Showing 225001 words to 228000 words out of 276165 words

Chapter 76 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

yanzu goma saura minti biyar,sai ki sha magani kiyi bacci ni kuma zan koma gida akwai abubuwan da zan gudanar kafin ranar da za a kama Alhaji ta yi"

"To na gode,gobe idan zaki zo fura nake so."

"Allah ya kaimu, baby akwai son shan daɗi,ohhh Bilkisu ba baby ba ko?"

Murmushi suka yi a tare, Any ta fita ta kirawo nurse aka yiwa Billy allura,sannan aka bata magunguna ta sha,babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta, Any tafiya tayi bayan ta tabbatar da ana baiwa Billy kulawar da ta dace.

Bayan ta isa gidan ta, dik wani inda films ɗin batsa yake a gidan nata ta tattara ta zuba a kwali,wasu kwalaben giya ne da kayan maye dik ta tattare su waje ɗaya,ɗakin ta ta shiga ta hau fito da sex objects ɗin da ta siya domin jin daɗin ta da abokan harkar ta ta kwaso su tayo waje dasu ta tara dika a ɗaki ɗaya,ta yi ƙudirin a lokacin da aka kama Alhaji komai ya lafa zata ƙona su,dan yanzu da ta fitar dasu ana iya samun wani magulmacin ya sanar da Alhaji abinda ke faruwa a yaran ta tinda dai harkar bariki ta sani babu amana,yana sanin ta bar harkar da suke yi zai kai ƙarar ta gaba su illata ta,gwanda kawai ta samu a kauda shi.

Shiri ta fara yi da kyau dan tarbar ranar da za su haɗu a club da Alhaji, bata kwanta bacci ba sai 2 na dare,bacci take yi cike da mafarkai kala-kala,babu mafarkin da ya firgita ta ya ɗaga mata hankali da ya wuce mafarki da Arica da tayi cikin wani irin mawuyacin hali,a gigice ta farka ta shiga banɗaki ta yi alwala ta fito,sallar nafila ta yi kafin ta yi addu'a ta zauna tana tunanin rayuwar da ta bari da kuma wadda take fatan ta gina anan gaba.


***************************

Da ƙyar Abdul ya sanar da Huzaimah abinda ya sanya shi kwantawa a asibiti, sannan ya roƙe ta da ta sanar dashi gaskiya idan zata iya zama da shi a haka, Huzaimah ta yi kukan baƙin ciki domin kuwa ba ƙaramin tausayi Abdul ɗin ya bata ba, dan haka sai tace masa,

"Na amince zan aure ka a haka,Allah ya baka lafiya,inshaa Allahu zaka samu sauƙi watarana baza ka dawwama a haka ba."

Abdul ya ji dad'in amsar da ta bashi sosai, dan haka sai kawai aka ci gaba da shirin biki, Huzaimah kuwa ta kame bakin ta ƙam bata sanar da kowa ba a dangin su ga abinda ke faruwa,sai dai kowa ya kula da rashin walwala da ke damun ta a ƴan kwanakin, wanda suka ta'allaƙa hakan da gabatowar bikin ta,sai kawai iyayen ta suka maida hankali wajen gyara amarya,har tsoron shan wasu daga magungunan matan da ake bata take yi, saboda ga lalurar da mijin ya sanar da ita yana dauke da shi,su kuma a ganin su zata je gidan kishiya dan haka dole ne ta sha maganin mata ta bugu dan kar a fita fada a wajen miji.

Innah Laminde kuwa da ta ji labarin ta yi Allah wadai da abinda Mommy ta aikata sannan sun haɗa nemawa Abdul neman magani da na gargajiya,sakin da ya yi wa Mommy ne ya ɓata ran ta har ta sa Sultan ya kira mata shi a waya,suna tare da Bilal Sultan ɗin ya kira, dan haka sai kawai Bilal ya miƙa masa wayar,bayan ya Karb'a sun gaisa da Innar ne ta ce masa,

'Haba Sarauta,da girman ka da hankalin ka zaka saki mace cikin fushi? Ka manta da cewar ba a son a yanke hukunci a cikin fushi? Ai da ka yi hakuri sai daga baya a zauna a san irin hukuncin da ya dace da ita,saki ba shine mafita ba.'

