Showing 39001 words to 42000 words out of 276165 words
Chapter 14 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
wa Billy tace,
"Lafiya ta qalou, kawai ina mamaki ne da Hajiya tace wai ana iya yi wa mutum allura har bakin shi ya yi qato irin nawa shi ake yayi,"
"Mun gama ɗora hotunan ki mu je sama mu ga me mutane za su ce, idan kina da rabo ma a yau kema ki samu customer ɗin ki na farko"
Sallama suka yi wa mai hoto da Hajiya K'waisa da ta kyafe ana shafce ta da hotuna zafafa dan kuwa ta sha ado na kece raini,adon da duk k'wak'k'wafin mutum ba zai taɓa gane namiji ne ba mace ba,sai dai idan ka san ko shi wanene to fa ka sani,idan baka sani ba baka sani ba.
Bayan sun hau sama sun shiga d'akin Billy ne, Billyn ta koma ta saka sakata sannan suka kwanta a gadon ta, kamar ba zata yi magana ba sai mommy ta ji tana faɗin,
"A zaton ki haka nan Hajiya take bayyanar da halittar mata a jikin ta gobe kuma aga babu shi? To bari na wayar maki da kai ki ji me ke faruwa. Hajiyata da kike gani jikin nan nata ya ci miliyoyin nerori kafin ki ganta a haka, na farko dai kin ga bakin ta ai kamar na mata ne ko? To shi wannan na musamman taje US aka yi mata dashen leb'e na musamman,daga baya kuma aka qara mata faɗin hancin ta, domin kuwa dacan hancin ta siriri ne sosai kuma dogon gaske, sai taje aka rage mata tsahon shi aka qara faɗin shi,sannan maganar mazaunai da qirjin ta kuwa riga ce aka auna jikin ta aka qirqirar mata dai-dai jikinta, ta yanda idan ta saka zaki ga kamar fatar ta ce a hakan, muna nan dake a duk sanda ta yarda dake ki ka fara shiga d'akin ta watarana za ki ga yanda abun yake, ko mu nan idan muna so mu yi hotunan da za su janyo hankalin customers a d'akin nan na hoto muna da wani d'akin sirri zaki ga irin waɗannan abubuwan kala-kala,kuma da manyan kuɗi sosai aka yo mata su dan ita bata son siyan abu haka kawai a titi, tafi son taje a auna ta a yi mata dai-dai ita ta yanda duk wanda ya kalla zai zaci nata ne,"
"Ikon Allah, lallai ɗan Adam na da abubuwan ban mamaki,"
"Duk abin mamakin ɗan adam bai kai Allah ba shi da yake busa rai, Kuma ya yi mana duk wani abu da muke da buqata, Kawai dai cewa zaki yi lallai ɗan Adam bashi da godiyar Allah, sai ni kuma in ce maki tabbas bamu da godiyar Allah domin ni ɗin nan da kike ji da gani na tattare kuɗi na kafff na kai an qara min nan d'ina wato mazaunai na saboda ina tsoron bayyana dukiyar da nake da ita a gane qazamar rayuwar danake aikatawa, ko kina tunanin haka suke a da? Mommy ki godewa Allah da ya baki jiki me kyau, a da ana ganin munin ki ne saboda ba kowa ne ya san darajar leb'en ki ba, ba kuma kowa ne ya san amfanin su ba a cikin mutanen mu, su turawa ai kashe miliyoyin kuɗi suke yi dan su samu ya nakin, Mommy na jima ina yaba dikka wata halitta ta jikin ki, kuma na ci buri kala-kala akan ta, ɗaya daga burika na shine in samu mazaunai irin naki, ba manya ba, ba qanana ba, masu shape kamar an auna, wannan shine dalilin da yasa sanda na tara kuɗi masu yawa na je aka yi min BBL,"
Baki sake mommy ke kallon Billy da ke shayar da ita mamaki da kalaman ta, cikin tsananin mamaki tace
"Menene kuma BBL ni Hadiza?"
