Showing 24001 words to 27000 words out of 276165 words

Chapter 9 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

tare da ɗaukan idanu.

Tana fita taga wata matashiya ɗauke da babban faranti abinci  da fruits da ruwa sai lemon kwali da sauri ta nufe ta zata Karb'a matashiyar ta haɗe fuska tace,

"Umarnin inda za a ajiye kawai zaki bani"

Jikin Mommy ne ya yi sanyi ganin irin kallon da matashiyar ke yi mata, kallo ne irin na kyankyami da raini ɗin nan, shanye wa ta yi ta nuna mata gefen gado inda wani ɗan qaramin table yake tace,

"Ajiye min a can"

"Ok"

Shine kawai abinda matashiyar ta ce ta wuce ta ajiye sannan ta fita tare da banko qofar d'akin saida Mommy ta kulle idanun ta.

Yarinyar na komawa kitchen ta jingina da jikin locker ɗin kitchen carbinet,abokan aikin ta dake cikin kitchen ɗin kuwa mace ɗaya namiji ɗaya suna nan tsaye suna ci gaba da aikace-aikacen su, tsayuwar ta ke da wuya gaba ɗayan su sai suka yo kan ta suna tambayarta,

"Ke bamu mu sha,ita kuma wannan wacece?"

"Hummm ni fa ina mamakin irin waɗannan mutanen, wai ace ko kunya basu ji suke baro gaban iyayen su su zo su dinga yin abin duk da wannan...."

"Keee Zubaida kama bakin ki,kar ki je ki yi shuka a idon makwarwa,mu dai ba dai ana biyan mu kud'in dake kashe mana buqatun mu ba? To mu kama kammu Allah ya shirye su, mu kuma ya kare mana imanin mu"

"Humm Ameen Sallau kai ma dai ka faɗa, Allah ya kyauta"

"Amma ai ba dai-dai bane mu dinga aiki a qarqashin waɗanda mun san daga inda kud'in su ke fitowa ko?"

"Ruby? Tsaya sauraren wa'azin muzuru ni dai kin ga na yi nan,ke in banda abinki ina ruwan ki da hanyar samun su? Ke dai ba hanyar taki samun bace damuwar ki? Kin tabbata ba wani mugun abun kike aikata wa ba ki ke samun kud'in ki to ke ina ruwan ki da inda suke samun nasu? Kin ga karb'i nan wanke min wannan na fara ɗora na dare,"

Aikace-aikacen su suka ci gaba da yi suna 'yan hirarrakin su sama-sama.

A can d'aki kuwa Zubaida na fita Mommy ta dira a saman abincin nan ta hau saɓa masa kamanni,ganin nama kaca-kaca a saman abinci ga kuma farfesun kayan ciki da juice kalar wanda bata taɓa gani ba ya gigita tunanin ta,ko ta kan shinkafar bata bi ba dan kuwa naman kaɗai ya wadatar da ita, sai da ta ci ta qoshi sannan ta kora da ruwan roba ta miqe tana sakin wata muguwar gyasa.

Billy ce ta shiga d'akin cikin wata iriyar shigar da sai a irin Nigerian films din nan na 'yan iska Mommy ke ganin mata sun yi ta, ga wani uban gashin doki da ta saka a kan ta sai mutum ya rantse da Allah a kanta ya tsiro dan ba ta inda ya nuna sanya shi aka yi.

Zara zaran faratan hannun ta irin na hannun Hajiya K'waisa ne suka fi bawa Mommy sha'awa dan kuwa an yi masu fenti me kyau an saka masu stones masu kyalli a jiki, tafe take ta na cin chewing gum ta na yatsina ta shiga d'akin riqe da wata jaka a hannun ta ta miqa wa Mommy ta ce,

"Sanya wannan mu je saloon ki na buqatar gyara kafin muzo dinner da Hajiya anjima, dan ganin kan ki kaɗai zai iya haifar mata da tashin zuciya ta qi cin abincin"

