Showing 174001 words to 177000 words out of 276165 words

Chapter 59 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

to."

Miƙa mata wayar yayi ya basu waje dan bai sani ba ko akwai maganar da za su yi da ɗan uwan ta,yana tashi kuwa suka hau hirar yaushe gamo, anan take jin dangin mahaifiyar ta sun zo yi musu ta'aziyya har da kawunan su maza dan su gan su, amma Baabaa ta sanar da su a Abuja Saddiqa ta tare da mijin ta,sun kawo musu tsaraba sosai har da awaki biyu mata da tumaki biyu da raguna biyu,sai kaji guda biyar da ƙwan zabi da ƙwarya manya biyu da ƙanana uku,gajiya yayi dayi mata lissafi sai yace,

'Ke da abubuwa sosai suka kawo fa, Innahr mu ma taso nabi su nace ta bari idan mun yi hutu sai naje nayi musu hutu idan mun dawo sai muzo da ita taga ɗakin ki,baki ga yanda Baba ya dinga murna ba da ya gansu,Baabaa tace babu shegen da zai taɓa kayan nan sai abinda kika ce ayi dasu za a yi,to fa shine Innoh ke ta jin haushi,ta daina kula kowa har gaishe da Baabaa ta dena yi.'

"Ohhh Sadeeq yaushe ka iya surutu haka? To Allah ya saka musu da alkhairi,inshaa Allahu zamu kai musu ziyara baki ɗayan mu wata rana,yanzu Baabaa yana kula ka?"

'Humm baya wani yi min magana fa har yanzu idan bani na gaishe shi ba, sai dai yayi ta kallo na idan na wuce ko ya hau matse k'walla ya fita ya bar gidan, ko kuma ya kore ni a inda yake,amma kullum Baabaa nace min nayi hakuri ba yin kanshi bane, to wai Yah Saddiqa yin waye idan ba yin kanshi ba?'

K'wallar da ta gangaro mata ta share tace,

"Ina Baabaa bani ita mu gaisa kar kud'in ya ƙare, kai dai kawai ka ci gaba da hakuri, ka kuma riƙe azkar ɗin ka na safe da yamma, koda ka ji ƙiwar yi dika kar ka manta yin falaƙi,nasi,da suratul ikhlas,kar ka manta da yin ayatul kursiyyu da faɗin Bismillahi alladhi layadurru....zuwa ƙarshe da kuma Hasbuyallahu....zuwa ƙarshe itama idan kayi haka yau da gobe sai kaga Allah ya baka ikon zama kayi su dika kaji? Allah yayi maka albarka yasa ka gama karatun ka lafiya."

'Amin Yah Saddiqa inshaa Allahu zan ƙara kiyayewa, ga Baabaan.'

Bai wani jima ba ya shiga uwar ɗakin Baabaa ya miƙa mata wayar, tana nan kwance a gado saboda sanyin da ake bugawa ta Karb'a tana yin sallama, bayan sun gaisa ta sake maimaita mata dik abinda Sadeeq ya sanar da ita sannan ta sanar da Saddiqa babu mai taɓa komai sai da izinin ta,cikin murmushi da jin daɗin yanda Baabaa ke nuna musu soyayya Saddiqa tace,

"Hajiya Baabaa tawa ni kaɗai ko Sadeeq ma na fishi matsayi a wajen ki,Baabaa ai da kai da kaya dik mallakar wuya ne ko? Me zai hana a yi amfani da ƙwan saboda kar su lalace har wajen su Yah Ameerah dik a aika,kaji da awaki da sauran su dik sai a zuba su a gidan awakin Yadiko na da da aka dena amfani dashi,ga Sadeeq nan sai ya dinga kula dasu zan dinga aiko kud'in sai musu abinci koda yaushe da maganin da za a dinga basu."

Cikin jimami Baabaa tace,

'Ina jin tsoron a dinga yi musu ɗauki d'ai-d'ai kamar yanda aka yiwa na Yadikon Sule har aka yi nasarar ƙarar mata dasu, kin san mutum mugun icce ne.'

"Babu komai Baabaa kowa yayi nagari ai dan kanshi ko?"

'Hakane, to ina shi wancan dan tsomodon yake ana ta hira ban ji ya ce uffan ba?'

