Showing 33001 words to 36000 words out of 276165 words
Chapter 12 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
goma,"
Cikin zaro ido da nuna tsantsar kwad'ayin abun duniya Mommy tace,
"Dan Allah fa? Yanzu kawai dan tana matsayin ruwa biyu sai ta yi kuɗi haka? Ohhh dama nima iyaye na 'yan wata qasar ne da na samu kuɗi masu yawa"
Dariya sosai Billy tayi kafin tace,
"A gaskiya Mommy da sauran ki, ke yanzu wa ya ce maki ruwa biyu na haihuwar qasar waje ake nufi? Babu komai da sannu zaki gane yaren namu yanzu dai abinda ya fi mahimmanci shine kafin lokacin da za a yi maki zafafan hotunan da za a ɗora a sabon account ɗin ki na social media da za a buɗe miki dole ne ki gyara rayuwar ki, wannan sakin bakin da kike yi duk ki dena, bakin ki kadarar ki ce a hankali zan koya maki yanda zaki sarrafa shi ina fatan ba zaki yi min musu ba a dikkan abinda na sanya ki yi har ki k'ware?"
"Ni kam Billy me zai sanya ni yi miki musu? Ai na ji na bi ne a tsakanina dake, me son ka ne kaɗai zai jawo ka wajen harkar samu, ba zan gaji da yi miki godiya da fatan alkhairi ba Billisious 'Yar Sanata"
Dariya suka yi suka tafa sannan Billy ta shiga nuna mata followers ɗin ta da comments ɗin mutane akan shigar ta da yanda take sanya kaya masu tsada da hawa motoci masu numfashi.
"Yanzu na sake ganewa duk motocin nan da kaya da gida wasu na qarya neeee wasu kuma gaskiya ne,"
"Yauwaa 'yar gari, ashe kin gane, nan gaba ma zaki fi gane ya harkar take, tinda duk sanda ki ka samu had'ad'd'un gayu masu ji da nera suka fara huld'a da ke ba sai an ce maki nan wajen yana da kyau ba tsaya a cire maki hoto hajiyata"
Dariya suke ta yi kafin Billy ta dura wani shaqiyyin ashar ta tashi zaune tana duba wayar ta............
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 12
"Billy me ya faru kike zabga irin wannan ashar ɗin haka? Hotunan...."
"Kin ga Mommy ki kwanta ki yi bacci sai da safe zamu yi magana, kar kuma ki fito duk hayaniyar da zaki ji"
Cike da mamaki Mommy ke bin Billy da ta fita a hayyacin ta da kallo, Billy kuwa cikin tsananin ɓacin rai ta bar d'akin ta sauka qasa, kwance ta ga Hajiya K'waisa a jikin saurayin ta suna hirar su ta soyayya, sai shagwab'a take zubawa kamar bata da wata damuwa a duniya da ta wuce na ta faranta wa wannan kyakkyawan matashin rai.
