Showing 87001 words to 90000 words out of 276165 words

Chapter 30 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

nan to gaskiya se an aura min shi,"

Wata uwar harara Bilal ya sakar mata sannan yace,

"Eh tinda shi igiyar shanya ne se a d'aura maki shi mana shashashar banza kai, haka kawai ya rasa wadda zai aura se ke da kika gama zuwa gidan wasu aikatau,"

"Ai ba gidan maqasqantan mutane naje aikatu ɗin ba gidan Ambasada ne"

"Ambasadan masu kwasar kashi ko na ina? Kin ma san ma'anar ambasadan ne ke?"

Bilal ya tambayi Billy da ta qi tashi tabi bayan iyayen ta, dan kuwa kowa ya ɗauki maganar ta a matsayin shiririta sun fita sun bar fadar, shi kuwa Sarki murmushi kawai yake yi irin nasu na manya dan kuwa ba tin yau ba Bilal ke sanya shi dariya idan yazo gidan, yaro ne mai barkwanci da son Abdul, duk wani abu na ci gaba yana jan Abdussaboor su yi shi su samu alkhairi a ciki, haka zalika idan yaga abinda zai cutar da Abdul ko menene shi yana tsayawa tsayin daka yaga ya kawar da abun nan, yana juyawa zai fita yaga yanda Mommy ta kafe itama a waje ɗaya Innoh sai janta take akan ta tashi su tafi gida taqi,cikin ɓacin rai Bilal ya kalle ta yace,

"Ke zaki tashi ki bi uwar ki ku bar nan ko se na zaro dorinar can na yi ta tafka miki? Ji min yarinya kin gama b'ata rawar ki da tsalle sannan ki zo kina yi wa mutane kukan munafurci,"

Abdul ne ya kama hannun Bilal ya ja shi zuwa cikin gida, dan idan aka bar shi ko a gaban waye zai iya kai wa Mommy duka kamar yanda yace, suna fita mai martaba yace,

" 'Yata ki yi hakuri ki bashi lokaci, ki kuma yi addu'a, matar mutum kabarin shi ce, idan kece matar shi dole zai dawo gare ki, idan kuma ba ke bace ina maki fatan Allah ya baki wanda ya fishi alkhairi,"

Da kuka Mommy da Billy suka bar fada, qin shiga motar Munir su Innoh suka yi sai suka kama tafiya a qafa zasu koma gida, duk inda suka wuce kuwa mutane sai bin su da kallo suke ganin qatuwar budurwa kamar Mommy na kuka a titi.

Munir kuwa be sake bi ta kan su ba ya ja motar shi daga shi sai Saddeqa dan kuwa Ɗan liti da sabon adaidaitan shi ya zo tini ya wuce neman kuɗin shi.

Innah Laminde kuwa bayan sun shiga ciki abinci ta sa aka haɗawa Abdul da Bilal, dan kuwa ta san yana buqatar kulawar ta a yanzu fiye da kowanne lokaci,ya na buqatar inda zai jingina ya ji sanyi a ran shi, dan haka ko maganar ma ba zata ɗauko masa ba sai bayan ya huta ta kawo masa maganar Bilkisu,gida bata qoshi ba ai ba an kai wa dawa ba.

Da kyar ta samu Abdul yaci abinci ya sha ruwa da fura ya shiga d'akin shi ya kwanta, nan fa Bilal ya zauna ya dinga bata labarin a halin da suka tsinci Mommy da yanda ya dinga jin bata yi masa ba tin haɗuwar farko,Innah Laminde ma ta bashi labarin zuwan su na farko gidan ita da Billy, haka suka dinga tattaunawa tare da shawarwarin yanda za su cusawa Abdul maganar Billy a ran shi har ya manta da Mommy, dik da cewa har yanzu Bilal baya son Mommy amma gwanda Billy akan Mommy a ganin shi.

