Showing 165001 words to 168000 words out of 276165 words

Chapter 56 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

da misalin ƙarfe 9:16pm, ko da ta shiga cikin gidan ta tarar da gidan shiru kamar babu kowa saboda sanyin da ake busawa sosai kowa ta shige ɗaki ta rufe da kaskon wuta ,a ƙofar d'akin Innoh ta tsaya tana k'wank'wasawa hawaye na zuba a idanun ta,Innoh na cikin zanin gado ta furta,

"Ka shigo mana ko ɗakin baƙon ka ya zama da kake yi min ƙwanƙwasa, ko kuma zuwa zan yi na ɗakko ka kamar jinjiri na shimfiɗe a gado?"

Mommy ce ta kutsa kai cikin ɗakin tare da fashe wa da kuka mai tsanani,a gigice Innoh ta diro a gado, da sauri ta ja gefe saboda ƙafar ta da ta kusan taɓa kaskon wutar da ta kai ɗaki domin shan ɗumi. Cikin damuwa da tashin hankali ta kalli Mommy tace,

"Ke lafiya kika zo mana gida a wannan tsohon daren kina kuka? Idan ma sakin ki yayi to ki koma ki faɗa masa ni Innoh nace auren ku mutu ka raba ne, bai isa ya sake ki ki saku ba,taso muje yaga yawa na, na kula shirun da muka yi kwana biyu bamu kai sunan shi wajen malam ba shi yas....."

Cikin kuka Mommy ta katse Innoh da cewa,

"Ni fa Innoh ba saki na yayi ba,ni ce da kai na nace ya kawo ni gida na faɗa maki mummunan labarin da ya same ni."

"To be sake ki ba uwar ki da uban ki na raye basu mutu ba kukan uban me kike yi haka Hadiza...Uffararan me sunan da ba a fad'e gatsal,sanar dani me yake faruwa to?"

Cikin kuka Mommy tace,

"Innoh wai fa mutanen gidan sarki ne ke ta murna wai suna zargin ina da ciki, shima uban gayyar har da cewa ya tabbata ba zargi yake ba ciki gare ni, jibi da mun je kano zai kai ni a duba ni a ga shin ciki gare ni da gaske?"

Gud'a Innoh ta damƙi hancin ta ta rotsa a tsakiyar kan Mommy da ta toshe kunnen ta ta rintse idanun ta dan baƙin ciki,cikin tsananin kuka tace,

"Innoh zuwa nayi ki bani shawarar yanda zan salwantar da cikin nan ba tare da kowa ya sani ba amma kike murna, Innoh cikin nan ba ƙaramin matsala zai zame min ba,zai lalata surar jiki na, zan zama ƙatuwar mace me tumbi, dan Allah Innoh ki taimake ni."

Wata uwar harara Innoh ta sakar wa Mommy sannan ta ja da baya ta nuna ta tace,

"Kin san Allah? A dik sanda na ji labarin ƙwarzane ya samu cikin jikin ki ta dalilin ki zaki ga yanda zan tsine maki ki bi duniya,ke kin san amfanin da cikin nan zai yi maki kuwa? Jikan gidan sarkin garin Ba mugu fa kike ɗauke da shi, ki sani a duk sanda kika haihu wannan abinda ke cikin naki zai jawo maki arziqi,Ameerah ma me auren talaka dan turin waya ta samu ciki suke murna ake ririta ta balle ke da kike da uwar kuɗi da mulki da kyakkyawar rayuwa? Ahir ɗin ki da zubar da ciki ko salwantar da shi,ki rungumi cikin nan da kyau da kulawa ya zame maki babban jari, kiyi maza ki koma wajen mijin ki, sannan kiyi nazari akan magana ta zaki gano me nake nufi da hakan."

Ba dan Mommy ta gama gamsuwa da Maganar Innoh ba ta yi mata sallama ta fita ta koma wajen Abdul dake ta chatting da Bilal yana sanar da shi zuwa jibi za su isa kano.

Ko da suka koma gida Mommy bata ce komai ba game da maganar cikin da suke hasashen tana da shi sai kawai ta ci gaba da harkokin ta,bayan sun kwanta kuwa duk yanda Abdul yaso ya samu natsuwa da ita ƙin yarda tayi saboda haushin shi take ji.

