Showing 126001 words to 129000 words out of 276165 words

Chapter 43 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

inda zan je, amma sab'anin haka a daren nan zan bar ƙauyen nan ke baki isa ki hana ni yin abinda zan yi ba,'

"Yaya tinda yarinyar nan ta fara magana na gane mun baro gini tun ranar zane, anan na gane MUN MAKARO wajen yi mata tarbiyya, Yayah a ƙarshe na gane Bilki na bin maza da mata dan kawar da sha'awar dake cikin zuciyar ta, anan na gano har yanzu Bilki bata san menene so ba biyan buƙatar sha'awar ta shi ta ɗauka a so,Yayah na gane cewa Bilki na da tsananin sha'awa tin tana ƙarama nayi sakaci nayi ganganci bamu ɗauki mataki ba muka sakar wa duniya ita har ta hora ta da tarbiyyar karnuka,Yayah yanzu maganar danake yi maki Bilki ta bi wani ƙato a mota sun bar garin nan a gaban idona, dik irin kira da alƙawarin tsinuwa da masifa da bala'in da na dinga jawo mata bai sa ta waigo bama balle ta dawo,"

Salati Innah Laminde ta sake sauke wa sannan tace,

"Na shiga uku ni Laminde, innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, ke duniya ina zaki je damu? A zuri'ar mu ake ta samun irin wannan lalacewar? Me duniyar nan ta zama ne yanzu? Lallai mu iyaye muna da babban ƙalubale a gaban mu, ashe kana tarbiyyantar da yaran ka su kuma suna yi maka kallon kai ba ɗan cikin mu bane mun san yanda za mu tafiyar da rayuwar mu yanda zamanin mu yazo mana da shi, yanzu meye abun yi? Kin san inda take aiki a lokacin da take aikin?"

"Ina fa Yayah, shine babban kuskuren da muka sake tafkawa a rayuwar mu,mun saki yarinya tana abinda ta ga dama ba tare da sanin ina take ba, wajen wa take, shin aikatau ɗin take yi ko karuwanci? Yanzu dai kin ga da kunne na naji kalmar da ta kirawo kanta da shi ba wani ne ya sanar dani ba, Yaya ina zan saka raina yanzu ni Ta Annabi? Na ci amanar haihuwa, na ci amanar Allah da manzon sa, ban kula da tarbiyyar yara na ba,dan Allah Yaya ki sama min mafita zuciya ta zafi take yi,"

Innah Laminde kanta ji take yi kamar ta saka kuka ko zata ji sauqin abinda ke cikin zuciyar ta, cikin sauri ta dafa kafaɗar Ta Annabi tace,

"Yauwaa bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu da dare zan sa Abdul ya kawo min matar shi nan, sai a tambaye ta gidan da suke aiki, wataqila acan za a samo bakin zaren,"

Sauke ajiyar zuciya Ta Annabi tayi sannan tayi wa yayar ta godiya sannan suka ci gaba da tattaunawa akan yanda za su bullowa lamarin, suna nan zaune suka ji ƙarar motoci da gud'a ana shigowa da amarya, band'akin dake cikin d'akin Innah Laminde tace Ta Annabi ta shiga ta wanke fuskar ta ta same su a parlourn ta a tarbi matar Abdul da ita, ba dan ta so ba haka ta shiga bayin ta wanke fuskar ta ta isa parlourn Innah Laminde, zaune ta ga Mommy cikin alkyabbar da Innah Laminde ta jima da siya ta ajiye tace ta matar Abdul ce, a kullum taga rigar sai tayi mafarkin ace Bilkisun tace ta sanya rigar, sai gashi ashe ba rabon ta bace 'yan d'akko amarya sun sanya wa Hadizan gidan Ɗanli,Mommy ce zaune gaban Innah Laminde wadda ta amsa gaisuwar ta, ta yi mata nasiha, sannan 'Yan uwan Innah Laminde suka shiga suka d'akko mata kyaututtukan auren da aka tanada domin ta, wanda ya haɗa da turarukan jiki da na wuta sai atampopi da laffaya da alkyabba guda biyu, sai dogayen riguna irin na sarauta guda uku, godiya Mommy da su Naja suka yi, nan dai kishiyoyin Innah ma suka yi kara suka ajiye nasu kyaututtukan har da kuɗi, daga nan aka ɗauki amarya aka nufi gidan ta da ita.