A can gidan Ɗan liti kuwa Munir ne ke sallama da Saddeqa bayan ya shiga sun gama sallama da Baabaa dan kuwa a ranar yake so ya koma aka yi wannan kiran, tsaye take a jikin motar shi suna yi wa junan su alqawarin kasancewa da junan su dik rintsi duk wahala,a haka Innoh da Mommy suka qaraso sai tada qura suke yi duk inda suka wuce kamar wasu shanu,cike da takaici Innoh ta tsaya a gaban su tace,

"Ku gama iskancin ku dole ne ka dawo ka auri Ameerah saboda 'yata ba zata mutu a banza ba saboda kai,ke kuma zaki shigo ki same ni ne,"

Ta wuce tabi bayan Mommy da ko kallo su Munir basu ishe ta ba,cike da damuwa Saddeqa ta sauke kanta qasa tana jin wani irin tsoro na taso mata tin daga zuciyar ta yana bayyana a saman fuskar ta,cikin sigar lallashi Munir yace,

"Kar ki damu da barazanar ta inshaa Allahu Munir na Saddeqa ne ita kaɗai, ina zuwa zan cewa Abbah ya zo ayi maganar nan a wuce wajen tinda na samu Ummee ta sanar da shi kuma ya yi farin ciki da hakan, kin ga yanzu dik wata fargaba bamu da ita ko?"

D'aga masa kai tayi tana aro jarumta ta sanya a fuskar ta saboda kar ya tafi yana tunanin damuwar da ya barta a ciki.

Kuɗi ya bata kamar kullum yau ma qin Karb'a tayi sai da ya dinga yi mata magiya da roqo sannan ta Karb'a tayi masa godiya ya tafi cike da kewar ta.

A can gidan su Billy kuwa.........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI












RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨















PAGE 33:











Tinda suka koma gida Billy ke yi wa mahaifiyar ta kuka akan ta san yanda zata yi a aura mata Abdul in dai ana so ta ci gaba da zama a qaunyen Ba Mugu in ba haka ba zata koma inda ta fito ba za su sake ganin ta ba,ita kuwa Ummah ta rasa inda zata sanya ranta ta ji sanyi saboda kukan Billy na qona zuciyar ta,duk yaran ta tafi son Billy a cewar ta ta fi su tausayi dan kuwa gashi har fita neman na kai tayi dan kawai taga ta wadata su da abubuwan arziqi su fita daga quncin talauci da ke damun mutanen Nigeria baki ɗaya.

A d'akin Billy suka yi masauki gaba ɗayan su, Ummah ce tace,

"Yanzu Bilkisu baza ki yi shiru ki ji wanne hukuncin zan yanke akan wannan maganar ba? Ki duba ki ji yanda kan ki ya ɗauki zafi saboda fitinannen kukan da kike yi?"

Mahaifin Billy kuwa cewa yayi,

"Kar ta yi shirun tinda akan ta aka fara irin hakan, ni kun ga fitata ma,amma ina so ku buɗe kunnuwan ku da kyau ku jini,maganar Sarki dai ta zauna dole a bita Bilkisu ki samu waje ki zauna daga yau babu ke babu komawa birni aikatau,kar kuma in samu labarin kin kori saurayi idan an zo zance wajen ki, ki tsaya ki bawa duk wanda yazo zance wajen ki dama ku fahimci juna, idan yayi miki sai a yi da shi, idan be yi maki ba sai ki sauya wani daga nan zuwa qarshen shekarar nan in Allah yaso zan aurar dake kin ji na faɗa miki,"

Yana gama maganar shi ya shuri takalman shi ya bar gidan, yana fita Billy ta saki wani uban ihun da ya janyo hankalin qannen ta maza guda biyu, nan take mahaifiyar su ta kora su waje, ta zauna a kusa da Billy da ta ɗora hannayen ta aka tana rusa kuka tace,

"Wai ni bana ce ki yi shiru bane? Ina sane da kalar son da kika taso kina yi wa Abdul tin kina qarama ba kuwa zan zuba ido ya kub'uce miki ba, na yi miki alqawarin sai kin auri Abdul hankali na da naki zai kwanta,zuwa dare kafin baban ku ya dawo daga shago zan je na samu Yaaya mu tattauna akan wannan maganar,Abdul naki ne ke kaɗai dan ko kishiya ba zan bari yayi miki ba bayan ya aure ki,"