"A yi min afuwa Innah amma ba zan iya ci gaba da rayuwa da Hadiza ba,baki ga yanda ta haukace ba a wannan lokacin,a gani na idan wuƙa aka bata zata iya rabani da raina kamar yanda take yawan faɗi,da in yi mata kishiya gwanda ta kashe ni,rabuwar mu ita ce tafi Innah."

'To tinda haka kace Allah ya kyauta,Allah kuma yasa hakan shine yafi zama alkhairi,yanzu ka sanar dani me ake ciki game da yaron ka? Dan ba zan bari ya taso a gidan Ɗan Liti ba,gida ne da babu tarbiyyar arziƙi kowa ya san da hakan.'

"Innah a dai yi haƙuri a bar mata shi,in dai ba ita ce ta dawo da shi ba da kanta."

'Kana ganin babu matsala zaman yaro namiji a hannun Hadiza SARAUTA?'

"Babu komai Innah inshaa Allahu."

'Ai shikenan,zamu bishi da addu'a,naji ma wai gidan su amaryar taka sun je jere sun ga kaya sai juyawa suka yi da nasu aka bar ƙalilan da za ta yi amfani da shi wanda babu a gidan.'

"Eh Innah, kayan sakawa kawai Hadiza ta ɗiba ai."

'To yaushe za a sallame ka?'

"Zuwa gobe Innah likitan yace zai sallame ni."

'Allah ya baka lafiya SARAUTA,Allah ya sa ka ci jarabawar rayuwar ka,inshaa Allahu da an sallamo ka ka taho gida za ci gaba da haɗa neman maganin dana gida,Allah ya sa a dace.'

"Amin Innah na gode a gaida mutanen gidan baki ɗaya,shekaran jiya ma ai mun gaisa da Mai martaba."

'Allah sarki ai baka ga yanda ya damu ba,Allah dai ya baka lafiya,mutanen gida kuma za su ji,sai da safe.'

Sallama suka yi Sultan na sake baiwa Innah Laminde labarin abubuwan da Abdul ya sanar dashi Mommyn ta yi masa,jimantawa tayi sosai sannan ta ce,

"Ai ta yi wa kanta,sai ta dawo ƙauyen ta zauna idan alalar zata ci gaba da saidawa bismillah."

Dariya ce ta ƙwacewa Sultan ya fita yana ta ɓaɓɓakawa kuwa.

Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya,yau gidan Sarkin garin Ba mugu sun tashi da farin ciki da annashuwar ɗaurin auren Yariman garin su wato Abdussaboor a karo na biyu,kowa ka gani cike yake da farin ciki,ango da abokin ango tare da ƙanin ango sun sha ankon farar shadda,sai da aka idar da sallar Juma'a sannan aka ɗaura auren Abdussaboor da Huzaimah akan sadaki nera dubu ɗari.

Hamdala Abdussabour ya dinga yi yana jin wani irin farin ciki na mamaye zuciyar shi,yana nan tsaye a bakin masallaci yana ta gaisawa da mutane ana taya shi murna ya hango Sule na tunkaro shi,nan take zuciyar shi ta buga ya tuna halin da yake ciki na rashin lafiya,yanayin da ya ga fuskar Sule a ciki ne ya daure masa kai ya sanya shi gyara tsaiwar shi yana jiran abinda zai je yazo.....................[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨










PAGE 91:










Bilal ne ya matsa kusa da Abdul ya ce,

"To ga fa ɗaya daga dangin marasa kan gado nan na tafe, ka gayyace shi ne dama ban da labari? Sultan ko kaine ka gayyaci tsohon surikin ku?"

Dariya Sultan ya gimtse saboda yanda ya ga Abdul na tsaye kamar a tsorace yake da ganin Sule,Sule kuwa na ƙarasowa sai ya saki murmushi har wawulon shi ya bayyana,sannan ya miƙawa Abdul hannu yana taya shi murmar auren da ya yi,wata iriyar muguwar dariya ce ta kama Bilal da Sultan saboda ganin wawulon Sule a bayyane kamar ƙofar shiga gari, shi kanshi Abdul sai da ya murmusa dan ganin wawulon da Sule ke dashi a cikin manyan haƙoran shi,da sauri Sultan da Bilal suka bar wajen suna sheƙa dariya,hakan ba ƙaramin ƙona ran Sule ya yi ba kuwa, ƙwafa ya yi sannan ya ce,

"Ba laifin ku bane, laifi na ne da na zo taron da ba a gayyace ni ba, dama anan nima nayi sallar Juma'a,kuma naji sanda aka ɗaura auren shi yasa na tsaya na taya ka murna,sai anjima Allah bada zaman lafiya."