Bai jima da gama yi mata naci ba bacci mai daɗi ya ɗauke shi, juyi tayi tana shafa cikin nata dake shafe zuwa cikakken ƙugun ta, sannan ta maida hannun ta saman ƙirjin ta dake a cike, tsaki ta ja a hankali ta furta.

"Allah ya kaimu kanon a gwada a gani,idan ta tabbata ciki ne dani gaskiya ba zan bari ba, Allah ya bani kyakkyawan jiki haka kawai na bari haihuwa da rainon yara ya tsufar dani? Inaaa ba zai yuwu ba, a gaban ido na Billy ta sanar dani BBL tayi a mazaunan ta dan kawai ta samu irin jiki na,mata da dama na kashe millions of dollars dan su samu irin sura ta se kawai na bari ta lalace da haihuwa? Sam ba zai yiwu ba gaskiya,da Innoh ke wani cewa Ameerah nada ciki ita taga zata iya ɗauka ta raina har ta haife amma ni kam ba zan iya ba inaaa sam-sam ba zata sab'u ba bindiga a ruwa."

Haka ta kwana tana tunani da ƙyar bacci ya ɗauke ta da goshin asuba,bata farka ba kuwa har aka idar da sallah a masallatai,dik yanda Abdul yaso tada ita taƙi bashi had'in kai ƙarshe ma ƙarya tayi masa tace tayi sallar komawa baccin tayi, dole ya ƙyale ta ya koma d'ayan d'akin yana shirye-shiryen yin meeting da abokan aikin shi da misalin goma na safiya.

Mommy kuwa tana can tana bacci bata farka ba sai 11am, tana farkawa wayar ta ta fara jawowa, ta buɗe data ta fara duba WhatsApp bata amsa saƙo ko ɗaya ba ta fita ta shiga TikTok ta tsaya taga video guda ɗaya sannan ta ajiye wayar tana saurarar wani videon da ta ke gani, a haka tayi alwala tayi brush ta tada sallah bayan ta fito tayi sallar hankalin ta duk na kan wayar.

Tana idarwa bata tsaya addu'a ba ta miƙe ta ɗauki wayar ta ta nufi parlour daga ita sai wata guntuwar rigar bacci kanta sai sheƙi yake yi saboda na nusamman taje Saloon aka gyara mata shi.

Abdul ta hango alamar yana yin video call dan haka sai ta samu gefe ta zauna ta natsu tana danna wayar ta,Abdul bai samu damar gama meeting ɗin shi ba sai 12pm dai-dai,cike da shagwab'a ta kalle shi tace,

"Baby yunwa nake ji ina abinda zan ci yanzu?"

Murmushi yayi kafin yace,

"Ina fatan kin yi sallah da kika tashi dan nasan baki yi ba kyale ki kawai nayi, And Maganar abinci kuma Baby ba ke kike dafa mana ba dama? Amma tinda naga alamar kin gaji ko zaki daure ki d'umama mana abincin da muka zo dashi jiya mu ci?"

Kallon shi tayi cike da rashin mutunci sannan tace,

"Ban gane ba? Baby yunwa fa nace maka ina ji sannan kace naje nayi dumame? Impossible!"

"Inyeee wato Impossible ko? Da kyau, bari ni naje na d'umama mu ci,Allah ya huci zuciyar maman biyu?"

Yana tashi ta ɗauki pillow ta wurga masa tana mita da dire-diren shagwab'a,shi kuwa gocewa yayi yana dariya ya gudu kitchen.

Ƙin komawa gidan su tayi kamar yanda tayi alƙawari suyi sallama,a cewar ta tana ganin babu abinda zai maida ta, dama Baban sune kawai ta damu suyi sallama,to akwai waya ta kira shi suyi ba sai sun haɗu ba.

Ranar lahari da zasu tafi kano kuwa da sassafe Mommy da Abdul suka gama shiri suka ɗauki hanyar garin kano.


**************************

"Babe na faɗa maki ki daina yi min bincike a d'akin can ko? Ko baki yarda dani bane akwai abinda kike neman ƙarin bayani akai naƙi yi maki?"