Billy na jin haka ta fara rage kukan ta, dan kuwa ta jima tana son Abdul bata jin zata iya haƙuri da shi ya auri wata ma balle Mommy, ai ko da take tafiya yawon banzan ta ba zai hana watarana ta yi aure ba, Abdul kuwa shi ta ajiye wa kan ta a duk sanda ta gama yawon barikin ta ta aura,ba wata 'yar hau ɗin da zata aure mata shi ta kyale ta, Mommy ta tabbata ta kula da kan ta dan kuwa yanzu qazamin yaqi zai b'arke a tsakanin su.

Wayar ta ce take ta ringing amma tana katsewa dan kuwa bata son amsa wayar Man Ummah na kusa da iya dan kuwa yana iya faɗin wata kalmar da zata bayyana ko ita wacece a harkar bariki, shi yasa take so Ummah ta tafi dan ta samu ta amsa kiran nashi, amma Ummah taqi tashi so take ta zauna da 'yar tata ta kwantar mata da hankali sosai.

Rashin ɗaukan wayar Billy kuwa a wajen Man ɗin nata ya jawo masa shiga babban tashin hankali, dan kuwa irin haka bata taɓa faruwa a tsakanin su ba, a sukwane ya fita ya bar gidan har yana mantawa da wayoyin shi,direct gidan Hajiya K'waisa yaje ya tarar dasu an saka musu bandage a hannu da wuya, cikin hanzari ya isa ya zauna a kusa da Samuel dake ta lallashin Hajiya K'waisa akan ta ci abinci amma taqi sai tararar da hawaye take yi tana faɗin,

"Shikenan asiri na ya tonu yarinyar nan ta rusa min duk wani shiri da tanadi na da nayi akan ta zuwa qarshen shekarar nan, Allah ya tsinewa wannan yarinya albarka ya hana ta morar kan ta matsiyaciya,yanzu dole na je a cikin waɗannan yaran da na saka a tsohon gidana na duba na ga wacce zan d'akko na rena kafin new year,ina murna ga yarinya 'yar shila komai yaji natural ba artificial ba shine ta watsa min qasa a ido,"

"Na ji baby an yi maki ba dai-dai ba amma ki yi hakuri ki ci abinci ki sha magungunan ki, ni da kaina zan sama maki wata ki yi hakuri kin ji?"

Da kyar Hajiya K'waisa ta buɗe baki Samuel ya sanya mata abinci ta hau taunawa kamar bata so, tissue paper ya zaro a cikin k'walin ta ya goge masa hawayen shi, Man da ya gaji da ganin dramar 'yan daudun ne yace,

"Wai ni Hajiyar mu me yake faruwa ne? Wa ya b'ata wa sarauniyar kyawawa rai yanzu na ɗauki mummunan mataki akan shi? Samuel me ya same ku haka ko hatsarin mota kuka yi ne na gan ku da bandage?"

Wani mugun kallo Samuel ya sakar wa Saurayin Billy daga baya ya kauda kai, dan ya ji kishin kirarin da aka yi wa K'waisan shi a gaban shi,sake d'iban abinci yayi ya bawa K'waisa ta Karb'a tana yatsina tare da yin wani mugun tari,shafa bayan ta Samuel yayi, a hankali tace,

"Hummm ai gwanda hatsarin mota da yarinyar nan ta kafa maka hauren ta ɗaya a jikin ka,yanda kasan dafin maciji ko kunama haka dafin dake jikin haqorin ta yake, yanzu haka zazzaɓi ne a jiki na,"

"Ah ah ! Wacece haqorin ta yake da dafi haka har ta kai ku da nad'e hannu da wuya da bandage?"

Cikin hargowa K'waisa yace,

"Kai ka ishe mu da surutu ka barmu mu ji da tashin hankalin dake gaban mu, tashi ka tafi dan Allah ita kanta Billy bana son ganin ta kar ta dawo min nan, bana son harka da 'yan hau, Amy dik iskancin ta bata taɓa yunqurin saka hannun ta a jiki na ba har ta bar gidan nan sai wannan me wakeken bakin kamar qofar gari,dama bahaushe yace man kad'e be saba da tandu ba, wasu alheri sam be kamace su ba sun fi son tsiya to taje can ta qarata, Sallau ! Sallau ! Ka haɗa min jakunkunan da na ce ka haɗa ko?"