"Kayi hakuri dan Allah,Bilal bashi da hali sam lamarin shi sai addu'a,na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, a gaida mutanen gida."

Sule na jin haka sai ya saki ran shi,daga baya ya yi wa Abdul sallama ya wuce gida,yana zuwa ya tarar da Ameerah ta zo,wanda da alama ma zuwan ta gidan kenan,dan kuwa a tsaye ya ganta tana cire mayafin ta zata yafa a igiya, tana gama yafawa ta hau ƙoƙarin kunce goyon ta, kayan jikin ta atampa ce riga da skirt sun karɓe ta ta yi kyau shar da ita,ita da yaron ta sun sha wanka sun yi fess da su,cikin masifa ta ce,

"Iyyy fa,wai na shirya muje biki gidan sarki nace ba zan je ba ko da a gidan shugaban ƙasa ake yi kuwa,in bama rainin hankali ba dan Allah ta yaya za ta kalle ni tace min wai naje bikin ɗan ƴar'uwar ta,yo ina ruwa na da su ni?"

Mommy ce ta share hawayen ta ta yi murmushin yaƙe bata ce komai ba sai ta karb'i yaron Ameerah ta zaunar da shi a ɗaya cinyar da ke kallon Amir ɗin ta,gani tayi Amir yafi yaron Ameerah ƙiba sosai da kuzari,sai ta kalli kayan jikin shi,kaya ne masu kyau amma basu da wani tsada,kallon Ameerah tayi ta ga har wata ƙiba tayi alamar tana cikin kwanciyar hankali da lumana a gidan auren ta,hawaye ne ya sake gangaro mata,domin kuwa Ameerah da ta raina gashi yanzu ta fita matsayi,tinda ko babu komai ita tana zaune a ɗakin mijin ta,ga kuma ɗan ta nan tare da uban shi.

Cikin sanyin murya Ameerah tace,

"Dan girman Allah ki dena kukan haka ya isa mana,Innoh ma gata can a ɗaki ina jiyo tarin ta da alama kukan take yi, shikenan akan namiji ɗaya sai ku maida gida ya koma kamar gidan makoki?"

Waje Sule ya samu ya zauna kafin ya ce,

"Ah toh dai faɗa musu,Innoh tin da aka sanar da ita labarin mutuwar auren nan take kuka tare da yiwa Baba masifa wai yaje ya hana auren, ta yaya zai hana auren da ba haramun bane? Baiwar Allah'n nan Baaba na ta ƙoƙarin kwantar masu da hankali dikan su Innoh ta sata a gaba da cin mutunci jiya sai da ta zubar da hawaye tana faɗin da ta sani tayi zaman ta gidan Alhaji,yanzu haka yau tin safe bata fito waje ba saboda ɓacin rai, na rasa yaushe ne ranar da Innoh zata ɗauki girman da Allah ya baiwa Baaba ta bata,kullum cikin raini da gatsali da rashin kunya take yi mata magana."

"Humm Allah ya kyauta kai dai Yah Sule,ina Baba ya tafi Innoh na cikin damuwa? Ai ya kamata ace ya zauna ya lallashe ta ko?"

"Ke fa Ameerah har yanzu baki da cikakken hankali,idan ya zauna a gida be fita nema ba ke zamu dafa a gidan?"

Zumb'ura baki Ameerah tayi kafin ta ce,

"Yah Sule kaima fa yanzu ya kamata ace ka fara aikin gwamnati ko kasuwanci,nan nan aka ce ka yi aikin koyarwa tin sanda ka gama makarantar ka fir ka ƙi, to yanzu gashi gotai-gotai da kai kana faɗin wai idan Baba be fita ba ni za a dafa,wannan ai abun kunya ne."

"Inshaa Allahu Ameerah komai zai sauya, Sulen da kika sani a baya ba shine a gaban ki ba yanzu, da na samu jari na halal zan kafa kasuwanci,sannan zan sake neman aiki a primary ɗin garin nan na ga ko za a dace,yanzu haka ina da kuɗi amma bana son gina kasuwanci na da kud'in haramun."

