Showing 168001 words to 171000 words out of 276165 words
Chapter 57 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
ma muka yi auren da kike shirin rabuwa dani? Me yasa zaki zubar da ciki na kamar wani cikin shege? A yanzu taƙama mata suke yi da cikin da suka samu ta hanyar aure, har su dinga yanga dashi suna sanar da duniya, ke me yasa zaki zubar da nawa?"
"Saboda bana son jiki na ya lalace ne ka rabu dani shi yasa !"
Sororo yayi yana kallon ta da wautar da ta furta,cikin kuka ta ci gaba da magana,
"Abdul jiki na ne kaɗai abinda na mallaka nake jin shi kaɗai ne zai sa ka ci gaba da so na har ƙarshen rayuwar mu ba tare da kayi min kishiya ba, haihuwa na lalata jiki baby dan Allah ka fahimce ni."
Kuka take yi sosai kamar an yi mata dukan tsiya, sassauta fushin shi yayi ya kama ta ta miƙe tsaye suka zauna a bakin gado, cikin kuka ta kalle shi ta tura baki tace,
"Dan Allah kar kayi min kishiya mutuwa zan yi idan na gan ka da wata a matsayin matar ka."
Murmushi yayi sannan ya hau share mata hawaye yace,
"Baby ba zan taɓa yi maki kishiya ba, wannan kayan naki ne ko kin manta da alƙawarin da nayi maki na kayan lefe ne? Sannan maganar ki ta wai jikin ki zai lalace in dena son ki wannan duk shirme ne,in har dan ni zaki zubar da cikin nan kina tsoron kar jikin ki ya lalace to ki kwantar da hankalin ki, ina son jikin ki Hadiza ba wai bana so ba, amma ni ke nafi so, ko baki da komai na jan hankali zan zauna dake har abada Hadizana."
"To ai alƙawarin da kayi min cewa kayi tare zamu je a haɗa lefe ba wai nazo naga akwatina da kaya a cike ba, dole nayi zargin ko aure zaka ƙara."
Lakace mata hanci yayi yace,
"Sarkin rikici, to naki ne ba na kowa ba,na cika alƙawari na saura naki, kin amince zaki haifa min yara iya yanda Allah ya bamu ba zaki min asarar k'wai na ko ɗaya ba?"
Daga kai tayi tana murmushi tace,
"Nayi alƙawari ba zan taɓa zubar da cikin jiki na ba matsawar ba zaka sauya min ba a lokacin da halitta ta ta sauya."
Rungume junan su suka yi suka hau farantawa junan su kamar babu abinda ya haɗa su.
******************************
Tinda Billy ta hau yi wa Amy tambaya akan tsohuwar matar ta da daddare suna kwance, ran Amy ɓaci sosai akan hakan,amma sai ta danne saboda ba yanzu bane lokacin da zata fitowa Billy a mutum,a daren ranar lallab'a Billy tayi da zazzafar soyayya ta mantar da ita komai tare da yi mata alƙawarin gobe zata yi mata wata babbar kyauta ta musamman.
Kamar yanda Amy ta yi alƙawari kuwa Billy na can na barci ta ƙarasa yin order ɗin abubuwan da take da buƙata, a cikin ƙasa da awa ɗaya Amy ta gyara ko ina ta shirya dik abinda take so tayi dan baiwa Billy mamaki idan ta farka daga nannauyan baccin da take yi.....
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 67:
Wanka ta shiga tayi tana gamawa tayi brush sannan ta haɗawa Billy ruwan wankan da ya sha flowers na musamman waɗanda ke gyara fata da shower gel mai kyau irin wanda Billyn ke amfani da shi,candles masu kyau da ƙamshi ta kunna sannan ta fita zuwa ɗaki hannun ta ɗauke da camera tana ɗaukan video saboda mutanen su na YouTube su ga yanda take ririta matar ta,cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya ta tada Billy daga bacci sannan ta taimaka mata ta shiga wanka, kafin ta fito ta wuce kitchen ta haɗa mata abinci, ta sake gyara abubuwan da ta shiryawa Billyn na musamman.
