Showing 105001 words to 108000 words out of 276165 words

Chapter 36 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

ɗaya daga cikin qaddarar rayuwar da ta haɗa ni da ke tin farko kika taimaka min a rayuwa ta ita ce ta sa na janyo mommy cikin rayuwar mu dan nima na taimake ta har abubuwan da suka faru suka faru,amma na yi miki alqawarin ba zan sake maimaita kuskuren da na yi a baya ba, ke ce mutum ta farko da ta inganta rayuwa ta irin ingantawar da uwa ce kawai zata baiwa 'yar ta,sannan ubane kawai zai kula da abinda ya haifa irin yanda kike yi min,Hajiya kin sani akan son zama dake da nake na aikata abubuwan da ke da kan ki kika roqe ni kar na shiga tsakanin ki da Mommy wanda da na san rabuwar da za a yi kenan da na yi duk yanda zan yi na raba ta da gidan nan kafin ta kai ga cin amanar ki har ta sanya hannu a jikin ku,cikin adalci da kyautatawar ki Hajiyata naga kin dawo mana da dik abinda muka samu a nan wanda da wata ce ko sisi ba zata bamu ba, dan Allah Hajiya kiyi hakuri ki maida ni matsayi na a wajen ki,"

Jikin Hajiya K'waisa ne yayi sanyi ganin irin kukan da Billy ke yi da kalaman da ta zuba cike da hikimar sace zuciyar K'waisan ,nan da nan ya tashi ya zauna a kujerar da Billy ke zaune ya rungume ta yana lallashi, dan kuwa yana son Billy yana jin ta kamar qanwar shi,shi yasa kafin ya kore su ma sai da ya daure ya ɗauki zugar Samuel,wanda daga baya ma akan yawan yi wa Samuel zancen Billyn saida suka samu sab'ani yayi tafiya canada yayi kwanaki be nemi K'waisan ba, da k'yar ta shawo kan abun ta suka koma dai-dai.

"Ya isa haka na yafe miki sai dai ina da sharad'i, dik da dama ko Mommyn ma nice na dage ki kawo min ita, amma a gaskiya bana so ki sake haɗa ni da kowa a barni da kai na na samu wadda zan raina na maida ita abinda nake so a wannan harkar,sannan dik sanda Baby yazo yana faɗa akan dawowar ki gidan nan ke ko zagin ki yayi dole ne ki jure, idan kuma kin san sa'insa zaku yi da shi tun wuri ki tattara komatsan ki ki koma qauyen ku, dan kuwa ba zan ɗauki raina min masoyi ba,"

"Na gode na gode sosai Hajiyata dama na san uwa ba zata yi fushi da 'yar ta ba,inshaa Allahu zan kiyaye dik abinda kika yi umarni akai, sai dai ina neman alfarma zan koma qauyen mu na zauna na wata ɗaya kafin na sake shawo kan iyaye na akan su barni na dawo aikatau dan kuwa magana taje har gaban sarkin garin mu yace kar a sake barin kowacce mace a qauyen mu fita aikatau.......uhumm Hajiyata Ina cousin d'ina da na sanar da ke a duk sanda na gama da bariki shi zan aura? To Mommy na can ta kasa ta tsare shi zata aura, d'azu yazo har d'akin mahaifiyar shi yake sanar da mu cewar a taimake shi a aura masa Mommy ko kuma ya mutu, wai ya tsane ni baya son sake gani na ko jin labari na in fitar musu a gida ,shine na fito na yo nan dan na san ke kaɗai ce zaki share min hawaye na,Hajiyata idan ya auri Mommy ni fa?"