Rasa ta inda zata fara nuna mata wannan hotunan Billy ta yi, da kyar ta samu natsuwa ta shige ta ta yi gyaran murya, a tare dikan su suka juyo suka bada hankalin su ga Billy, cikin murmushi da sakin baki irin na wanda ya sha barasa ya bugu Hajiya K'waisa ta kalli Billy tace,
"Laaafiyaa ki ka dawo ? Na zaci ma kun yi bacci ai duba da cewa yau kun gaji da yawa"
"Hajiya ko zaki iya tasowa ki ga wani abu yanzun nan? Ya na da mahimmanci ki gan shi yanzu yanzun nan,"
Da jin haka Hajiya K'waisa ta san tabbas wannan abun da Billy ke magana akai na da mahimmanci,dan haka sai ta tashi zaune da kyau ita da saurayin ta,ta yi wa Billy izinin ta isa gaban ta dan ta sanar da ita abinda take son sanar da itan, cikin ɗari-d'ari Billy ta isa gaban ta ta buɗe wayarta ta nuna mata hotunan da ta gani suna yawo a social Media,wata qara Hajiya K'waisa ta sanya tare da dukan table ɗin da ke gaban ta sannan ta ce,
"Ni Any za ta yi wa irin wannan cin amanar? Hotuna na da dana yarda da ita na aminta da ita ta ɗauke ni su zata baza wa duniya ta gani bayan ta yi min k'wacen fiancé d'ina ta bar qarqashi na? Lallai qarshen Any ya zo Billy, idan ban gama da yarinyar nan ba maganar mutane ta tabbata akai na uwata zina ta yi ta haife ni bani da uba,Allah ka tsinewa ranar da na san yarinyar nan, Allah ka tsinewa ranar da na jawo yarinyar nan a jiki na maida ita mutum har ta samu damar yaudara ta irin haka, Billy d'akko min makullin mota,"
Da sauri saurayin ta ya kama ta ya riqe gam a jikin shi yana lallashin ta,
"Baby calm down na ehhh ! Kar ki tada hankalin ki haka akan wannan abun, dan ta sanya tsofaffin hotunan ki a social media se me? Waye be san ki ba dama? Hakan ya rage maki masoya ne ko me? Kin san yanzu videos ɗin ta basa trending so take ki kula ta ki yi mata raddi ta yi going viral saboda ke ɗin shugaba ce kuma abar koyi ce a wajen qananan asshoshi irin ta,sannan ke kin san a kaff social media platforms ɗin nan ana ji da ke kin sani ko baby? To shiru ma magana ce ki kyale ta kar ki kula su, sannan yanzu idan kin je gidan ta duk abinda ya same ta ke za a zarga, ki kyale ta muna nan zata kawo kan ta da kan ta a lokacin ne ni da kai na zan taya ki salwantar da rayuwar ta"
Kuka sosai Hajiya K'waisa take yi ta na zage-zage, gashi Billy da saurayin ta Samuel sai danne ta da bata baki akan kar ta yi retaliating ta kyale maganar suke, kwalbar barasa ta buɗe ta d'aga sama ta kafa a bakin ta ta dinga kwankwad'a, bata ajiye ba sai da ta sha mai yawa, a nan Hajiya K'waisa ta gama koke-koken ta da zage-zagen ta ta yi bacci, Samuel da Billy ne suka tallabe ta suka kai ta d'akin ta suka kwantar,Sam yaso k'warai ya kwana da ita dan ɗebe mata kewa amma yana da tafiya a gaban shi, dama sallama yazo yi mata, kuɗi ya ajiye mata masu yawa in dollars ya yi gaba.
Ko ta kan kud'in Billy bata bi ba ta hau cire wa Hajiya K'waisa kayan jikin ta dan ta ji daɗin bacci, tunawa da gargad'in Samuel kafin ya tafi ne ya sanya Billy murmushi,
"Aikin banza wai lalle a mazaunai ni me zan yi da ita? Ai wannan sai kai dama, shashasha kawai"
Tsayawa ta yi ta qarewa Hajiyan tata kallo bayan ta cire mata makeup da gashin kanta, dariya ta tintsire da ita sannan ta ce,
"Waiiii sunan wani abu wai shi siddabaru in ji masu sihiri,"
Ajiye komai a inda ya dace ta yi sannan ta rufe d'akin bayan ta kashe mata fitila ta koma nata d'akin ta kwanta tana maida numfashi,
"Kaiiii ina buqatar wanka da ruwan d'umi mai kyau, kyawun ta yanda na gajin nan Man na nan, amma ba komai zamu haɗu anjima ta TikTok, wataqila ma yana can yana jira na,"
Wanka ta faɗa ta jima a cikin ruwan d'umi ta na gasa jikin ta dan har bacci ma ya fara ɗaukan ta ta buɗe idanun ta sannan ta fita daga kwamin wankan ta d'aura towel ta koma cikin d'aki,sai da ta tsane jikin ta sannan ta kunna laptop ɗin ta ta shiga TikTok ta danna Kiran Man ta tarar yana jiran ta kamar yanda ta yi zato.
