Showing 144001 words to 147000 words out of 276165 words
Chapter 49 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
da wannan lokacin ne?
Ƙarar gate taji alamar an buɗe za a shigo da mota, cikin sauri ta tashi tana murna ta ajiye wayar ta buɗe ƙofar shiga gidan tayi ta kama ƙugu tana murmushi,sai da ya gyara parking ɗin motar sannan ya kashe fitilar dake haska ta, Abdul ne ya fito cikin sauri ya nufo ta, fita ta ƙarasa yi da gudu ta nufi wajen shi,Abdul kuwa tana zuwa sai ya d'aga ta sama yana juyi da ita a tsakar gidan tana ta dariya, a haka suka rankaya ciki suka zube a kujera,sai da suka gama yi wa junan su maraba sannan Mommy ta shagwab'e fuska tana wani karye jiki tace,
"Baby na yi kewar ka ina ka shiga haka baka kira ni ba kuma na kira ka baka ɗauka ba?"
"Humm baki dan irin halin da na shiga ba yau bayan na ajiye ku a kasuwa baby,ban sani ba ko kun shiga da wani abu ne me wari cikin mota ɗazu,gashi na ci danwake da bana ci sosai, sai haka ya sa ciki na yayi ta juyawa yana ciwo, ina zuwa gida na dinga amai da zawo, sai dai cikin ikon Allah abun ya tsaya da na sha magani nayi bacci, shine yanzu na ɗan watsa ruwa bayan nayi sallah na taho gida,"
Cike da tausayawa ta hau shafa shi tana yi masa sannu,tashi tayi tana juya jikin nan nata dake rikitar da Abdul ta wuce dinning tana kiran yaje yaci abinci,cikin sauri kuwa ya bi bayan ta dan kuwa bai yi zaton ma tayi girki ba, ya gama saddaƙarwa tea zasu sha su kwanta kawai.
Lafiyayyiyar shinkafa da miya ta zuba masa gefe kuma farfesun kifi da ya ji kayan lambu ta zuba, sai lemon kankana da ta haɗa masa da taimakawar Naja,mamaki ne ya kama Abdul ya saki baki yana kallon Mommy, a hankali ya kama hannun ta yana murzawa yace,
"Baby dik ke kika girka wannan? Ni fa na zaci baki iya bane shi yasa baki yi, har ina ta tunanin idan mun koma Kano na saka ki a makarantar koyon girki?"
"Ai kuwa da na gode maka, da gaske ban iya girki ba, wannan ma Aunty Naja ce ta taya ni,itace tazo tayi ta min faɗa saboda na ce ban yi girki ba,"
"Kaiii ai kuwa dole ne na bata tukuici, Allah ya saka mata da alkhairi, bani abincin naci naji dan na baki maki,"
Nan take suka zauna suna cin abinci suna hirar su har suka gama,sallar isha'i Abdul ya tafi bai dawo ba sai ƙarfe tara,da gasasshiyar kaza da wata kankanar ya dawo,godiya Mommy tayi ta Karb'a taje ta adana, murmushi Abdul yayi dan kuwa yaji daɗin sauyin da ya samu daga gare ta,kallo suka tsaya yi wanda daga ƙarshe suka tattara suka koma ɗaki suka hau baza soyayyar da Mommy tafi so.
Washegari bayan Mommy ta shirya sun ci abinci jellop ɗin taliya da kifin da suka soya a jiya sai Abdul ya ɗauke ta ya kaita gida, wanda yake fatan da an kai Ameerah d'akin ta yawon zai tsaya a haka.
A can yau ma ta tarar da Naja, gaisawa suka yi Mommy ta hau bata labarin kaff abinda ya faru har da na soyayyar da suka sha a daren, Naja dariya ta dinga yi, Innoh na gefe tana sauraren su ita da Ameerah basu ce komai ba, wanka Naja ta sa Ameerah yi bayan ta gama jin hirar da Mommy ke yi mata, Ameerah na fitowa Mommy ta deb'o kayan kwalliya da turaruka dan su gyara Ameerah.
