Showing 252001 words to 255000 words out of 276165 words
Chapter 85 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
har sanda Allah zai bata lafiya,fatan mu dai shine Allah ya bata lafiyar ta miƙe a kan ƙafafunta."
Hawaye ne suka zubowa Ɗan Liti ya kalli Mommy yana laso harshen shi da ke can saman haƙoran shi ya ce,
"Allah ya yi miki albarka Uwata,na gode,na gode,ba dan ke ba da ban san yanda zan yi da uwar nan taku ba,ke Naja taso mu tafi kar dare ya yi mana a hanya."
Sallama suka yi wa Mommy suka tafi,ita kuwa anan ta zauna ta ci gaba da kula da Innoh,a zuciyar tana godewa Abdul da ya wadata ta da kuɗi a lokacin da tana gidan shi.
*****************************
Dik da gargaɗin da Mai Dusa ya yi wa Billy akan kar ta je garin Ba Mugu be hana ta ɗaukan wanka ba ta sayi tsarabar ta gijif,ta saka a bayan motar Man su kama hanyar ƙauyen Ba Mugu dan ganin iyayen nata.........
*To Billy Allah shi kai lahiya.*
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBITAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 102:
Tin a hanya Billy ke ta mitar ƙin bin su da Anny ta yi,domin kuwa ta tabbata Ta Annabi zata so ganin ta saboda shaƙuwar da ta shiga tsakanin su mai ƙarfi. Man kuwa sai lallashin ta yake yi yana nuna mata dalilan da Any ta kawo masu ƙarfi wanda sune suka sa bata bisu ba,da ƙyar ta haƙura ta dena jan maganar ta kama wata.
A haka suka isa garin Ba Mugu fuskar ta ɗauke da farin ciki. A ƙofar gidan su Billy Man ya ajiye motar shi. Billy na tattara jakar hannun ta da ledar da ta yo musu tsaraba ta fruits da sauran kayan maƙulashe Man ya fita ya buɗe mata motar,kayan hannun ta ya rage mata sannan suka isa inda Shamsu ke ƙoƙarin rufe shagon shi da ya mayar shagon saida harawa da dusa. Baki ya washe sannan ya karkaɗe hannun shi ya miƙawa Man suka gaisa,cikin gidan ya yi musu jagora suka shiga cike da farin ciki.
Billy na yin arba da Fadilah sai suka tafi a guje suka rungume junan su Hauwa kuwa washe baki take ta yi kamar gonar audiga,Ta Annabi ce ta fito yafe da mayafi tana tafa hannuwa ta na faɗin,
"Lale maraba,lale da mutanen kano,yanzu kuke tafe? Bismillah ku shigo daga ciki."
Suna tsaka da murna da farin cikin ganin junan su suka ji hayaniya a ƙofar gida matasa na faɗin,
"Tana ina? A fito mana da ita mu jefe makira mazinaciya ! "
Cike da tashin hankali Mai Dusa dake cikin ɗaki ya fito ya na kallon su Billy da Man da suka rikice da tsoro,a hankali ya ce,
"Kai Shamsi zo nan ka kira min sanƙira ka ce ya sanar da sarki abinda ke faruwa a gida na,tinda ai Malam Liman ya san da ɗaurin auren Bilkisu da wannan yaron,Yaya Buhari ya faɗa masa da kan shi."
Cikin sauri Shamsu ya fita ya kutsa ta cikin fusatattun matasan ya nufi fada a guje,kafin ya isa fada Ameerah ta dawo daga gidan su,da ƙyar ta samu suka barta ta shiga gidan,sai da ta shiga ta ajiye goyon ta sannan ta zindimi taɓaryar da Ta Annabi ke dakan fura ta yi waje a guje tana ihu,duk kiran da Mai Dusa ke yi mata bata ji shi ba,ganin ta da doguwar taɓarya a guje ne ya sa matasan yin baya a guje suma,sai da ta tsaya a ƙofar gidan ne tana haki ta hau magana cikin bala'i ta ce,
"Ku har kun isa ku zo ƙofar gidan mu ku yi mana hauka? To shegen da be fasa abinda ya yi niyya ba uwar shi yawon kwararo tayi ta haife shi,matsiyatan banza kawai,waye a cikin ku baya aikata saɓon Allah? Ko shi kallon film ɗin batsar da kuke yi halal ne? Ba se da kuka kalla ba sannan kuka gano me ta aikata a ciki har kuke neman ku dinga yi wa mutane hauka a gida?"
