Showing 231001 words to 234000 words out of 276165 words
Chapter 78 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
musu hannu ya wuce.
Cikin gida Billy ta kirawo yara suka kai musu akwatinan su kafin su shiga gidan,Ummah na ta shirin ɗora abincin rana ta ga ana shiga da akwatina masu matuƙar kyau,Ameerah kuwa na zaune a bakin ƙofar shiga ɗakin ta taga shigar akwatinan,cikin sauri ta rufe rigar ta da take shayarwa ta saɓa yaron a baya ta nufi inda aka ajiye akwatinan,baki ta yage tana kallon su Billy da Any da ke sallama suna shiga gidan,ganin Billy ce ya sanya Ameerah washe baki tace,
"Laaa Billy yau kece a gidan namu? Tabdijam wata sabon gani,ai ni na zaci kin fantsama bariki baza ki dawo ba sai kin fara kasa taba da sigari a faranti kina zama a ƙofar gida ƴan bariki na zuwa siye,ko kuma ki ɗauki farantin aka kina yawo lungu da saƙo kina faɗin ga gorosss asai sigariiiii."
Murmushin baƙin cikin kalaman Ameerah ne ya ƙwacewa Billy da Any,Ta Annabi kuwa haushin kalaman Ameerah ne suka sanya ta zabgawa Ameerah dake ɗauke da goyo mari,cikin tsananin fushi da rashin kunya Ameerah ta juya zata wanke Ta Annabi da mari Shamsu ya shiga gidan,wata iriyar sufa ya yi ya riƙe hannun Ameerah yana haki................
*Jama'a na gaji aradun Allah mu haɗu a next page.*
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 93:
Yarfe hannun ta ya yi gefe ɗaya sannan ya daddage ya dinga zuba mata mari hagu da dama,tin Ta Annabi na jin daɗin marin da Shamsu ke yi wa Ameerah har sai da ta dawo tausayin ta, cikin sauri ta koma bayan Ameerah dake shirin kaiwa ƙasa ta kunce goyon dake bayan ta,wani irin kuka jaririn ya tsanyara kamar ya san meke faruwa da mahaifiyar shi.
Cikin haki Shamsu ya nuna Ameerah zai yi magana Mai Dusa ya shiga gidan cikin tsananin tashin hankali da damuwa,yanayin yanda yake tafiya ne ya sa Shamsu saurin isa gare shi ya tare shi,wani irin numfashi yake fitarwa kamar wanda ake matsewa huhu,a hankali ya hau nuna Billy da Any hannun shi na karkarwa,bakin shi dake rawa ya buɗe ya ce,
"Bilkisu kin cuce ni kin ci amana ta,Bilkisu kin cutar da kan ki kin lalata rayuwar ki duniya da lahira,me ya dawo dake gida na bayan kin san me kika aikatawa kan ki?"
Cikin daurewar kai Ta Annabi ta kalli mijin nata ta ce,
"Malam wannan waɗanne irin kalamai kake yi haka akan Bilkisu? Yanzu fa suka zo ba a jima da ajiye su a mota ba,yarinya ta tafi tayi kusan shekara biyu bata gida yanzu ta dawo sai kuma ka dinga faɗin munanan kalamai akan ta?"
"Ki tambaye ta da ta tafi me ta aikata? Bilkisu ni Mai Dusa na yi Allah wadai da danasanin haihuwar ki,na tsinewa ranar da kika zo duniya Bilkisu,da nasan haka zaki koma idan kin girma da a ranar da aka haife ki na murɗe miki wuya sai dai a yi zaman makokin ki ba dai bikin sunan ki ba."
Fadila wadda shigar ta gidan kenan ce ta yarda jakar makarantar dake hannun ta tace,
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ! Yah Bilkisu me ya dawo dake gidan nan kuma a dai-dai wannan lokacin bayan kin san abinda kika aikata? Shikenan yanzu kin jawo min bala'i da masifa wataƙila auren nawa ma da ko ranar shi ba a kai ga sakawaba ya fasu kenan har abada, na tabbata babu mai aure na saboda abinda kika aikata,Allah ya isa tsakani na dake ba zan taɓa yafe miki ba."