"Baby i am sorry, babu abinda nake bincike fa na musamman,kawai ni ina da karambanin taɓa duk wata na'ura mai ƙwaƙwalwa idan na ganta,"

"Tooo ! To ki guji bincike musamman a can d'akin gudun nar ki ga abinda zai hana ki Zaman lafiya a rayuwar ki baki dayan ta."

Rungume juna Billy da Amy suka yi suka hau soyayya kafin daga ƙarshe Amy tayi mata sallama ta tafi aiki,Billy kuwa na jin ta ita kaɗai sai ta hau TikTok tana kallon Videos tare da yin sababbi tana ɗora nata.

A haka taci gaba da latse-latse har ta gaji ta kashe computer sannan ta koma parlour,zaman ta keda wuya taji ƙarar ƙararrawar shiga gidan,rigar ta wadda da kaɗan ta rufe ƙirjin ta ta gyara kafin ta tashi cikin yanga ta isa bakin ƙofar ta buɗe.

Wata baturiya ta gani tana kallon ta a tsorace, tana waige-waige, cikin sauri tace mata,

"You have to leave,you have t...to...to leave before it's too late for you, leave before it is too late for you, leave while you can...."

Tana gama faɗin haka matar ta bar wajen da gudu tana kare fuskar ta daga CCTV camera ɗin unguwar,kafin Billy ta gama tuna a inda ta taɓa ganin matar matar ta bace wa ganin ta, kyab'e baki tayi ta d'aga kafad'a sannan ta koma ciki ta zauna tana kallo,hankalin ta gaba ɗaya ya tafi wajen maganganun matar nan, dan haka ta ƙudirta a ranta zata tuntub'i Amy taji anya babu abinda take boye mata da ya danganci rayuwar ta ta baya kuwa?...........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI












RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨













PAGE 66:









Tin daga gate ɗin shiga gidan ta fara ganin sauye-sauye, domin kuwa an sakewa ƙofar gate ɗin fenti daga baƙi zuwa brown da ratsin golden a jiki, fentin dake jikin gidan kuwa gaba ɗaya milk ne,murmushi ta saki ta kalli Abdul wanda tini ita yake kallo dan yaga yanayin fuskar ta,cikin farin ciki tace,

"Baby naga an cire ƙarafan dake jikin ginin gidan nan an ƙara tsawon katangar kuma an sauya fentin gate ɗin?"

Kallon ta yayi cikin fara'a yace,

"Aikin Bilal ne wannan,ni dai kawai na san nace masa ina son ya maida gidan nan yayi kyau yanda zai ƙayatar da ganin ki,ina fatan kwalliya ta biya kud'in sabulu?"

"Ai kuɗin sabulai ma ta biya wannan ba kud'in sabulu ba baby,gaskiya na gode sosai Allah yasa kafi haka."

"Amin ya Allah, li am glad you like it."

Motar shi ya shigar gidanbayan dattijon mai gadin ya buɗe masu gate ɗin,Bilal suka tarar a tsaye yana latsar wayar shi, ko d'aga kai beyi ba balle ya kalle su, fuskar nan tayi kicin-kicin kamar ta mai jin kashi,bai motsa daga inda yake ba har sai da Abdul da Mommy suka isa gaban shi ɗauke da akwatinan su,Abdul na jan biyu mommy na jan ɗaya hannun ta ɗaya riƙe da handbag,Abdul ne ya kalle shi yace,

"Man ya dai na gan ka ka wani tsume kamar wanda ya sha maɗaci?"

Yatsina fuska yayi ya amsa gaisuwar Mommy a shaƙe sannan ta rab'e su ta wuce ciki,a shaƙe Bilal yace,

"Lafiya ragas nake ni raini ne bana maraba da shi shi yasa nake kama mutunci na tin kafin a ga wajen kwana na a kawo min raini."

Sai yanzu Abdul ya gane me yasa yake ɓata rai, wato ganin mommy ne ya dagula masa lissafi, tinawa yayi da yanda suka yi da Bilal ɗin a waya a lokacin da Abdul yace masa idan ya gama da gyaran gidan ya siyo musu abinci sannan ya jira su iso a haɗu a ci gaba ɗaya a yi hirar yaushe gamo,dagewa yayi akan shi fa sam ba zai zauna inuwa ɗaya da Mommy ba dan shi har yanzu ba wani ƙaunar ta yake ba, shi dai da yaji ya kuma gani to yaje can su ƙarata,da kyar Abdul ya shawo kanshi ya amince zai jira su iso a gaisa amma ba zai zauna wani cin abinci da su ba, abincin ma da ba ita ta dafa ba shi ya siyo? Murmushi Abdul yayi yace.

