace,
"Kai Manniru jeka maza ka samo min ganyen magarya ka yanko likkafani a had'o da turaren muski a shagon nan na musuluci, ka yi sauri a wanke ta a kai ta gidan ta na gaskiya,na tabbata mala'ikun rahama ne suka ɗauki wannan ruhi na salihar baiwa mai yawan ibada,"
"Ku kar ku maida ni mahaukaci mana uwar waye ta mutu ake maganar likkafani da ganyen magarya?"
"Uwar su Saddiqu ce ta mutu gata can a d'aka, ba abinda zamu yi da ya wuce hakuri,Allah ya bamu hakurin rashin ta gaba ɗaya shiga ciki ka ganta ka yi mata addu'a,"
Wani irin jiri ne ya kwashi Ɗan liti yayi taga-taga zai faɗi Munir ya yi saurin taro shi, nan take fuskar Ɗan liti ta koma jajawur,to abinka da farin mutum ya shiga tashin hankali,salati ya dinga bugawa ya kai ya komo ya kasa shiga d'akin,sai ya d'aga labulen kamar zai shiga sai ya yi baya ya kasa shiga, yana nan tsaye Munir ya fita ya sallami mai adaidaita sahu ya bashi ɗari biyar ya tafi yana mitar an kira shi an shanya shi a banza.
Innoh ce ta rarrafo saboda jin abinda ke faruwa tana kuka shab'e-shab'e take faɗin,
"Na shiga uku na lalace ni Innoh na rasa abokiyar zama mai mutunci, na rasa abokiyar zama mai hakuri da kawaici, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, Yadikon Sule Allah ya jiqan ki ya yi miki rahama, Allah ya sa halin ki na gari ya biki,kaico mun yi rashi mun yi babban rashi,malam ka nutsu ka shiga ka yi mata addu'a,hakuri zamu yi da wannan babban rashin da ya same mu"
Cikin tsawa yace,
"Rufe min baki munafukar banza munafukar wofi ! Duk ta sanadin wa ciwon dare ɗaya ya kama ta idan ba ke ba da munafukar 'yar ki? Shikenan ta mutu hankalin ki ya kwanta ko? Gani se ki dafa yamushasshen jikin nawa ki ta ci, gani...nace gani ki dafa ki cinye !"
Tsaye Ɗan liti ya yi a gaban Innoh da ta saka hannayen ta dika biyu ta toshe bakin ta tana zubar da hawaye,a hankali Saddeqa ta fito tana bin Innoh da Ameerah dake rakub'e a jikin tagar d'akin Yadikon tana hawaye da kallo, murmushi ta yi mai ciwo sannan tace,
"Na sani kowanne mai rai yana da ranar mutuwar shi da kuma sanadin mutuwar tashi, ke Ameerah ke ce sanadin mutuwar tawa uwar ! Ke ce sanadin mutuwar uwa ta, ba zan yafe maki ba, ba zan taɓa yafe maki ba har abada,amma ba zan yi maki komai ba saboda mahaifiya ta a daren da zata mutu ta sa na yi mata alqawari ba zan sake faɗa dake da kowa ma a gidan nan ba, saboda ke ɗin jini na ce, wannan itace mahaifiya ta kuma abinda take koyar damu kenan a koda yaushe, wato mu so junan mu,dan haka na bar ku da ubangijin da ya halicce ta idan har kune sanadin rasuwar ta ya bi mata haqqin ta, sannan ya bi mana hak'k'in mu ni da ɗan uwa na na mayar da mu marayu da kuka yi,"
Tana kaiwa nan a maganarta ta wuce d'akin Baabaa ta kwanta a gadon ta na qasa dake parlour ta dinga rera kuka mai cin rai,gani tayi kukan ba zai kai ta ko ina ba, sai ta tashi ta yi alwala ta dinga sallah a kowacce sujjada tana nema wa mahaifiyar ta gafara da rahamar Allah.
Da kyar Ɗan liti ya iya shiga d'akin ya zauna a gaban gawar Yadiko,nan take ranar da ya fara ganinta tana tallan tsintsiyar laushi da man shanu ta faɗo masa a rai, har ranar da suka yi aure suka hayyafa duk sai data bijiro masa, kuka ya dinga yi yana yi mata addu'ar Allah ya yi mata rahama,bayan Munir ya dawo ne Baabaa ta kwashe ruwan da ta zuba ta maida wani, nan da nan aka gyara Yadiko Baabaa ta wanke ta tasss, Munir da Ɗan liti suka taya ta aka nad'e ta a likkafanin ta,wato kayan ta na qarshe kenan,kayan da kowa zai saka na qarshe kenan a rayuwar sa, dan haka mu dena fankama da almubazzaranci da jin kai,idan muna da shi mu taimaka wa wanda bashi da shi sai Allah ya suturta mu a lahira da suturtawar shi da babu wani wanda zai yi mana a duniya da lahira bayan shi.
Kafin qarfe tara na safiya tayi gari ya ɗauka Yadikon Sule ta rasu, gida ya cika da hayaniya,wanda dik abinnan da ake yi Sule na cikin d'akin sa yana bacci bai san ana yi ba, to ya kwana aikin da ba a saka shi ba, ya kwanta a makare dole bacci ya buge shi sosai, yana nan baki a hangame be san ana yi ba sai da qanwar Yadikon tazo daga can rugar su dake qasan garin Ba mugu sakamakon wayar da Baabaa ta sa a yi mata,haka tazo tana kuka da qarfi tana fulatanci.