Cikin wani irin yanayi Mommy ta kalle shi tana neman ƙarin bayani,a ruɗe Ameerah tace,

"Yah Sule sata kake yi ne da kake tsoron taɓa kud'in haram?"

Hararar ta ya yi sannan ya miƙe zai shiga ɗakin shi,yana gaf da shiga ɗakin ya tsaya sai ya fasa ya nufi ɗakin Baaba,ya jima yana Sallama kafin ta amsa masa da ƙyar ya shiga,yana shiga ya ganta kwance magashiyan tana rawar sanyi, cikin sauri Sule ya ɗago ta yana jijjigawa,maida ita ya yi kwance ya fita da sauri waje yana k'wala wa su Mommy kira,kafin su isa ɗakin Sadeeq ya dawo daga makaranta, jakar shi ya wurgar ya afka d'akin dan yaga me ya gigita Sule ya fito daga ɗakin Baaba yana k'walawa su Mommy kira, rawar sanyin da Baaba keyi ne ya firgita Sadeeq dan kuwa bai taɓa ganin tayi irin haka ba, a gaggauce ya miƙe ya ɗakko babban bargo daga ɗakin Baaba ya rufe ta dashi,kamar wadda aka rufawa garwashi a lokacin tsananin sanyi haka ta cafke bargon ta sake ƙudindinewa a ciki,murya na rawa Sadeeq yace,

"Baaba ki yafe min dan Allah, da nasan baki ji sauƙi ba da ban tafi makaranta ba,sannu Allah ya baki lafiya,bari na kirawo Alhaji na sanar dashi idan yaso ko asibiti ne sai a kai ki."

"Ah ah Sadeeq kar a kirawo Alhaji,ai sai a d'aga masu hankali,bari a kirawo Baba sai ya sanya ta a mota a kai ta asibitin,idan yaso daga baya sai a sanar dasu."

Cikin sauri Sule ya hau neman wayar Ɗan liti, cikin sa'a kuwa ya same shi,nan take ya sanar da shi dik abinda ke faruwa,Ɗan liti kuwa yace gashi nan dama yana hanyar dawowa daga kano ne ya ajiye fasinja ya ɗebo wasu.

Kafin yazo Mommy ta goya Amir ta sauyawa Baaba kaya,Innoh na ɗaki har a wannan lokacin bata fito ba dik kuwa da cewa an sanar da ita halin da Baaba ke ciki,Ameerah ce ta zauna ta dinga zazzaga mata masifa kamar ita ta haife ta,cikin tsananin ɓacin rai Ameerah tace,

"Ni fa Innoh har yau na rasa gane baƙin cikin me kike yi da Baaba,a kullum baiwar Allah'n nan bata da burin da ya wuce na ta faranta mana rai mu ƴaƴan ki,sannan ta zauna dake lafiya a matsayin ki na matar ƙanin mijin ta, amma kin ƙi ki zauna da ita lafiya,yanzu gashi can bata da lafiya,rashin lafiyar da bamu taɓa ganin tayi irin ta ba an sanar dake amma shine kike nuna ke babu ruwan ki da sabgar ta baza ki je ma ki yi mata sannu ba."

"Ba zan je ba ɗin dan uban ki,idan naje ɗin cire mata ciwon zan yi? In ce dai na yi mata addu'a Allah ya sawaƙe."

Baki sake Ameerah ke kallon Innoh da ta yi nisa bata jin kira,sallamar Ɗan liti ne ya sanya Ameerah miƙewa da goyon yaron ta ta yi waje, tana zuwa ta hau baiwa Ɗan liti labarin abinda ke faruwa, cikin sauri ya nufi ɗakin Baaba, yana zuwa sai ya cire bargon da ta rufa dashi ya ce,

"Uwata da Ameerah ku kamo ta a kai ta mota,idan baza ku iya ba Sule ɗakko ta mu je."

"Ai Baba inaga za su iya, ni kaina har yanzu ƙashin ƙafata bai gama dawowa dai-dai ba,ko ka manta halin da nake ciki?"

Da sauri Mommy da Ameerah suka duƙi Baaba Sadeeq na taya su suka kai ta mota,sanda suka ajiye ta a motar sai da suka kalli junan su,banda numfashi babu abinda suke saukewa,Baaba bata da wani ƙiba,mace ce irin ƴar firit ɗin nan,shi yasa da suka ji nauyin da take dashi suke mamaki.

