Showing 156001 words to 159000 words out of 276165 words

Chapter 53 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

OIL*
*HAIR CREAM*
*HAIR MASK*

*GA MASU SON SIYAN ƊAYA KO SARI SU NEMI WANNAN NO 09031416423*







PAGE 61:









"Ashe har na yi lalacewar da Abbe zata ci min mutunci a gaban ka? Abbe fa 'yar ɗan uwan ka? Kuma Saddiqa tafi sauran ƴaƴan ka matsayi a gidan nan ashe ban sani ba sai yau,yaran nan tsurar sadakin su ka basu babu ko sisi akai amma ita har da ƙarin wasu kuɗaɗen, da kyar Ɗan liti, mu zuba mu gani shege ka fasa, duk wanda yace zai ja da ni Innoh zai kuwa kwana kuka,"

Ɗaki ta shige tana jin baƙin cikin abinda ya faru,tare da cin alwashin ɗaukan mummunan mataki akan Ɗan liti da Saddiqa, shi kuwa Ɗan liti ya kasa ce mata uffan sai ya samu waje ya zauna ya dora hannun shi a guiwar ƙafar shi yana tunanin irin rayuwar da yake ciki.

Washegari da sassafe su Abbe suka kammala shirin tafiya Abuja,Saddiqa kuwa tana sallah tana hawaye,lokacin da suka zo tafiya kuwa kuka ta dinga yi tana roƙon Baabaa akan ta zo su tafi tare idan yaso sai ta dawo,ba zata iya tafiya ita kaɗai ba babu Yadiko babu Baabaa.

Baabaa ma kuka ta dinga yi tana baiwa Saddiqa hakuri, cikin kuka Baabaa tace,

"Kiyi hakuri Saddiqa ba zan iya binku Habuja ba,da zan iya da na biku an kai ki ɗakin Manniru da ni, Manniru ga amanar marainiyar Allah nan, idan kaci amanar ta sai amanar Allah ta ci ka, ka kula da ita kamar yanda zaka kula da rayuwar ka ko fiye da hakan ma, ga Sadeequ nan ku je tare idan su Abbe za su dawo sai a dawo da shi, Allah yasa wannan aure naku mutuwa ce zata raba shi,Allah yasa kiyi koyi da kyawawan halayen Mahaifiyar ki ko ma ki fita nagarta,Allah yayi muku albarka ya azurta ku da zuri'a mai albarka,maza ku kama hanya kar kuyi dare Allah ya tsare."

Kuka kawai Saddiqa take yi ta ƙanƙame Baabaa bata son rabuwa da ita, ita take gani a matsayin mahaifiya a yanzu, taso ace ƙanwar Yadikon ta ta samu halartar kaita d'akin mijin ta amma da alama hakan ba zai samu ba saboda sun tafi kudu daga ita har mai gidan ta, dama sauran dangin Yadikon sun jima a can suna kiwo da saida dabbobi lokaci zuwa lokaci, aiken kayayyakin kitchen irin na fulani da zannuwan gado uku manya da mafitai da tsintsiya sai tsabar kuɗi dubu ɗari uku da hamsin dangin Yadiko suka yi mata,Saddiqa tafi son ganin su sama da abinda suka aiko mata dashi, amma babu yanda zata yi haka ta Karb'a tayi godiya Munir ya saka mata kayan a bayan mota kud'in ta kuma a akwatin kayan ta.

Munir ne ya kalli Baabaa dake riƙe da ƙunshin kayan ta tana sharɓen kuka, cikin natsuwa yace,

"To ke yanzu grandma dole sai kin koma gidan can? Kiyi zaman ki anan ke da Sadeeq mana ai ina ga kamar zai fi maki can ko?"

"Ah ah barni na koma ɗaki na na ci gaba da sana'a ta ta ƙosai da siyar da goro ina ganin gilmawar jama'a, mutane ma ai rahama ne, idan na zauna a wannan ƙaton gidan ni kaɗai babu mai shiga da fita ai sai tunani yayi min yawa ko? Maza ku kama hanya takwas har ta yi kuna tsaye."

Abbe ce ta ja Saddiqa da kyar ta sanya ta a mota, sai da motar su ta tashi sannan Baabaa ta sake damƙe makullin gidan da suka rufe da jakar kayan ta ta ɗauki hanyar komawa gidan Ɗan liti.

