Showing 75001 words to 78000 words out of 276165 words
Chapter 26 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
damuwar da take ciki,idanu kawai Mommy ta zuba mata tana binta da kallo tuhuma,dan kuwa bata san ina take nufi su je ba,yanzu a tsorace take da duk wani bil adaman da zai zo yace mata wai su je wani waje, to fa yanzu zata nuna maka rashin amincewar ta akan hakan.
Da kyar mommy ta yarda ta sanya dogon wando da wata rigar sanyi mai laushin gaske kalar pink me hasken kanta babu hula sai gashin dokin ta me kama da na mutane, takalmi Miranda ta sanya wa mommy a saman safar qafar ta ta kama hannun ta suka fita.
Tinda suka fita Mommy ke qarewa gidan kallo mamaki dik ya ishe ta wai nan gidan mutum ɗaya ne,bayada uwa ba mata ba d'a babu jika,lallai dole ya kashe maqudan kuɗi ya siyi mace ya kawo ta gidan ya azabtar da ita kamar yanda yayi mata, hawaye ne suka zuba mata a idanun ta ta sa hannu ta share ta ci gaba da bin bayan Miranda har suka isa lambun gidan, anan fa mommy ta sake baza idanu da hanci tana shaqar iskar ubangiji tare da qanqame jikin ta tana jin yanda sanyi ke ratsa ta,murmushi tayi da ta ga qanqara na sauka se ta tara hannun ta tana mamakin ganin ta, kusan gaba ɗaya qanqarar ta rufe ganyayyakin wajen da tukwanen da aka shuka wasu furanni, Miranda ce ta matsa kusa da ita tana murmushi ta furta,
"This is called snow,"
(Wannan shi ake kira da qanqara)
Kallon ta Mommy tayi tana sake maimaita me ta faɗa a zuciyar ta, Miranda kuwa maimaita me tace ta sake yi har sai da mommy ta maimaita itama daga nan suka yi dariya a tare, daga nesa da su suka ji an kwalawa Miranda kira suna juyawa suka ga Alex ya na kallon su a fusace ya furta,
"Get back in here you fools,"
(Ku dawo ciki ku wawaye)
Cikin sauri Miranda ta kama hannun mommy a tsorace ta hau jan ta dan su koma ciki, Mommy kuwa dake 'yar gidan Innoh ce uwar taurin kai sai ta cije ita a dole ba inda zata je......
*Me rabon shan duka?......*
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 28:
Tsayawa yayi yana ganin yanda ake jan Mommy tana dagewa,nan take yayi wa Miranda umarnin ta saki Mommy ya ga iya gudun ruwan ta, ana sakin hannun ta kuwa ta hau zagaye gidan da gudu tana neman hanyar barin gidan,dik inda ta nufa sai ta ga babu hanyar gudu,gate ɗin qarfen guda ɗaya ne kuma a kulle yake ba yanda za a yi ta gudu ,tafe take tana ihu tana faɗin a taimaka mata ta yi da hausa ta yi da turanci amma babu wanda ya san ma tana yi balle a taimaka mata ɗin,ba zato ba tsammani ta ji mutum a bayan ta a tsaye, ta na juyawa ya kife ta da wani gigitaccen mari sai da jini ya zubo ta hancin ta, idanun ta da suka qanqance suka yi ja saboda kuka ta zuba masa tana mamakin marin da ya zabga mata be ji ko d'ar a zuciyar shi ba, cikin zubar hawaye ta kalle shi tace,
"Me na yi maka ka mare ni? Ka barni in tafi gidan mu na gaji, na gaji da rayuwa na gaji da komai, bana son kuɗin ka barni in koma Nigeria,"
Mommy ta qarasa maganar ta cikin ihu da kuka da tare da kai wa baturen nan wani irin duka da naushi sai da ya tafi taga-taga kamar zai faɗi amma ya yi saurin cakewa da qasa da takalmin shi baqi sau ciki mai matuqar tsada, cikin haɗe haqoran shi waje ɗaya da fushi mai tsanani Alex ya furta,