A gaban shi ta dinga shafa mai ta na juyi shi kuwa yana daga can gefe ya na screen recording ɗin video ɗin da suke yi, ganin hirar tasu ta qazanta ne ya sanya ni rufe musu qofa na koma d'akin Mommy,ina shiga na tarar da ita ta baje a gado ta na ta neman inda za ta ga wannan hoton da ta fara gani a wayar Mommy, hoton ya yi mata kama da ta san fuskar amma ta rasa a ina ta san fuskar.
Duk duban ta bata gano inda zata ga wannan hoton ba, dan kuwa ita bata TikTok datar da take sanyawa qarama ce watarana ma da wannan App ɗin take amfani wanda ake kira da d'an mukulli wato free data da ita take WhatsApp, dan haka gajiya ta yi da bincike a Facebook ta kashe data ta saki wata hamma mai tsaho ta na tuna sanda Billy ke yi mata albishir ɗin gobe za su je a sauya mata sabuwar waya, sannan ta fara lumshe ido ta kwanta.
Cikin zuciyar ta take ayyana,
'Ban fa yi sallah ba,anya ba zan daure na tashi na yi sallah ba yanzu?.....kai bari na bari da asuba na haɗe su yanzu bacci nake ji, naga ma tunda na zo ba wanda na ga ya kai goshin shi qasa a gidan nan mutuwar yawa kuwa Kaka ce'
Sake muskutawa ta yi ta kwanta da kyau ta ja bargo saboda sanyin AC dake ratsa ta, a haka Mommy ta kwanta ba tare da ta rama sallolin dake kan ta ba,ta bar su sai gobe ta yi su dika da asuba.
A can d'akin Billy kuwa bata samu kwantawa bacci ba sai qarfe uku na dare, dan kuwa bayan hira da suka sha da Man transfer na kuɗi masu yawa ya yi mata, daga baya ta yi qarar account ɗin Any domin a rufe shi sannan ta kwanta bacci ba tare da ta tuna sallah ba balle ta yi ta.
************
Washegari da safe ba wanda ya farka a cikin mutanen nan uku da asuba balle har a yi maganar sallar asuba ɗin, mommy ce ma ta farka qarfe goma na safe ta yi wanka ta wanke bakin ta sannan ta yi alwala ta rama sallolin ta, wanda dika raka'a biyu ta dinga yi wai qasaru take yi, sannan daga qarshe ta yi asubar wannan ranar ta tashi, Hajiya K'waisa kuwa da matsanancin ciwon kai ta tashi saboda giyar da ta kwankwad'a a daren jiyan,dan haka Sallau ya yi mata had'in hangover ya kai mata ta sha ta na yatsina kamar ta na shan magani, daga qarshe ta tashi ta shiga wanka ta gama ta fito ta yi shafe shafen ta da tsara kwalliya kamar ba abinda ya faru a daren jiyan.
A d'akin ta ta yi breakfast sannan ta ɗauki makullin motar ta ta fita ba tare da ta sanar da kowa inda ta tafi ba, tinda Mommy ta idar da sallah ta ke hamma dan kuwa yunwa take ji sosai,tunani ta fara yi shin kayan jiya zata mayar jikin ta tunda basu yi datti ba kuma sababbi ne, ko wasu zata saka a jikin ta, ko kuma a cikin nata nada da tazo da su zata saka ta fita cin abinci?
