Showing 186001 words to 189000 words out of 276165 words
Chapter 63 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
Ba mugu,idanun ta ne suka sauka akan wata jar mota dake zaune a layin garin nasu, cikin sauri suka nufi wajen suka tsadance da driver, ba jimawa bayan ta biya ya sallami ƴan union na wajen ya dauke su suka bar tashar.
Tafiyar awa ɗaya da wasu ƴan mintinan ce ta kai su garin Ba mugu,direct gidan malamin tsubbun da Aunty Naja ke kai su suka nufa,suna isa Naja ta ce wa driver ya jira su ba jimawa za su yi ba.
Koda suka shiga sun tarar da malamin tsibbun zaune da kayan aikin shi yana jiran su, dan kuwa tin a daren ranar da za su zo Naja ta sanar da shi zuwan su,kallon su yayi yana wani lashe baki kamar baƙin maye,kallon Mommy ya yi yana wani ƙanƙance ido ya ɗaga hannu yana nuna ya ce,
"Ah ah ! Wannan ba ita bace matar yariman garin nan namu wadda mijin ta ke son yi wa kishiya kwanan nan?"
Gaban Mommy ne ya yanke ya faɗi,cikin sauri ta zauna a gaban shi kamar zata shiga cikin kayan duban nashi,murya na rawa ta ce,
"Dan Allah malam ka tausaya min kamar yanda ka tausaya min da farkon zuwan mu, ko nawa kake buƙata zan baka,bana son kishiya bana son wanda yake son kishiya,ban taɓa sanin ina son miji na haka ba sai da ya sanar dani zai ƙara aure."
"Kwantar da hankalin ki, tin a daren jiya da Naja ta sanar dani zuwan ku na hau yi maki aiki, sai dai ban zaci za a zo dake ba shi yasa kika ga ina mamaki,yanzu me kike so ayi wa ita yarinyar da zai aura ɗin? Kina so a haukata ta ne, ko a kashe ta, ko kuma a sa tabi duniya kowa ya manta da ita?"
"Ni bana son a yi mata ko ɗaya daga cikin waɗannan malam, so nake kawai a raba su, a sanya musu tsananin ƙiyayyar junan su,ta yanda ko ganin juna baza su sake ƙaunar yi ba har abada balle su auri junan su,ko a sanya mata lalurar da zai guje ta ita kanta taji bata son auren shi saboda lalurar."
"In dai wannan ne an gama, sai dai wani hanzari ba gudu ba, a binciken da nayi na gano cewar yariyar a ma'aikatar mijin ki take itama."
"Kan uban can ! Dama abokiyar aiki Abdul yayi mace shine bai sanar dani ba? Yaushe ma suka fara yin masu aiki mata a wajen nasu? Malam dan Allah ni so nake ma duk wata mace dake wajen a kora ta,bana son kowacce mace ta raɓi miji na indai ba muharramar sa bace."
"An gama, sai dai zaki saki bakin aljihu sosai saboda wannan aikin babban aiki za a yi maki,saniya za a yanka wa aljanu su sha jini sosai a yi wa almajirai sadaka da naman."
"Malam ko nawa ne zan biya ayi aikin nan bani da matsala akai,ni dai dan Allah ina son aikin yafi na baya kyau,na yarda da kai zaka yi ma abinda ya fi hakan,dan haka ka bani No wayar ka da Account no ɗin ka sai na tura maka kud'in."
Babu ɓata lokaci ya karantawa Mommy No wayar shi tayi saving, sannan ya bata account No ɗin shi tayi masa transfer ɗin kud'in aikin har ma da ƙari,cike da jin daɗi suka baro ƙauyen Ba mugu ko ziyara bata kai wa su Innoh ba.
Koda suka koma gidan su sun tarar da gidan a rufe kamar yanda suka barshi,hakan ne ya baiwa Mommy tabbacin Abdul bai dawo ba, girki ta tashi ta yi mai daɗi tayi amfani da maganin da malamin nasu ya bata,tana gamawa ta wuce d'aki ta sheƙa wanka ta sanya riga da skirt na wani material mai laushi,kalar kayan ta amshi farar fatar ta da ciki yasa ta ƙara yin haske mai kyau,nan da nan gida ya kaure da ƙamshin turaren wuta mai haɗe da maganin sihiri,tafe take tana ƙara hura garwashin da bakin ta a zuciyar ta tana fatan Allah yasa malamin nan ya gama aikin da ya rage a daren yau.