Ko da aka kai amarya ango ne ya fita ya kama hannun matar shi ya tsaya yayi wa kowa godiya sannan yace ga motoci nan za su maida kowa gida, daga fad'ar haka kowa ya gane ango dai baya son 'yan rakiya, dan haka babu musu kowa ya shiga mota aka maida shi gidan da ya sauka daga bangaren amaryar har zuwa na angon.

Amarya da ango kuwa da bismillah suka shiga gidan su bayan ya shigar da motar shi ya kulle da kyau tinda kyaututtukan amarya Mommy ma na ciki gobe sun kwashe abun su, kallon gaban gidan da suke fatan gina rayuwa ta musamman a cikin shi suka tsaya suna yi, gidan da suke fatan tara nasu zuri'ar a cikin shi, gidan da Mommy ke fatan ya kasance nata ita kaɗai har abada, dan kuwa yanda take so da ƙaunar Abdul ne ya sanya ta ƙin ƙarasawa cikin gidan ta coge suka tsaya kallon kallo ita da angon nata..............
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI















RUBUTAWA : HAERMEEBRAEH ✍️✨














PAGE 49:







Kallon Mommy Abdul yayi fuskar shi ɗauke da annashuwa da annuri sannan yace,

"Bismillah mana ko kuma so kike yi na ɗauke ki na kai ki ciki da kai na kamar yanda ake yi a films ko a littafan hausa?"

Fara'ar fuskar shi ce ta ɗauke dan ganin yanda Mommy ta yi serious babu alamun wasa a fuskar ta tace,

"Abdussabour ba zan shiga gidan ka ba dik son ka da nake yi har sai ka yi min alƙawarin da zai sanya zuciya ta natsuwa da kai,"

Cikin rashin fahimta Abdul ya kalle ya yace,

"Sanar dani alƙawarin da kike so nayi maki yanzun nan na yi miki shi,farin cikin ki shine nawa Habibty,"

Hannun shi ta kama dika biyun ta riqe su a nata kamar wadda aka ce za a raba su sannan tace,

"Ina so kayi min alƙawarin baza ka yi min kishiya ba har ƙarshen rayuwar mu,ko da nan gaba wani zai ce ka ƙara aure in dai bani bace ba baza ka ƙara ba,"

Ba tare da zurfin tunani da nazari akan kalar girma da matsayin alƙawarin da yake shirin amincewa akai ba ya sake jimƙe hannayen mommy yace mata,

"Na yi maki alƙawari har abada ba zan yi maki kishiya ba, Hadiza ni Abdussabour naki ne ke kaɗai zuciya ta ke kaɗai take so take kuma kwad'ayin kammala rayuwar ta da ita har abada,zamu iya shiga yanzu?"

Sunkuyar da kanta tayi ƙasa tana jin wani irin farin ciki da annashuwa na kama ta,sai kawai ta sanya hannun ta ta rataye nashi suka ci gaba da takawa a tare har suka kai bakin ƙofar da zata sada mutum zuwa cikin main house ɗin,makulli ya sanya a ƙofar ya buɗe sannan ya sanya ƙafar dama ya shiga da amaryar shi,babu wutar lantarki dama jannareta aka kunna a gidan dan haka suna rufe ƙofar ƙarar ta ragu,kallon gidan Mommy ta dinga yi tana godewa Allah da ya nuna mata zata yi rayuwa a irin wannan muhallin,basu samu suka zauna ba har sai da Abdul ya gama nuna mata ko ina na cikin gidan tana ta murmushi tare da yi masa godiya.

A master bedroom suka yada zango,inda suna shiga Abdul ya cire babbar rigar shi sannan ya cire wa Mommy alkyabbar jikin ta ya rataye musu a jikin wani royal ƙarfe na rataye kaya,kayan ɗakin gaba ɗaya kalar gold ne mai kyalli da ɗaukan idanu, sai glass mai kyau dake haska su manya manya a jikin wardrobe.