Dariya sosai Saddiqa tayi da jin sunan da Baabaa ta baiwa munir, cikin dariya tace,

"Baabaa ai baki ganshi ba yanzu,yayi ƙiba kamar ba shi ba."

'Ai dole yayi ƙiba Saddiqa, amarci wasa ne? naji ma kin tara yawu a bakin naki da alama ina da rabon ganin jikana.'

Cikin jin kunya Saddiqa tace,

"Baabaa sai anjima a gaishe min da Baabaa idan ya dawo."

Dariya Baabaa tayi tana hamdala, gorin da Innoh ke yawan yi mata akan su Mommy nada ciki Ƴan Abuja kuwa shiru ya ƙare, yaye bargon ta tayi ta sakko cike da fara'a da wani k'warin guiwa ta saka rigar sanyin ta tin ta marigayi baban su Alhaji Baban Gida,tayi mata yawa rigar k'warai amma haka take zumbula ta kamar jamfa idan sanyi yazo,cike da fara'a ta kama hanyar fita daga d'akin nata zuwa tsakar gida...........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI










RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨









PAGE 70:





Cike sa farin ciki Baabaa ta miƙawa Sadeeq dake kwance a saman gadon karan parlourn nata waya tace,

"Maza kirawo min Saliha."

"Wai kina nufin Ummin Abuja?"

"Akwai wata bayan ita ne?"

Girgiza kai yayi alamar ah ah babu, ya karb'i wayar ya kira Ummi,bayan ta ɗauki wayar ya gaishe ta ne ya bawa Baabaa da bakin ta yaƙi rufuwa,gaisawa suka yi sannan Baabaa tace,

"Saliha ashe jika kuka kusan yi shine ba za a sanar dani ba na fara tanadin daddawar daka yaji?"

'Kai amma yaran yanzu dai basu da kunya, har sun sanar dake Baabaa?'

"Yo meye aciki? Ai ba zunubi suka aikata ba, kuma ni ba sanar dani suka yi ba, wannan yarinyar na kirawo naji tana tara yawu shine daga nayi mata magana ta kashe min waya,nace to bari na kira naji darrr."

'To Baabaa sai a taya ta da addu'a Allah ya bada rayayye mai albarka, Allah kuma ya sauƙaƙa mata rainon ciki da goyo.'

"To Amin dai Saliha, Allah yasa tayo gadon mahaifiyar ta wajen rainon ciki da goyo."

'Amin Baabaa.'

Hira suka ɗan taɓa kafin daga ƙarshe suka yi sallama da junan su, Sadeeq Baabaa ta k'wala wa kira bayan ta fita waje tace,

"Kai taho ka ɗakko dusa da ruwa a baiwa waɗannan ragunan, wa ya sani ma ko su zan aika Abuja a yanka idan wannan ƴar albarkar ta haihu? Ko kuma acan Baban gida zai sai masu raguna da shanu a yanka Allah masani,to abinka da masu hannu da shuni baka sanin me za su yi sai dai kaga sun aikata kawai."

Cikin sauri Innoh dake ƙulla alale a leda ta kalli Baabaa tace,

"Wai kina nufin itama Saddiqan ciki gare ta?"

"To ƴaƴan ki ne kaɗai masu mahaifar ɗaukan ciki a duniya da baza ta samu ciki ba itama? yau naji wata tambayar banza yarinya da mijin ta? Ai ina sane da duk iya shegen da kike shukawa a gidan nan, Innoh kin ƙi fita a sabga ta ko? Kin raina ni saboda kawai ina matar wan mijin ki,baki ganin tsufa na balle ki raga masa,a haife na haife ki Innoh,idan baki raga min dan furfurata ba to ban san dan me zaki raga min ba kuma."

Tura baki gaba Innoh tayi bata ce komai ba,tinda suka yi arangama da aljanun shalele ta ke ɗan d'aga wa Baabaa ƙafa, bata cika yi mata rashin kunya kai tsaye ba, sai dai tayi ta zabga habaici da shaguɓe.

Ranar nan Baabaa har sadaka tayi sannan tayi alƙawarin washegari ma zata sake yin sadakar ƙosai mai zafi da safe dan ta sake godewa Allah akan kyautar da yayi musu na samun jika daga wajen Saddiqa.