Ta bangaren Abdussabour kuwa tinda aka tashi aiki Maimoon ta ja shi suka sake fita,wannan karon zuciyar shi bata son fitar ko kaɗan amma babu yanda zai yi da ita,dama bahaushe yace tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa zai doka,dan haka Abdul ya riga da ya san cewa ya d'akko ruwan dafa kan shi.
Hotel ɗin da suka je ranar farko shi suka sake komawa,tin da suka shiga Maimoon ke ƙoƙarin jan ra'ayin Abdul ɗin amma yaƙi bata haɗin kai, cikin fushi ta zaro wayar ta tana wani cika tana batsewa tace,
"Tinda na kula ban da amfani a wajen ka, bari kawai na watsa video ɗin mu duniya taga irin abinda kake yiwa yaran mutane,dan kuwa dik wanda ya gani zai tabbatar da ranar farko na fara kusantar namiji,kai kuma me kake da shi da zaka kare kan ka?"
"Ya kike so in yi ne Maimoon? Gaba ɗaya gangar jiki na ta ƙi bani had'in kai, kwata-kwata ni bani da wata sha'awar sake kusantar ki."
"Au haka ma zaka ce min? To na ji baka da sha'awar sake kusanta ta, ya maganar auren namu yanzu?"
Shiru yayi yana roƙon Allah ya kawo masa mafita,yayi nadamar kasa jure sha'awar ɗan ƙanƙanin lokacin da yayi, yanzu gashi biyan buƙatar da yayi na ƴan mintuna na neman sanya shi a nadama har zuwa ƙarshen rayuwar shi.
Kamar wadda aka mintsina haka Maimoon ta miƙe tsaye,wani irin nishi tayi sannan ta kama marar ta,cikin gigicewa ta saki wayar dake hannun ta ƙasa ta fasa wani irin ihu,a guje Abdussaboor ya nufi wayar hannun ta jikin shi na wata iriyar rawa,direct videon da take ƙoƙarin watsawa a duniya ya goge daga wayar gaba ɗaya,jakar ta ya hau dubawa ya samo camerar da ta ɗauke shi video a ranar su ta farko,babu tunanin komai ya hau goge dik wani abu dake kan camera ɗin,sannan ya rotsa ta a ƙasa, sai da ya kammala dik wani goge-gogen da yake son yi ne hankalin shi ya kai kan Maimoon dake yashe a ƙasa tana murƙususu kamar wadda ake shirin zarewa rai.
Cikin kuka da fitar hayyaci ta miƙa masa hannu tana faɗin,
"Ka taimaka min zan mutu,ciki na ciwo yake yi."
"Kamar ya in taimaka maki,ina ce yanzu kike neman sanya ni a bala'i? Kin ga tafiya ta, ga wayar ki nan ki kirawo wata a cikin ƙawayen ki ta taimaka maki."
"Dan girman Allah Sir ka taimaka min, bana so na mutu yanzu, wayyoo Allah na zan mutu."
Tausayin tane ya kama Abdussabour,cikin sauri ya taimaka mata ya ɗaga ta ya ajiye ta a saman gado, gani yayi jinin ya dena zuba amma dik da haka bata daina murƙususun da take yi ba,No wata ƙawarta tace ya kirawo tazo ta maida ita gida,babu b'ata lokaci kuwa ya nemo No ya kara mata a kunne, baya ma so a ji muryar shi a san suna tare,cikin nishi da fitar hayyaci Maimoon ta ce,
"Khairi dan Allah...ki zo Royal hotel ki ɗauke ni banda lafiya."
