Showing 138001 words to 141000 words out of 276165 words

Chapter 47 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

musu yayi musu tsada, sun so su cuce shi amma ya nuna musu ya san kan kasuwa,a haka suka loda kayan a babbar motar da suka zo da ita suka bashi kud'in shi kimanin dubu ɗari da hamsin suka tafi.

Murna shamsu ya dinga yi, ko gida bai shiga ba ya wuce gidan su Ameerah direct.........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI

















RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️ ✨










*MAHREEN 1K*
*MAIDA TSOHUWA YARINYA 1K*
*KYAKKYAWAR FAHIMTA 500*














PAGE 54:











Kwance take laga-laga a tsakar gida dik jikin ta ya ɓaci da zawo da amai, tin Innoh nayi mata dariya tana faɗin,

"Allah ya ƙara marowaciyar banza da wofi, ki rasa wanda zaki yi wa rowa sai uwar da ta haife ki,"

Har sai da ta dawo tana faɗin,

"Ohh ni Innoh matar Ɗan liti anya ba guba yaron nan ya baki ba dan ki ci ki mutu kowa ya huta da halin ki? Allah ya baki lafiya taso na kai ki bayi ki dena ɓata min tsakar gida, ji yanda ƙudaje ke bin ki Ameerah,"

Dik yanda Innoh taso ta taimaka wa Ameerah ta kasa, ƙarshe tunawa tayi da Baabaa da ta ga jikokin ta na zawo da amai sai ta jiƙa musu kuka ta basu, da izinin Allah suna sha sai ciki ya d'aure ya dawo dai-dai, da gudu Innoh ta afka madafi ta haɗawa Ameerah kuka ta tashe ta ta bata a baki, ta na shanyewa ta koma ta kwanta tana murƙususu.

Daren jiya Ameerah gaba ɗaya ta saka naman nan mai ƙuli da farin maggi a gaba ta cinye dika ita kaɗai, ga lemo da ta sha mai zaƙi roba biyu,wannan dalilin ne ya sanya cikin ta lalacewa, Innoh na zaune ta tasa ta a gaba tana ta zabga mata sannu, ta tuna kalmar da ta faɗawa Ameerah a daren ranar,

'Ki ci kiyi zawo,'

Nan take ta hau nadama a ranta tana faɗin,

'Allah ka sa yarinyar nan ta warke,wannan zawayi yayi yawa,'

Tabbas yau Innoh ta gano kaifin da bakin uwa ke da shi akan yaran ta, wataƙila da bata yi mata mugun fata ba da haka bata faru ba,suna nan zaune Ameerah zawo ya tsaya aman ma ya tsaya sai rashin ƙarfin jiki, Innoh kuwa ta ce ba zata iya wankin kashi ba dan haka jira take yi ta samu ƙwarin jikin ta sai ta tashi ta yi wanka da ruwan da Innoh ta zuba mata.

Sallamar Shamsu ce ta sanya Ameerah buɗe idanu da sauri tana wurga su zuwa hanyar shiga gidan, fatan ta bai wuce Allah ya sa kar ya shiga gidan ba saboda kar ya ganta a wannan mawuyacin halin da take ciki na amai da gudawa, Innoh ce ta ware murya tace masa,

"Kai shigo ciki dan wadda ka zo wajen nata bata da lafiya ba iya fitowa zata yi ba,"

Rasa inda Ameerah ta samu ƙarfin jiki tayi, tana tashi sai ta sungumi babbar butar da Innoh ta zuba mata ruwa dan shiga bandaki ta gudu bayin,tana shiga ta durƙusa tana maida numfashi, jiki babu ƙwari ta cire kayan ta ta hau wanka da ruwan butar, bata fito ba sai da ta gyara jikin ta tsaf,Innoh ce ta miƙa mata zani da hijabi tana faɗin,

"Kiyi sauri ki fito yaron nan na jiran ki,"

"To"

Shine kawai abinda ta furta ta d'aura zani ta sanya hijabi a jikin ta, kayan da ta cire ta d'ebo ta zuba a bokitin ƙarfe ta ja ruwa a rijiya ta zuba musu, Shamsu na zaune a tabarmar da Innoh ta shimfid'a masa, kallon Ameerah yayi yaga ta faɗa masa kamar wadda ta kwana rashin lafiya, maida kanshi ƙasa yayi yana jiran ta gama abinda take yi tazo su gaisa ya wuce kasuwa.