"You filthy bich ! you are going to pay for this,"
Da hannu ɗaya ya hau jan Mommy dan ya shigar da ita cikin gidan amma ya kasa, nan take ta nuna masa renon qauye cin tuwon dawa da shan kunun gero daban da kurb'ar costard,duk yanda yayi ya ja ta zuwa cikin gidan kasawa yayi, ganin tana so ta bashi kunya a gaban ma'aikatan shi ne ya sanya shi duqawa ya sab'e ta a kafad'ar shi, da kyar yake tafiya ciki da ita saboda yanda take mutsu-mutsu da zillo tana neman sauka qasa daga jikin shi,suna shiga cikin gidan aka rufe da key ya kira ma'aikatan shi maza suka ɗauki Mommy tana ihu tana harbe-harbe da qafafu suka maida ta benen da take, a qasan dakin da aka sauke ta suka watsar da ita kamar abun banza suka ja qofar suka bar wajen, a guje ta isa jikin qofar d'akin tana ci gaba da ihu da neman agaji, cike da fushi Alex ya karb'i allurar da aka riga aka haɗa masa tin kafin ya isa cikin gidan, dan sun riga da sun san halin shi ya saba drugging duk wata yarinyar da ya siya ya mayar da ita abar shaqatawar shi,shi dai kawai ya gansu cikin maye tofa abun yafi bashi nishad'i,sannan yana sawa ya samu sauqin sarrafa su ba tare da sun yi masa musu ko gardama ba.
Yana shiga d'akin ya tarar da ita a takure a gefen gado tana gunjin kuka tare da neman taimakon a fitar da ita tana so taje gida ta gaji,murmushin mugunta yayi ya isa gaban ta hannun shi ɗaya a bayan shi,yana zama ya shammace ta ya zurkud'a mata allurar nan be zare ba sai da ruwan ya qare a jikin Mommy,nan take kuwa ta yanke jiki ta faɗi a wajen, cikin farin ciki Alex ya d'aga ta daga qasa ya kwantar a gado sannan ya fara rage kayan jikin shi.
Abinda yayi mata yau yafi wanda yayi mata a farkon haɗuwar su, dan kuwa ya yi wa Monmy dukan tsiya ya fitar mata da jini sosai a jikin ta kafin ya hakura ya kyale ta.
Miranda da ta shiga gyara ta kuka ta dinga yi tana tausayawa Mommy da bata san inda kanta yake ba, tana gama gyara ta ta fita ta bar d'akin ta wuce zuwa na Alex ,cikin kuka da ihu baturiyar ke yi masa faɗa akan idan ya kashe ta fa? Ya fa kashe mata biyar kenan fa,hakan be ishe shi ba? Cikin harshen turanci yace mata,
"Eh be ishe ni ba, kuɗi na na sanya na siye ta baiwa ta ce ! dika baqaqen fata bayin mu ne ! abun wasan mu ne su ! ki fita ki bar min nan kafin kema na yi miki abinda na yi mata, ban ɗauke ki aiki dan ki faɗa min abinda zan yi ba,ki tabbata ta ji sauqi a cikin kwana biyu saboda zata yi baqo na musamman...Mike ne zai zo shima ya yi nishad'i,"
Miranda na jin sunan da Alex ya ambata jikin ta ya hau rawa, tabbas idan wannan azzalumin yazo sai dai buzun Mommy dan kuwa ba zata qara moruwa ba har abada, shi har ta baya neman mata da maza yake yi,cike da ladabi ta bashi hakuri ta bar wajen.
Nan take zuciyar ta ta d'arsa mata lallai zata taimaki Mommy ta bar gidan koda kuwa hakan na nufin rasa tata rayuwar ne, abinda uban gidan nata yake yi yayi yawa.
Haka ta dinga bawa Mommy kulawa ta musamman dan kawai ta samu ciwukan jikin ta su warke, cikin ikon Allah kuwa Mommy ta fara iya takawa da qafafun ta tana zuwa band'aki a kwana na biyu da faruwar wannan mummunan rashin imanin da Alex ya gwada mata.