Wani ƙyarmasasshen matashi ne ya fito fili ya ce,
"Eh mun ji mun kalli haramun ɗin,amma ai mijin ki shine yake tura mana mu kalla."
"Gidan ku ya je ya janyo ku yace dole se kun kalla? Ba kud'in ka ka ke sakawa ba a tura maka? Kai koda a gida ka kalla kai kaɗai cikin sirri dole sai ka saka kuɗi sannan ka kalla,kaga kenan kai ka kai kanka,kuma dik zunubi zunubi ne,zunubin da Allah ke yafewa shine wanda ake yiwa tuba na gaskiya da niyyar ba za a sake komawa wannan zunubi ba."
Hayaniya ce ta kaure a tsakanin matasan da Ameerah,wasu na so ayi cikin Ameerah kawai a ragargaje ta a afka gidan a kashe Billy da Man,wasu kuma suna ganin kawai su tafi su bar su. Suna nan suna hayaniya a tsakanin su Mai Dusa ya fita ya ce wa Ameerah.
"Ke Ameerah shiga gida ! Rabu dasu su bi takaina su shiga gidan nawa tinda basu da mutunci."
Hannu Ameerah ta sa tana nuna su ɗaya bayan ɗaya kafin ta yi ƙwafa ta faɗa gida riƙe da tabarya kamar wata tsohuwar ƴar daba. Matasa na nan tsaye suna yiwa Mai Dusa rashin kunya Sarki ya aika daga fada a kira duk wanda yake a wajen,sannan Bilkisu da mijin ta da Mai Dusa ma su je gaban sarki yana son ganin su.
Da jin haka matasan nan sai jikin su ya yi sanyi,babu yanda suka iya akan dole suka ɗauki hanyar tafiya gidan Sarki. Se da suka yi nisa sannan Man da Billy da Mai Dusa suka shiga motar Man suka nufi fada. Suna isa suka ratsa ta tsakanin matasan a tsorace suka samu waje suka kwashi gaisuwa a gaban sarki. Bayan waje ya lafa ne Sarki ya tambayi bahasin zuwa gidan Mai Dusa a dinga yunkurin yin kisa a cikin ƙauyen shi.
Nan take wani tsageran matashi a cikin samarin ya miƙe ya isa tsakiyar fada ya duƙa gaban Sarki ya kwashi gaisuwa,sannan ya ce,
"Allah ya baka yawan rai,yarinyar nan Bilkisu ƴar gidan Mai Dusa mazinaciya ce,watannin baya aka dinga yaɗa videon ta a garin nan tana aikata masha'a a kasar masu jan kunne,da ace zina da maza kawai take yi da da sauƙi ranka shi daɗe,amma abun nata ya yi yawa har mata ƴan'uwanta take bi, ƙarshe ma har auren jinsi tayi."
Sarki ne ya nisa yana sauraren dika bayanan matashin,cikin zuciyar shi yana tunano yanda Abdul ɗin shi ya faɗa tarkon zina a baya,lallai wannan zamani da muke ciki abun tsoro ne,kusan kullum ma abubuwan gaba suke yi. Gyaran murya Sarki ya yi sannan ya ce,
"To kai dik a ina ka san an yi waɗannan abubuwan dika?"
Kame-kame ya fara yi saboda tinawa da maganar da Ameerah ta yi musu,cikin kame-kamen ya ce,
"Ammm ranka ya daɗe...uhummm damaaa..ihummm dama...."
Hannu Sarki ya ɗaga masa kafin ya saki murmushin manya ya ce,
"To ka ga kaima ba za ka iya maimaita a inda ka gani ba ko? To ai kamar haka ne itama ta tuba zuwa ga Allah wanda ta saɓawa,wanda idan ta yi zunubi shi yake da ikon hukunta ta ko ya yafe mata,ba wai ƴan Adam ba da su kansu masu aikata zunubai ne. Mu sani ɗaukan hukunci irin haka ba namu bane,sakamakon abinda ta aikata da a ƙasar da ake aiwatar da shari'ar musulunci ne sai a tsayar mata da hukunci,amma a irin ƙasashen nan namu sai dai mu yi wa mutum nasiha,idan ya gyara tsakanin sa da Allah haka ake so,idan kuma ya bijire sai a miƙa shi ga hukuma,idan hukuma ta hukunta shi ya dawo ya ci gaba da abinda yake yi mara kyau sai a bar shi da Allah ya ɗauki mataki akan shi da kan shi.