Cikin kuka Fadila ta ratsa zata wuce su,Billy da jiri ya ke ɗiban ta saboda gano abinda ke faruwa ta tafi luuu zata faɗi,gefe Fadila ta koma Billy ta faɗi yiiiiff a ƙasa,cikin kuka Fadila tace,
"Ki tattara dake da matar taki ku bar mana gida kawai kafin mutanen gari su gane kuna nan,baku da amfani a cikin al'umma tinda kuka ƙetare iyakar Allah irin haka."
Cike da tsawa Shamsu ya ce,
"Idan baki faɗa min abinda yake faruwa ba kika sake magana sai na tattaka ki anan,haka kawai daga dawowar yarinya ku saka ta a gaba ke da Baba kuna faɗin munanan kalamai akan ta?"
Cike da tsawa itama Fadila ta ce,
"Dole ne mu faɗi munanan kalamai akan ta saboda abinda ta aikata ya yi muni,Yah Shamsu ina zaune a aji a islamiyya naga an yi group ana magana ƙasa-ƙasa ana kallon wani abu sai a juyo a kalle ni,gajiya nayi da kallon da ake yi mini na leƙa,ina zuwa na ga...ina zuwa naga videon Yah Bilki namiji na amfani da ita ta baya,wani na gaban ta wani na saman kan ta,ban gama kallon wannan ba wata tace,ai tana da video ɗin ta ma wanda take ita da matar ta,yau sati biyu kenan da ta d'akko daga vidmate tana tsoron nunawa mutane,ina duba videon Yah Bilkisu ce da wannan la'ananniyar suna sumbatar juna tare da yin abubuwan da basu dace ba,ki faɗa min shin har yanzu ke musulma ce ko kin fita daga addinin namu shima?"
Gaba ɗaya mutanen wajen sun daskare da mamaki da tsoro,Billy kuwa Any ce ta taimaka mata ta tashi,rungume junan su suka yi suna kuka,cikin kuka Billy tace,
"Na tuba na daina dik abinda idanun ki suka gane maki Fadila,wannan shine dalilin daya sanya na dawo gida,dan girman Allah ku yafe min...Baba..Baba dan Allah ka tashi ka yafe min,ba zan sake maimaita abinda na yi a baya ba saboda son abun duniya da son zuciya,na tuba ga Allah kuma har abada zan mutu ina neman gafarar Allah,dan girman Allah ku yafe min, Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una Anam dan Allah ki faɗa musu mun tuba,hisba ma sun shaida mun tuba."
"Mu bamu shaida ba Bilkisu,kin san irin kunyar da kika sa naji yau a kasuwa kuwa? Yaron shagona ke goranta min akan abinda kika aikata saboda ya yi laifi na yi masa faɗa har ta kai ga na kore shi,yana tafiya ya tura min videon ki subhanallahi,gaki nan tsirara maza uku na amfani dake da mata guda biyu,ke karya ce ! Maza har uku akan ki ga mata biyu dik ke kaɗai? Bayan yaron nan ya tura min sai da ya turawa mutanen dik da yake da lambar su a wayar shi, kafin wani ɗan ƙanƙanin lokaci shagona ya cika da mutane ana zagi na,da ƙyar wasu bayin Allah suka kare ni suka ce ai babu laifi na dan kin aikata wannan abun,tinda guduwa kika yi kika bar gida,Bilkisu kin cuce ni,kin cuci zuri'a ta da ke kan ki, yanzu wa zai aure ki tinda kin auri mace ƴar'uwar ki?"
Rarrafawa Billy tayi gaban mahaifin ta tana kuka ta kama ƙafar shi ta ce,
"Baba dan girman zatin Allah ka yafe min,na tuba ba zan sake ba,Baba ka tausaya min ka yafe mi...."
Wani irin gigitaccen mari ne ya sauka a kuncin Billy,bata damu da ta sanya hannu ta sosa ba balle ta kare koda wani da yafi wannan zai sauka a fuskar ta ta,duka Ta Annabi ta rufe Billy dashi ko ta ina tana faɗin,
"Kin yi asara Bilkisu,kin yi wayon banza,da nasan haka zaki zame mana masifa a rayuwa da kashe ki nayi ko na ɓarar da cikin ki,ku tashi ku fita ku koma inda kuka fito dan uban ku."