Kukan da Billy tasan yana d'aga hankalin k'waisa ta saki tana lafewa a jikin shi, nan da nan kuwa tsanar Mommy da haushin ta ya mamaye zuciyar shi, cikin masifa ya zame Billy a jikin shi ya hau tafa hannu yana faɗin,

"Ai kuwa yanda ya ce ya tsane ki to kuwa itama sai mun sa shi ya tsane ta ta yanda ko inuwar ta ba zai so gani ba ballantana ita kanta, ki share hawayen ki ki kwantar da hankalin ki wanda ya taɓa ki ni ya tab'o,"

Da jin wannan kalaman daga bakin k'waisan alheri Billy tayi hamdala ta godewa Allah sannan ta ci gaba da zuga Hajiya K'waisa, qarshe dai Man da ya ga an manta da shi ya musu sallama ya tafi da alqawarin gobe da sassafe zai je ya maida Billy gidan su tace masa ba da sassafe zasu tafi ba sai dare dan kuwa so take hankalin kowa ya tashi idan sun neme ta sun rasa.

*******************************

Yau babu makaranta su Saddiqa sun samu hutun kwana uku kafin su koma boko a ci gaba da shirin zana jarabawar WAEC da NECO wannan dalilin ne ya sanya Saddiqa komawa baccin safe da nufin bakwai da rabi ta farka ta zo ta yi abun karyawa ta gyara waken alale ta niqa almajirai su tafi talle, Ameerah kuwa daren ranar ta kasa bacci saboda tunanin zuwan Alhaji Baban Gida da maganar auren Munir da Saddiqa da aka yi wanda ita Saddiqa ta ɗauka Baabaa ta faɗa ne kawai saboda aljanun ta da suka tashi ba wai tana nufin hakan ba.

Tsakar gidan shiru dan kuwa ko Baabaa ba zata yi qosai ba a ranar saboda ko waken ma bata gyara ba a jiya balle a kai ga maganar niqa, bayan haka ma yau babbar rana ce a wajen ta ta tabbata Baban Gida ba zai tsallake maganar ta ba zai zone a yi maganar auren Saddiqa da Manniru kowa ya huta.

Shirun da Ameerah taji ne ya sanya ta tashi ta shiga wanka ta wanke bakinta da brush da toothpaste, sannan ta shirya cikin kayan sallar ta da take ji da su, dik da cewa ta rame ta yi fari fayauu sai uban dogon baki da manyan ido hakan bai hana ta yin kyau ba, d'akin Saddiqa ta shiga cikin sand'a ta buɗe hand bag ɗin Mommy ta ɗauki turaren sihirin da taji Innoh da Mommy na magana akai,ta duba da kyau ta jinjina kai sannan ta ɗauke kwallin sihirin shima ta sake lallab'awa ta bar d'akin, d'akin ta taje ta shafa turaren sannan ta saka kwallin ta koma ta mayar ta ɗauki mayafin Mommy na abayar ta ta zira takalmin Mommy baqi ta bar gidan gaba ɗaya da nufin zata je gidan su Munir ta sace zuciyar shi kamar yanda Mommy tayi wa Abdul.

Sauri kawai take ta zubawa a qoqarin ta na isa gidan ba tare da ta haɗu da kowa ba, tin daga nesa idan ta hango namiji ko mace sai ta samu waje ta rab'e ta buya dan bata son tsautsayi ya gitta a samu akasi,tafe take tana fad'in,

"....Iyi saboda an ga ni bana kawo kuɗi irin shafaffiya da mai Mommy shi yasa ake ware ni ba a son ci gabana ba kuma a son dik abinda nake so,to ni zan sama wa kaina mafita da farin ciki yau sai dai a d'aura auren nan da ni amma bada waccan munafukar ba,ni ce musu aka yi bana son jin daɗin kenan da za a bawa kowa zaɓin ran shi a hana ni nawa,"

Karaff taji ta daki mutum cikin sauri ta d'aga kai dan taga waye babu b'ata lokaci kuwa idanun su ya sarqe da na juna, qamshin jikin ta ya daki hancin shi,wani irin lumshe idanu yayi tare da sakar mata murmushi mai tsada.