Bayan kwana huɗu da sanin samuwar cikin Saddiqa, Innoh ta fara shiri zata je Kano dan duba Mommy,rawar kai kawai take zubawa kamar mai zuwa makka,kayan ta kaff ta sa ta wanke ta yi musu ninki mai kyau ta jera a jaka, Sule ne ya zauna yana sanar da ita ta bari su tafi tare ko babu komai zai riƙe mata kaya tinda ta dage ita zata je ba zata bar Naja taje ba,cikin sauri tace,

"Yau na fara zuwa gidan Mommyn da zan buƙaci ɗan jagora? Kuma haka kawai dan mune mahaukata sai mu rakita mu dika muje mata gida? Ah ah wannan ma dan tayi waya tace bata jin daɗi ne da babu inda zan je,"

"Innoh tinda akai auren yarinyar nan ta koma kano fa kike yi musu zarya, ba a rufa sati uku baki samu dalili kin je kin cinye sati ɗaya ba, haba Innoh ! Sannan naga dai ma bake tace tana so kije ba,Aunty Naja tace ki kira mata taje ta zauna da ita har sai ta haihu."

Dafe ƙirji Innoh tayi tace,

"Kana nufin nabar Naja taje tayi kusan wata biyu ko uku gidan Mommy ni ina nan zaune baki sake kamar ita tayi min naƙudar yarinyar? Ba zai yu ba, ni zan je da kai na nima na ci daɗin da ake ci, haka kawai Allah ya kawo min hanyar hutu sai na ƙi Karb'a tinda kai kaƙi ka je ko ɗan aikin nan a firamare ka kama ana baka albashi, daga ƙarya sai yawo da waya ka iya babu fuss balle ka dinga kashe min ƴan silalla,itama waccan marowaciyar ko zuwa nayi na tarar da nama gidan ta sai tace na mijin ne ta b'oye abinta, an saka maka naman miya gidanta ka ci uku to ina dalili? Ku barni naje inda zan huta, itama Najar da ta haihu tana da kamar Mommyn ba bari na zatai naje gidan ƴarta ba."

Kuka suka ji an fashe dashi a tsakar gida,ba kuma kukan kowa bane face na Naja da ta gama sauraron dik abinda Innoh ke faɗi akan ta,tayi matuƙar mamaki da jin kalaman Innoh akan ta,dama Mommy ce tayi mata waya akan taje ta zauna da ita har ta haihu shi yasa ta shiryo dan ta sanar da Innoh tinda duk kusancin ta da Mommy dole ta sanar da Innoh,ashe ashe Innon bata bata wannan matsayin da kusancin ba a rayuwa, ashe abun duniya zai iya rufe wa Innoh ido taci mata mutunci haka har da gorin haihuwa?

Da sauri Sule ya fita ya riƙe jakar Naja dake gursheƙen kuka zata bar gidan,cikin matsanancin tausayi ya hau bata haƙuri,ita kuwa mai gayya mai aikin fitowa tayi idanu sun yi mata mici-mici ta hau borin kunya tana faɗin,

"Naja lab'e kika fara yi min a gida na? Ashe har ta kai mu ga haka Naja? To a gaskiya idan dai haka zaki dinga yi ki dinga zaman ki a gida kina kula da Goggo in ba kiran ki nayi ba kar ki zo, irin haka ai sai ki ja mutane su dinga ganin baƙi na dan na faɗi gaskiya,ita dama gaskiya ɗaci gare ta in ji ɗan hausa."

Ɗan liti ne ya shigo a hanzarce ya ɗauki buta ya zaga, ba jimawa ya fito yana ƙarasa gyara zariyar wandon shi,kallon Naja yayi dake ta kuka ta kasa magana,cikin damuwa ya ce,

"Ke Naja me ya samu Goggon? Mutuwa akai ko me?"

"Baba ba mutuwa akai ba, Innoh ce take yi wa Aunty Naja gorin haihuwa dan kawai Yarinyar nan tayi waya tace Aunty Naja taje ta zauna mata har sai ta haihu,shine Innoh tace ba inda Aunty Naja zata je ita zata je ta zauna da ƴarta saboda kawai ana cin daɗi gidan Mommyn."