"Brazilian Butt Lift kenan, ana amfani da kitsen sassan jikin mutum ne a qara masa a mazaunan sa, misali, za a iya cire kitsen bayan ki ko cikin ki ko cinyoyin ki duk a tara maki su a mazaunai, shi yasa zaki ga wasu na da irin jikin ki, nan kuwa ba haka Allah ya yi su ba su suka je aka yi musu da kud'in su,kamar dai ni,"
"Yanzu Billy jiki na dama yana da kyawun da har wani zai ji sha'awar dama ya zama nashi?"
"Mommy what are you saying? Baki da ido ne? To me ya sa mazajen garin mu musamman masu kuɗi da 'yan boko ke ta nuna maki soyayya? Ba dan shegen wulaqancin da kika zuba masu ki na kin kula su ba da kin jima da zama mai kud'i tun a qauyen Ba mugu,"
"To amma Billy soyayyar tasu ai ba ta domin Allah bace, jiki na suke so da na yi musu maganar aure suke guduwa qarshe har kowa ya dena sunsuna ta"
Dariya Billy ta yi tace,
"Wai sunsuna kamar wata karya, ke tunda fa ki ka zo kika dena maganar yayana, wato kin ga inda zaki dinga samun nerori kin yada shi ko? Alqawari be ce haka ba fa mommyn Ɗan liti,"
"Ba haka bane Billy, muna gaisawa sosai ma, dan ko jiya da dare sai da muka yi hira da shi kafin na yi bacci, bari ma ki ga wasu zafafa da ya tura min d'azu,"
Wayar ta ta janyo suka kwanta sosai a gadon Billy suka fara kunna videos ɗin da suka rikita musu lissafi cikin qanqanin lokaci, a hankali Billy ta yi amfani da wannan damar ta fara taɓa Mommy, nan take shaid'an ya yi rinjaye suka dulmiya cikin sab'on Allahn da ke girgiza al'arshin Allah, sab'on Allahn da ya fi zina zunubi,sun jima a haka Billy na daf da samun cikar burin ta akan Mommy hankalin mommy ya dawo jikin ta, da sauri ta ture Billy da ke samanta ta na faɗin,
"Meye haka muke yi ne Billy? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una meya same mu haka?"
"Dalla ki tsaya mu qarasa abinda muke yi kin wani tashi kina abu kamar baki son abinda nake yi miki,"
"Ba zan iya wannan ba Billy, ke mace ce fa 'yar uwa ta,wannan ai qazanta ne,"
"Qazanta? Amma kike bari namiji ya taɓa ki? Meye marabar dambe da faɗa?"
"Za a iya yin faɗa ba tare da kokowa ba, amma shi dambe dole sai jiki ya gogi jiki, Billy wannan abun ya yi qazanta da yawa ba zan iya irin wannan ba, wannan ɗin ma da nake yi bana fatan na dawwama a cikin shi,"
Cikin ɓacin rai Billy ta buɗe wa Mommy qofa tace,
"Fita ki tafi d'akin ki sai da safe"
Jiki a mace Mommy ta riqe hannun Billy tace,
"Fushi ki ka yi? Dan Allah ki yi...."