Dan haka daga yau bana son na sake jin makamancin abinda kuka aikata ya faru a garin nan,tinda kuma baku wuce Allah ya yi maku irin jarabawar da ya yi mata ba,gaku nan a cikin ku na hango wasu da anan fadar tawa aka sha yanke musu hukuncin wasu laifukan da suke aikatawa,har yanzu sun dena?"
Amsawa Sarkin fada ya yi da,
"Ah ah Allah ya baka yawan rai"
Sarki ya gyara zaman shi kaɗan sannan ya ce,
"To kun gani? Dan haka kar na sake ji ko ganin kun maimaita abinda kuka yi yanzu,ku baku san wannan tozarcin da kuke yi musu sai ya d'aga darajar su a wajen Allah ba ku kuma ku samu zunubi? Kar fa ku manta zina laifi ne na tsakanin bawa da Allah,idan ya yafe musu ku kuma kuka shiga fushin shi fa?"
Mai Dusa ne ya duƙar da kai gaban sarki ya ce,
"Ballantana ma Allah ya baka yawan rai,yana daga cikin tuban da suka yi,yaran nan suka sadaukar da dukiyar su kafff zuwa ga mabukata,suka kama sana'a a can kano ta halal,har ta kai ga ita Bilkisu ta auri wannan bawan Allah'n,Man Liman tawo ka bada shaida,ana kuma iya kiran yayu na su bada tasu shaidar,dan kuwa suna nan komai ya wakana."
Sarki ne ya ce
"To alhamdulillahi ai haka ake so,ana so idan bawa ya aikata zunubi ya gano laifin shi,sai ya tuba ya gujewa wannan zunubin,idan da hali ma ya bar wajen da ake yin wannan zunubin ya sauya sabuwar rayuwa,Allah ya sanyawa auren ku albarka,ku tashi ku tafi bana so na sake jin abinda ya faru na tashin hankali ya maimaita kanshi."
Haƙuri matasan nan suka bayar,Billy ta miƙe kanta a kasa ta shiga gidan Sarki,se da ta gaida Innah Laminde,sannan take sanar da ita duk abinda ya faru,jajantawa juna suka yi sannan Innah Laminde ta sake yi mata nasiha mai ratsa zuciya,kafin ta shiga ɗaki ta d'akko mata tukuicin auren da ta d'aura,murna Billy ta dinga yi tana godiya,da zata tafi sai Amir ya rikice da kuka,saboda tinda ta shiga gidan ta ɗauke shi tana yi masa wasa,ganin yanda yake kuka sosai ne ya sanya mata jin dama ace Innah Laminde zata bata shi,da ta tafi dashi ta riƙe shi,da ƙyar aka karɓe shi a hannun ta ta musu sallama ta tafi.
Man ne ya buɗe mata mota ta shiga suka isa gida,Mai Dusa kuwa har ya isa ya sanar da su Ta Annabi yanda abubuwa suka kasance a fada,hamdala Ta Annabi ta yi sannan ta ce,
"Alhamdulillahi mun godewa Allah da ya kawo mana karshen wannan tashin hankali,kaga se su kwana abun su ko malam?"
Shigar su Billy ce ta katse masu hirar da suke yi,Billy zama ta yi ta ce,
"Ai kuwa yanzu zamu koma Ummah,dan gaba ɗaya a tsorace yake,ya ce mu tafi kawai idan an kwana biyu an gama shirin tarewa ta na tare sai ku je ku ga waje."
"Hakan ma babu laifi,Allah ya tsare ya kiyaye ku,Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a me albarka,Allah kuma ya kawowa Anam ɗina miji itama tai auren ta,bari na ɗakko saƙo ki kaiwa ƴa ta."
D'aki Ta Annabi ta shiga ta hau kwaso tsarabar da ta tanada tin kafin su zo,ledar Man daban ta Anam daban haka ta miƙa musu,godiya suka yi Man da Shamsu suka fita waje suka kwaso tsarabar da suka zo musu da ita ta kayan abinci. Suna gamawa suka yi musu sallama suka kama hanyar komawa Kano.