Bayan ƙawar Maimoon ta amsa ne Abdul ya kashe wayar ya sake gyara mata kanta ya faɗa banɗaki,sai da ya gyara jikin shi sannan ya fito ya kalle ta,tana nan kwance yanda ya barta sai murƙususun ciwo take yi,cikin sauri ya tattare nashi ya nashi ya bar ɗakin,tinda ya fita yake zuba sauri be tsaya ba sai a bakin motar shi,a guje ya ja motar shi ya bar hotel ɗin ya nufi gida. Tin a hanya yake jin kanshi na yi masa wani irin nauyi,tsananin ƙiyayyar Maimoon yake ji tana ninkuwa a zuciyar shi fiye da ƙin da yake yi mata a baya,hankalin shi gaba ɗaya ya tafi gida, fatan shi kawai ya buɗe idanun shi ya ganshi a gaban Mommy,a yau ya yarda ya amince Mommy itace rayuwar shi,itace farin cikin shi,ba zai taɓa iya ci gaba da rayuwa mai daɗi ba idan babu ita,ba ya jin zai iya yi mata kishiya,furucin da yayi mata na zai ƙara aure ma jin shi yake yi kamar ya aikata babban zunubi, ya zai yi ya wanke kan shi a wajen Mommy ne?
Da wannan tunanin ya tsaya a wani super market yayi wa Mommy siyayya,yana fita ya tsaya a wani shahararren wajen gashin kaji ya saya mata har guda biyu ba dan babu a gidan ba,sai dai yayi hakan ne kawai dan yasan tafi son gashin waje,gida ya nufa yana addu'ar Allah yasa ta dena fushi da shi,zai bata haƙuri har sai ta yafe masa, zai bata kulawa fiye da yanda yake bata a baya.
Ko da ya isa bakin gate ɗin gidan ji yayi kanshi ya sara da ƙarfi har sai da ya dafe kan da hannu ɗaya,a hankali yaji hankalin shi na dawowa jikin shi, waje ya fita ya buɗe ƙofar gidan ya shiga sannan ya koma ya shigar da motar shi ya kashe,sai da ya fitar da kayan da ya siyo sannan ya koma ya rufe gidan.
Tin kafin ya juya baya yaji ƙarar buɗe ƙofar shiga gidan,juyawa yayi a hankali ya hango ta tana tahowa cikin takun ta mai ɗaukan hankalin shi,murmushi ta sakar masa ta lashi leb'en ta na ƙasa tana wani kashe masa idanu,kallon leb'en ta da suka sake kumbura saboda tsufan da cikin ta yayi,shi dai duk duniya baya jin akwai wadda ta kai masa Hadizan shi kyau.
Kamar yaron da yayi kewar mahaifiyar shi, haka Abdul ya tafi wajen Mommy da sassarfa ya rungume ta yana sauke manyan ajiyar zuciya,a cikin zuciyar ta ta jinjinawa aikin Malamin ta, sannan ta rungume Abdul da kyau a jikin ta, sumbatar tsakiyar kanshi tayi sannan tace,
"Baby mu shiga ciki na gaji da tsayuwa, kasan yanzu nayi nauyi bana jure tsayuwa."
Da sauri ya sake ta ya nufi kayan da ya zo dasu ya kwashe yabi bayan ta,ita kuwa sai wani juya mazaunan ta da tasan suna ɗaukan hankalin shi take yi,a haka suka shiga gidan ya zube komai a saman center table ya rungume ta a jikin shi,cike da shagwab'a Mommy ta ɗan ture shi tana tura manyan leb'unan gaba ta tace,
"Ni dai ka ƙyale wa masoya na ni, tinda ka daina so na,ina ce aure za ka ƙara? Sai ka jira amaryar ka tazo sannan ka..."
"Allah ya tsare ni da ƙara aure ina da mace kamar ki,ko ranar ma raina ne ya ɓaci akan abinda kika faɗa akai na shi yasa, inshaa Allahu alƙawarin mu na nan ba zan taɓa yi maki kishiya ba."
Kallon shi tayi tana wani kashe ido tare da ɗage gira tace,
"Da gaske kake ba zaka yi min kishiya ba?"
"Har abada,ke da kishiya sai dai a aljannah idan Allah ya mallaka min matan aljannah."