"Fita ki tafi d'akin ki nace, bana son surutu da na hau live a TikTok d'ina zan samu wadda zata maye min gurbin ki har da qari, kema ki yi joining ki sha kallo yarinya ni ba macen da wata mace zata wulaqanta bace,ki duba zaki ga yanda nake da daraja a wajen mata, a biya min buqata kuma a biya ni da nera ke wani lokacin ma har da daloli biyana ake yi, bana nima zan gagara na dena tsoron kowa, zan fito da dukiyar da nake da ita duniya ta shaida, ki je sai da safe"
Gaba ɗaya sai mommy ta ji kamar bata kyauta ba, amma ba yanda ta iya dan kuwa Billy ta hasala da yawa, fita tayi daga d'akin ta na share kwallar da ta fara zuba mata abinda ya faru tsakanin ta da billy na sake bijiro mata a kwanyar ta, wannan ai qazanta ne,kuma abun kyankyami ne hakan a wajen ta,da wannan tunanin ta shiga d'akin ta, wayar ta ta kunna ta shiga TikTok ta ga yanda matan Arewa ke ta yin abubuwa marasa ma'ana da amfani, idan kuma ta duba ta kalli videos na mutanen kudu sai ta ga ko comedy za su yi sai ya ba wa mutum nishad'i da kuma wani saqo a cikin shi, ga kuma masu tallata kayayyakin su da gwanjon su da duk wani abu da suke siyarwa, mu kuwa mutanen Arewa koda zamu tallata kayan ba kowa ne ke tallatawa da kyau yanda ya kamata ba har ya samu alkhairin da ake samu a TikTok din,matan Arewa masu zaman kan su kuwa da damar su sun fi tallata kayan mata da na maza ta yanda za su samu damar tallata kawunan su da kuma kalamai na batsa, a haka suke tara manyan followers saboda yanzu duniyar ta koma idan ka iya kalamai na batsa a yi da kai, idan ka iya sanya vidoes na tsiraici ko hotuna na tsiraici a yi da kai, idan kazo da wa'azi ko duba page ɗinka ba a yi balle a kalla har ayi following, ko da an yi following ana ganin baka yin abinda mutane ke so na kauce hanya sai su yi unfollowing ɗin ka.
Mommy na nan na kallace-kallacen mutanen TikTok kala-kala zuciyar ta na ingizata da ta yi joining live ɗin Billy ta ga me suke yi a ciki, hannunta ta saka ta yi joining ta tsaya tana jiran tsammani.
Ba jimawa kuwa ta gan ta cikin live ɗin tsundum,kunnuwan ta kuwa nan take suka fara jiyo mata kalamai da badaqalar da ake yi a live ɗin, idanunta ta rintse dan ganin wata da ta kunna camera ɗin ta ta na wasu abubuwan da duk mai hankali ba zai tsaya kalla ba, da sauri Mommy ta kashe wayar ta gaba ɗayan ta ta kife ta jikin ta na rawa sosai.
Ashe dama yaran hausawa na irin wannan mummunar rayuwar a social Media? Ita a zaton ta turawa ne kawai ke ire-iren lalacewar nan a ɗauke su a video a dinga tura musu suna gani a groups, ashe-ashe Yaran hausawa kuma musulmai suna aikata wannan lalatar,kamar wadda aka daketa akanta ta yi saurin faɗin,
"Sule...tabbas Sule ma abinda yake yi kenan, ashe shi yasa baya so ko motsi yaji ana yi ta wajen d'akin sa ya dinga fitowa yana masifa kenan ana damun shi yana bacci, tabdijam ! Ya zan yi yanzu to? Na zauna in ci gaba da wannan rayuwar ko kuma in tattara in gudu tun kafin na yi lalacewar da ba zan iya juyawa ba?"
*To makaranta Mommy na neman shawarar ku*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 15:
Tunda aka yi faɗa tsakanin Baabaa da Innoh suka dena yi wa junan su magana, Baabaar ce ma watarana takan leqa daga tsaye idan Yadiko na yi wa Innohn gashin baya tana zunduma ihu ta yi mata sannu tare da faɗin,
"Ohh ni Baabaar Abbe ciwo ya samu masu baki shikenan kuma hayyaroto ya qaru, Allah ya sawaqe to,"
A duk lokacin da Baabaa ta faɗi haka sai dai Innoh ta yi k'wafa kawai dan ita kaɗai ta san me take qullawa a ranta za ta aikata wa Baabaa a duk sanda ta ji sauqi, Yadiko kuwa yau kwana uku kenan da faruwar abun bata gaji da zuwa taimaka wa Innoh ba, domin kuwa a ranar da abun ya faru ma ita ta taimaka mata ta kai ta d'akin ta, ba godi bare na gode daga wajen Innoh amma haka take hidima da Innohn, watarana ma sai dai ta dinga ja mata Allah ya isa dan a cewar ta da gayya take danne mata bayan da ruwan zafi duk bakin su ɗaya da Baabaa so suke yi su ga bayan ta.