"Man kana da matsala gaskiya,mu je ciki ni a gajiye nake bana maraba da wannan sabon halin naka sam."

"Ni ma ba maraba nake da naka sabon halin ba,kaga tafiya ta, ina maka barka da dawowa lafiya, kar ka manta gobe a fito aiki."

Hannu ya miƙawa Abdul suyi sallama Abdul ya saki baki yana kallon Bilal, kallon wai da gaske baza ka shiga mu ci abinci tare ba yake masa,har Bilal zai wuce Mommy ta leƙo kai babu ɗan-kwali sanye da matsattsun riga da skirt na atampa tace,

"Baby ka shigo ka huta mana ka tsaya a waje tin ɗazu."

Bilal ne ya kalli Abdul yace,

"Idanun ka sun gane maka dalilin ƙin shiga ta gidan ka yanzu ko?"

Ba tare da ya sake magana ba ya wuce ya hau machine ɗin shi roba-roba fari mai kyau ya bar gidan,Abdul ne ya ja akwatinan shi ya shige cikin gidan,direct bedroom ya kai kayan ya ajiye sannan ya fito ya zube a kujerar dake zagaye da babban parlourn nasu,cikin muryar gajiya yace,

"Washhh Allah na na gaji,Baby ɗan duba dinning ki kwaso mana abinci nan mu ci yunwa nake ji."

Mommy dake ta zagaye gidan tana kallo tare da santin yanda aka ƙawata gidan ne tace,

"To ina zuwa ɗan bani minti biyar."

Sai da ta koma d'akin da ta ajiye kayan ta sannan ta sauya kayan jikin ta zuwa wata ƙaramar riga dan taji dad'in sakewa sannan taje ta kai musu abinci ta ajiye a center table ɗin dake parlour tayi serving ɗin su.

Sakwara ce da miyar agushi taji nama da kifi kala-kala, sai lemon kwali da farfesun kifi, buɗe ciki mommy tayi sosai taci ta ƙoshi kafin ta saki wata gyatsa mai ƙarfi sanna ta zame ta na hamdala, kallon ta Abdul yayi yana dariya yace,

"Waiii baby wannan wace iriyar gyatsa ce haka, da alama kin ƙoshi da yawa."

"Alhamdulillahi,tinda nake a rayuwa ta ban taɓa cin irin wannan abincin ba,sai dai nakan ji ana ce sakwara da miyar taushe ko agushi amma ban taɓa ci ba sai yau,ni fa ba dan na taɓa shigowa garin nan ba ma akwai abubuwa da dama da ban taɓa ci ba ko gani da ido na."

Kallon ta Abdul yayi da tausayawa sannan yace,

"Ai kuwa inshaa Allahu zaki ji daɗi a garin nan,dik wani abu da kike son ki ci sai kin ci shi indai ina da hali."

Washe baki tayi ta koma inda yake ta zauna a jikin shi tana farin ciki,cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Mommy ta hau birkitawa Abdul lissafi, sun jima suna zuba tsantsar tsagwaron soyayya a sabon parlourn nasu Mommy ta sake sauya sabon salo dan gamsar da Abdul,murya a shaƙe ta furta,

"Baby gobe ka kaini asibiti a zubar da cikin nan saboda mu ci gaba da zuba soyayyar mu babu takura."

Abdul jin shi yayi kamar wanda aka zubawa zuma a baki yana cikin sha a buɗe bakin a watsa masa maɗaci,cikin wani irin yanayi ya zame jikin shi a nata yana maida numfashi ya kalle ta dan son jin shin da gaske ne ita tayi magana ko jimawar da gidan yayi babu kowa ne ya jawo aljanu suka samu mahalli a gidan? Kallon shi tayi ta kafe shi da ido sannan ta sake kai hannu tana shafa jikin shi tace,

"Baby i am serious,zubar da cikin nan ne kawai zai sa mu..."