A gigice Ta Annabi ta ajiyewa Ameerah jaririn ta a ƙasa ta nufi kitchen ta ɗako ƙaton itace ta yo kan su Any a guje zata shirga musu,cikin zafin nama Shamsu ya riƙe ta,ihu ta hau yi tana kuka tana zagin su Billy,da ƙyar Shamsu ya samu nasaarar kai Ta Annabi d'aki sannan ya dawo dan ya taimakawa Mai Dusa ya kai shi ɗaki shima,da ƙyar ya iya ɗaga mahaifin nasu daga ƙasa suka fara takawa zuwa ɗaki,sai da suka gota Billy dake tsugunne tana kuka Mai Dusa ya tsaya ya ce,
"Ba za ki zauna min a gidana ba,dan haka ki tabbatar da kafin wayewar gari kin koma inda kika fito,ban damu da ki shiryu ko ki ƙara lalacewa ba,kin riga da kin bar mana tabon da har ƙarshen rayuwar mu zamu yi ta dakon shi."
Da sauri Billy ta sha gaban su Shamsu ta tsugunna gaban Mai Dusa ta ce,
"Na amince zan koma inda na fito Baba,amma ina roƙon ku kamar yanda na tuba ga Allah,dan Allah kuma ku yafe min,ko bajima ko ba dad'e ina nan zan jira yafiyar ku a gare ni,zan jira ku ku yafe min saboda na sani na cutar da ku."
Any na gefe tana ta kiran wayar Man bata shiga,yanzu taya za su bar garin nan ba tare da wata masifar ta sauka akan su ba? Suna murna sun gudo ƙauye daga birni saboda su samu mafaka ashe sun fafake mafakar tasu tun kafin su samu fakewa?
Mai Dusa bai kula Billy ba suka wuce ɗaki shi da Shamsu,banda kuka babu abinda Ta Annabi take yi,Ameerah kuwa jikin ta dik ya yi sanyi saboda jin wanda suka fita fitsara,sai jijjiga yaron ta take yi amma ya ƙi shiru,goya shi tayi sannan ta ce,
"Bari na kirawo muku babana yazo ya fitar daku daga garin nan,dan kuwa babu makawa mutane idan suka gama hasala za su zo su ɗauki mummunan mataki akan ku,wanda ma bai aikata abinda yakai naku muni ba sun ɗauki mataki akan shi balle ku?"
Jiki na rawa ta shiga ɗakin ta ta d'akko wayar ta,dik yanda ta dinga Kiran wayar Ɗan liti bai shiga ba, ƙarshe ma baturiya ce mata tayi wayar a kashe take,cike da tsananin tashin hankali Shamsu ya fita ƙofar gida,ya dawo,ya sake fita ya dawo,ya rasa wacce iriyar shawarar zai yanke,shi me yasa bai samu damar ganin videos ɗin su Billyn ba? Cikin sauri ya kauda wannan tunanin yana son ya sama masu mafitar da za su bar Garin Ba Mugu lafiya.
Oda suka dinga ji ana dannawa a ƙofar gida,a zaton su ma Man ne ya dawo ɗaukan su tinda Any ta tura masa saƙo,suna fita da akwatuna niƙi-niƙi sai suka ga Ɗan liti,cikin sauri ya buɗe motar ya ce,
"Ku shigo na sauke ku a kano,fusatattun matasan garin nan na can fadar Sarki suna neman izinin a basu dama su ɗauki mataki akan ku dan sun samu labari wai kun shigo gari."
A guje Any ta ja hannun Billy dake waiwayen gidan su suka afka motar,Shamsu ne ya buɗe bayan motar ya watsa masu akwatinan su,suna shiga Ɗan liti ya ce,
"Maza ku duƙar da kawunan ku ƙasa,kar nima ku jawo min bala'i lalatattun banza,ku rasa iskancin da za kuyi sai auren jinsi,kaiii Allah ya wadaran naka ya lalace,jakin dawa ya ga na gida."
A guje Ɗan liti ya ja motar shi ya bar garin Ba Mugu da su Billy dake maƙale a motar suna shan faɗa da masifar shi,da ace zai kula da kyau ma da ya hutar da kan shi,dan kuwa basa cikin natsuwar sauraren shi balle su gane me yake faɗa.