Bayan Ameerah ta gama dik abinda take yi ne taje inda Shamsu ke zaune ta ja kujera ƴar tsuguno ta zauna, kallon Inda Innoh ta zauna tayi dan taga ko zata tashi ta basu waje, sai taga Innoh bata da niyyar tashi, cikin ɗan haɗe fuska tace,

"Innoh ki ɗan bamu waje mana dan Allah,"

Washe baki tayi tace,

"Kayya ai da kun yi hirar ku hankali na ma na can wata duniyar,"

Tashi tayi ta shiga d'aki ba dan ta so ba, tana shiga ta maƙale a jikin labule ta kasa kunne dan ta ji me za a ce, Ameerah ta san halin mahaifiyar ta sarai dan haka hannun Shamsu ta kama a hankali suka shige d'akin ta suka rufe ƙofa, da jin haka sai Innoh ta kama baki ta damƙe tare da waro idanu waje,me yaran nan ke shirin aikatawa a gidan?

Shamsu kuwa na ganin haka sai ya hau washe baki yana murna, a zaton shi wani abu Ameerah keso su aikata shi yasa ta ja shi d'aki, suna shiga ta samu waje a katifar da mommy ta bari ta zauna tana satar kallon aljihun shi da ta hango damin kuɗi a ciki,gefen katifar ta nuna masa tace ma masa,

"Bismillah zauna ka tsaya kamar wani soja,ya kamata fa kayi ka kawo kuɗin lefen nan a samu a gama dik abinda ya dace, na matsu nima na ganni a ɗakin miji na kamar kowacce matar aure,"

Washe baki Shamsu yayi ya zauna a kusa da ita, wani irin wari yaji ya daki hancin shi, wari ne da ya kasa tantance daga inda yake fita a jikin Ameerah, cikin dabara ya janye jikin shi ya koma gefe yana zaro idanu waje, hannu ya sanya a aljihun shi ya ɗakko dubu ɗari ya miƙa mata yace,

"Ga wannan, dubu ɗari ne ki haɗa lefen ki, ni kuma zan yi amfani da kuɗin waje na na gyara shago na na ƙofar gidan mu na haɗa solar a dinga kawo caji ina yi wa mutane turin fina-finai da waƙoƙi saboda mu dinga samun na cefane,"

"Ai kuwa shawarar nan tayi kyau, dama ko shekaran jiya sai da Yah Sule ya gama mitar baka da aikin yi, to alhamdulillahi ga aiki ya samu,"

"Ai dama rayuwar nan komai a hankali ake gina shi, bari na je kasuwa naga yanda hali zai yi,kar ki manta a siyo turare da yawa a kayan lefen nan dan Allah."

"To ba zan manta ba Allah ya bada sa'a,"

Shamsu ne yayi saurin buɗe ƙofa ya shaƙi wata iskar 'yanci,hamdala yayi cikin sauri ya fita ya bar gidan, Ameerah kuwa cikin sauri ta zare dubu ashirin ta b'oye,kafin Innoh ta shiga ɗakin nata ta gama b'oyewa ta miƙe zata fita suka ci karo a hanya, kallon kallo suka hau yi wa juna, Innoh ce tace,

"Yanzu Ameerah iskancin naki har ya kai na ki ja namiji ɗa...."

Maganar tace ta maƙale a dai-dai lokacin da Ameerah ta zaro maƙudan kuɗi ta miƙawa Innoh,

Cikin sauri Innoh tace,

"Ko da yake ma mace da mijin ta ai kai bawa ba ka sa musu ido ba, wannan kuma na maye?"

"Na lefe na mana, yanzu ni dai dan Allah a kirawo Aunty Naja da Mommy su zo a san ya ake ciki ,na gaji da zaman gidan nan ina so a had'o kaya na dai-dai kud'in nan daga yau zuwa gobe a kai ni d'aki na,"

"Inshaa Allahu kuwa gobe a d'akin ki zaki kwana,ina zuwa,"

Waje ta fita ta ɗauki wayar ta ta kirawo Mommy ta kirawo Naja ta sanar da su abinda ke faruwa, alƙawarin zuwa suka yi dan su je kasuwa a had'o kayayyakin da suka sawwaƙa a kai Ameerah d'akin ta.