"Shut up Hadiza ! Yi min shiru nace ! Kina da hankali kuwa? Kin san me kike faɗa kuwa? Na zubar da gudan jini na fa kike nufi? Ashe baki da hankali ban sani ba? To menene ribar soyayya idan ba haihuwar ba? Haihuwa na daga cikin ribar da kowanne ma'aurata ke fata da burin samu, shine ni Allah yayi min kyauta sai kice na zubar? To idan kuma wannan ne kawai ƙwan mu a duniya da ni dake fa? Shikenan sai mu zauna babu haihuwa? Amma kin bani mamaki Hadiza dama ba sona kike yi ba nake ta wahal da kaina akan ki?"

Cikin kuka Mommy ta taro shi tace,

"Haba baby ya zaka ce bana son ka daga faɗa maka gaskiya...."

Cikin tsananin ɓacin rai da tada jijiyoyin kanshi Abdul ya kalle ta yace,

"Ko da ganganci cikin nan ya zube ba da son ranki ba ki sa a ranki ni Abdussabour na gama auren ki kenan."

Tashi yayi ya ɗauki kayan shi ya mayar jikin shi sannan ya wuce wani ɗaki na daban ya faɗa wanka,wanka yake yi amma gaba ɗaya tunanin rashin hankali irin na mommy ya addabi zuciyar shi, dama ba ta son shi auren shi kawai tayi? Ahh bata son shi mana, ai dik wanda yake son ka ba zai ki haɗa zuri'a da kai ba sai dai idan Allah ne bai kawo ba,shine shi ya samu take neman ta masa asara, lallai maganar Bilal na neman tabbata,da dikkan alama bata son shi, wani irin zafi yaji a ƙirjin shi,a haka ya gama wanka ya fito yana shafa mai,akwatinan da ya sa Bilal ya had'o mata lefe ya kalla, sai yaji ranshi ya ƙara ɓaci, yana nan yana kashe mata dukiyar shi dan su zauna su ji dad'in rayuwar su ashe ita tanadin da take masa daban,wataƙila da gaske so take ta rabu dashi shi yasa bata son haihuwa da shi, gaban shi ne ya yanke ya faɗi a lokacin da yayi wannan tunanin, cikin sauri ya hau saka kaya dan yaje ya same ta yaji dalilin da yasa take so ta zubar da cikin jikin ta.

Kafin ya gama shiryawa ya fita ta shiga d'akin,turus tayi tana bin akwatinan da kallo, nan take gaban ta ya faɗi ta hau bin shi da kallo, idanun ta ne suka fara yi mata ƙuna saboda hawayen da ya taru a cikin su babu shiri,cikin sanyin murya tace,

"Wannan akwatunan fa? Aure zaka ƙara Abdul ban sani ba? Yaushe ma muka yi aure da zaka sake yin wani auren?"

Ganin yanda hankalin ta ya tashi ne ya faranta ran Abdussaboor,cikin haɗe fuska yace,

"Eh aure zan ƙara, dama zuciyata ta jima tana raya min cewar ba ƙauna ta kike yi ba watarana zaki barni, shi yasa na haɗa lefe na ajiye saboda rana irin ta yau sai gashi ba a je ko ina ba kin nuna min ba zaki iya zama dani ba."

Wani kukan kura tayi ta nufi akwatunan ta hau naushi tana watsi dasu tare da faɗin,

"Baka isa ba Abdussabour ! Ni kaɗai ce matar ka har abada, babu maganar kishiya a tsakanin mu Abdul, auren mu dani da kai sai yafi auren zobe ƙarko,ina so ka sa a ranka ni Hadiza ni kaɗai ce matar ka."

"Ta yaya zaki zama mata ta ke kaɗai kina so ki zubar da ɗa na dake jikin ki wanda bai zo duniyar ba? Sharad'in zaman ki matata ke ɗaya Hadiza shine ki zauna dani tsakani da Allah, kuma ki haifa min duk cikin da Allah zai azurta mu dashi, idan kin amince shikenan, idan baki amince ba ƙarin aure babu fashi."

Cikin kuka ta zube a ƙasa tace,

"Yaushe ma muka yi auren da zaka yi min kishiya Abdul?"

"Nima abinda nake ta nazari akai kenan Hadiza, yaushe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login