Bakin Ameerah na rawa ta hau nuna shi tana kulle idanun ta tace,

"Amma dai shamsu ubangiji Allah ya tsine wa gaba ɗaya dangin ku na nan qauyen da na maqotan shi, Shamsu ka cuce ni ka lalata min rayuwa ta ba zan taɓa yafe maka ba har duniya ta nad'e,"

Kuka Ameerah take tana kumawa tare da zagin shamsu, shi kuwa banda bata hakuri da qoqarin riqe mata hannu babu abinda yake yi, cikin tsananin shauqin soyayyar da ta kama shi a cikin 'yan sakwanni yace,

"Kiyi hakuri fitilar zuciya ta,tabbas zuciyata yau tayi gamo da haske mai walqiya da ya haskaka ta daga tsananin duhun da ta jima a cikin shi, Ameerah ki taimake ni ki karb'i soyayya ta idan na rasa ki ban aure ki ba mutuwa zan yi,"

"Za kuwa a yi jana'izar ka kafin azahar dan uban Mai Dusa, idan ka cika shege ka biyo ni gidan mu hyahyahya kawai,Allah ya saka min rusa min yhiri na da ka yi Allah ya tsinewa zuri'ar gidan Mai dusa,"

Dika bakin ta ta wage tana rusa kuka ta kama hanya zata koma gida dan kuwa magana ta qare, yanda asirin yake aiki shine idan ka saka turare da kwallin wanda ya fara shaqar qamshi kuma kuka haɗa ido dashi to shi zai maqale maka ya so ka har ya aure ka, ta riga ta san yanzu ko sau dubu zata saka ta rasa Munir dan haka tana jin Shamsu na biye da ita yana mata magiyar ta karb'i soyayyar shi ta masa banza ta yi gaba, suna tsaka da tafiya taga motar Munir ta wuce ta a hankali ta nufi gidan su, wani irin kuka ta sake rusawa ta juya tana neman madokin da zata sheme shamsu da shi ko ya mutu ta huta da baqin ciki, rasa abinda zata kwad'a masa tayi sai kawai ta kwashi gudu ta yi gida, Shamsu ma rufa mata baya yayi suka kasa tsere har gidan Ɗan liti.

A tsakar gidan Ɗan liti kuwa Munir ne yake taya Saddiqa hura wutar murhu wadda fitowar ta kenan daga d'aki ta hau hura wuta zata ɗora ruwan zafi, Baabaa na ganin su ta hau washe baki tayi komawar ta d'aki tana fatan Allah ya dawwamar da farin ciki a rayuwar Saddiqa,Saddiqa kuwa gaba ɗaya ta gigice da tsoron kar Innoh ko Baban su ga abinda ke faruwa, ta sani Innoh na ganin haka zata hau kiran ta da sunayen 'yan iska kala-kala.

Ameerah ce ta shiga gidan a guje tana kuka, ganin Munir na taya Mommy kunna wuta a murhu ne ya sanya ta a haukace ta je ta d'ebi ruwa a rijiya ba tare da ta kula kowa ba ta na gama jawowa ta sheqa a saman murhun tana huci ta hau zage-zage kamar jikar bamaguje, tsananin ɓacin ran abinda tayi ne ya sanya Munir miqewa tsaye a fusace zai yi mata dukan tsiya Ameerah ta sheqa da gudu d'akin ta tana gunjin kuka ta kulle qofar tana ci gaba da zagin su.

Ɗan liti ne ya dawo daga siyo suger ɗin shan kokon safe yaga ta'asar da Ameerah tayi sai ya hau salati, cikin fushi kuwa Munir ya kalle shi yace,

"Baba Saddiqa ba zata yi wahalar kunna wutar yin girki ba a gidan nan yau dan ba jaka bace ita, waccan mahaukaciyar da ta kashe wutar ta jiqa murhun ita ya kamata a sa ta kunna wutar ta girka abincin da mutanen gidan za su ci....ke zo nan !"