Zama Mommy tayi a bakin gado jikin ta yayi mugun sanyi, yanzu to gata an yi auren fari amma babu budurcin da za a baiwa ango, wata iriyar matsananciyar nadamar yawon da tayi ce ta mamaye ta lokaci ɗaya,cikin sauri ta miqe ta nufi band'aki ta rufe qofa, a jikin qofar ta jingina ta fashe da kuka mai ƙuna, tin tana yi a tsaye har sai da ta zauna a ƙasan tiles ɗin banɗakin dake a tsaftace,jin alamun kamar kuka take yi ne ya sanya Abdul zuwa jikin ƙofar yana k'wank'wasa cike da damuwa mommy tace,

"Yah Abdul kayi hakuri,kayi hakuri da abinda na aikata wa rayuwa ta dan kuwa kai mummunar ƙaddarar ta afkawa,Yah Abdul ni ba budurwa bace, bana tattare da budurci na na zubar da shi ba ta hanyar da ta dace ba, wannan video da hotuna da Billy ta tura maku tabbas ni ce ba ƙarya, kuma ina cikin wajen gyaran jiki ne kamar yanda ka yi hasashe, amma ...."

"Ya isa haka Hadiza, abinda ya faru a rayuwar ki ta baya yariga da ya wuce, abinda ya faru a rayuwa ta ta baya nima yariga da ya wuce, a yanzu rayuwa zamu gina ta tsakani da Allah, babu cuta babu cutarwa, aure muka yi a yanzu kuma aure zamu raya har mu hayayyafa da izinin Allah,dan haka ki dena tada hankalin ki komai ya wuce,amma tambaya ta anan shine ya aka yi kika san Bilkisu ce ta tura min hotunan nan?"

"Yah Abdul na gode da zaka karɓe ni a yanda nake, na yi maka aƙawarin zama mace ta gari wadda zata tsare maka mutuncin ka har abada,ba zan sake shashancin da na aikata a baya ba,na gano Billy ce ta tura saboda ita da bakin ta ta sanar dani ta waya d'azu da ana rububin d'akko amarya, ta kira ta sanar dani dik abinda ta aikata wanda ya sanya jini na tafasa naji na tsani kaina na tsane ta, ta nuna wa Innah Laminde, ta turawa Yah Bilal da Sultan sannan har yanzu akwai a wayar ta bata goge ba,kuma ta yi alƙawarin sai ta yaɗa a social media idan ban amince mata ba,"

"Ban gane idan baki amince mata ba? Ki amince mata ayi me?"

Buɗe ƙofa mommy tayi ta fita ta zauna a gefen gado tace,

"Billy na so na, ko ince tana sha'awa ta, ta jima tana so na amince mata mu keb'e na ƙi, to shine yanzu take bani tsoro da videos da hotuna na akan idan ban saka rana na amince mata mun keb'e ba zata watsa ni a duniya,"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, what ! Kina nufin ku aikata mad'igo fa kenan? Kin taɓa yi ne?"

Cikin sauri Mommy tace,

"Haram, ban taɓa aikata mad'igo ba,wannan dalilin ne ma yasa muka dinga samun saɓani da ita Billyn, ta neme ni na ƙi amincewa,"

"Kar ki damu, Allah ya kaimu gobe zan ji da komai, yanzu ki tashi kiyo alwala mu gabatar da nafila, na fara jin yunwa akwai abinci a kitchen da Sultan ya ajiye mana sai mu ci, ko bakya jin yunwa?"

Cikin sauri Mommy tace,

"Kaiii ina ji mana sosai ma"

"Da kyau amarya ta, maza shiga kiyi alwala bari nazo,"

Tana faɗawa band'aki ya fita ya zauna a parlour tare da tallabe kan shi ya zabga tagumi,yanzu shikenan ya auri macen da ta gama rayuwa da wasu? Shikenan Bilal da Sultan da mutanen da bai san adadin su ba sun gama gane masa jikin matar shi,gashi kuma yanzu bai san iya ina videos da pictures ɗin ta zai tsaya ba.