Washe baki Mommy ta yi tace,

"Laaa ai na ma wanke kan, na shiga kwamin wankan nan na haɗa ruwa kamar yanda ki ka faɗa min na yi,"

"Uhumm na gani amma ai baki fita ba dan ko brush baki yi ba, yanzu dai jeki ki saka wannan mu tafi lokaci na qure wa"

A gaban Billy Mommy ta cire towel ɗin ta ta hau sanya kayan da aka bata, hakan da ta yi kuwa ba qaramar fitina ya kunna wa Billy ba da ta jima ta na fakon ta tinda ba tun yau ba suka saba cire kaya a gaban junan su, a cewar su ai duk mata ne meye a ciki? Abinda Billy ke da shi Mommy na da shi dan haka ba wani abu bane dan sun ga junan su tsirara,danne abinda take ji game da mommyn ta yi ta ayyana a ranta,

'Idan kere na yawo zabo na yawo watarana za su haɗu ne, Allah dai ya kai damo ga harawa...'

"Ina ta magana baki jini ba, nace na gama mayafi zan saka ko hijabi?"

"Mommy wai me yasa ki ke abu ne kamar wata ba wayayyiya ba? Ke nan fa ko yawo kika so yi tsirara ba me hana ki,taho mu wuce ko baki ga meye a jiki na ba?"

(Hummm yarinya ta gwada yawo a kano tsirara ta ga ikon Allah...ba sai na yi dogon sharhi ba)

Da waɗannan kayan Billy da Mommy suka shirya suka ja qofar d'akin za su fita, takalmin da mommy ta saka mai tsini ne,saboda rashin sabo sai ya dinga gurd'e mata qafa, suna fita daga d'akin kuwa hankalin ta ya yi bala'in tashi saboda tunawa da ta yi dole ta benen nan za su sake bi su sauka qasa............

*A zo a kama mommyn gaye a saukar ta qarrr*
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI










PAGE 10:










A natse Billy ta dafa kafaɗar Mommy ta ce,

"Mommy ki natsu ki kalli dai-dai inda zaki ajiye ƙafar ki kawai kar ki kalli can ƙasa,to wai ke yanzu a haka zaki waye ki na tsoron bene fisabillahi? Meye a cikin hawa bene sai kace wata wadda zata taka girgije?"

Cikin rawar murya da jiki Mommy ta qanqame hannayen Billy gabaki d'ayan su ta ce,

"Ba zaki gane ba ne billy ji nake yi kamar ana waina ni,riqe ni kar ki sake ni, ni da za ku taimake ni ko a d'akin mai gadin gidan nan ku ajiye ni bana son wannan d'akin da sai na yi cinikin rayuwa ta sannan na hau shi"

A haka suna surutu har suka sauka Mommy bata san ma an sauka ba, ganin ta sauka lafiya ne ya sanya ta sakin wata ajiyar zuciya mai qarfin gaske sannan ta fashe da dariyar farin ciki ta ce,

"Ashe ma ba wani wahala,"

"To dama in ba dan ke ba ma meye a hawa bene dan Allah? Yanzu dole ne mu koma ki sake gwadawa,saboda bana so ki hasala Hajiya ta gaji da shirmen ki ta yi maki korar kare, gidan nan ya ajiye 'yammata iri na da irin ki sun fi goma wasu sun samu nasara a irin rayuwar da muke yi har sun jawo wasu a jiki suma sun zama wasu, wasu kuma wauta da rashin rabo da qauyanci irin naki yasa ba aje ko ina da su ba aka rabu rayuwar su ta yi munin da ta fi ta kare, dan haka ki maida hankalinki ki zama k'wararriya akan abinda ki ke yi ta haka ne zaki yi ta samun ci gaba har ki jawo wasu kema kamar yanda na jawo ki ni kuma Hajiyata ta jawo ni cikin wannan harkar"

(Ci gaban mai haqon rijiya kenan)