Sule ne ya buɗe gidan gaba ya shige Mommy da Sadeeq suka zauna da Baaba a baya, Ameerah kuwa tana komawa cikin gida ta kwashi tarkacen ta tace gidan mijin ta zata koma dan bata ga me zata zauna tayi ba a gidan,dik Kiran da Innoh take yi mata akan taje ta ɗora masu abinci bata koma ba,tafe take tana mita da masifar halayyar Innoh.

A asibiti kuwa tashin farko ana gwada jinin Baaba aka gano ya haura sosai,dan haka magunguna da allurai aka yi mata aka ɗaura mata ruwa babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta,sai da aka gama komai Mommy ta biya kuɗin sannan suka kira Alhaji Baban Gida suka sanar dashi abinda ke faruwa,godiya ya yi musu sannan ya ce gobe yana nan tafe,bayan sun kammala wayar ne mommy ta kirawo Abbe ta sanar da ita,kuka Abbe ta sanya tana faɗin ta shiga uku ta lalace,da ƙyar Mommy tayi jarumta ta kauda tata damuwar ta baiwa Abbe hakuri,no Shalele kuwa Sadeeq ya kirata ya sanar da ita,fatan samun sauƙi tayi wa Baaba sannan tace tana nan tafe anjima.

********************

A cikin makeken resort ɗin Alhaji babban club ɗin yake,waje ne da ya ƙunshi sashe-sashe,akwai ɓangaren ɗakunan baƙi,sai wajen swimming pool da aka saka kujeru masu haɗe d rumfa da table kashi-kashi,wata iriyar wuta ce a wajen mai sauya launi ke haske wajen,gefe kuma wajen kaɗe-kaɗe ne an kunna kiɗa na tashi,sai can ciki inda bar ɗin shaye-shayen kayan maye yake,kowa ka gani a wajen akwai abinda yake aikatawa,wasu mata ne zalla suke shagalin su, wasu kuma maza da mata ne suke soyayyar su,sai kuma bangaren maza zalla,a ɓangaren mazan ne na jiyo hirar wasu matasa,nan na gano fiancé ɗin Sam a cikin su yana bada labarin irin halin da Sam yake a ciki.

"Humm ai nake faɗa maku tin daga ranar ban sake haɗuwa da shi ba, ƙarshe dai jiya naji an ce wai yana asibiti ya faɗa coma nace to Allah ya fitasshi lafiya ni dai na yi gaba,ba zan iya da tashin hankali ba."

"Shege me kyau,wato ka ci biredi ka yaga leda ko? Amma gaskiya baka kyauta ba baka yi amana ba,dik irin kud'in da Samuel ya dinga kashe maka amma shine ka guje shi a lokacin da yake neman taimakon ka?"

"To a bariki dama akwai amana ne? Ƙyale ni dan Allah na ci duniya ta da tsinken tsire a barni na ji ma da giɓin da aka yi min mana."

Shewa suka yi sannan suka ci gaba da rangaji suna takawa a hankali, kiɗan da ke tashi na ratsa su da kyau. Tin da ta shigo wajen matasa ke kai gaisuwar su suna yi mata jinjina,wasu sababbin zuwa wajen da basu santa ba sai suka bi ta da kallon birgewa,domin kuwa shigar ta ta tafi da su,ga wani irin ƙamshi na musamman dake tashi a jikin ta,kai daga ji ka san nera ta koka wajen siyan tiraren dake jikin ta.

Sanye take da wasu milk colour suit takalmin ƙafar ta baƙi,sai tabarau ɗin da ta manna a idanun ta da ya kusan rufe rabin fuskar ta baki,gashin kanta ta d'aure a tsakiyar kanta yana lilo kamar yanda ta saba,hannun ta kuwa sanye yake da tsadadden agogo sai manyan zobunan zinare da ta zuba,tafe take tana busa wata ƙatuwar sigari kai kace namiji ke tafe ba mace ba.

Mutanen dake gadin ta sai bud'a hanya suke yi har suka shiga wani ƙaton waje na musamman,Alhaji na ganin ta ya miƙe tsaye cikin fara'a ya nufe ta, rungume juna suka yi sannan suka kama hannun juna suka hau tafiya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login