Tin da sassafe Miranda ta yi wa Mommy bayanin abinda take so tayi mata,Mommy bata wani gane ba sosai amma tinda taji kalmar escape ta san kub'utar da ita Miranda ke son yi, ai kuwa da sauri Mommy ta rungume ta tana godiya,Miranda kuwa fita tayi ta yi wa saurayin ta da ke cikin ma'aikatan gidan alama da komai ya zama ready.
D'akin Alex Miranda taje ta na yi masa tambayoyi akan irin shiga da kwalliyar da yake so a yi wa Mommy yau saboda zuwan baqon shi na musamman.
Nan take Alex ya saki baki yana yi mata lissafin abinda yake so a yi wa Mommy da ko sunan ta be sani ba,shi dai kawai ya san ya sayawa kanshi abun nisha'di, suna nan suna ta lissafe-lissafe saurayin Miranda ya fitar da Mommy daga gidan cikin wata boyayyiyar hanya, suna fita daga gidan ya bata kuɗi da wata takarda yace idan ta samu taxi ta basu sannan ya lullub'a mata rigar sanyi mai kauri a jikin ta, qafar ta na sanye da takalmi sau ciki me kyau, gudu kawai Mommy take tana so ta bar unguwar ta yi nesa da gidan sosai.
Taxi ta gani ta tsayar ta faɗa tare da miqa masa takardar da aka bata haɗe da dala guda ɗaya kamar yanda saurayin Miranda ya yi mata nuni, babu b'ata lokaci driver ya ja mota ya hau kwalta suka miqa, Mommy bata kwantar da hankalin ta ba sai da ta ga sun yi nisa sosai da gidan sun shiga jama'a sosai dan kuwa can unguwar su Alex unguwa ce ta masu hannu da shuni, gaba ɗaya layin ma gida uku ne a wajen maka-maka kamar ginin wata babbar makarantar.
A bakin wani hotel motar ta tsaya Mommy ta buɗe ta sauka, canjin ta ya bata ya yi gaba abun shi, cikin qanqame jikin ta ta hau tafiya tana waige-waige tana zubar da hawaye,yunwa take ji sosai amma bata jin zata iya tsayawa cin abinci,waje ta samu ta rakub'e ta dunqule waje ɗaya ta fashe da kuka tana faɗin,
"Ya Allah na tuba, Allah ka gafarta min ba zan sake fita yawon karuwanci ba, ba zan sake kallon fina-finan banza ba ko karanta littafin banza balle har na yi sha'awar kusantar zina,Allah ka kawo min dalili mafi alkhairi da zan koma qasata, Allah ka shiga lamurana, La'ilaha'illalla anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,"
Tun Mommy na kuka da hawaye har hawayen suka dena fita ta samu waje ta sake takurewa saboda sanyin dake ratsa ta, mutane kuwa idan suka zo wucewa wasu sai su wurga mata kuɗi a zaton su mabaraciya ce,tana nan zaune wani security ya fito daga cikin hotel ɗin ya tashe ta yana yi mata magana akan ta bar wajen ko ya kirawo mata police,cikin d'aga kai ta hau cewa,
"Dan Allah ni ka kira min 'yan sandan ma su maida ni qasata ko haqqi na ba zan tsaya a bi min ba mun haɗu a qiyama da mugu,"
Tura ta mutumin ya dinga yi har saida Mommy ta bar wajen ta samu wani wajen ta zauna tana ci gaba da rawar sanyi.