Ya kira Saddiqa dake sanye da riga da zani da mayafi a rakub'e, cikin sauri ta isa zata durqusa ya damqi hannun ta suka bar gidan, Ɗan liti tsaye yayi yana kalle-kalle dan kuwa zuciyar shi a shafe take bata tunanin komai balle ya san ma matakin ɗauka, yana nan tsaye yaga Innoh ta fito yafe da mayafi da zani a qugun ta bata da riga a jikin ta kuma a haka tayi sallar safiya dan ba za a kira ta da sallar asuba ba,gaba ɗaya ana ganin qirjin ta saboda tsofewar mayafin jikin ta ta zubar da yawun da ya cika bakin ta wanda tin tana sallah ta tara shi saboda rashin wanke baki,cike da masifa tace,

"Yanzu Malam kana tsaye yaro qarami ya gama yi maka tsiwa ya ja hannun 'yar ka suka bar gidan? To uban waye zai yi abun karin ga niqan waken alale nan dik ta tsallake ta bar gidan? Ka juya kaje ka nemo ta dik inda ta shiga ta dawo ta gama aikin dake gaban ta ,"

Baabaa ce ta fito tace,

"Kin dai san yau ne ranar da nake saka ran auren Saddiqa da Manniru ya faru ko? Sannan wai tsayama ita ce matar gidan ko kuwa ke? Ko baki da 'yan matan da suka girme ta a d'akin ki da su ya kamata suna aikin komai a gidan nan amma saboda qin gaskiya da zalunci kike saka yarinya aikin da kika san yaran ki ba za su yi ba ! Innoh ki kiyayi Allah, kar ya yi maki kamun kazar kuku ki zo ki na ganin hukuncin yayi tsauri da yawa,"

"Ke dalla busasshiyar tsohuwa ki wa mutane shiru, magana nake da miji na ba ke ba,sannan Manniru ai ke kika damu da jikan ki, Ameerah ta tafi qarfin auren wannan siririn yaron, ni ai kin riga da kin sani ba qaunar haɗa zuri'a dake nake yi ba, dan haka ki kama tsufan ki,aiki kuma babu ruwa na da yaushe ne ranar auren ta, ko minti ɗaya ne ya rage indai tana cikin gidan nan sai tayi shi,"

"To mu zuba mu gani,"

Sallamar Shamsu ce ta dawo da Ɗan liti cikin hayyacin shi daga kallon sa'insan da su Innoh ke yi, gaba ɗaya ya rame ya fige ya fita a hayyacin shi,kai da ka gan shi zaka tabbatar da yana cikin damuwa da tashin hankali, abubuwa da dama na cin zuciyar shi amma bashi da iKon yin magana, tunawa yayi da sanda ya dawo ya tadda shamsu a qofar gidan nashi har suka gaisa yace masa wajen Ameerah yazo.

****************************

A can Abuja kuwa Alhaji Baban Gida da iyalan shi ne suka shirya tsaf dan zuwa qauyen Ba Mugu Ummeen Munir murna fal zuciyar ta na jin hukuncin da Baabaa ta yanke akan ceto marainiyar Allah daga qangin wahala da bauta.

A kanon dabo jirgin nasu ya sauka inda suka tadda Munir da Saddiqa na jiran su su ɗauke su zuwa qauyen Ba mugu su dira a gidan Ɗan liti..........[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI

















RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨













*Assalamu alaikum dan Allah masu tambayar novel ɗin gidan Ɗan liti daga farko ku yi hakuri ku duba page ɗina dake a facbook mai suna HAERMEEBRAERH'S NOVELS ko a wattpad saboda an yi nisa da yawa ba zan iya koda yaushe in ta tura pages ba gaskiya. Shi yasa nakan ce ko da page ɗin farko bai yi maku ba kuna tarawa maybe gaba in ana comments zaku ji sha'awar karantawa. Idan kuma dik ba ku yin Facebook da wattpad ku yi haƙuri a gama a haɗa document na gode.*

*Masu tambayar jiya ba a yi posting ba,to alhamdulillahi an dan binciko file d'ina ne ina fatan Allah ya kankare mana zunuban mu baki ɗaya.*







PAGE 41:











Ummeen Munir ce ta kalli qafar Saddiqa da ta fito daga gaban mota zata koma baya domin baiwa Abban Munir damar shiga gaban motar taga babu takalmi a qafarta ta cikin mamaki tace,

"Ke Saddiqa ina takalmin ki? Ya za a yi gand'amemiyar budurwa dake ki dinga yawo babu takalmi?"