Ɗan liti sakin baki yayi yana kallon Innoh da kunya ta gama baibaye ta,ido ya raina fata, sai a lokacin da Sule ke maimaita abinda ya faru ta gano inda tayi kuskure, Naja ce fa, Naja Ƙanwar ta abokiyar cin mushen ta, Naja dake yi mata aiki da jiki da abinda take dashi na sana'ar ta dan farin cikin ta, Naja dake taya ta kashewa da binnewa.

Kallon duk da suke binta da shi ne yayi mugun kashe mata jiki ta hau borin kunya tana faɗin,

"To Allah ya baki haƙuri Naja'atuwalle ƙanwata ta kainaaa,ai abun be kai haka ba,ga kuɗin mota da na guzirin hanya Allah ya kiyaye, idan kin je ki gaishe ta,Allah ya raba ƙalau."

Wani irin mugun kallon tsana Naja ta wurgawa Innoh,sannan ta hau goge hawayen ta tana shessheƙa irin ta wanda ya ci kuka ya gajin nan,baki na rawa tace,

"Idan kika ganni a gidan Hadiza ki tsine min Innoh ! Daga yau babu ni babu zuri'ar ki, ina kike sanda ƴar taki ta kusan kashe auren ta tin a garin nan da ƙazanta da rashin iya girki naje na koya mata? Ina kike sanda ƴar ki Ameerah take zagin uwar mijin ta da yi mata rashin kunya mijin ta ya sanar dani naje har gidan ta na gyara mata zama? Kina ina sanda mijin Ameerah ya kirani akan baƙar ƙazantar da take yi naje na ci mata mutunci har ta gyara yake godiya? Dik baki san an yi wannan ba saboda ni na ɗauke su tamkar ƴaƴana na ciki na shi yasa ban taɓa zama na sanar dake ba ban kuma sanar da kowa ba ciki har da Goggo da nake kwana nake tashi da ita,ina dubin duk ɗaya ne,ashe ke abun duniya zai iya rufe maki ido kiyi min haka,to daga yau babu ni babu ke alaƙar mu ta yanke."

"Alaƙar ku zata ƙara ƙarfi da ikon Allah,ku yi hakuri na yi muku katsalandam a maganganun ku,dik abinda ke faruwa ina jin ku, ina Naja? In tambaye ki mana, dik abubuwan nan da kika lissafa kin yi wa yaran ta dan wa kika yi?"

Cikin share hawaye Naja tace wa Baabaa,

"Dan Allah nayi mana Baabaar Abbe? Da ba dan Allah nayi ba ai da na faɗa duniya ta sani."

"To Alhamdulillahi,na san ke kina da hankali ba kamar wance da ba a kama sunan ta ba,ki yi wa Allah a yanzun ma ki je ki kula da yarinyar da ta baki matsayi irin na uwa, da ace uwar masu gida bata ɗauke ki da mahimmanci ba da ba zata nemo ki ba, ko ba haka ba Ɗanli?"

Da sauri Ɗan liti ya hau gyad'a kai kamar agama lizzad sannan yace,

"K'warai kuwa Yaya maganar ki gaskiya ce,sannan ma ni ai babu uban da ya gaya min zashi binni,wato na fita sana'a ina can ina neman nakai sai na dawo naga gida babu kowa, kin tattare kin tafi birni cin arziƙi kin bar ɗan wahala a gida ko? To babu inda zaki je."

Cikin borin kunya da hauragiya Innoh ta hau faɗin,

"Dama ina zanje tinda suna da ƙanwar uwa a raye? Ni dama nasan wannan abun da ya faru tsakani na da ƴar uwa ta sharrin maƙiya ne ana hassadar zaman amanar dake tsakanin mu, shine ake so ayi mana farraƙu, Naja kiyi hakuri dan Allah ki kama hanya ki je,yo idan baki je ba wa zai je?"

Nan dai aka haɗu da Baabaa da Ɗan liti tare da borin kunyar Innoh aka baiwa Naja hakuri har ta hakura,Ɗan liti ne ya kaita tasha ta haye abun hawa ta lula sai Kano.

*******************************

Wani babban hall ne dake cikin sannanne kuma ƙayataccen hotel ɗin dake garin Abuja cike da mata da maza da kuma jinsin ƴan daudu marasa alƙibla,wani irin kiɗane ko ta ina da ihun matasa da dattijan dake cikin wajen ke ta tashi,kwalaben giya ne ko ta ina irin masu tsadar nan da kofunan gilashi ke ta gilmawa,dik wanda nashi ya ƙare a sake cika mishi.