A can gidan Alex kuwa Miranda ce ta gama sauraren shirmen shi sannan ta duqa alamar gaisuwa ta bar wajen nashi ta nufi wajen Mommy, tana shiga d'akin ta tabbatar da an kub'utar da mommy sai kawai ta k'walla qara mai qarfi tare da kwasar gudu ta hau benen da Alex yake, a hanya suka haɗu da shi ta hau numfashi tana nuna masa hanyar benen Mommy, a gigice ya bi bayan ta suka shiga d'akin,gani yayi be gan ta ba, sai ya shiga har band'aki ya hau neman ta amma be same ta ba, qarshe dai babu inda ba a duba ba amma babu mommy babu kayan ta, cikin Kuka Miranda ta hau cewa,
"Yanzu ina ta tafi gashi bata san kowa ba kuma bata da lafiya ina jin tsoron kar ta haɗu da 'yan iska su yi mata fyad'e,"
Kuka ta dinga yi da ya sanya Alex cire zargin da sanya hannun ta a gudun mommy wanda nan take ya tuna ma ai tana sashen shi d'azun itama komawa tayi ta ga bata nan.
Nan da nan fa bature ya dinga masifa yana kiran dika ma'aikatansa dan gano wanda ya kubutar da mommy a gidan.
A can cikin gari kuwa Mommy na nan nata watangaririya a gari bata da kowa da zai taimake ta ta koma Nigeria, sai dai ma kyara da nuna mata ita ɗin ba kowa bace da zata dinga zuwa tana rab'ar su har da zata nemi taimako a wajen su.
***************************
"Ohhh ni K'waisan alheri na shiga uku, wai a yi mutane dan ruwn zumar soyayyar da suke kur'bawa na da zaqi se a dena ganin su online? Kin ga bama Mommy kaɗai ba har da ɗan tijarar nan ma baya hawa ko TikTok ne in fact account d'in shi da na sani babu shi yayi b'atan dabo,"
Wayar shi ya sake kangawa a kunnen shi da alama kiran waya yake yi amma shiru, ba alamar ma tana shiga balle ya sama ran za a ɗauka, tsaki ya ja me qarfi yace,
"Baby ni fa ina jin tsoro, haka kawai zuciya ta ke bugawa da ta tuna bawan Allahn nan da ko cikakken sunan shi ban sani ba, million sha uku muka ci nashi banda wanda yake kashewa yarinyar nan, kana ganin dai wayar da ya sai mata ta milliyoyin nerori,nif ko sunan sabon resort ɗin nashi da yace zai buɗe ban sani ba, anyaaaa?"
Samuel ne ya kama hannayen Hajiya K'waisa cikin sigar lallashi yace,
"Kwantar da hankalin ki my love kar ki d'aga hankalin ki ki fara quraje a fuska,'yan bariki ne fa dik inda suka je za su dawo gida ne,ita waccan uwar gantalin ina ta tafi ban ganta ba?"
"Hummm wani customer ne ya taya shine ta tafi ita ai kaga tana kirana a gaisa a san halin da take ciki, amma banda waccan uwar tinb'elen,"
"Kar ki damu zata dawo lafiya ki bata kwana uku idan bata dawo ba sai a baza hotunan ta wajen mutanen mu wataqila a samu wanda ya ganta,"
"Allah ya sa a gan ta lafiya ba a gutsire ko a yanke ba, duk sanda kuwa na ɗora ido na akan ta se na sa tsinin farce na na sace mata leb'en nan,"
Dariya Samuel ya sanya yace,
"Ragadada kenan,"
"Heeeee ragassss !"
Hajiya K'waisa tace suka tafa da Samuel suna dariyar shaqiyanci.