Duk abinda Billy ke faɗa yana shigewa cikin kan mommy kuma ta gamsu da bayanan ta dan haka cikin rawar jiki ta kama qarfen benen ta sake gwada hawa, idanun ta na zubar da hawayen tsoro bakin ta ɗauke da kiraye kirayen sunayen duk wanda take ganin zai zo ya kawo mata agaji a wannan yanayi da take ciki,dan kuwa hatta da sunan Ameerah sai da ta kirawo a wannan yanayin, takaicin ta kuwa kamar ya kashe Billy, gajiya tayi da tsayuwa ta samu kujera ta zauna ta fakaici idanun Mommy ta kunna camera ta na yi mata video,ta na gamawa kuwa ta yi posting a account ɗin ta na TikTok, dama ta rasa content ɗin da zata yi creating ta yi posting a ranar,nan da nan kuwa mutane suka hau gani ana yin comments kala-kala da likes, ta na nan zaune sai sheqa dariya take yi har Mommy ta yi sakkowa ta qarshe, a wannan lokacin kuwa ta na jin ta wasai ba wata fargaba balle tashin hankali dan kuwa ta gano hawan benen ba wani kayan gabas bane ba, tana sakkowa tace da Billy,

"Ashe ma ba wani wahala hawa da saukar,da fari na tsorata ne kawai,yanzu kuwa ina jin ko wanda yafi wannan laulayawa ma ina iya hawan shi"

"Good muje to?"

Makullin mota Billy ta zara guda ɗaya a inda suke ajiye makullayen motocin gidan suka buɗe qofa suka fita harabar gidan cike da yanga,wajen motar da za su hau suka nufa Mommy na biye tana kallon ikon Allah,bata gama tsinkewa da lamarin Billy ba sai da taga ta shiga motar ta kunna ta da kan ta sannan ta buɗe wa Mommy gefen direba ta yi mata izinin shiga, a rikice Mommy ta kalli Billy da ke toshe idanun ta da wani baqin gilashi ga kid'a na tashi cikin hauragiyar yaren mutanen kudu, da qarfi Mommy ta d'aga murya tace,

"Billy yaushe ki ka iya mota? Billy lamarin ki na nema ya fi qarfi na fa?"

Wani shu'umin murmushi Billy ta saki sannan ta ce,

"Dan Allah ki shigo kina b'ata mana lokaci, akwai abubuwan da baki sani ba da yawa game da ni,amma a hankali lokaci zai bayyana maki su,fata na ki rage wannan qauyancin da kike yi dan zai jawo maki raini a gaba a irin wannan duniyar tamu,ina fatan kin gane?"

Zama mommy tayi tana gyad'a kai zuciyar ta fal tsoro da fargabar anya ba zata juya ba daga wannan makauniyar tafiyar da ta faro a cikin rayuwar ta?

Mai gadi ne ya wangale musu gate Billy ta take mota suka bar harabar gidan,tun a hanya Mommy ta kula da yanda manyan motoci ke shawagi a cikin wannan hamshaqiyar unguwar, banda kallon su da gine-ginen dake wajen ba abinda Mommy ke yi,tafiyar da suka yi bata kai ta rabin awa ba suka isa wani makeken waje wanda Mommy ta kasa yarda wai iyakar gyaran kai ake yi a wajen saboda girman shi da tsaruwar shi, tunda suka fito ta ga manyan mata da 'yan mata kyawawa da kuma wanda kwalliya ta rufawa asiri sai nera da ta qara gyara sufar su suna shige da fice a wajen.

Suma shiga suka yi cike da jin kan su su wasu ne, Billy sai qoqarin nuna wa Mommy yanda zata yi tafiya take yi a fakaice,a haka suka shiga Billy ta gabatar da Mommy a matsayin wadda take so a yi wa gyaran ciki da waje,(gyaran kai ,waxing, gyaran qafa da hannu da kwalliya) sai tace musu zata je ta dawo kafin magariba su wuce.