Wani irin ƙunci yake ji a cikin ran shi da rad'ad'i,tabbas ya aikata mummunan kuskure na lalata yaran mutane da yayi a baya,wasu yaran ma makaranta aka aiko su suyi amma haka ya dinga amfani da kyan shi da kud'in shi ya ja ra'ayin su har sai da suka amince masa suka aikata masha'a,wasu kuma dama can sun baro gidajen iyayen su da nufin zaman kan su ba shi ya fara lalata da su ba,ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi sannan ya miqe yace,

"Tabbas dik abinda bawa ya shuka sai ya girbe shi, ko a duniya ko a lahira, na godewa Allah da abun ya tsaya akai na, Allah ka kare min zuri'a ta da ƙanne na mata, Allah ka basu mazaje na gari ba iri na ba, Allah kasa daga wannan darasin ya zama mun kiyaye gaba dani da ita kanta Hadizar, yanzu na riga na gane cewar da na aikata zina gwara na ƙara aure,"

Wata iriyar fad'uwar gaba ce ta riske shi a lokacin da ya tuna da alƙawarin da yayi wa Mommy, kallon hanyar d'akin nata yayi sannan ya sake furta,

"Allah ka shiga dikkan lamura na,"

Motsin Mommy yaji daga bayan shi ta fito sanye da wata arniyar rigar bacci mai santsi iya cinyoyin ta sutum-sutum masu laushi da ɗaukan idanu,cinyoyin da mata da yawa suke biyan miliyoyin kuɗi dan a yi musu dashen irin ta,gashin ta da ya sha wanki ta tattare a tsakiyar kanta sannan ta nufe shi sai baza qamshi take yi,Abdul na ganin haka ya washe baki, dan kuwa abun nema ne ya samu, dik da yana jin yunwa ba zai bari wannan damar ta wuce shi ba,har ya tunkare ta ya tuna da ko nafila da addu'ar da ake yiwa amarya bai yi ba dan haka sai ya ci burki yana nazari, wannan fa aure yayi ba bariki ba, da sauri ya kauda kan shi ya juya ya wuce kitchen, Mommy kuwa tsayawa tayi dindiris kamar an dasa ta a wajen me hakan ke nufi? dik sai taji guiwar ta ta sage kunya ta kama ta( dama in ba dan sabo da bariki ba amarya a daren farko ina ita ina irin wannan abun?) a hankali ta juya ta koma ɗakin ta ta samu abayar ta ta zira a saman kayan ta ta zauna a bakin gado tana hawaye, da ta san haka zai yi mata da bata zubar da ajin ta ba, ai a zaton ta ya waye haka shine ya dace suyi a daren su na farko.

Ko da Abdussabour ya dawo d'akin ɗauke da leda mai layi layi sai plates da cups tare da ruwan sha roba biyu ya ganta zaune tana hawaye, sai ya ajiye kayan hannun shi a gaban ta sannan ya miqa mata hannu alamar ta sauka taje gare shi, cikin tura baki ta kama hannun nashi ta zauna tana shagwab'a,murmushi yayi sannan yace,

"Haba amaryata fushin fari ai ba naki bane ko? Ai bana so mu fara abinda zamu tsaya bamu cimma burin mu ba shi yasa kika ga na gudu,ina so mu ci mu ƙoshi sannan muyi nafila mu godewa Allah sai kuma koma mai zai faru ha biyo baya ko?"

"Hakane kuma, na zaci ko ƙyamata kake yi,"

Da sauri ya kama fuskar ta ya ƙurawa fuskar tata idanu yace,

"Habaa ƙyama kuma? Bari ki ga mu ci abinci na nuna maki wani abu."

Murmushi suka yi a tare sannan suka hau cin abincin su,sai da suka ci suka ƙoshi sannan Abdul ya koma ɗakin da yake mallakin shi ne ya watsa ruwa a gaggauce yayi alwala sannan ya sanya jallabiyya mai haɗe da wandon ta ya sanya turaruka masu ƙamshi ya wuce d'akin ta, zaune ya ganta saman abun sallah da alama tayi alwala ma, sai kawai ya shiga gaba ya tada sallah.