Rasa wanne zata sanya ta yi kafin hankalin ta ya ɗauku wajen wata riga kalar rawaya nan take ta ɗauka ta sanya ta a jikin ta,dan kuwa rigar bata da nauyi gata mai kyau da ɗaukan hankali,ta na sanyawa kuwa rigar ta zauna das a jikin ta kamar an auna ta, ga kalar ta bi fatar jikin ta ta yi kyau, kallon kanta a qaton madubin da ke gabanta tayi,nan take ta yi juyi sannan ta kalli gashin dokin da aka haɗe da nata ta ga yanda ya kwanta a kanta kamar asalin nata,murmushi ta yi ta maida leb'unan ta ciki ta tsuke su,a hankali ta sake su sannan ta qara gyara su ta busowa kan ta sumba, ta na nan tana shiririta har sha biyu da mintuna biyar suka wuce, murd'a qofar d'akin ta aka yi aka shiga, Billy ta gani sanye da guntun wando da guntuwar riga kan ta sanye da hula irin wadda ake sakawa idan an sanya gashin doki,zama tayi a saman gadon Mommyn ta na qarewa halittar mommyn kallo da kyau,cikin ranta take yaba kalar fatar Mommy da kyawun dirin ta, bakin ta ta kalla ta ga yanda take wani tsuke shi tana yanga,murmushi Billy tayi tace,
"Ko ke fa, haka kawai da ki dinga wani sakin leb'e kamar ganda, mu je mu karya, na ga Hajiyata ma ta fita da alama asibiti zata je,"
Tashi tayi ta yi gaba Mommy na biye da ita, har sun kusan sauka daga bene Mommy tace,
"Hajiyan bata da lafiya ne da zata je ganin likita?"
"Ba abinda ya shafe ki bane, yanzu dai ki zo mu karya muna da abubuwan yi da yawa, dan ma Allah yasa ki na son wannan harkar a ran ki kuma dama kina da sha'awar harkar hutu samun dama ne baki yi ba, sai sauqaqa min aiki na kike yi,"
"Habaa Billisious 'Yar Sanata, waye baya son hutu? Ai duk wanda yace maki baya son hutu a rayuwar nan karya yake yi ko wanene shi, kawai dai ya dangata da hanyar da mutum ya zab'a ya huta."
"Hakane kema kin ce wani abu....Zubaida ba zaki kawo mana abincin bane ? Ko sai na zo na ɗauka da kai na ne?"
Cikin bada umarni da b'acin rai Billy ke magana, wanda hakan ya sanya Mommy sake gyara zaman ta, dan kuwa bata son ganin wannan zubaidar kallon da take yi mata na sa ta ji ta a muzance kuma a qasqance.
Cikin haɗe girar sama da ta qasa Zubaida ta shiga ɗauke da abincin su, ta na ajiyewa ta juya ta ci gaba da d'akko sauran, saida ta gama ne ta hau zuba musu, cikin ladabi ta kalli Billy tace,
"Ki yi hakuri Aunty na ga baku tashi da wuri bane shi yasa ban kawo ba gudun kar ya yi sanyi tunda baki son abinci da sanyi"
Hannu kawai Billy ta d'aga mata, sannan Zubaida ta bar wajen, Mommy ce ta saki murmushi bisa hango kanta da tayi ta tana zuba nata mulkin a gidan.
A haka suka ci abincin su suka tashi sannan suka koma sama, Billy ta shirya suka fita siyan waya da ta yi wa Mommy alqawari, ko da suka shiga shagon sai Mommy ta ga Billy suna hira da mai shagon kamar wasu qawayen juna anan ta kula da matar ta qi yarda yaran shagon su karb'i kuɗi wajen Billy,bayan sun gama da wajen wayar ne za su tafi matar tace,
" 'Yar sanata wannan babban kifin fa?"
"Qawata ce,sai anjima bari mu je muna da abubuwan yi sosai"
"Na ga alama"
A hanzarce suka bar shagon har sai da mommy ta tambaye ta wacece wannan ɗin,
"Itama ɗaya ce daga matan da Hajiyata ta taimaka wa a lokacin da suke tsananin buqatar taimako, daga baya ta samu wani saurayi ɗan siyasa mai kud'in gaske yake shagwab'a ta da nera, yanzu haka tana da manyan shaguna na saida kayayyaki kala-kala guda huɗu a garin nan ɗaya a Abuja, wannan wayar ma kyauta ta baki gashi nan sai a yarda wannan akwalar,"
Cike da zumud'i Mommy ta karb'i k'walin tana duba wayar tare da qudirin idan sun je gida a yau zata buɗe duk wani social media da a baya bata samu damar bud'ewa ba saboda rashin isasshiyar data,juyawa ta yi ta kalli Billy da ke tuqi cikin k'warewa tace,
"Amma me yasa naga kina sauri baki so ki gabatar dani sosai a wajen ta"
"Duba da abinda ya faru a daren jiya kaɗai ya isa ya sa ki gane a bariki baka yarda da kowa, kanka kaɗai ka sani a duk inda ka shiga"
Shiru mommy tayi kafin tace,
"Yauwaa dama ina so na tambaye ki game da abinda ya faru jiya, hoton wa...."