Da gudu Sallau ya fito daga kitchen ya tsaya gaban K'waisa yace,

"Eh na haɗa Hajiyata,"

"To d'akko ka bawa wannan bawan Allah'n dika jakunkunan ɗaya ta Billy ɗaya ta Mommy bana so na sake ganin ɗaya daga cikin su,a kai wa wani sarkin gari da yawa maye ba zai ci kan shi ba,shi yini da arziqi ai ya fi kwana da tsiya, zan nemo wasu su maye gurbin su, mata fa kullum kawo kan su suke yi ni ce ma na ke qin kulawa masu buqatar taimako na ware masu gida na musamman suke baje haja da kolin su,ina zuwa wajen su na ce ina neman wadda zan mayar 'yar gata kamar yanda nayi musu zan samu masu son zama kamar su ko ma fiye da su ma, dan haka tashi ka bar min gida kafin raina ya fi haka ɓaci,"

Duk yanda saurayin Billy yaso ya baiwa Hajiya K'waisa hakuri qi tayi ta dinga mafisa da bala'i qarshe Samuel ya shiga suka yi masa kaca-kaca suka kore shi,jiki babu k'wari haka ya zuba jakunkunan a motar shi ya bar gidan,direct hanyar qauyen Ba Mugu ya ɗauka dan kuwa be ga ta zama ba irin wannan mummunan abun ya samu masoyiyar shi, wataqila shi yasa ma bata ɗaukan wayar shi.

***************************

Mommy ce kwance a d'akin Innoh a saman gadon ta mai rumfa tana ta tsiyayar da hawaye,ta gaji da kukan amma ya qi dena zuwa bata taɓa nadamar zaman ta 'yar bariki ba sai yau,irin nadamar nan da mutum ke jin dama za a dawo da hannun agogo baya da be aikata abinda yayi ba mara kyau, mommy bata taɓa sanin soyayyar Abdul ta ci qarfin zuciyar ta kamar haka ba sai yanzu da ya furta ya tsane ta baya son sake ganin ta, idan baya son ganin ta ai ita tana son ganin shi ko? Ya zata yi da soyayyar shi? Wa zai aure ta yanzu?

Hasken da ya haske idanun ta ne ya sanya ta rintse idanunta ta juyar da kan ta ɗayan bangaren ta ci gaba da kukan ta,cikin halin ko in kula Innoh tace,

"Au wai har yanzu kukan kike yi ? Lallai iska na wahal da mai kayan kara, ba nace ki dena kukan ba zan ɗauki mataki akan matsalar taki ba? Na kula da ke da Ameerah kashe kan ku kuke son kuyi ku huta, ni a duniyar nan akwai wanda soyayyar shi zata kai ni kwance ne? Ko uban ku da muka yi soyayyar yarinta har ta kai mu ga aure yace baya sona gaba na zan kama balle wanda be aure ni ba,Ita tana can kwance wata da watanni tana fama da son maso wani,kema shine zaki zo ki jibge min ku zama biyu ko? To ni ba uwar wahalallu bace miqewa zaku yi kuyi sharafin ku yanda kuke so aure ne sai an yi shi,bari ma ki gani, Ameerah ! Ameerah miqo min waya ta in kin gama kiran wahalar da kika sa kan ki, na faɗa maki wannan yaron jikan kafaffiyar tsohuwar nan ba zai amsa kiran ki ba ko me zaki yi,"

Ameerah ce ta fito daga d'akin ta daga ita sai ɗaurin qirji,fuskar nan ta faɗa daga manyan idanu sai dogon baki, wuya ya zurma ya yi qashi k'wandala-k'wandala, yawu ta zubar ta shiga d'akin Innoh bakin nan se tashin wari yake yi tace,

"Gashi,"