Shiru Mommy tayi bata ce komai ba, dan kuwa tasan bata isa furta komai ba a wannan gaɓar,hannun Abdul kawai ta ja ta wuce dashi band'aki ta taya shi wanka, sai da ta taimaka masa ya sanya kaya sannan suka fito parlour dan su ci abinci,Aunty Naja Mommy ta kirawo tazo ta gyara dik abinda ke buƙatar gyara, sannan suka zauna suka ci abincin su tare suna ta hira, sosai Abdul ya sake da Naja har baya jin nauyin nuna wa Mommy soyayya da kulawa a gaban ta, kallon juna Mommy da Naja suka yi suka saki murmushin da su kaɗai ne suka san ma'anar shi.
***********************
Kwanan Billy biyu bata cin abinci, kullum energy drink Any ke bata da wani lemo na diet,jikin ta da aka yi wa sabon BBL ya ƙara kyau da bada shape mai kyau, kwance take a saman cinyar Any tana shafa sabuwar magen da Any ta siyo mata saboda ɗebe kewa,cikin shagwab'e fuska Billy tace,
"Babe, waini meye dalilin da yasa kika ce ba zan ci abinci ba sai dai waɗannan lemukan da na gaji da sha? Ina craving cin abinci kala-kala,ni ba azumi nake ba ba komai ba amma na ƙi cin abinci?"
Shafa fuskar Billy Any tayi tace,
"I am sorry baby,ki ƙara hakuri, yau da yamma jiran da muke yi zai zo ƙarshe,kin san dai na sanar dake akwai wani show da za a yi wanda zamu samu mahaukatan kuɗi ko? To yau da dare za a yi shi, after that you can have whatever you want my darling."
Cike da zumud'i da kwaɗayin abinda Any ta sanar da ita za su samu ta tashi zaune tace,
"To yanzu da yaushe za mu fita zuwa wajen show ɗin?"
"Sai 11am za a fara show ɗin,amma kafin nan zamu je saloon za a gyara mana jiki ok?"
"Ok, Allah ya kaimu."
"Ameeen."
Sai da Any ta gama tura saƙonnin da zata tura a email, sannan suka yi shiri suka tafi saloon, suna shiga Billy tayi ido biyu da matar nan da ta taɓa zuwa har gida tayi mata gargad'i akan ta gudu daga wajen Any,cike da mamaki Billy ke bin matar dake ta kaucewa saboda kar Billyn ta nuna ma ta san ta............
*Assalamu alaikum mutanen ƙwarai masu albarka,ina godiya sosai da addu'o'in ku a gare ni, Allah ya bani lafiya alhamdulillah, Allah ya ƙara mana zumunci domin shi. Yauwaa za ku ga na dawo da kiran Amy da Any, saboda mistake nayi tin farko sunan Any ne ba Amy ba, a ci gaba da karatu da hakuri, a kauda kai akan errors a ɗauki darasin dake ciki, na gode da tunatar dani kuskuren da na yi,inshaa Allahu idan an kammala dika zan bi nayi editing da kyau.*
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️ ✨
PAGE 76:
Har aka kammala masu gyaran jiki da gashin su Billy bata sake sanya idanun ta akan baturiyar nan ba,ko sama ko ƙasa haka ta neme ta ta rasa,cikin zuciyar ta kuwa cike yake fal da mamakin rashin sake ganin baiwar Allah'n da bata yi ba har suka bar wajen.
Direct wani hotel suka nufa,hannun ta cikin na Any suka isa wani ɗaki mai masifar kyau,dik yanda zan kwatanta maku yanda ɗakin ya haɗu ba lallai ku fahimce ni ba,abinda na sani kawai shine, ɗakin ya haɗu,an kashe masa dukiya an wadata shi da kayan ƙawa.
Baki Billy ta saki tana bin Any da kallo, wayoyi da makullin mota Any ta ajiye a saman gado sannan ta faɗa ta kwanta tare da faɗin,
"Washhh Allah na ! Na gaji sosai, baby come here, come and lay down with me."
Baki Billy ta rufe sannan ta sake buɗe wa ta furta,
"Wow ! This is incredible, this room is hug and beautiful,baby wai kina nufin dik kin mallaki dukiyar da zaki dinga irin wannan extravagant rayuwar?"