"Dan Allah tambayoyin sun isa haka Mommy,ko dai barin wannan harkar zaki yi ne ki fara aikin jarida?"
Tsuke baki Mommy tayi bata sake cewa komai ba amma fa zuciyar ta cike take da tambayoyi masu tarin yawa.
Ko da suka isa gida sun tarar da gidan shiru kamar babu kowa, ba tare da tunanin komai ba Sallau na buɗe musu qofar shiga gidan suka shiga ciki,Mommy na sanya qafar ta ciki tayi tozali da abinda ya kusan sanya ta fad'uwa qasa warwas............
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH
PAGE 13:
Da sauri mommy ta qara kutsa kan ta cikin gidan dan son tabbatar da abinda idanun ta suka gane mata,direct wajen motsa jikin da aka keɓance a cikin babban parlourn qasan ta nufa, hannu ta sanya ta na nuna mutumi/matar da ke gaban ta tana motsa jiki hankali kwance cikin rausaya da rangwad'a irin na mata, pod ne manne a dika kunnuwan ta dan haka bata san ma su Mommyn sun shiga ba sai da ta kashe injin da take motsa jiki a saman shi zata sauka ne tai ido biyu da mommy da ke tsaye cikin tsananin mamaki,
"Qalu Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ! Meye haka zaku shigo wa mutane waje babu sallama se kace gidan arna,gaba daya ni kun firgita ni, ke Billy kin duba TikTok kuwa? An sauke account ɗin waccan matsiyaciyar,"
"Eh na duba Hajiyata ai jiya ban kwanta ba sai da na tara abokan arziqi muka yi reposting account ɗin ta, na san shine dalilin sauke mata shi da aka yi,"
"Ke hangai rufe bakin, ki samu waje ki zauna Sallauuu kawo mata juice da alama qishin ruwa take ji ko kin gajiyar da 'yar mutane tunda ke dai ba kya zama waje ɗaya"
Rintse ido Mommy tayi tare da sanya hannayen ta dika biyu ta dafe kan ta, shin wa take gani ne wai haka? Dama mafarkin da ta yi a daren jiya ne zai zame mata gaskiya?
'Sanye take da rigar bacci ta fita kitchen shan ruwa ta ga namiji ya fito mai kama sak da Hajiya K'waisa, hakan ya yi matuqar razana ta har ya yi sanadiyyar zubewar ruwan da ke hannun ta, garin ta gudu sai santsi ya ɗebe ta ta faɗi a cikin ruwan wannan namijin ya zo ya tsaya akan ta ya na ta sheqa mata dariya hannun sa ɗaya riqe da qugun sa, ɗayan kuma yana kurb'ar lemo a glass cup'
Da sauri ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka ta karb'i cup ɗin juice ɗin da Sallau ya miqa mata ta kafa baki ta kwankwad'e tare da faɗin,
"Babbabani ruwa"
Dariya Hajiya K'waisa da Billy suka sanya a tare sannan Hajiyar ta ɗauki wayoyin ta ta kalli Mommy, irin kallon nan na sama da qasa ta na yi ta na taunar chewing gum, sannan ta sa kai tana rausaya qugun ta ta wuce sama,nan take Mommy ta hau hango Hajiyan a cikin kayan mata na alfarma da manyan sarqoqin zinare da take zubawa ta yi kwalliyar da ko wata macen ba zata iya irin ta ba, cikin kad'uwa Mommy ta furta,
"Na shiga uku ni Hadiza me zan gani? Dama Hajiyar taki ba mace bace namiji ne? D'an