Mommy na jin Billy zata tafi ta barta a wannan wajen sai ta ji wani irin tashin hankali da damuwa ya mamaye ta, da sauri ta damqi hannun Billy tana muzurai, murmushin yaqe Billy tayi ta kama Mommy suka koma gefe tace mata,

"Ki zauna anan yanzu zan je na dawo akwai abinda zan gabatar mai mahimmanci kar ki ji komai na ce su yi maki duk abinda ya dace, kin ga na bada kati na su cire kuɗin su dan haka na biya kud'in yi maki komai,zaki gode min da zarar an kammala, dan Allah ki dena abinda kike yi ki saki jikin ki nan wajen Hajiyata na da maqiya sosai a wajen,da zarar aka ga abinda kike yi sai ki zubar mata da aji kuma ni zata yi wa faɗa, ki kama kan ki dan Allah"

Yaqe Mommy ta yi sannan ta saki hannun Billy ta bi matar da ke tsaye tana jiran su gama sallama, Mommy na shigewa wajen da ake gyaran jiki Billy ta fita daga building ɗin ta wuce wajen Man ɗin ta dan kuwa sun yi kewar junan su matuqa bata fatan su kwana basu gana ba,ta tabbata kafin nan kafin a gama gyara Mommy sun gama abinda za su yi sai ta dawo su wuce gida, bata so ta b'ata wa Hajiyan ta rai tunda har ta sanar da su za su yi dinner tare, da ta jira su gwanda su su jira ta.

Tinda aka shigar da Mommy wajen gyaran jiki basu fito ba sai da Billy ta dawo ta nemi inda suke aka ce suna wajen yin k'walliya, direct d'akin da ake yin kwalliya Billy ta shiga, sanda idanun ta suka sauka akan Mommy da ta sauya kamanni saboda gyara da kwalliya da ta sha sai da ta rikice, nan take ta ji wani irin kishi da hassada ya d'arsu a ran ta, cikin jimanta lamarin ta ayyana,

'Anya ban d'akko ruwan dafa kaina ba kuwa? Kar fa naje garin taimako ta ture gwamnati na ta kafa tata sai dai na jira ta kwashi babban kaso a bani qarami'

"Ranki ya dad'e gata nan an kammala duk abinda ki ka ce a yi mata, amma fa wannan qanwar taki akwai ta da tsoro da raki,"

Yaqe Billy tayi tace,

"Haka take, ina godiya gaskiya kun yi aikin da ya dace ku yi harma da qari,dan haka dole ne a qara maku wani abu"

Ta faɗa tana mai zuge jakar ta ta dakko kuɗi kimanin dubu goma ta baiwa mai kwalliyar, godiya mai kwalliyar ta yi mata sannan Billy ta yi wa Mommy umarnin su wuce su tafi shopping, gashin dokin da aka sanya wa mommyn ta kawar da wanda ya sauka a saman fuskar ta ta miqe tsaye ta na qara kallon kanta a madubi da kyau, tabbas ita ɗin mai kyan diri da fata ce ta sani, amma bata taɓa zaton tana da kyau a fuskar ta irin haka ba sai yanzu,sai a yau ta ke ganin ashe ma bakin nata da ake yi wa iya shege wata kadara ce ta daban da Allah ya yi mata,dan kuwa ya ɗauki kwalliyar da aka yi masa tsafff ya qawatu ya qawata fuskar ta.

"Hahaiiiii ! son a sani ne fa ba wani abu ba, matar da har yau a qarqashin wata take bata da gidan kan ta ai barikin nata bai kai ko ina ba"

A fusace Billy ta juya ta kalli 'Yan matan dake danna waya suna cin chewing gum suna dariya qasa qasa tare da kallon Billyn suna ci gaba da yi da ita a gaban idon ta, har zata tanka su ta tuna da gargad'in Hajiya K'waisa na ta kiyaye yin qananan faɗan da za a kai ta wajen police, dan kuwa hakan ba k'aramin taɓa mata qima yake yi ba a gan ta kullum tana neman alfarma a wajen 'Yan sanda manyan su da qananan su.