Tinda ta shiga gidan take kwad'a sallama babu wanda ya amsa ta kasancewar Innoh ce kawai a madafi, Ɗan liti ya fice,Sule kuma yana ɗakin shi yana maida baccin asara,kasancewar jiya tin sha biyu na dare da ya hau live a TikTok bai samu ya sauka ba sai biyar na asuba,wata sabuwar budurwa yayi mai suna Malika ABJ, yarinya ce mai matuƙar kyawun fuska da kyawun sura,dogon gashin ta irin na indiyawa da cikakken ƙirjin ta sune suka fi ɗaukan hankalin Sule, idan kuwa tana magana ji yake yi kamar ya gan shi a gaban ta saboda shauƙi,muryar ta mai azabar daɗi kawai yake da burin saurare a koda yaushe safe da rana da maraice da zai samu, dan haka shi fa yanzu ne lokacin auren sa dan kuwa yayi mata.


"Gida sai kace gidan arna bawa yayi ta doka sallama babu mai amsa masa?"

"Mtsewww, 'Yan Habuja sun wuce sun bar mana alaƙaƙai almasifatu kurjin guiwa,da za su tafi me yasa baki bi su ba ƙarshen ƙauna."

"Dallah ware ke me kika sani game da ƙauna ko soyayya tinda ko kan ki baki san yanda zaki so ba balle mijin ki da yaran da kika sha wahalar haifa? Kuma alkafidaru ƙunjin guiwa da kika kira ni da shi kin san da wa kike, dan ni itace sa'ar yi na ba dan ta kwanta dama ba."

"Da uwar tawa kike? Ni fa Yaya dik abinda za muyi dani dake ki dena sako uwa ta dan ba sa'ar ki bace."

"Ai ni sa'ar ki ce ko? Nace ai ni sa'ar ki ce ko? Kinga Innoh idan baki kiyaye ni ba bana sai na hau ruwan cikin ki nayi sukuwa ni da bafulatana ta sai hanjin ki sun bayyana a bainar nasi,idan kuma kina ganin ƙarya ne dan Allah ki ci gaba da yi min rashin kunya,yanda gidan nan yayi shiru alamu ne na babu kowa daɗin na lugude ki kenan ba maceci."

Tinda Innoh ta fuskanci da gaske Baabaa ta dawo da wani ƙarsashi ajikin ta sai ta buga cinya tace,

"Ahayyyeee tabdijam."

Tana faɗin haka ta miƙe tana muskuta mazaunai tayi ɗaki tana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa yanda Baabaa baza ta ji ta ba,bismillah Baabaa tayi ta buɗe d'akin ta, sai taga dik yayi ƙura domin jikokin ta dake kwana da ita sun koma gidan iyayen su,shara ta hau yi tana karkad'e ƙura, tana gamawa tayi wanka ta kunna rishon ta ta dafa taliya da manja tana da yajin ta ta zuba da soyayyan naman da tazo dashi ta ci ta sha ruwa, hamdala tayi ta saka ruwan wanka tayi tayo alwala daga nan, sallar walaha/dhuha tayi sannan ta shirya ta shiga maƙota ta sanar da kowa ta dawo gobe akwai yin ƙosai goro kuma ranar kasuwa za ta ɗakko a ci gaba da sana'a, bata koma gida ba sai da ta taɓa hira dan kuwa a can maƙota tayi azahar da la'asar sannan ta koma gida.

Ko da taje gida ta tarar da Innoh da Sule sai Naja a tsakar gida suna hira,Sule sai ya hau murnar ganinta yana tambayar yaushe ta dawo bai da labari? Yatsina fuska tayi sannan tace,

"Aiii baƙin halin uwar taka be bata damar sanar da kai na dawo ba kenan? To ɗazu na dawo da safe."

"Masha Allahu ai gwanda da kika dawo comedy ya dawo gida barka da dawowa."

"Waye kwamde ɗin? Ni fa Sule bana ciki da shaƙiyancin ka tom."

Dariya yayi ya bita sashen ta dan ya san Baabaa bata da rowa dole ta sammasa ɗan abinda ta dawo da shi,Naja na gaishe ta ta yatsina fuska ta amsa ciki ciki ta buɗe d'akin ta ta faɗa tana faɗin,

"Munafukan banza kamar ba nan za su zauna su haɗe kai suna zagi na tare ba, shine take sunne kai kamar ta Allah."