A kwana na huɗu da faɗan ne Munir ya zo qauyen Ba mugu, gida kuwa ya cika da murna da farin cikin yara da manya dan kuwa ya zo musu da tsaraba sosai, doya kanta ya kawo ta kai d'auri biyu,ga dankalin turawa cike da qaramin buhu, shinkafa buhu ɗaya taliya da makaroni kowanne kwali d'ai-d'ai, sai katon ɗin maggi ɗaya, motar da ya zo da ita ma abin kallo ce haka yara suka bi suka yanyane ta ana ihun baqon Baabaa na Abuja yazo, wanda jin hakan ba qaramin qona ran Innoh yake yi ba.
Munir yafi kama da Baabaa a kaf jikokin ta,sai dai shi yana da manyan idanu wanda ya d'akko daga wajen mahaifiyar shi, fari ne shi tasss kyakkyawa mai qaramin jiki kuma bashi da tsaho sosai, gashin kan shi irin na fulanin nan ne mai nannad'ewa ya tara shi kuwa sosai kamar a yi masa kitso,sai dogon gemu da ya dace da qaramar fuskar shi, yara sai zuwa suke yi suna kallon shi suna faɗin albarkacin bakin su game da kyawun shi, Sadeeq kuwa tinda Munir ya isa garin da hantsi duk inda ya sanya qafa shima nan yake ajiye tashi, sai aka yi sa'a kuwa tasu ta zo ɗaya da yaron, dan kuwa Munir ya yaba da halin shi da natsuwar shi,yaro ne mara surutu sosai,ko da zai yi magana ma to mai ma'ana yake yi.
Lokacin da Sule ya dawo daga yawon shi ya tarar da had'ad'd'iyar motar Munir a qofar gidan su sai ya samu kan shi da tsayawa ya k'yafe ya dinga ɗaukan hotuna kala-kala ba tare da ya san motar ko ta waye ba.
Yana gamawa ya shiga ciki ya doka sallama, sai ya ga takalma masu kyau da tsada a qofar d'akin Baabaa, Innoh ce zaune a tabarma a tsakar gida ta jinginu da gini sanye da qatuwar rigar sanyi saboda sanyin da aka fara yi na ratsa ta ,a dole aka yi dabarar da aka zura mata riga Yadiko ta kamo ta ta zaunar da ita tsakar gida, dan kuwa tana son ta ga k'wal uwar daka itama sai dai baqin hali ya hana ta sakin ran ta a yi murnar zuwan Munir ɗin da ita.
Sule ne ya ja bokitin qarfe ya zauna a gaban Innoh sannan ya ja kwanon da ke gaban ta ya buɗe, alale ce cikin ragowar kwantan da Ameerah ta dawo da shi daga talla sai kuma tsokokin nama da ta uzzira wa Ɗan liti ya siyo mata, a cewar ta tana da buqatar cin nama kafin bayan ta ya dawo dai-dai.
"Ajiye shi dan uban ka, kana can kana yawon tazubar uban ka ya siyo min dan na ci na maida komad'a tinda an dage sai an ga baya na a gidan nan,yau da kana nan wata qarmasasshiyar tsohuwa ta isa ta sheme ni ne? Amma kai kullum kana can waje kana yawo, idan ka dawo gida kuma kana d'aki kana baccin asara"
"Yasin se na ci nima wa ya ce ki ajiye baki cinye ba? Naman ma duk ya wani bushe, Innoh waye wai ya zo na ga wata arniyar mota a waje? Ko Yah Munir ɗin ne ya iso?"
"Yaya a gidan uwar ka? Idan na sake jin ka kira shi da Yaya sai na ci maka mutunci, yaron da tun da ya zo sannu bata haɗa shi da kowa ba a gidan yana can wajen kakar shi?"
Yadiko ce ta fito zata hura wutar girkin la'asar ta ce,
"Kaiiii Innoh, har d'aka fa ya shiga ya gaishe ki, da ya gan ki babu lafiya ma sai da ya yi miki ya jiki sannan ya shiga waje na nima muka gaisa ya wuce d'akin kakar shi, sannan menene a ciki dan ya kira shi da yaya be girme shi bane ko me?"