K'wafa ta yi ta ja hannun Mommy suka bar wajen, ko da suka fita sai Mommy ta ji ana ta kiraye-kirayen sallar magariba, kallon Billy da ranta yake a matuqar b'ace ta yi tace,

"Yanzu idan zan yi sallah wannan faratan za su ɗauki ruwa kuwa? Sannan shi wannan gashin na ga kamar hula ce aka sawa gam ya manne da kai na ta ina ruwa zai shiga na yi shafar kai?"

(Tambaya zuwa ga masu sanyawa faratan su fenti da kuma sanya attachment daga mommyn gaye)

Cikin fushin dake cin ranta ta juya ta kalli Mommy tace,

"Idan Sallah kika biyo ni yi nan garin sai ki yi bayani sai na kai ki gidan manyan malaman garin nan a buɗe maki masallacin mata kina jan su sallah,kin ga Mommy bari na buɗe miki wannan harkar tamu ki ji ya take idan kin ga zaki iya ki bini tun yanzu ki san ina ki ka shigar da kan ki da kan ki, idan kuma kin ga baza ki iya ba gwanda tin yanzu mu rabu kowa ya san inda dare ya yi masa.

Maganar gaskiya Mommy ba wani aikatau da nake yi da ya wuce aiki da jiki na da Allah ya bani ina biya wa mace ko namiji buƙatar su, su kuma su zube min kud'ad'e maqudai na biya tawa buqatun na yau da gobe,ina kuma yin hakan ne ta hanyoyi da dama,kamar  su wayar nan ta zamani da ki ka gani a hannayen mu ina nufin ta social media kamar su WhatsApp, TikTok, Instagram, Telegram ke har ta Twitter yi muke yi,sannan ina iya bin mutum duk qasar da yake so dan na taya shi shaqatawa ko kuma a nan gida Nigeria,ni ɗin nan da ki ka ganni ba qaramar yarinya bace, tsoron zagin da za a yi wa iyaye na ne yake sanyawa nake rage wasu abubuwan,wannan shine dalilin da yasa kika ga sai na yi shekaru ban je gida ba,saboda iyayen da suka haife ni ma basu san asalin me nake aikatawa ba,dan haka idan kin ga zaki iya ki yi in baza ki iya ba ga hanya nan kafin komai ya yi nisa ki koma qauyen Ba mugu ki ci gaba da bawa Yah Shamsu jikin ki yana lalubewa babu ko sisi"

Tana gama fad'ar waɗannan maganganun da suka sanya Mommy yin suman zaune ta ja motar da mugun gudu suka isa wani shopping mall dake kusa da saloon ɗin da suka je ta samu wajen parking ta yi ta fita ta tsaya tana jiran Mommy da har a wannan lokacin bata gama fita daga cikin rud'anin da ta afka ba.

Sigari ta fitar ta kunna ta hau busawa abinta hankalin ta kwance, masu wucewa na kallon ta, abinda ya sake d'aure wa Mommy kai kenan, dama Billy na shaye-shaye,sannan a bayanan ta ta ji kamar maza da mata dika take bi anya zata iya yin wannan rayuwar irin ta su Billy kuwa? A hankali jiki babu k'wari ta fita,Billy na ganin ta fita bata ce mata komai ba ta yiwa karan sigarin ta doguwar zuƙa ta fesar sannan ta yar ta bi ta take ta sa kai suka shiga shopping mall ɗin,wajen da ake saida qananan kaya na mata suka nufa, Billy ta dinga kwasar wa Mommy ta na kara mata a jikin ta, da ta ga sun yi mata sai ta ɗaukar mata, a haka saida ta ɗebar mata kala goma sannan ta kwashi takalma biyar da purse uku masu kyau ta wuce wani d'aki ta sa mommy ta shiga ta dinga gwad'awa, daga qarshe ta bar wata bingilar riga kalar purple mai duhu wadda take iyakar ta guiwa da siririn hannu ta qirjin ta an tattare ta kaɗan, murmushi Billy ta yi ta daki mazaunan Mommy ta ce,

"Da kyau Hadizan Ɗan liti, mu je na san yanzu Hajiya na can ta dawo,mu je ki bata mamaki qawata, yanzu ace Baba D'an


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login