Kamar yanda Sule kuwa ya kyautata mata zato haka ne ya faru, wani dambun nama da soyayyan nama da cincin dik sai da ta bashi yaci yayi godiya ya tafi,Saddiqa ce duk ta tarkace abinda ya rage ta haɗe mata shi ta sarrafa wanda zai sarrafu wanda kuma Baabaan ce zata girka duk sai ta haɗe mata su ta sa mata a jakar ta,tinda ko an tafi an bari babu mai amfani dashi sai dai ma wani abun ya lalace a banza.


*************************


Sun isa Abuja da azahar a gajiye direct gidan Alhaji Baban Gida suka sauka, Ummi da Y'an matan ta har da ƙawayen ta sai murnar ganin amaryar Munir suke yi,wata ƙawar Ummi dake tsananin kishi da ita mai suna Hajiya Sa'a ce ta yatsina fuska tace,

"Ahhh dama a ƙauyen naku kuna da irin waɗannan kyawawan matan shine ba a faɗa min ba Suhail yaje ya samo mata shima?"

Murmushi kawai mutanen wajen suka yi dan kuwa kowa ya san yanda take kishi da Ummi,ita a son ta komai Ummi tayi itama tayi shi ko tayi wanda yafi na Ummi, sai aka yi rashin sa'a mijin ta bai kai Alhaji Baban Gida samu ba gata tana da yara da yawa, kud'in makarantar su ma da hidimar su kaɗai ya ishe su lalura.

Har suka shiga ciki Saddiqa bata d'aga kai ta kalli kowa ba,suna shiga parlour ta durƙusa har ƙasa ta gaishe da Ummi, sannan ta bi ƙawayen ta tana gaisarwa ɗaya bayan ɗaya, hakan da tayi kuwa ba ƙaramin burge su yayi ba, sun tabbatar da yarinya ce mai tarbiyya ba kamar irin yaran su da idanun su ya bude ba idan za a gaida babba ana yi ana yatsina kamar abun dole.

Har ta durƙusa zata gaishe da Khaleesat sai taji Anisah ta fashe da dariya tace,

"Wannan ƙanwar mijin ki ce zaki gaisar gwanda ma ki miƙe kafin ta raina ki,"

Dariya wajen suka ɗauka sai Saddiqa ta miƙe a kunyace ta gaishe da ƴan matan da za su yi sa'annin juna dasu, miƙa mata hannu suka yi suka gaisa sannan suka ja ta zuwa ɗakin Anisah, suna shiga suka zaunar da ita a bakin gado,Anisah tace,

"Zauna ki huta kun shawo hanya,ke Khalee ɗauko mata abinci dan na san halin Yah Munir baya saiwa mutum abun motsa baki a hanya haka zaku taho a yunwace."

Khaleesat ce ta zumɓura baki tace,

"Na faɗa maki Yah Anisah bana son sunan nan sunan fa gunki ce a India,"

Murmushi Saddiqa tayi dan kuwa ko karyawa bata yi ba tana ta azabar kuka,a tare suka fita suka bata waje, band'aki ta shiga ta yi alwala ta zo ta tada sallahr azahar,tana idarwa suka shiga ɗauke da manyan farantai biyu, daya lemon kayan itatuwa ne na musamman Ummi tayi mata,gefe kuma fruit salad ɗin da ya ji ayaba da madara sai kwakwa da soyayyan riɗi ne, d'ayan farantin kuma fried noodles ce da ta ji kayan lambu da kayan ciki, sai pepper chicken da salad ɗin dankalin bature.

Saddiqa dai tunda take a duniya bata taɓa cin irin wannan abicin ba, sai taji duk ta raina girke-girken da ta iya ashe girki na birni? Suna ajiye mata suka sake tashi za su fita cikin sauri tace,

"Dan Allah kar ku fita, zan iya ci a gaban ku bana son zama ni kaɗai."

Murmushi suka yi suka koma suka zauna, suna hira ta na cin abincin ta cikin natsuwar da take ta basu sha'awa,su a tunanin su irin ƴar ƙauyen nan ce kuma ƙazama dan tin suna yara idan sun je suna ganin su Ameerah da Mommy suna ganin yanda suke gudanar da rayuwa, ita kuwa koda yaushe tana makaranta daga safe zuwa yamma, shi yasa basu wani santa ba.