Minti talatin da d'oriya Billy ta ɗauka kafin ta gama shiryawa cikin wata ƴar mitsitsiyar riga mara dogon hannu,rigar fara ce tasss mai santsi,gashin kanta kuwa da aka yiwa ƙari da na shago ta gyara shi sai reto yake yi tana sanya hannu tana gyara shi babu wanda zai kalli Billy a wannan shigar ya ce ta haɗa jini da musulmai,cike da yanga take tafiya har ta isa tsakiyar parlourn,ganin abinda Amy ta shirya mata ne ya sanya ta ja da baya cike da mamaki ta damƙe bakin ta tana tsallen murna da ihun murna a lokaci ɗaya.
Dariya Amy take yi tana ɗaukan ta a video,cikin sauri Billy ta riƙe balonbalon ɗin dake yawo cikin iska mai cike da ado ta hau karanta abinda ke jikin ta,
'BEST WIFE IN THE WORLD'
Hawayen farin ciki ne suka hau zubo mata a hankali ta dinga bin duk wata jaka tana ganin abubuwan da Amy ta siyo mata a matsayin gift,rantsattsiyar waya 'yar yayi ta fara ɗakkowa tana kallo tana ihun murna tare da rungume Amy, daga nan kuma ta buɗe wata ƙaramar jaka mai faɗi sabuwar laptop ce a ciki, da headphone kalar laptop ɗin,sai turaruka chocolates da rigunan bacci, wata sarƙa ta buɗe a ɗan ƙaramin box mai azabar kyau,kwaɗon sarƙar an yi shi da farin ƙarfe mai alamar zuciya, Amy ce ta Karb'a ta ɗaurawa Billy dake ta kukan farin ciki.
Makullin motar da Amy ta damƙawa Billy ne ya sanya ta saurin kashe camera ɗin wayar dan kuwa gaba ɗaya Billy ta afkawa Amy ta hau sumbatar ta cike da farin ciki, Amy kuwa bata ƙyale Billy ba sai da ta sake shayar da ita madarar soyayyar da ta cire mata dik wani zargi a ranta game da Amyn.
Rayuwa suke yi babu sallah babu salati balle su tuna daga tushen da suka fito daga ciki ko addinin da suke kai, rayuwa suke yi cike da kashe dukiya da faranta wa junan su rai ba tare da tunanin halal da haram a zamantakewar su ba,a haka har Amy ta koyawa Billy tuƙi a ƙasar saboda gudun samun ticket da sauran tsarabe-tsaraben ƙasar na dokoki.
Ranar farko da Billy ta kula da salon soyayyar su ya fara sauyawa,taso ta tambayi dalili amma sai idanun ta ya rufe da tsantsar farin cikin da take samu daga wajen Amy bata yi magana ba, tayi shiru gudun kar ran Amy ya baci, shirun da ya zama sila kuma mafarin shigar rayuwar Billy tashin hankali da bala'i.
Dik daren duniya Amy kan baiwa Billy wasu ƙwayoyin dake sanya ta jin shauƙin kasancewa da mace koda kuwa bata da ra'ayi da farko,cikin ƙanƙanin lokaci takan gigice ta farwa Amy su dinga aikata abubuwan da baki ba zai taɓa iya lissafawa ba,a hankali Amy ta fara gayyatar wasu matan suka ƙara yawa dik da cewa Billy na matsanancin kishin Amy, amma sai Amy ta nuna mata cewar ai babu komai saboda jin daɗin su ne baki ɗaya dan haka kar ta damu kuma su turai hakan ba wani abu bane an saba.
Watarana Billy na zaune da rana bayan Amy ta fita inda a kullum take kira da wajen aiki, dik da taƙi sanar da Billy a kamfani ko ma'aikatar da take aiki ta gwamnati,a Instagram taga Man ɗin ta yayi posting wani hoton su bai rubuta komai a ƙasa ba sai hoton zuciya da ya sanya guda biyu,ƙurawa hoton idanu Billy tayi, nan take ta hau tunawa da moments ɗin su a tare,tsohuwar zumar ƙaunar shi ce ta motso mata,ba tare da tunanin komai ba ta zuba No shi a wayar ta ta kira shi, ta jima tana ringing bai ɗauka ba har ta katse,daga ƙarshe dai message Billy ta tura masa cewar ita ce ya ɗauki wayar ta.