Sunkuyar da kanta qasa tayi tana satar kallon Munir da ran shi ya ɓaci bayan tuna abinda ya faru da safe da yayi, sai da suka shiga mota kowa ya natsu Munir ya tada motar suka fara qoqarin barin airport ɗin, nan take Saddiqa ta manta da maganar da Ummee tayi ta ci gaba da kalle-kalle saboda sanda suka taho ma shi take yi dan kuwa bata taɓa barin qauyen Ba mugu ta shigo kano ba sai wannan karon.

Ummee ce tace,

"Kun yi shiru kun kyale ni ina takalmin ta ko su mutanen garin naku haka suke barin budurwa tayi yawo babu takalmi?"

Tsaki Munir ya ɗan ja kaɗan sannan yace,

"Ummee ba zaki yarda da abinda zan faɗa maki ba wataqila sai kin je gidan kin ga yanda wannan qatuwar matar ke azabtar da Saddiqa, kin san Allah Ummee ko da ace bana son Saddiqa zan iya auren ta dan kawai na raba ta da gidan nan,ballentana ina son ta ina qaunar ta yarinya ce mai natsuwa da kamun kai ga ilimin addini da na zamani,to me mutum yake nema a wajen matar da zai aura da ya wuce wannan? Nasabarta dai ita ce tawa kin ga kuwa ko ta ina Saddiqa ta cika macen aure,Ummee kar ki manta da kyawun da Allah yayi mata wane namiji me hankali ne zai so mace kamarta ta kub'uce masa?"

Murmushi Alhaji Baban Gida yayi yace,

"Babu kam Yallab'ai Munir jikan Baabaa sarkin rikici,"

Hajiya Saliha ce tace,

"Abban su Baabaan kake kira da Sarkin rikici? Lallai zan kuwa sanar da ita,"

Cikin dariya Munir yace,

"Kar ma ki fara wannan kuskuren shi Abbah komai yayi daidai ne a wajen ta amma ke ko ni muka kuskura muka kira ta da wannan sunan aljanar ta bafullatana ce zata yi qoliqoli da mu ta baje a ruwan cikin mu ta qunsa mana barkono a ido, Abbah zan so ace kaga yanda ake drama a gidan nan, kusan kullum se an yi faɗa basa ko gajiya,"

Murmushi Abbahn yayi sannan yace,

"Haka suke tin fil'azal basu gajiya da zagin juna ko ci wa juna mutunci, dambe kuwa har mamakin yanda Baabaa ke iya dukan Innoh nake yi,Allah dai ya kyauta amma tabbas zaman Baabaa ya qare a garin nan dan kuwa har ita zamu tattara mu koma Abuja,"

"Tabdijam zan kuwa ga qarfin ikon ka yau Abbah, in ba mutuwa ba babu me raba Baabaa da qauyen nan, ka sa ido ka gani zaka ce dama na faɗa maka,"

Haka suka isa qauyen Ba mugu cikin nishad'i da hirarrakin da Saddiqa ta kasa sanya baki a ko ɗaya, ko tambayar ta aka yi abu sai dai ta kalli Munir ta mirror shi kuma ya bada amsa, tin daga nan Mahaifan nashi suka gano akwai shaquwa tsakanin su kuma akwai yarda da amana irin wanda ake son kowanne ma'aurata su kasance da shi, to su sun yarda da junan su sun kuma bawa junan su amanar kawunan su tin kafin auren ma.

Ko da suka isa gidan Ɗan Liti sai suka tarar da gidan shiru babu mutane a gidan,mamakin inda mutanen gidan suka shiga ne ya kama Alhaji Baban Gida, nan take ya zaro wayar shi mai kyau da tsada ya hau kiran Baabaa,tana d'agawa tace,

"Kun iso ne?"

"Eh Baabaa amma naga gidan ba..."

"Maza ku qaraso fadar sarki muna can ku kaɗai muke jira,"

Cike da mamaki Alhaji Baban Gida ya ce su je su shiga mota munir ya kai su fadar sarki, jinjina kai kawai yake yi yana mamakin yanda suke ɗaukan abu da zafi, yanzu fisabillahi menene abun tafiya fadar sarki kuma?

Koda suka isa fada sun tarar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login