"Ah ah Mommy kitso zan yi wa yarinyar nan, ban isa bar mata kai ta tafi a haka gidan miji ba,ke kuma dan uban ki saura idan kin je ki bari se yayi wata ɗaya baki wanke kin tsefe ba,ya dad'e yayi sati biyu, ki wanke tasss ki je gidan Haule mai kitso a kama miki shi, ta haka ne ma zaki dinga karb'ar 'yan kud'ad'e a hannun shi,su maza da na kitso da na lalle ake samu a yagi abinda aka yaga, dan wasu mammaƙo ne da su."
Tura baki Ameerah tayi ta zauna zaman kitson ba dan ta so ba, Innoh ce ta hango roll on a cikin kayan da aka d'akko dan gyara Ameerah dashi, ɗauka tayi tana jujjuya wa tana kallo, Mommy ce tace mata,
"Wannan roll on sunan shi, a hammata ake sakawa, kawo ki gani,"
Mommy Karb'a tayi ta buɗe ta goga a hammatar ta dake aske ƙwal babu gashi,tana gamawa ta rufe ta ajiye tace wa Innoh,
"Kin gani? To haka ake sakawa"
Cike da mamaki Innoh ta ɗauka tana juyawa a hannun ta, bud'ewa tayi ta d'aga ƙaton damtsen ta ta saita hammatar ta dake cike da kore-kore shuɗi-shuɗin gashi,wata iriyar zufa me duhu ce ke fita a wajen, Ameerah da ta sha wanka ana yi mata kitso ce taga Innoh tana shirin kai roll on hammatar ta, cikin sauri ta kufce ta miƙe dan ta isa ta k'wace abun ta, amma inaaa ta makara, kafin ta ƙarasa Innoh ta danna roll on a hammatar ta goga ta kuma gogawa, ɗaya hannun ta ɗaga zata goga Ameerah ta fashe da kuka tana faɗin,
"Alqur'an se kin biya ni abuna Innoh, in na yarda hyegiya nake,"
Dariya Naja da Mommy suka dinga yi, Sule dake zaune bakin rijiya yana chatting bai kula kowa ba a gidan sai da ana wannan dramar sannan ya juya yana ta dariya shima, da kyar Naja ta lallashi Ameerah tace za a wanke mata abunta ta dena kukan ya isa haka, Sule ne yace wa Innoh ta zuba masa shinkafar da aka dafa saboda 'yan kai amarya yaci zai fita.
Da yamma bayan an gama yi wa Amarya kitso an shirya ta, matan unguwa da dangi suka dinga zuwa,jellop ɗin shin shinkafar wasu suka ci kafin a rankaya kai amarya.
A motar Abdul aka sanya Ameerah aka wuce da ita sauran matan kuwa da ƙafa suka isa,kowa ya shiga ɗakin Ameerah sai ya yaba ƙoƙarin da aka yi wajen cika mata shi da kayan ɗaki masu kyau da tsada,ba a shigar da amarya d'akin ta ba har sai da aka gabatar da abubuwan da ake yi na al'ada idan an kawo amarya, Mahaifiyar Shamsu sai sanya albarka take yi tana fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a mai albarka.
Da misalin ƙarfe goma bayan kowa ya watse Ango shamsu ya iso gidan shi kaɗai da 'yar ledar shi ta siyan baki.......
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA :HAERMEEBRAERH ✍️✨
*SANARWA !*
*Dik mai son karanta littafin GIDAN ƊAN LITI KYAUTA ta bi shi tin yanzu ta wattpad ko Facebook page ɗina ko kuma Whatsapp Channel d'ina da nakan tura maku links ɗin su lokaci bayan lokaci,idan aka gama ya zama document zai zama na kuɗi ne da yardar Allah,mutanen da na yiwa alƙawari idan an gama document zan tura masu kuma na san su sun sanni ana gamawa zan sanar sai su yi min magana na tura masu kyauta...ku dinga patronizing ɗin mu manaaa kar a dinga harkar wasa tare ci banban i beg...lols...DAGA YANZU DUK WANI TSOHON NOVEL ƊINA DA NAYI EDITING KO ZAN YI EDITING ANAN GABA ZAI ZO MAKU NE A 300 KACAL BABU YAWA...amma MAIDA TSOHUWA YARINYA da MAHREEN su 1k ne kowannen su.*
*Dan Allah mutanen k'warai muna barar ADDU'AR ku zuwa ga mahaifin biyu daga cikin mutane masu matuƙar mahimmanci dake cikin group ɗina (Zainab & Hafast Naphada) wanda Allah yayi wa rasuwa yau kwana bakwai kenan. Allah ya jiƙan shi yayi masa Rahman ya kyautata makwancin shi, Allah ya haɗa kan zuri'ar shi yayi musu albarka.*
PAGE 57:
Zaune ya tarar da Ameerah idanun ta ƙyamas babu ko ɗigon hawaye, sai wata iriyar fargaba da tsoro da tashin hankali a cikin su,murmushi yayi dan kuwa tunanin shi ya bashi cewa Ameerah bata san komai ba game da rayuwar aure, shi ne babban dalilin shigar ta tashin hankali da damuwa har ta kasa ɓoyuwa.