**************************
"Ranka ya dad'e ni dai da an bi shawarata an yi musu had'in zumunta da yarinyar nan Bilkisu kaga shikenan an yi tuwona mai na kuma dakan d'aka shiqar d'aka tankad'en bakin gado lomar kwanciya,"
Murmushi mahaifin Abdul ya yi har sai da haqoran shi suka fito kafin ya kalli matar tashi me tsananin biyayya, amma wannan karon tana so ta cusa wa yaron ta ra'ayin auren zumunta wanda shi kuma baya son hakan,
"Amma dai qarshen hausar nan ke kika qarata ko ? Dan dai a shekaru na sittin da uku ban taɓa jin ance wata lomar kwanciya ba sai yau,"
Dariya ta yi mai sauti kafin tace,
"Wai ai dan in tabbatar maka da kusancin alaqar ne idan ka manta,"
Gyara zaman shi yayi sosai sannan yace,
"Laminde ba wai ina gudun yaron nan ya haɗa zuri'a da qanwar ki da kuke uwa ɗaya uba ɗaya bane, ina guje miki kar a zo zumuncin ku da kuke riritawa na shekara da shekaru kuna bawa kowa sha'awa ya rushe azo ana dana sani a lokacin da bashi da amfani, da ace ita macen ce tace bata so iyayen ta na iya tursasa ta kuma tayi hakuri ta aure shi,se ki ga saboda rauni irin na mace daga baya ta saki jiki ta fara son mijin, amma Lami akwai matsala akan auren da namiji ne baya son mace aka tursasa shi, abun be cika haifar da da'me ido ba,amma yanzu abinda zamu yi shine,mu dage da yi masa addu'a Allah ya zab'a masa mace ta gari mai albarka,"
"Maganganun ka gaskiya ne ran sarki ya dad'e,kuma in Allah ya so zan dage da yi masa addu'a Allah ya shige mana gaba,"
"Yauwaa matata 'yar aljannah da izinin Allah, wato saurin fahimtar ki da hakurin ki tare da kawaicin ki na sawa a kullum in ji ina sake son ki da qaunar ki,"
Wani murmushi tayi tana sunkuyar da kai irin na jin kunya, a haka suka ci gaba da hira a tsakanin su suna magana akan makarantu biyu da Abdul ɗin ya bada kwangilar a gyara,tare da hirar Saddeqa da ɗan nasu ya sa qanin shi Sultan ya gano masa a wane gida take a qauyen.
****************************
Duqe take a bakin wata shara tana leqa kan ta dan ta ga ko mazan da ta ga suna kallon ta daga qarshe suka fara bin ta sun tafi? Daga can nesa idanun shi ya sauka akan idanun ta dake tsiyayar da hawaye tana leqe wanda da dikkan alama a tsorace take....................
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH
PAGE 29:
Wani irin bugawa zuciyar shi tayi da qarfi, ya sake saurin duba inda yake ganin idanun Mommy dake zubar da hawaye, shin tsabar yawan tunata da yake yi ne ya sanya take yi masa gizo a irin wannan yanayin da ya ganta a ciki ko kuwa ya abun yake ne?
Zuwa suka yi daf za su wuce ta kusa da drum ɗin zubar da sharar Abdul ya kalli Bilal yace,
"Guy kana ganin abinda nake gani ko kuma ni kaɗai nake ganin akwai mace acan tana lab'e tana kuka?"
Juyawa dai-dai wajen da Abdul ya kalla yana magana Bilal yayi, kafin Bilal ya bashi amsa suka ga ta yanko da gudun tsiya ta qanqame Abdul ta na fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, cikin kukan tace,
"Dan Allah yayana ka taimake ni kar su kama ni,sato ni aka yi aka kawo ni qasar nan, na samu na kub'uta daga hannun mutumin da ya siye ni yanzu kuma wad'ancan 'yan daban na bina za su kama ni,"
Hannun ta Abdul ya kama ya janye ta daga rungumar da ta yi masa,cikin wani irin yanayi na tashin hankali ya ce,
"Saddeqa right ? Ya aka yi aka sato ki daga qauyen Ba mugu aka kawo ki wannan qasar? Waye a kaf qauyen nan yake da zamar aikata hakan ba tare da an sani ba? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, muje masaukin mu sai ki bamu labari da kyau,"
Ganin shigar da ke jikin Mommy bai sa ya ji k'yamar ta ba ko yayi zargin wani abu mara kyau daga gare ta, hasali ma tausayin ta da mamakin ganin ta a wannan qasar shi yafi damun shi, tabbas idanun ta da girar ta ne suka tabbatar masa da cewa wannan Saddeqa ce, amma kuwa duk wanda aka kama da wannan aika-aika sai ya hukunta shi hukunci mafi muni kuwa a rayuwar shi.
A bangaren Mommy kuwa jin ya ambaci Saddeqa sai ta shiga rud'ani da