Bayan tafiyar su da minti goma ne matasa suka yo zuga zuwa gidan Mai Dusa, ihu suka dinga yi tare da faɗin a fito musu da su Billy yau sai sun baƙunci lahira tinda sun ce su ƴan iska ne,ganin kamar raina masu hankali Shamsu yake yi da ya ce basu nan sun gudu da suka samu labarin abinda ke faruwa sai kawai suka afka gidan,duk wani abu mai kyau sai da suka dinga fatali da shi da sunan neman su Billy,wannan abun da suka dinga yi shine ya yi sanadiyyar suman Mai Dusa,ganin halin da ya shiga ne ya sanya Ta Annabi fitowa tana kururuwa ta ce,
"Ku taimaka min miji na ya mutu,dan Allah ku fita ku tafi neman su a can waje basa nan,mu kammu mun yi Allah wadai da abinda suka aikata,a cikin jimami muke dan Allah ku barmu muji da abinda ke damun mu, Shamsu ka duba min mahaifin ka baya motsi."
Shamsu ya jima da shiga ɗakin tinda ta fito tana kuka ya afka,gani yayi mahaifin nasu na da rai amma ya suma,dan haka sai ya fito ya ɗebi ruwa ya watsa masa ya gyara masa kwanciya,matasan nan kuwa sun fita saboda ganin halin da Ta Annabi ke ciki,Sun tabbata suma a cikin damuwa suke.
A can hanya kuwa su Billy basu zauna a kujera ba har sai da suka bar ƙauyen Ba Mugu da wasu ƙauyikan dake kusa da shi sannan suka zauna cike da jimamin abinda ya faru,ko da suka isa kano a tasha Ɗan liti ya sauke su ya bi layi dan yin lodi ya koma ƙauyen su,dik godiyar da su Billy keyi masa bai kula su ba sai ya shige motar shi ya zauna,yana hango su suka samu abun hawa suka bar tashar.
Hawaye ne suka hau zarya a kuncin Ɗan liti,yanzu da Mommy bata yi aure ba da tini da ita a wannan badaƙalar,ashe irin wannan soyayyar ta lalacewa Billy take nufin tana yi wa Mommy? ashe dama akwai irin waɗannan mutanen masu auren jinsi da neman maza ta baya bai sani ba? Kanshi ya kwantar a jikin sitiyarin motar ya rushe da kuka.
"Kaicon rayuwar mu, kaico na,wace iriyar tarbiyya muka baiwa yaran mu? Me yasa muka biye wa ruɗin duniya da son abun duniya tare da jahilci yaran mu suka lalace? Yanzu ta ina zamu fara gyara tarbiyyar yaran da suka riga suka girma?"
Yana tsaka da koka tashin hankalin da ya tunkaro su aka ƙwanƙwasa gilashin motar shi,a cikin dabara ya goge idanun shi sannan ya buɗe ya fita,abokan da ya yi a tashar ne suka hau hira dashi suna bashi labari akan sababbin shugabannin tashar da aka naɗa,wannan labaran ne ya ɗebe masa damuwar dake ran shi har aka zo kan shi ya fara lodi dan komawa ƙauyen Ba Mugu.
A gidan Billy motar da ta ɗauke su ta ajiye su,sun jima tsaye suna kallon gidan da ta same shi ta hanyar haramun kafin su kwashi kayan su su buɗe gidan su shiga,suna shiga parlour Billy ta ware murya ta dinga kuka kamar zuciyar ta zata fashe dan baƙin ciki da damuwar da take ciki.
Cikin kuka Billy ta ce,
"Ya Allah mun tuba,Allah ka yafe mana,ina zamu kai wannan zunubin da muka ɗauka? Mun cutar da kawunan mu da iyayen mu,mun cutar da al'umma da muka aje musu mugun abun kallo,na gaji da rayuwar nan Allah ka ɗauki raina in huta !"
Any ce ta isa gaban ta ta hau lallashin ta, ita kanta hawaye ne ke gudu a kuncin ta,bata da kowa da zai kunyata akan abinda ta aikata,amma still kunyar kanta da kanta take ji,yanzu da Malam na raye haka zai ga wannan baƙin cikin? Wata zuciyar ce ta ce mata,
'A yanzu ma da iyayen ki basu raye dik abinda kika yi mai kyau ko mara kyau ana tada su a nuna musu.'