Juyi ya yi ya ga yanda duk ya b'ata jikin shi, rigar shi mai datti ya ja ya goge iya abinda zai iya goguwa wanda ya bushe kuma ya zauna ya kankare yana ta haɗe gira da mamakin me ke faruwa a gidan nasu ake ta hayaniya da koke-koke?
*Sharhi*
To jama'a ga dai sule nan kun ji kuma kun ga a yanda ya farka daga bacci, ɗan uwa ka faɗa min idan kai mutuwa ta ɗauka a haka fa? Ko kuma idan ke mutuwa ta ɗauka a haka fa? Me zaki ce wa Allah? Ba zaki ji kunyar abinda zaki bari a faɗa a kan ki ba bayan babu ke? Ga dai Yadikon Sule ta rasu kowa na yabon ta, zaki so ki yi kyakkyawan qarshe ne ko mummuna? Zaɓi yana hannun ki/ka.
Wando ya sauya ya saka wata rigar sannan ya fita daga d'akin nashi dake fitar da tsami da wari,a jikin ginin d'akin shi ya tsartar da yau ya na qanqance ido, ganin Saddeqa zaune a gaban doguwar qawa nad'e ne ya sanya gaban shi muguwar fad'uwa, da sauri ya tafi gaban gawar da takalmi ɗaya a qafar shi ya durqusa,cikin tashin hankali yace,
"Waye a kwance? Waye ya mutu?"
Waige-waige ya fara yi, ya ga kowa na nan a mutanen gidan su banda Yadiko da Mommy, da sauri yace,
"Ina Yadiko na? Ina Mommy?"
Cikin fulatanci yaji qanwar Yadiko na kuka na kiran ainahin sunan ta tana yare, da sauri ya tashi ya leqa d'akin Yadikon be gan ta ba, nan take ya gane ita ce ta rasu, kuka ya sanya yana faɗin,
"Wayyoo Allah Yadikona Allah ya jiqan ki, uwa ta gari me son ci gaban mu, kullum faɗa take yi mana akan mu shiryu mu zama yaran kirki amma muna ganin laifin ta, Yadiko Allah ya gafarta miki Allah ya yi miki rahama"
Da kyar aka samu Sule ya natsu ya yi shiru, Munir ne ya kalle shi yace,
"Tashi ka je ka yi wanka ka yi sallah dan da ganin ka yanzu ma ka tashi daga bacci ko sallah baka yi ba"
Jiki ba kwari ya tashi ya wuce ya yi wankan sabulu ya burbura alwala ya koma dakin shi ya tada sallahr da be iya ba, be kuma damu da koyo ya san ya ake yin me kyau ba, yana sallah ya na kuka domin tunawa da yanda Yadiko ke yi masa faɗa idan yana alwala, takan ce,
'Anya sulemanu na, anyaaa ba zaka zauna na koya maka alwala me kyau ba, na koya maka yanda ake sallah da kyau ? Kai dai kullum a wanke kaya seti ɗaya a saka a wanke takalmi a riqe waya ana yawo a gari? Sule ka zama mutumin kirki dan Allah ko mun ji daɗi'
Matasa kun ji illar biyawa kai buqata ko? Babu wankan tsarki an ɗora da ibada, to ku faɗa min ta ina ibadar zata karb'u?
Hawayen shi ya share ya sallame sallar ya fita aka kai Yadiko gidan ta na gaskiya, kowa ya yi mamakin yanda Sadeeq ya yi hakuri yake ta yi wa mahaifiyar shi addu'a, Saddeqa ma banda addu'a babu abinda take yi wa mahaifiyar ta.
Bayan an dawo daga kaita ne kowa ya natsu ana ta karb'ar gaisuwa, qanwar mahaifiyar Yadiko mai suna Jumare ta kira Saddeqa d'akin Yadiko ta zaunar da ita ta bata kunu a kofi,da kyar Saddeqa ta samu ta sha, ta na sha tana kuka, Munir kuwa shi ya bawa Sadeeq abinci yaron be qi ci ba, sai dai duk loma ɗaya idan ya sanya ta a bakin sa sai ta jima yana juya ta, haka aka kwana ranar gaba ɗaya gidan kowa na cikin jimami da damuwar rashin da aka yi na Yadiko, hatta Innoh sai da mutuwar ta girgiza ta, Ɗan liti kuwa har nama an bashi a ranar a cikin abinci amma ya kasa ci,hatta da ruwa baya iya sha dan haka cikin dare zazzaɓi mai zafi ya rufe shi, asibiti aka kai shi aka sanya masa ruwa.
Ɗan liti be dawo dai-dai ba sai da aka kwana huɗu da rasuwar Yadiko sannan ya fara iya shan kunu.
********************
Bayan rasuwar Yadiko da kwana bakwai Innah Jumare ta dage sai ta tafi rugar su da yaran 'Yar uwar ta, aka buga aka raya ta ce ita sam ba zata bar yara a gaban kishiya ba, kishiyar da ta san ba qaunar 'yar uwar ta da yaran ta take yi ba,duk yanda Baabaa ta so ta bata hakuri qi