Bayan kimanin mintuna uku sai ta sake kiran shi ya ɗauka cike da zumud'i, muryar shi na rawa yace,
"Babe ina kika shiga? Me yasa kika barni...wannan shine alƙawarin da muka yi wa juna?"
"Kai fa ka nuna baka so na in tafi kawai na jawo maka masifa a ƙauyen mu, kai fa ka fara korata kuma baka neme ni ba har na gama rayuwa ta a kano na dawo nan ƙasar, ya kake so nayi idan ka daina yayi na?"
"Babe ba haka bane, ke kin sani ba zan taɓa iya daina son ki ba, son ki a cikin jini na yake,na kuma neme ki a sabon gidan ki,ranar da naje ban same ki ba sai Amy, itace ta bani tabbacin kin yi tafiya ƙasar Canada itama ba jimawa zata yi ba zata bar gidan ta rufe ta tafi karatu UK,baby i missed you so muchhh."
Wani irin yanayi Billy ke ji a wannan lokacin, ta tabbata wannan yanayi ne da ta saba ji game da Man tin fil azal babu wata ƙwaya dake aiki a jikin ta,cikin ƙanƙanin lokaci Billy da Man suka koma social media suka fara hira irin tasu ta ƴan bariki,a hankali hirar su ta fara kauce hanya wanda ya sanya Billy saurin katse shi da faɗin,
"Man kasan fa yanzu nayi aure bai kamata mu zaƙe ba,saboda kar na zama mai cin amanar aure."
(Sokuwalle as if auren Allah da Annabin rahama tayi)
A ɗan tsorace ya tashi zaune yace,
"Aure kuma? Wane irin aure kika yi Billy babu labari a gari?"
Murmushi tayi ta sake murza zoben hannun ta sannan ta riƙe sarƙar dake wuyan ta tace,
"Tabbas na yi aure Man, ni da Amy mun yi aure yanzu haka muna tare ta fita aiki ne shi yasa baka gammu tare ba,"
K'warewa Man yayi da yawun bakin shi, cike da damuwa da tashin hankali ya tashi zaune yace,
"Baby kina nufin kin yi auren jinsi dake da Amy? Ke kuwa me ya kai ki aikata wannan mummunan abu? A zato na dik iskancin da muke yi watarana zamu shiryu mu koma ga Allah,amma shine ke kika girmama zunubin ki kika kai kan ki ga auren jinsi? Anya wannan Billyn da na sani ce?"
Motsin da Billy taji ne ya sanya ta gane cewa Amy ta dawo, cikin sauri tayi wa Man dake cikin kid'ima sallama ta kashe kiran nasu sannan ta hau bin chats ɗin su tana gogewa. Bata jima da goge komai ba Amy ta shiga ɗakin nasu,yi tayi kamar kallo take yi a laptop ,dan haka d'aga wa Amy hannu ta yi tare da busa mata kiss sannan suka hau hira a tsakanin su,kallon Amy Billy tayi wadda da dikkan alamu a gajiye take tubus, wanka ta faɗa Billy na faɗin bari tayi musu oder ɗin abinci dan ta kula Amy ta gaji sosai baza su samu fita cin abinci a restaurant ba kamar yanda suka saba.
***********************
Zaune yake a shagon shi da wasu ƴan mata yana tura masu sabbin videos ɗin da ya d'akko a daren jiya wanda ko kallon su ma bai samu damar yi ba saboda bashi da lokaci,murna suka dinga yi saboda ganin akwai irin nasu wato na zallan mata dake neman junan su,har ɗayar zata kunna sai ƴar'uwar ta da suke tare ta hana ta tana yi mata alama da ido kar a ji su,murmushi suka sakar wa junan su dan kuwa sun riga da sun san ina zasu haɗu su kalla har su aikata abinda suka gani.