Cikin sauri ta miƙe tsaye tana faɗin,
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ! Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una! Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una! Ya Allah ka gafarta mana ka kawo mana mafita mafi alkhairi, Allah mun tuba, Allah kai shaida ne mun tuba."
Haka suka dinga kuka har suka gaji suka tashi suka yi sallolin dake kan su,ko abinci basu nema ba haka suka kwanta baccin wahala mai cike da mafarkai kala-kala.
****************************
Rayuwar gidan su Abdul rayuwa ce ake yin ta cike da farin ciki da kulawa,Abdul na iyakar ƙoƙarin shi dan ganin ya sauke dikkan haƙƙoƙin Huzaimah dake kan shi,wannan dalilin ne ya sanya ya saba mata da romance,ta haka yake samu ya biya mata buƙata,shi kuwa yana nan a naɗe kamar lagwani dan kuwa baya iya yin komai,watarana har tsoro yake ji idan ya ga babu wani ci gaba da yake samu akan matsalar tashi,likitoci na iyakar ƙoƙarin su akan shi,haka ma masu magungunan gargajiya suma suna nasu ƙoƙarin,dan kuwa na musamman Innah Laminde da Mai Martaba suke samawa gudan jinin nasu magani.
A hankali Huzaimah ta fara son wannan soyayyar da suke yi ta wuce matakin da suke kai, kwad'ayi da son haihuwa sun dabaibaye rayuwar ta,dik yanda take dannewa tana jurewa hakan be hana ta shiga damuwa da tashin hankali ba,a hankali ta fara rama kamar me ciwo,dik tambayar da Abdul zai yi mata bata iya bashi amsa,watarana idan ya matsa mata ma kuka take yi,ya sha kiran Bilal gidan dan ya tambayar masa Huzaimah ko akwai abinda ke damun ta,ƙarshe sai tace masa babu komai,a haka suka ci gaba da rayuwa damuwa na cin zuciyar Huzaimah a boye, a zahiri kuwa tana nan tana kula da mijin ta da rainon soyayyar da suke ta ginawa.
***********************
Jikin Baaba ya yi sauƙi sosai har ta warware ta koma sana'ar ta ta saida goro da ƙosai,Alhaji Baban Gida ya gaji da roƙo da lallamin Baaba akan ta koma Abuja ko ta koma gidan shi dake nan ƙauyen amma Hajiya Baaba ta ƙeƙasa ƙasa taƙi amincewa,dan haka tinda ya koma Abuja bai sake zuwa ba,sai dai Ummi da Munir sun zo yafi sau uku,watarana ma har da su Anisah suke zuwa.
Wataranar lahadi da yamma Mommy na zaune a tsakar gida ita da su Innoh da Amir Naja ta sallama gidan,cike da fara'a Mommy ta miƙe tana yi mata lale maraba,Innoh ma sannu da zuwa tayi mata suka zauna aka dasa hira,waya Naja ta ɗauka ta yiwa Mommy message sannan ta sauke wayar suka ci gaba da hirar su,kallon Naja Mommy tayi a cikin wani irin yanayi na rikici da ɗaurewar kai bayan ta gama karanta saƙon da Naja ta tura mata,murmushi Naja ta sakar mata sannan ta lumshe idanun ta dika biyu ta duƙar da kai kaɗan hannunta na rawa Mommy ta ɗauki wayar ta ta hau yi wa Naja reply...........
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 94:
Sun jima suna hira kafin daga bisani Aunty Naja ta miƙe tsaye tana karkaɗe jikinta ta ce,
"To ni bari na tafi gida, na san yanzu haka Goggo na can tana jirana na je na ɗora tuwon dare,gwanda ku gashi muna zaune har Innoh ta gama komai."
"To sai yaushe kuma?"
"Ban gane sai yaushe ba? Yaushe rabon ki da gidanmu ? Ai Goggo ma fushi take yi dake idan baki sani ba na sanar dake,ta ce tin sanda ta kori wani gajiyayyen saurayin ki mai kai kamar bushiya kika daina zuwa kwana wajen ta."
Dariya suka fashe da ita sannan suka tafa kamar wasu ƙawaye,cikin dariya Mommy ta ce,
"Hamzy gaye ne fa na bayan layin nan namu,nu kaina yaron nan mugun takaici yake bani, sa'an fa Ameerah ne wai amma ya zo neman aure na tsabar rashin kunya,ina sane na gayyace shi can