Har zai zauna daf da ita ya tina azabar da ya shaƙa rannan a jikin ta na wari musamman daga bakin ta, da sauri ya koma ya zauna ɗan nesa da ita yana faɗin,
"Amarya..Amaryar Shamsu kenan, Amarya ba zaki taɓa yi mini laifi ba ko da kin mari fuskar shamsu,to yau dai gani ga Amarya ta ƙarshen tikatiki tik in ji bahaushe ko?"
Yaƙe tayi masa kawai ta saka hannu ta goge zufar dake kwance a leɓen ta na sama, sannan ta kalle shi tace,
"Sannu da zuwa,"
Daɗi ne ya kama shamsu, dan kuwa beyi zaton haka daga wajen Ameerahn dake nuna masa tsananin ƙiyayya ba,cikin tsananin fara'a ya ɗan matsa kusa da ita kaɗan, sai yaji bata tashin wari irin na rannan, sai ma wani ƙamshi da yaji na musamman na fita a jikinta, nan take ya sake jan jikin shi a hankali ya matsa, ƙamshi ne ya sake ziyartar hancin shi, cikin sakin jiki da ita ya isa daf da ita ya kama hannun ta da ya sha baƙin lalle babu ja ko ɗaya,dan kuwa baƙin ma da kyar ta bari aka yi mata shi,abun ka da farar fata sai baƙin yayi mata kyau,ledar hannun shi ya ajiye a gaban ta, a hankali ta shaƙi ƙamshin, nan take ta gane kaza ce ba tsire ba,sosai Ameerah take iya banbance menene a cikin duk ƙunshin da zata gani,saboda yawan aiken ta da Mommy keyi wajen siyan dangin tsire, balangu, kifi da kaza.
Murmushi ta sakar masa domin kuwa nan take damuwar dake ƙasan ranta ta kau, ƙasa suka sauka suka zauna suka hau rige-rigen buɗe ledar,babu bismillah babu komai suka hau cin naman kazar nan suna korawa da fanta,Ameerah kuwa har ƙashi take taunewa ta tsotse wani ta had'iye wani ta zubar.
Suna kammala cin naman kaza Shamsu ya zaro kyalle a aljihun sa suka goge hannayen su sannan suka haura gado, hira suka fara yi kamar dama can sun saba da juna babu sallar nafila da sabbin aure keyi balle a kai ga addu'ar da aka sunnanta ana dafa kan amarya a karanto mata kafin a gabatar da komai.
Abu kamar wasa sai ga Ameerah kwance a jikin shamsu suna kallon ire-iren fina-finan da ya saba ɓata dare yana kalla ko kuma ya tura groups-groups na WhatsApp,cike da shauƙin abinda yake kalla yace mata,
"To kin dai gansu nan su nake so na fara sana'a da su da zarar na kammala gyara shago na,irin wannan ana tura duk ɗaya nera ɗari ne fa, to a rana inji wani aboki na yace idan abun ya karɓe ni sai nayi dubu biyar ko sama da haka, saboda manya da yara mata da maza ke har dattijai ma zuwa suke a tura musu,"
"Kai dan Allah? Lallai wannan ba ƙaramar sana'a bace, Allah ya bada sa'a,"
(Sai kace abun arziki ake neman sa'a daga wajen Allah...sun manta da tsantsar zunubi da azabar da za su sha a wajen Allah saboda yaɗa alfasha da suke yi)
A hankali Ameerah ta fara shigewa Shamsu, wanda dama yana sane ya hau nuna mata saboda ya ja ra'ayin ta dan ya kula bata san komai ba,shi zai fara buɗe matar shi a leda,hamdala ya dinga yi da Allah bai dubi halin shiba ya bashi kamilalliyar yarinyar da idon ta bai gama bud'ewa ba.