Sule na kammala tura musu videos ɗin su suka biya shi ya sallame su ya hau turawa wasu dake kan layi cike da farin cikin samun kuɗin da yake yi a kwana biyun nan. Haka ya dinga tura videos da hotuna har ma da stickers ga waɗanda ke da buƙatar hakan yana amshe kuɗaɗen shi a hannu da banki, rana na yi ya shiga gida ya samu an gama abincin rana ya zauna yaci ya ƙoshi sannan ya cewa Ameerah ta dafa musu shinkafa da miya da salad da dare zai kawo musu nama su ci da shi,cike da murna ta hau yi masa godiya da fatan Allah yasa kasuwa ta fi haka.
Ɗan ƙaramin cikin ta da ya tasa ya shafa sannan ya ce,
"Ameeen matata,Allah ya ƙara bud'a mana na sangarta ki a ƙauyen nan,"
"Ameeen ya Allah Shamsuna dan Allah ka had'o min da kifi da gandar Talle me nama."
"An gama matata, ai indai za ki dinga faranta min ni kuwa babu abinda ba zan yi miki ba a duniya sai dai idan bani dashi ne kuma wannan dole a haƙura."
A haka shamsu ya koma shago cikin farin ciki, bai jima da zama ba aka kira sallah ya sake rufewa ya tafi masallaci, malam liman ne ya tsayar da shi bayan an idar da sallah yace yana son magana da shi idan babu damuwa. Cikin ran shamsu yaji haushin kiran da liman yayi masa dan kua ya san dole wa'azi zai yi masa,amma babu yanda ya iya dole ya bishi yaji da wacce yazo.
Sai da liman ya bari kowa ya fita sannan ya kalli Shamsu da ya gaji da jira yana hango ƴan kuɗaɗen da zai yi missing a iya tsayuwar da suka yi,gyaran murya Malam Liman yayi yace......
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH
PAGE 68:
"Malam Shamsi ina zaune aka zo aka sanar dani wani mummunan labari mara daɗi shekaran jiya bayan an idar da sallar azahar,ka san Nafi'u mai kananzir na tsakiyar kasuwa ai?"
Nan take cikin Shamsu ya bada wata ƙara, domin kuwa ya riga da ya san inda labarin zai tuƙe,ɗaga kai yayi yana wani cin magani, dan kuwa ya riga da ya ƙudirta dik wata nasiha ko wa'azi da Man Liman zai masa ba zai ji ba, tinda ba shine mutum na farko da ta taɓa yi masa nasiha akan ya daina abubuwan da yake yi ba,an sha yi masa a social media yafi shurin masaƙi, baya ma karantawa yake barwa masu nasihar kayan su balle ta shige shi, dan haka yanzu ma ba sauya zani zata yi ba, zai ɗauki maganar liman ne a tazo mu ji ta ya ƙara gaba, customers ɗin shi na can na jiran shi,ba tare da Liman ya damu da sauyawar Shamsu ba ya ci gaba da maganar shi domin sauke haƙƙin zaman tare a matsayin sa na dattijon unguwa da ake girmamawa,dan haka cikin sassauta murya yace,
"A gaskiyar magana labarin da na samu game da rasuwar shi ta girgiza ni matuƙa, shine babban dalilin da yasa nace idan kowa ya kasa yi maka magana ciki kuwa har da mahaifin ka da yake ganin ai sana'a kake yi, to ni zan yi maka magana,yanzu Shamsi fisabillahi a kafatanin sana'o'in duniyar nan ka rasa sana'ar da zaka yi sai ta turawa mutane alfasha da fasadi? Yanzu kana dai ji Nafi'u ya mutu an same hyi a hyagon/shagon shi hannun shi riƙe da waya yana kallon fina-finan nan na turawa ana ta abubuwa babu kyawun gani,kafa sani ita mutuwar nan da take ta yi mana ɗauki d'ai-d'ai bata da lokacin zuwa ƙayyadadde,dik sanda lokacin bawa yayi wallahi se ya tafi ko bai shirya ba,dan haka ina mai yi maka nasiha Shamsi kar ka bari mutuwa ta riske ka baka tuba ba, alqur'ani kaje lahira walakiri ya damƙe ka ba zaka samu damar tuba ba ko bayani domin kuwa aikin gama ya riga da ya gama, bakin alƙalami ya bushe."