A can gidan Abdussabour kuwa tinda suka farka yake jin yunwa, jiya ya kawo dik wani kayan abinci da ya kamata ace suna da shi, amma da dare sai amsowa yayi a gida,da safe ma gashi bata dafa musu komai ba har tara na safiya yayi,hamma yayi yace,

"Baby yanzu ba kiyi mana abincin safe ba kike Maganar zaki je gida had'o lefen Ameerah? Kar fa ki manta ke amarya ce, dika-dika kwanan ki nawa ne da tarewa da zaki dinga fita anyhow? A washegarin ranar da kika zo gidan nan sai da na kai ki gidan ku, me yasa kike haka ne?"

Shagwab'e fuska tayi sannan ta kwanta a jikin shi tace,

"Haba baby yanzu wa Ameerah take da shi da zai yi mata irin wannan hidimar idan ba ni ba? Na zata kai a waye kake ba zaka damu da surutun mutane ba, sai dai kashhh gashi tin kafin wani ya magantu kai ka fara magana,a mota fa za ka kai ni ba wanda zai gammu,"

"Hummmm, to yanzu me zan ci idan kin tafi baki dafa min komai ba?"

"Idan ka ajiye ni sai ka wuce gida ka ci abinci ni kuma na ci a gidan mu ko?"

Tashi tayi ta hau shiri yana kallon ta, ita kuwa tana sane ta hau tub'e wa a gaban shi, dan ta san yanda jikin ta ke da matuƙar tasiri a wajen shi, ba kaɗan ba Abdul ke yabawa da surar Mommy shi yasa ko laifi tayi masa akwai zama na musamman da take yi ya wanke laifin ta, tin da aka yi auren nan kullum cikin ƙorafi yake, dai-dai da wajen da suke bacci bata san ta gyara ba balle ta share, gidan dik ya fara ƙura,'yan kwanukan da yake karb'o abinci a gida dik suna ajiye a sink bata wanke su ba.

Tana gama shiryawa tsaf cikin doguwar riga ɗaya daga cikin wanda Abdul ya siya mata wayar ta ta hau ringing, dubawa tayi taga Innoh ce,amsawa tayi ta kara a kunne, tana gama jin saƙon Innoh ta kashe wayar ta zazzage kayan ta dake akwati a saman gado ta ɗauka ta ce masa,

"Baby na shirya taso mu tafi."

"Wannan kayan da kika juye a nan fa?"

"Akwatin nake da buƙata, Innoh tace kud'in da Shamsu ya bayar na lefe ba zai isa a siyo da akwati ba, shi yasa zamu yi amfani da wannan a zuba mata kayan a ciki,"

"Mu je an sai mata wasu,"

Cike da murna Mommy ta maƙale shi tana sumbatar shi, abun ku da tsohuwar hannu tini ta mantar da shi fushin da yake yi na rashin cin abinci da bai ba, cike da so da ƙaunar juna suka rufe gida suka tafi gidan Ɗan liti..........

*Yau rubutun ba yawa saboda abubuwa sun min yawa a karanta da hakuri...masu tambaya daga farko ku min uziri an yi nisa da yawa ba zan iya sake turowa ba daga farko gaskiya,mai son karantawa daga farko dan Allah ta duba page ɗina na Facebook, ko wattpad ko WhatsApp channel d'ina na gode.*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
















RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨










*MAHREEN 1K*
*MAIDA TSOHUWA YARINYA 1K*
*KYAKKYAWAR FAHIMTA*














PAGE 55:










A shirye Mommy ta tarar da Naja tana cin ɗan waken da ya sha mai da yaji a gidan nasu, babu ko gaisuwa ta zauna tana faɗin,

"Washh Allah na, Innoh nima zubo min abincin in ci kafin mu wuce yunwa nake ji ko karyawa banyi ba kafin na fito,"