A hankali ya fara sarrafa Ameerah cikin salon da dik ya saba gani yau da gobe a wayar shi, sai dai abinda ya bashi mamaki shine yanda Ameerah ke neman goge masa hadda da nata salon da ta koya a littattafan hausa na batsa da take karantawa da wanda ta gani a videos ɗin da take satar wayar Mommy tin a da tana gani.
Dik wani tsoron halin da zata shiga idan shamsu ya gano ƴar hannu ce ita ya kau a ran ta, fargabar da ta sanya ta tsattsafo zufa a fuskar ta ta riga ta gudu, tsantsar kwad'ayi da maitar biyan buƙatar tane kawai a zuciyar ta dik abinda zai biyo baya ya biyo baya.
Ameerah ta jima da mantar da shamsu a halin da ya same ta har sai da dare ya tsala komai ya dawo normal a tsakanin su sannan ya tuna a halin da ya same ta,cike da b'acin rai ya tashi zaune ya ɗasa mata duka a cinyar ta yace,
"Tashi munafukar Allah ta'ala, a gidan uban wa kika zubar da mutuncin ki?"
Shiru Ameerah tayi tana tunanin shin asirin da aka yi dama dan kawai ya aure ta ne ko yaya? Ai ta zaci komai tayi masa ba zai tanka ta ba balle har ya dake ta ko ya zage ta, wani yawu ta had'iya mai ƙarfi wanda ta ji shi ya daki maƙoshin ta kafin ya wuce cikin ta da ƙyar, cikin dakiya da ɗaure fuska ta zauna tana kallon shi tace,
"A gidan uban da ka je ka zubar da naka, ko ji kake ban san abubuwan da kake aikatawa bane tin a da da Mommy da Umbon gidan Mai Tafarnuwa? Ko kana jin ban san me kake yi da Tsaharen gidan...."
Dariyar yaƙe Shamsu yayi sannan yace,
"Ke ni ya isa haka ba tone-tone nake nema ba, aikin gama ya gama kin shammace ni kawai, naso nima a daren farko na na samu cikakkiyar mace amma...."
"Ba kai kaɗai ne kaso hakan ba malam, ni kaina na so na samu kamilin namiji amma na ɓige da auren ka, kar ka manta ni ban yi irin yawon da kake yi ba, sannan ƴan mata nawa da basu ji ba basu gani ba kayi wa fyad'e ko ji kake ban sani ba?"
"Na ce ai ya isa haka ko? Mu haɗu mu rufawa juna asiri Ameerah kar wanda yaji sirrin mu dan Allah,"
"Idan ka rufe nawa waye zai ji naka?"
Sauka yayi daga gadon yana haɗe rai, cikin cinkishe fuska yace,
"Ai sai ki tashi mu yi wata dabara kuma, dan kuwa gidan su Baba har yau suna al'adar duba ɗakin amarya dan su ga ko ta kai mutuncin ta ko bata kai ba, idan suka san fanko na kwaso dani dake mun shiga uku,domin kuwa suna da yaƙini akan babu yanda za a yi ɗan su ya auri macen da bata kai mutuncin ta ba face shima bai kai nashi ba sai Allah ya haɗa shi da dai-dai shi, dan haka ki sauko ki ga dabarar da zamu yi saboda mu rufawa kammu asiri,"
Jinjina kai Ameerah tayi ta sauka daga gadon, dan kuwa ta tabbatar da kaff garin daga sashen da fulani ke zama sai zuri'ar gidan Mai Dusa sune suke yin wannan al'adar ta duba gadon amarya a washegari idan an kai ta d'akin mijin ta dan su tabbatar da ta kai mutuncin ta ko akasin haka.