Qanqance ido Innoh tayi sannan tace,
"Sannu guntsi fesa, da ke nake ko da d'ana? Ni fa bana son sa ido sana'ar banza sana'ar da ba uwa ba riba,na kasa dake balle nace ki ɗauka? Mamalam gida duk ya zama gidan 'yan kuci ku bamu, se ki bari idan an kasa doyar se a baki kason ki kin ji daɗin shiga maganar da bata shafe ki ba kwad'ayayyiya kawai"
"Innoh ni ce kwad'ayayyiyar? Dan na faɗi gaskiya shine zaki kirani da kwad'ay....."
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una! Allah Allah Allah ka nuna min ranar da zan shigo gidan nan in ga ana hirar arziqi, kai in gan ku shiru ma kowa na harkar gaban ta ze fi min alkhairi akan wannan tashin hankalin da kuke yi a kullum, habaa ! Ina shi Mannirun yake?"
Yadiko ce ta iya amsa masa da,
"Yana d'akin Baabaa, Sannu da zuwa Malam"
Ko kula ta be yi ba ya wuce d'akin Baabaa da ke zaune ta tasa shalelen jikan ta a gaba da abinci kala-kala da ruwan pure water leda uku a faranti se mangwaro masu zaqin gaske, shi kuwa Munir ya dage yana ta shan mangwaro bayan ya gama cin dambu,Sadeeq na gefen shi yana shan mangwaro shima, Baabaa kuwa na ta zuba masa hira.
Labulen d'akin Ɗan liti ya saki bayan ya shiga ciki ya samu gefen gadon qasar Baabaa da ya sha katifa ya sha lullub'i ya zauna,hannun sa ya zura ya ɗauki mangwaro ɗaya a ƙwarya ya kafa masa haqora sannan ya amsa gaisuwar Munir da ke murmushi yana gaishe shi,
"Lafiya qlou Manniru ka zo lafiya? Ya baban naka da ita Hajiyar? Kuna nan lafiya qlou da sauran 'yan uwan naka dika ko?"
"Lafiya qlou kowa yake Baba, sun ce ma a gaishe ka,"
"Allah sarki ina amsa wa, kai kuma zaman qauye ne yake baka sha'awa ka taho yi mana hutu,mu muna so mu gudu mu hyiga birni kai kana zuwa qauye"
Baabaa ce tace,
"Yo ba dole ba kai kuwa Ɗanli uwar da ta haifi uban sa na qauye ai dole ya kawo ziyara,"
Munir ne yace,
"Ah ah fa tsohuwa ki gyara kalaman ki, kice Babar Baban shi tana qauye, ya daga zuwa na zaki dinga zagi na a fakaice"
Dariya Baabaa da Ɗan liti suka yi, suka ci gaba da hirar su ta yaushe gamo, Ɗan liti bai baro d'akin ba sai da ya ci ya qoshi saboda dama girkin Innoh ne Yadiko ke taimakawa ta yi tunda Innoh dai bazata iya ba, kuma baya son zama a wajen Innoh saboda yawan qorafi da kan qara.
Qarfe shida da minti goma na yamma Yadiko na madafi ta na kwashe tuwo gefe ɗaya kuma miya na saman wuta tana ci gaba da dahuwa. Saddiqa ce ta dawo daga Islamiyyah a gajiye ta na shiga gidan ta yi sallama ta saqale hijabin ta a igiyar shanya ta ɗauki buta za ta zaga dan kuwa a matse da fitsari ta dawo daga makaranta, cikin saurin da take yi zata shiga band'aki ta yi karo da Munir ya fito hannun shi riqe da buta ya gama kama ruwa, da sauri ta ja da baya ta yarda butar hannun ta sannan ta dafe qirji ta na kiran sunan Allah, dan kuwa bata san da zuwan shi ba, sannan bata taɓa tsammanin ganin shi