Hannu Any ta sake miƙawa Billy a karo na biyu, a hankali Billy ta kama hannun nata suka kwanta sosai a gadon manne da junan su,hannun Billy Any ta haɗe da nata sannan ta sumbaci bayan hannun ta kafin ta ce,
"Baby wai har yanzu kina da shakka ne akan irin dukiyar da nake da ita? Ok lets do something,me zai hana muyi renewing signing ɗin takardun auren mu, wataƙila ta haka ne zaki fi gane me nake nufi, ina zuwa."
Cikin zuciyar Billy wani irin farin ciki ne ya mamaye ta, bata da burin da ya wuce na taga ta mallaki rabi ko dika dukiyar Any,amma a zahiri sai ta shagwab'e fuska ta kwantar da kanta a bayan Any dake making call, sai da ta bari ta gama wayar da take yi sannan ta ce wa Any,
"Haba Baby ! Ni fa ba wai ban yarda dake bane, me yasa zaki ce a kawo maki takardu na sake sanya hannu? Na yarda na amince komai kika mallaka kamar nawa ne,kawai bana gajiya da shan mamakin kalar dukiyar da kika mallaka ne, idan ban manta ba kud'in kama ɗaki a hotel ɗin nan na wuni ɗaya ya kai miliyoyin nera tamu ta Nigeria,and i see no reason why da zamu zo nan muna da gida mai kyau muyi westing kuɗi masu yawa haka."
Sai da Any ta sumbaci Billy dake wani marairaicewa kamar babu wani mugun nufi a ranta sannan ta ce mata,
"Sweetheart kar ki damu,ko nawa zan kashe akan ki ba faɗuwa bane, riba ce mai girma,saboda ina son ki ok? Dan haka kar ki sake hango dukiyar da nake kashewa akan ki, ki dinga hango soyayyar da nake baki, kina jin yunwa ko? Bari a kawo mana koda salad ne da drinks na yi maki alƙawari zuwa gobe zaki fara cin abinci kamar yanda kike so,a yau ina so mu raya daren nan ne da soyayyar da bamu taɓa yin irin ta ba, ina so na nuna maki wata hanyar samun farin cikin ma'aurata irin mu wanda wataƙila kin sha jin labari amma baki taɓa yi ba, kin san ina son ki ba zan taɓa cutar dake ba ko? Kin san dik wani faɗi tashi da nake yi akan ki ne ko? Na yi maki alƙawari zan tara mana dukiyar da mu da yaran mu da jikokin mu dik sai sun more ta kafin mu koma ƙasar mu."
Maganganun Any sun karya zuciyar Billy har ta fara zubar da hawaye, ji take yi a ranta duk duniya babu wanda zai so ta sama da Any,cikin sauri ta haɗe tazarar dake tsakanin su, ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi,a hankali Any ta janye jikin ta daga na Billy sannan ta mike ta nufi ƙofar, buɗewa tayi taga wani bature tsaye,kallon juna suka yi Any ta kashe masa ido ɗaya sannan ta karb'i takardun hannun shi ta d'aga yatsun ta biyu tayi masa alama da kai,shima yatsan shi ya d'aga mata sannan ya yi murmushi ya bar wajen, ɗakin ta koma tayi tsalle ta haye gado sannan ta ja Billy Jikin ta, wasanni ta soma yi mata sannan tace,
"Baby zo nan da hannun ki ki rubuta, dik dukiya ta zan raba ta biyu rabin ya zama naki, ko da sani na, ko babu sani na zaki iya cire kuɗi kiyi abinda kike so,matso nan ga pen ki sa hannu."
Ba tare da wani tunani ba Billy ta karb'i takarda ta fara saka hannu,sai da ta saka hannun nema ta karanta layin farko, lambobin kud'in da ta hango ne suka ɗauke mata hankali ta hau ƙissimawa a ranta.
'Yanzu idan aka canja waɗannan dalolin ko million nawa za su koma a can gida Nigeria?'
Room service ne ya sake buga ƙofa, babu b'ata lokaci aka shigo da kayan shaye-shaye da maƙulashe aka jere masu a saman table ɗin dake gaban gadon,nan fa yawun