A hanya Billy kuka ta dinga yi,tana tina mummunar rayuwar da baza ta taɓa mantawa da ita ba,ta riga ta san ta yiwa kanta illa babba,gashi tana tare da iyayen ta a gari ɗaya tafiyar awa ɗaya da wasu mintina ne za su kaita wajen su amma babu halin ta zauna cikin dangi ba tare da tsangwama ba. Lallai rayuwar bariki bata da riba a wajen mutanen kirki,ribar bariki a wajen ɗan bariki kawai take,sune idan suka mallaki dukiya da dik abinda suke da buƙata suke ganin sun gama samun komai a rayuwa.
*******************************
A cikin shekarar da Azizah ta kammala School of Health ɗin ta ta dawo gida a cikin shekarar aka sanya ranar auren ta ita da Bilal. Farin cikin da Bilal da Azizah suka shiga baya misaltuwa,Bilal kuwa na ganin tasku a wajen Abdul,dan kuwa da ya yi abu Abdul zai hau shi da faɗa yana faɗin,
"Se in fasa baka ƙanwar tawa."
Kan dole Bilal ke yiwa Abdul ladabi na musamman ba dan ya so ba. Azizah kuwa da iyayen ta na can na gyara ta saboda gabatowar bikin ta. Dik wata al'ada da ake gabatarwa a lokacin biki an gabatar a shirin bikin Azizah,kama daga kai kayan na gani ina so har lefe dika an kai mata,iyayen Bilal sun yi bajintar da shi kanshi be san sun yiwa auren shi wannan tanadin ba,har kukan farin ciki sai da ya yi da yaga yanda ƴan'uwan shi ke fito da gudummawar da suka tara masa.
Bayan wata biyu da kai lefe aka fara hidimar bikin Azizah da Bilal.ranar kai Amarya ne Abdul ya haɗu da Suhailah ƙanwar Bilal dake Yola tana karatu,kallo ɗaya ya yi wa yarinyar ya ji ta kwanta masa a rai,bai yi ƙasa a guiwa ba kuwa wajen sanar da Bilal abinda yake ji game da Suhailah,nan take rawar kai da iyashege ya tashi a wajen Bilal,rantsuwa yake yana kumawa sai ya wahal da Abdul kafin ya bashi auren Suhailah,Abdul kuwa dariya kawai ya yi ya ce,
"Indai zaka bani auren ta ai ko goya ka kace in yi zan yi Bilal."
*Too mutanen k'warai masu albarka kuna ganin idan Bilal ya bar Abdul ya auri ƙanwar shi Suhailah ya kyauta kuwa? Tinda dai ya fi kowa sanin menene matsalar Abdul.*
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 103:
Gagarumar walima Any ke haɗawa cikin sirri ba tare da sanin Billy ba. Anam ta gayyaci dangin amarya da ango har ma da manyan malaman da za su yi wa'azi a wajen walimar ba tare da sanin Billy ba. Sauye-sauyen da Billy ta gani game da Any har ya fara bata tsoro, dan haka sai ta shirya tinkarar Anyn dan ta ji ko ta aikata mata wani laifin ne yasa take janyewa daga gare ta.
watarana da yamma suna zaune Billy ta kula da Any na yawan amsa waya da saƙonni akai-akai,babban abinda ya fi damun Billy shine idan Any zata yi wayar sai ta tashi daga inda take ta keɓance kanta,wanda hakan ba ɗabi'ar su bace,cikin dakewa Billy ta ce,
"Wai ni kam dan Allah akwai abinda na yi maki ne kike ɓoye min? Idan na yi wani laifin ne da ban sani ba ki sanar dani mana saboda na gyara amma ba wai ki dinga ƙyale ni ba kina rayuwa kamar ke kaɗai ce a gidan nan."