Hajiya K'waisa na gano cikin wata iriyar shiga ta alfarma hannun ta cikin na Samuel suna rawa sai wani yanga yake yana kwantawa a jikin Sam ɗin,wayar Alhaji dake kallon su Hajiya k'waisa ce ta hau ringing,yana nan zaune a d'akin da aka ajiye computers ɗin dake haska CCTV camera ɗin da aka dasa a wajen taron.

Murmushi yayi sanda yaga mai kiran nashi,amsawa yayi ya kara a kunnen shi yace,

"Ƴar kunama ga zaƙi ga harbi ya aka yi ne?"

'Alhaji naji shiru shine nace bari na kira naji ya akwai kaya a ƙasa ne? Gobe nake son nakai baby na asibiti akwai wani ɗan aiki da take so a yi mata,ni kaina ina ganin idan an yi mata aikin zamu more shi,fatan mu dai Allah yasa yayi kyau,na tabbata kud'in da zamu samu za su ninku akan na yanzu,kaga kafin ta samu sauƙi sai a sauya ta da wata.'

"Amy kin ƙi gane wa har yanzu, na sha faɗa maki duk aikin da za a yi wa yaran nan baya wani tasiri sama da idan mai natural aka samu,kinga yarinyar nan da na taɓa kaiwa Alex ta haɗu,yanzu haka gani ga su K'waisa ina kallo a kwamfuta,da ace zan ɗan matsa su da na ji inda zan sake samo ta,ko da tsiya da bala'i ne sai na mayar musu da ita,kin san saboda abinda tayi har yau na kasa saka ƙafata a ƙasar nan, sun riga sun sanar da mutanen su idon su ido na a ɗauke ni kawai."

Dariya Amy tayi kafin tace,

"Gwanda ma ka hakura da ita kasa K'waisa ta nemo maka wata, zata iya dan duk wasu manyan karuwai da ƴan daudu a ƙarƙashin ta suke,saboda a labarin da naji wajen baby tace yanzu anyi mata aure da ɗan sarkin garin su."

"Ko da uban wa aka yi mata aure tinda ta shiga harkar bariki ta yarda zata saida jikin ta saboda kuɗi na siya da tsada,to fa sai ta koma inda ta fit[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI








RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨








*Dan Allah masu nema daga farko kuyi hakuri ku duba wattpad, ko Whatsapp channel d'ina mai suna TASKAR HAMIBRAH anyi nisa da yawa ba zai yu na dinga tura pages har 71 ba gaskiya. Dik group ɗin da suka ga bana tura musu, basu yin  comment ne ko reacting shi yasa nake zaton ba a bi.*




PAGE 71:




"A dai bi a sannu Alhaji kar a saka garaje a lamarin."

In ji cewar Amy dake bin Billy da kallon ƙasa-ƙasa irin na ƙwararrun ƴan bariki,sun jima suna tattaunawa da Alhajin kafin su kashe wayar. Alhaji kuwa yana ajiye wayar tashi a aljihun rigar shi sai ya ɗauki landline ɗin dake saman table ɗin dake gaban shi yayi kiran waya, bai jima da ajiye wayar ba wasu murɗaɗɗun maza sanye da baƙaƙen kaya suka shiga office ɗin nashi.

Tsaye suka yi masa kamar wasu dakaru kowannen su yana ɗauke da bindiga a soke a jikin shi,wani mai baƙin gilashi Alhaji ya kalla yace,

"Maza ina so a taho min da K'waisa yanzun nan,bana son a bata damar bijirewa, idan ta bijire ko aka ne ku kawo min ita nan."

"An gama Alhajin Allah."

Juyawa suka yi a tare kamar waɗan da suka sha horo akan yin hakan suka fita,ta cikin CCTV camera Alhaji ya hango yanda suka taso ƙeyar K'waisan Alheri zuwa ofishin nashi,kafin su iso ya taso yana gyara zaman jacket ɗin dake jikin shi ya jingina da jikin makeken teburin da yake zaune a ofishin nashi.

Cike da yanga da magana a natse K'waisa ya isa office ɗin yana yatsina da taunar cingam,kallon sama da ƙasa ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login