Kallon ta suka yi gaba d'ayan su cike da mamaki, yatsina fuska tayi tace,

"To ban girka ba, ko rannan ma daga gidan Sarki aka kawo min wanda Sule ya kawo muku, kin dai san ba wani girki na iya ba sosai,jiya ya kawo kayan miya har da su nama da kifi wai ayi girki, haɗe su nayi na jefa a fridge ba zan iya ba,"

"Kashhh amma dai Mommy an ji jiki, yanzu a kawo miki nama da kifi ki kasa sarrafa wa? To idan baki iya yanzu ba sai yaushe zaki iya? Kin ga muje mu dawo naje gidan naki naga abinda zan iya taimaka maki da shi, ke baki san akan girki ba kaɗai sai ku samu matsala da namiji? Tabdijam, a gaskiya Yaya wannan dik laifin ki ne,habaa yarinya kamar Mommy ace tana fad'ar bata iya sarrafa abinci ba kanta tsaye? Inaaaa ba za a yi haka da ni ba, maza ci ki tashi mu bazama kasuwar mu gama da can mu je gidan naki naga uwar da kike yi,"

Tura baki Mommy tayi tana ƙunƙuni tana juya ɗan waken da Innoh ta zuba mata, Innoh kuwa gum tayi da bakin ta, dan kuwa bata da abun fad'e, kuskure ne an riga da an tafka shi, yarinyar da take ganin tana baiwa wahala da aikin gida wato Saddiqa babu abinda bata iya girkawa ba sai wanda bata sani ba,idan saddiqa tayi girki har santi take yi, haka Ɗan liti ma har so yake ace Saddiqa ce tayi girki ko Yadikon ta.

A gaggauce suka kammala cin abincin su Ameerah ta fito sanye da hijabi da niƙabi wai zata bi su, babu wanda ya hana ta sai suka miƙe suka fita baki d'ayan su, a waje suka tarar da motar Abdul yana kwance ya lumshe ido saboda matsananciyar yunwar da yake ji,nan take Mommy ta saki salati tace,

"Laaa ni fa na ma manta tare muke da shi, gashi shima be karya ba,"

Wani mugun kallo Naja ta sakar wa Mommy sannan ta ja hannun ta ta mintsine ta, ƙara Mommy ta saki tana yarfe hannu, cike da jin haushi tace,

"Sokuwar banza kawai, ai sai mu koma ki shigo da shi a zuba masa abincin yaci kafin mu wuce, kaiiii ni dai Naja ina ganin tashin hankali yau,"

Cikin sauri ta ja hannun Ameerah suka koma ciki, a gaggauce ta samo kwano mai kyau aka zuba wa Abdul ɗan wake da mai da yaji aka nemo spoon aka saka masa aka kai soro, tabarma Ameerah ta shimfida sannan ta koma ta samo kwanon silver mai murfi aka zuba masa ruwan randa aka ajiye, Mommy ce ta shigar dashi soron tana ta zumb'ura baki tace masa,

"Bismillah, ni na manta baka karya ba sai da muka fito, dan Allah kayi hakuri,anjima zan yi maka girki mai daɗi idan mun dawo na yi alƙawari,"

Murmushi yayi ya ja kwanon ya bude, ɗanwake ne yayi masa sallama, yaƙe yayi mata dan kuwa baya cin ɗanwake, gudun kar tace ya raina wa gidan su sai ya ɗauki cokalin ya fara kai wa bakin shi da bismillah,yana fara ci a hankali ai ya ji ba irin wanda ya saba ci bane na flour wannan an yi masa had'in wake, dawa, da alabo,santsi da daɗin shi ne ya sa Abdul cinyewa tass ya yi hamdala dan kuwa baya jin zai iya shan wannan ruwan,hamdala yayi ya tashi ya karkad'e jikin shi yace su same shi a mota.

Mommy ce ta zauna a gaba Naja na bayan ta, Ameerah kuwa buɗe saitin bayan Abdul tayi ta zauna, da sauri Abdul ya juya yana kallon ta dan ganin me ta shiga dashi iskar motar ta sauya nan take? Gani yayi hannun ta babu komai sai wata ƙaramar baƙar leda, jinjina kai yayi da ya gane tsabar tsagwaron warin jikin tane haka, Naja ta gane dik abinda ke faruwa dan haka sai taji kunya duk ta kama ta, banda harara babu abinda take zabga wa Ameerah har suka isa kasuwa.