"Um um umhhhh ! Fitar min a d'aki shegiya qazamar banza, duk qazanta ta yarinyar nan kin shallake tunani na, kan uban can gunnusuru, Ameerah kashe kan ki zaki yi da wari ko? Kece tsamin hammata da warin baki ga uban warin dake fitowa a jikin ki kamar wadda bata tsarkin kashi? Kaiii subhanallahi"

Waje Innoh ta fito ta tsirtar da yawu ta koma d'akin ta tana ci gaba da masifa ta danna kiran Naja, kamar wadda take jira kuwa ta ɗauki kiran,babu sallama Innoh tace,

"Ke 'yar uwa ki zo ki yi min rakiwa ina zaune za a sabauta min yara,ki zo maza ina da buqatar ki raka ni wajen me kankat,"

"An gama kuwa dama jiran kiran wayar ki nake Ameerah ta kira ni tana kuka tace min wancan matsiyacin yaron ya tafi ko neman ta be yi ba balle suyi sallama sai ma fita da Saddeqa da yayi a mota kuma suka dawo a mota ya wuce babu ko sallama"

"Hummm ke dai bari, dik da bana son haɗa zuri'a da waccan 'yar tsurut ɗin tsohuwar ina ga dole na bawa Ameerah abinda take so in ba haka ba halin da take ciki ya ta'azzara mutuwa zata yi, warin da take yi kaɗai ya isa ajalin ta,"

Dariya Naja tayi sannan tace,

"Gani nan zuwa Yaya kar ki yi wa 'yata mugun baki, Allah ya tsare ta da mutuwa akan d'a namiji"

"To Ameen ki yi sauri muje mu dawo da wuri,"

"To Yaya,"

Suna kashe waya ta miqe ta hau shirin fita, Saddeqa kuwa tana can gaban murhu tana hura wutar dora abincin rana, tana yi tana sharar hawaye saboda rashin mutuncin da Innoh tayi mata da zagin Yadikon Sule da bata ji ba bata gani ba da ta gama kafin ta bata umarnin ɗora abincin rana.

A gaban idanun ta Ameerah ta zauna a bakin rijiya ta saka hannu a ruwan tukunyar da ta jawo dan ta ɗora girki ta kurkure bakin ta ta zubar,tana ganin sanda na qasan yayi tsalle ya koma tukunyar, dole ta zubar ta sake d'auraye tukunyar ta zuba wani,ji tayi zuciyar ta na tashi a lokacin da ta tsaya kusa da Ameerah tana d'iban ruwa, nan take amai ya yunquro mata saboda warin hammata da wani hamamin da bata san daga ina yake fitowa ba a jikin Ameerah, ganin Saddeqa na son yin amai ne ya b'ata ran Ameerah cike da rashin mutunci ta shaqo Saddeqa ta saka a hammatar ta tana duka tare da zagin ta, nan take kuwa Saddeqa ta wanke Ameerah da aman da take ta qoqarin dannewa,ashar Ameerah ta d'ura ta sake kamo Saddeqa da ta galabaita ta shaqe ta tana duka, Innoh na ganin su taqi kula su balle ta raba, Naja na zuwa ta ja ta suka fita suka bar gidan a cewar ta ai Saddeqa ce tayi wa Ameerah rashin kunya, dan haka a bar su ta lallasa ta gobe bata qara ba.

Yanda Ameerah ke jijjiga jikin ta tana aikin qarfi haka warin jikin ta ke qara fitowa, kafin wani lokaci Saddeqa ta galabaita cikin ta taji yana juyawa kamar zata zaga gashi ta kasa k'watar kanta a hannun Ameerah dake ta jibgar ta tana kuka,salati Baabaa da ta idar da Sallar azahar ta doka tace,

"Yanzu Ameerah kashe marainiyar Allah zaki yi? Ina fa ji dan rashin adalci uwar ki ta gama zagin ta tasss har da mamaciyar dake qasa sannan aka haɗa ta da aikin girki, be ishe ku ba shine kike ta dukan ta kamar kin samu jaka yanzu me tayi maki kike mata wannan.......subhaballahi shin meye ya mutu a tsakar gidan nan me wari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login