Jikin Shamsu ya ɗan yi sanyi kaɗan,dan kuwa tabbas jiya da aka bashi wannan mummunan labarin akan mutuwar Nafi'u bai ji daɗi ba, sai yaji kunya ta kama shi kamar shi aka gani a wannan yanayin, amma kud'in da yake samu wajen tura wannan abun da wa'azi yace mutane su zo ya tura masu koda na auren ne ba zuwa za suyi ba,tinda dai ba shi yake iskancin ba ai babu ruwan shi, ba wanda ya isa hana shi sana'ar shi gaskiya, sunkuyar da kai yayi kamar na Allah yace,
"To Man Liman na gode da shawarwarin ka, inshaa Allahu zan dena, kasan komi nada lokacin sa,Allah kuma mai shiryar da wanda yaso ne a sanda yaso, mu bayin Allah bamu isa muce wane dan wuta bane ko wane ɗan aljannah bane ."
"K'warai da gaske, maganar ka gaskiya ne, amma kuma ai ita halal a bayyane take, sannan kuma haramun ma a bayyane take,kaga kenan bai kamata dan taƙamar mutum Allah mai yawan gafara bane yaje ya dinga aikin ganganci, idan kuma bawa ya ci gaba da zunubi cikin izgili da sanin sa to fa Allah zai masa azaba mai rad'ad'i."
"Haka ne malam,Allah ya sa mu dace, bari naje iyali na jira na zan kai abun miya."
"To Allah yasa mu dace a gaida Mai Dusan na kwana biyu ban ganshi a wajen sallah ba."
"Zai ji inshaa Allahu."
Shamsu na fita ya doka uban tsaki yace,
"Kaiii wasu mutanen akwai su da shegen saka ido, yanzu dan Allah kana limami ina ruwan ka da abinda nake yi? Wai har ya gane Baba baya zuwa masallaci sai kace gadi yake yi ba jan sallah ba, kaiii Allah ka raba mu da maƙiya masu hassada."
A haka ya isa gida yana ta masifa,dik da yaga ƙofar shagon shi cike da matasa da magidanta bai hana shi shigewa cikin gida ba,dan kuwa ranshi a mugun ɓace ya koma gidan yana son ko ruwa ne ya ɗan kora kafin ya fita,a tsakar gida ya ganta yashe a ƙasa ta zuba ruwa ta kwanta tana ta juyi, cikin sauri ya isa gaban ta ya d'ago ta yace,
"Lafiyar ki kuwa ana sanyin nan ki kwanta a cikin ruwa a ƙasa salon mura ta kama ki,wato dan saka ni siyan magani kika zauna a cikin sanyi da sanen ki? To tashi ki koma ɗaki,ina girkin shinkafar da nace kiyi zan siyo nama da dare?"
Tsartar da yawu tayi mai shegen kauri da wari sannan ta dube shi tace,
"Amma dai Shamsu baka da tausayi,kana ganin halin da nake ciki shine kake tambaya ta shinkafa? To gidan saida abinci zan baka ba shinkafa ba,haba shamsu, haba shamsu, yau ko baka ƙauna ta ka tausaya mun tinda kai musulmi ne."
Kuka ne yaci ƙarfin Ameerah ta kasa ci gaba da maganar da ke ranta,cikin ɗan toshe hanci ya tallabo ta ya miƙar da ita tsaye dan ya taimaka mata su koma ɗaki,juyawa tayi dan sake zubar da yawun da ya sake taruwa a bakin ta, tana zubarwa wani ya biyo ta ya taɓa rigar shamsu, a gigice ya sake ta ta tafi luuu zata faɗi kuwa, da sauri ya taro ta yana ɓata rai, dan kuwa babu damar yin magana.
Suna shiga ɗaki ya ajiye ta a bakin gado yace,
"To yanzu dai kiyi hakuri ki kwanta ki huta da dare zan shigo mana da abinda zamu ci."
Cikin hanzari ta ɗaga kai tana yi masa murmushi,da ƙyar ya samu