Cikin sauri Shamsu ya tattare zanin gado yayi waje da shi ya ɗauki ɗaya daga cikin sabon bokitin su ya saka ya hau wankewa da sabulun wanka, yana gamawa ya shanya ya koma madafin mahaifiyar shi ya kunna risho ya dora ruwan zafi ya kai musu suka yi wanka suka koma d'akin.
Mahaifiyar Shamsu na jin dik abinda ke faruwa sai ta hau hamdala tana sanya musu albarka dan kuwa a zaton ta Ameerah budurwa ce basu son aga zanin gadon su a lalace shi yasa shamsu ya wanke tin kan kowa ya gani.
Bayan sun koma ɗaki shamsu waje ya samu a saman gadon ya kwanta zuciyar shi sam babu daɗi,ita kuwa Ameerah baccin ta ta hau yi cike da natsuwa da salama.
Wai wanzami baya son jarfa,ta yaya zaka lalata yaran mutane ka tsammaci samun kamilalliya? Wallahi tin wuri idan kana da wannan tunanin ma a ran ka ka cire shi, domin kuwa matsawar ka yi soyayyar shan minti da 'yar wani ka sani dik natsuwa da shigar budurwar ka hijabi zai wahala ba a yi da taka ba, idan kuwa ka taɓa aikata oga kwata-kwata to ka tabbata dik natsuwar budurwar ka sai kaje za ka sha mamakin rijiyar da za ka afka, idan kuma Allah ya sa ka tsallake rijiya da baya to ka sani ko Allah yana son ka da rahama ne yana so kayi taubatan nasuha ko kuma talala yayi maka, ko kuma a dangin ka ka jawa wata salihar da bata ji ba bata gani ba wani irin ka zai je ya lalata ta itama.
A haka amarya da ango suka kwana kowa da abinda ke cikin ranshi, da asubar fari Umman su Billy ta fito ta ga shanyar da ta ga shamsu yayi a daren jiyan ta bushe, sai ta sanya hannu ta cire zanin gadon ta hau ninke musu tana murmushi,tana sane ta ninke zata kai musu dan ta sake ganin a halin da zata tarar da Ameerah.
Sallama ta zabga a bakin ƙofar d'akin tana jiran Ameerah ta fito ta tabbatar da zargin ta, Ameerah kuwa har ta dire zata fita Shamsu yayi sauri ya riƙe ta yayi mata nuni ta koma ta zauna ta langwab'e, dariya tayi ta kuwa ta koma ta kwanta shi ya fita,gaishe da mahaifiyar shi yayi ya hau sosa ƙeya zai karb'i zanin gadon nasu yace,
"Na so na samu farkawa da wuri na ɗauke ai sai bacci ya ɗauke ni daf da asuba saboda jiya bamu yi bacci sosai ba tana ta kukan bata da lafiya,"
"Asshaa ! Allah ya sawaƙe, yanzu me kuke buƙata?"
Cikin sauri Shamsu yace,
"Ruwan zafi dan Allah,jiya naji tsoron kar na ƙarar maki da kananzir shi yasa ban sake ɗora mata ba,"
Ameerah na d'aki tana jin takaicin Shamsu, dan kuwa ta zaci zai ce abinci suke buƙata saboda wata jahilar yunwa da take ji sai taji yace ruwan zafi, cikin takaici ta furta,
"Gyatumar ka zan fige da asubar nan da zaka nemo min ruwan zafi ina jin yunwa?"
Umman su Billy kuwa cike da farin ciki tace masa,
"Kar kaji komai ka koma ka kula da ita bari naje na kunna wuta a ɗora muku,Allah ya bata lafiya,ba dan ɗan fari bane kai shamsu da da kaina zan zabga guɗa da asubar nan, amma dole na haƙura safiya tayi a kira Goggon ka a sanar da ita ta faɗawa dangi matar ka ta cika mace nice shaida."
Tana tafiya ya saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ya koma ɗakin ya tarar da Ameerah ta cika tayi famm kamar ta fashe, kallon ta yayi yace,
"To meye kuma kike b'ata rai yanzu da asubar nan?"
"Yanzu shamsu fisabillahi a tambaye ka me muke buƙata kace wai ruwan zafi? To uwar me zan da hyi