Tinda suka fara basu tsaya ba saida suka yi raka'a biyun nan da ake yi, sannan Abdul ya yi wa Mommy addu'a ya ja ta ya hau cire mata mayafin jallabiyyar ta, Mommy na ganin haka kuwa bata yi ƙasa a guiwa ba wajen miƙewa ta kashe fitilar d'akin ta fara karantawa Abdul haddar da ta kwaso a gidan Hajiya K'waisa.

Washegari da safe haka suka farka a gajiye da misalin bakwai na safe, a gurguje Abdul ya miqe ya shiga band'aki dan ya tsarkake jikin shi, Mommy na lalubawa taji baya nan sai ta miƙe ta bi bayan shi,nan ma bata bar su sun fito sun yi sallar asuba ba sai da suka b'ata lokaci.

Abdul ne ya ja su sallah suna idarwa ya miqe yaje d'akin shi ya ɗakko wayar shi yana ta zabga murmushi saboda nishad'in da ya samu a daren jiya da kuma safiyar yau din,yana duba wayar sai yaga missed calls ɗin Innah Laminde dana Bilal da Sultan sai Sudaif wani cousin ɗin su ta bangaren mahaifin su,cikin sauri ya kirawo Innah, cike da ladabi ya gaishe ta ta amsa, sannan tace masa,

'Sarauta ina son da dare misalin takwas na dare ka kawo min matar ka akwai tambayar danake so nayi mata,'

Shiru ya d'anyi kafin yace,

"To Innah Allah yasa dai lafiya,"

Muryar ta ta saki kamar babu wata matsala sannan tace masa,

'Babu komai Babana kai dai Allah ya kaimu kuzo ɗin kaji koma menene, a gaishe ta,'

"Za ta ji na gode, sai mun zo ɗin,"

Bayan yayi sallama da mahaifiyar shi ne ya kirawo Bilal da Sultan da Sudaif, dika gaisuwa ce sai tsokana da ya samu daga wajen Bilal, gaba ɗayan su haushin su ma yake ki yanzu dan sun gane masa matar shi babu kaya,a gaggauce ya gama wayar da su ya koma d'akin Mommy, samun ta yayi zaune tana waya da Sule,zama yayi a gefen ta yana sunsunar ta yana lumshe idanu.

"....eh dan Allah ka d'akko min dika ka kawo min yanzu, idan yaso in kazo zan baka sai aje a siyo mata masu kyau a je a ajera mata itama a kaita d'akin ta.....tom sai ka zo,"

Tana kammala wayar ta ajiye ta kwanta a jikin Abdul tana yi masa kukan shagwab'a,

"Yah Abdul yunwa nake jii,"

"Ni kaina yunwar nake ji, da zan samu ƙari da na so,"

Ture shi tayi a jikin ta tana dariya ta fita daga d'akin da gudu ya bi bayan ta yana dariya, haka suka yi ta zagaye parlourn suna dariya har yayi nasarar kama ta suka zube a kujera,cikin maida numfashi da sauri da sauri tace,

"Da gaske fa yunwa nake ji, har wani jiri jiri nake ji,"

"Kina jin jiri kika wahal dani? Anyway babu komai Sultan zai kawo mana abinci yanzun nan, dan Allah ina son yi maki wata magana Sweety.."

Cikin sauri Mommy ta b'ata rai ta kalle shi tace,

"Ka kira ni da kowanne suna amma banda wannan bana so,"

Mamakin b'ata ran nata ne ya kama shi, amma sai ya danne ya ce,

"To baby yayi maki?"

Murmushi tayi ta narke a jikin shi tace,

"Eh yayi min Babyna,"

"Tooo gidan baby da baby kenan ko?"

D'aga kai tayi tana dariya,ci gaba da magana yayi yace,

"Na roqe ki dan Allah kar hanya ta haɗa ki da Sultan ki tsaya gaisawa da shi ko Bilal, ni yanzu dik haushin su ma nake ji, ita kuma waccan mara kunyar zan sa a nemo ta dan na karb'i duk wani abu naki dake wajen ta gudun kar ta yi min b'arna,"

"Inshaa Allahu haka ma baza ta samu ba, ai shege shi yasan makwancin shege, na san maganin ta ka barni da ita"

"Ah ah fa, bana son ki sake involving kan ki cikin rayuwar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login