Murmushi kawai Any ta yi mata,ba tare da ta ce komai ba,wayar ta ce ta ƙara ringing sai ta miƙe tana amsawa zata fita,hanya Billy ta tare mata tana kallon Any tare da neman ƙarin bayani akan tambayar da ta yi mata,kallon gargad'i Any ta yiwa Billy sannan ta yi mata nuni da yatsun ta akan ta bata hanya ta wuce,matsawa Billy tayi ta koma saman kujera ta zauna cike da damuwa a ran ta,shin ko dai Any bata son ta yi aure ta tafi ta barta ne? Murmushi Billy ta yi ta miƙe dan ta bi bayan Any ta lallashe ta,sannan ta nuna mata cewar gidan ta wajen zuwan ta ne a duk sanda ta so,tana fita babban parlourn su ta tsaya tana wangale baki cike da mamaki,daga ƙarshe ta sanya ihun murna ta tafi da gudu ta rungume Ta Annabi da su Fadilah,rasa inda zata saka kanta tayi dan murna sai kawai ta fashe da kuka ta rungume Any,Any kuwa Video take ɗaukan ta idanun ta fal hawayen farin ciki. Wata iriyar kewar iyayen ta ke cin zuciyar ta wannan lokacin,rungumar da Billy ta yi mata sai ta karya mata zuciya,nan take ta hau kuka jikin ta har yana jijjiga,zama suka yi a kujera Billy na share mata hawaye,cikin kuka kamar ƙaramar yarinya ta ce wa Billy,
"Ina kewar iyaye na Bilkisu,ki godewa Allah naki suna raye,gashi har Allah ya nuna musu auren ki,ni kuwa duk burin da Malam da Mama suka ci akai na basu ga ko ɗaya ba."
Ta Annabi ce ta taka zuwa inda Any da Billy suke zaune suna kuka,dafa kafadar Any tayi ta ce,
"Allah ya jiƙan iyayen ki Anam,Allah ya yi musu rahama,daga yau ina so ki sa a ran ki ke ƴar gata ce,saboda kina da wasu iyayen a raye bayan wanda suke ƙasa,kin ga kenan nauyin addu'a biyu ya hau kan ki yanzu,ni da Baban su zamu zame maki iyayen da kika rasa har ƙarshen rayuwar mu."
Cike da murna Any ta rungume Ta Annabi tana kukan farin ciki,rashin sabo da runguma ne ya sa Ta Annabi ƙyalƙyalewa da dariya,cikin ƙanƙanin lokaci taji ƙaunar Any na huda zuciyar ta, addu'a ta dinga yi mata har sai da Billy ta tura baki ta ce,
"I am jealous ooo,to ni kuma fa?"
Fadilah ce ta ce,
"Cewa zaki yi mu kuma faaa?"
Dariya suka yi dikan su,daga baya Any ta shiga kitchen ta fara gabatar musu da abinci da abubuwan shan data tanadar musu,suna zaune suna cin abinci Billy ta ce,
"Ashe suprise ɗin da kike haɗa min kenan shi yasa kike ta wani share ni? Kin sa ina ta tunani kala-kala a rai na,babu abinda ban tina ba ko shi na yi maki kike fushi dani."
Any da Hauwa ne suka kalli juna suka tafa suna dariya,su kaɗai suka san me suke ƙulawa,kan Billy ne ya sake kullewa,amma sai ta yi shiru bata sake cewa komai ba,ta ɗauki hakan a sabo da Any tayi da su Fadilah ta waya,suna kammala cin abinci aka yi wa Any waya,ita kaɗai ta ɗauki key ɗin shago ta fita,ta jima sosai a waje kafin ta dawo cikin gidan.
Hira ta tarar da su Billy na yi da ƴan'uwan ta,babu ɓata lokaci kuwa ta shiga suka ci gaba da yi da ita.
Washegari da sassafe bayan sun yi sallar asuba Billy ta hau ƙoƙarin komawa bacci,Ta Annabi ce ta tashe ta ta hau yi mata gyara irin nasu na mutanen da da ya ƙunshi kayan gyaran jiki na musamman da muke amfani da su yau da gobe a gidajen mu,wanda basu da illa ga fata balle su jawo cancer ko wata cutar da zata lalata fatar mutum (ku nemi littafin MAIDA TSOHUWA YARINYA na HAERMEEBRAERH dan samun kayyakin gyaran jiki a sauƙaƙe. 09031416423 yana nan akan farashin #1000 kacal,akwai abubuwan gyaran jiki na ciki da waje da littafin ya ƙunsa guda 40 wanda har sana'a mutum yana iya ɗaukan wasu ya fara yi).
Rawar kan da Fadilah ke yi ne