Bayan fitar Ameerah da Naja ne Abdul ya baiwa Mommy kuɗin da za su sai akwati da nashi gudummawar, godiya ta dinga yi masa sannan ta fita ta same su, Naja tayi wa bayanin komai sannan ta tabbatar mata da tace masa ya jira su su gama siyayya ya maida su gida.

Bata gama rufe bakin ta ba Abdul yayi mata waya, murmushi tayi ta dauka ta kara a kunnen ta, cikin wata iriyar murya taji Abdul yace,

"Baby zan wuce gida ciki na na juya min, zan aiko Sultan ya ɗauke ku idan kun gama,"

Kafin ta bashi amsa ya kashe wayar shi saboda yanda cikin shi ke juya masa, tunawa yayi da kodai Ameerah ce tayi sakun ɗan waken da ya ci dazu a gidan surukan nashi? Wani yunƙurin amai ne ya taso masa ya kulle motar ya bata wuta ya bar kasuwar a guje.

Abdul bai tsaya a ko ina ba sai a gidan Sarki, yana isa ya tarar da gidan an cika da mata ana ta hira, d'akin shi ya shige ya wuce band'aki ya hau kwarara amai, yana tsaka da amai yaji zawo ya kama shi, da gudu ya cire wandon shi ya hau saman toilet ya hau zazzage cikin shi, ya jima yana zawo da amai kafin ya samu salama ya yi wanka ya gyara wajen ya fito a daddafe,a gado ya kwanta yana maida numfashi,da kyar ya tashi zaune ya janyo first aid kit ɗin shi ya buɗe ya ɗauki maganin amai da gudawa ya sha da ruwan roba sannan ya koma ya kwanta yana numfashi da kyar, bacci ne mai daɗi yayi gaba da shi cikin salama.


A can kasuwa kuwa siyayya ta yi siyayya sai Ameerah taga Naja na kwasar turare da tooth paste da brush, murmushi tayi tace,

"Kamar kin san kuwa se da Shamsu yace a sai turare da yawa,"

Tsaki Naja tayi ta banka mata harara tace,

"To ba dole ba Ameerah, kin kuwa ji warin da kike yi? Ban taɓa jin irin warin nan ba tinda uwa ta ta kawo ni duniya, haba Ameerah, me yasa kike yin abu kamar ba mace ba? Ki duba ki ga yanda Mommy ke zuba gayu, dik inda ta zauna sai ƙamshi ya kama wajen, ko abu ta riƙe sai kin ji ƙamshi a jikin shi,gaskiya yanzu ne na san Yaya ta tafka kuskure, ko me muke so mu zama ko mu samu sai fa mun taimaki kammu,"

Shiru suka yi gaba d'ayan su dan kuwa daga Naja ta gama da Ameerah sai ta koma kan Mommy, a haka suka gama siyayya wajejen ƙarfe biyu na rana, mommy na kiran Abdul sai taji wayar na ta ringing amma ba a ɗauka ba, ƙarshe har sun yanke shawarar yaran dake musu dako su samo musu adaidaita su hau, sai ga kiran Sultan ya sanar dasu inda yake, Ameerah tafi su sanin kan kasuwar ita ta ja su suka tafi, a daidai wannan lokacin rana ta sake dukan Ameerah ita kanta da kyar take shaƙar jikin ta,gudun tafka abun kunya kar Sultan yaji warin da take yi sai tace su yi gaba akwai inda zata je,Naja ce ta fara faɗa ko kula ta Ameerah bata yi ba ta wuce.

Da kuɗin hannun ta ta koma kasuwa ta hau siyayyar banza da wofi kawai dan ganin tana da kuɗi,ba tare da ta yi tunanin adana su ba ko a gaba za su yi mata amfani ta kashe dubu takwas sannan ta ɗauki hanyar gida a ƙafa ta lungunan da ta saba bi,samarin ta na da ta dinga gani ta cikin niƙabi tana murmushi ita kaɗai har ta isa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login