Tana cikin cin abincin Anisah tace,

"Na manta Ummi tace ki shanye fruit salad ɗin nan kar ki rage mana naki ne ta haɗa maki na musamman, tana nan shigowa idan kin gama cin abinci ku sake gaisawa."

Murmushi tayi zuciyar ta cike da son ganin Ummin dan kuwa ba ƙaramin shaƙuwa suka yi ba a ɗan zaman da suka yi a ƙauyen Ba Mugu,dik yanda Saddiqa ta so nuna jin kunyar ta sai da Ummin ta sa ta ware suka zama kamar ƙawaye.

Tana gamawa kuwa Ummin ta shiga ɗakin hannayen ta biyu a buɗe tana dariya tace,

"Taso taso ƴata nayi kewar ki sosai."

Ai kuwa da sauri Saddiqa ta tashi ta isa gare ta ta rungume Ummi nan da nan hawaye suka fara zubo mata, cike da shagwab'a tace,

"Ummi kinga Baabaa taƙi zuwa kooo?"

Kama Saddiqa tayi suka zauna a bakin gado ta hau share mata hawaye tace,

"Ai Baabaa ba zata zo ba dama na sani, ita fa gani take yi data baro garin nan mutuwa zata riske ta ba a ɗakin mijin ta ba,bayan bata sani ba dik inda ajalin bawa yake dole sai ya taka ya je can sannan ya mutu,kar ki ji komai kina da ni a garin nan ga ƴan uwan ki nan baza mu barki kiyi kewa ba kin ji?"

D'aga kai Saddiqa tayi sannan ta ce,

"Na gode sosai Ummi Allah ya ƙara girma."

"Amin ya Allah,amma dai an ware ni an manta dani a gidan nan, an dena yayi na,wai ace nine yau zan shawo tafiya nazo gida ko ruwan pampo ban samu ba balle na roba, lallai rayuwa sauyi-sauyi."

Dariya suka kwashe da ita baki d'ayan su cikin dariya Ummi ta tashi tace,

"Yi hakuri Son gaba ɗaya hankali na yayi gaba, ka san mun saka gobe ne za a yi event ɗin bikin ku kafin akai amarya gidan ta amma mutanen nan sai da suka zo dan su ji daɗin ɗorar da labarin yanda suka ga amaryar ka a ranar farko, to Alhamdulillahi basu ganta yanda suka zata ba,sun tafi da mamaki a zuciyoyin su magana kuma fal bakunan su,muje na baka abinci, ku kuma idan an yi la'asar Anisah ki kai ku saloon ɗin ayi maku dik abinda ya kamata na gyara, ki sake tunawa masu kwalliya su fa zo akan lokaci bana son ɓata lokaci, ke kuma Khaleesat ki kira masu abinci su yi abinci da wuri bana son african time da ake faɗa ɗin nan."

"Yessss Ma'am"

Suka haɗe baki suka faɗa suna dariya,rayuwa suke a gidan kamar ƙawayen juna, a gaba ta sanya Munir dake ta kallon Saddiqa wadda ke satar kallon shi ta ƙasan gashin idanun ta,murmushi yayi kafin ya wuce,abinci Ummi ta bashi yana ci suna hira.

Bayan sallar la'asar su Saddiqa suka shirya Anisah ta ɗauke su a mota suka tafi Saloon, kowa ya sha mamakin yanda kan saddiqa yake da tsaho da cika kuma a wanke fess babu dattin komai,gyara mata shi aka yi dan tace bata son a saka relaxer tafi son gashin ta natural, ana gamawa da kanta suka wanke mata hannu da qafa aka yi gyaran farce,bayan sun kammala ne aka zauna zaman tsara mata ƙunshi baƙi da ja mai kyau hannu da ƙafar ta. Su kan su su Anisah sai da aka yi musu wankin kai da kunshin, basu bar wajen ba sai bayan magariba sannan suka koma gida.

Da dare ma Ummi bata bar Saddiqa haka ba sai da tayi amfani da HAMIBRAH BODY SCRUB ta murje mata jikin ta da shi sannan ta bar shi ya dan yi minti sha biyar a jikin ta kafin ta wanke ta mulke jikin ta da HAMIBRAH FACE OIL da kuma HAMIBRAH BODY OIL,nan da nan Saddiqa ta ɗauki wani irin sheƙin amarci. Munir tunda suka dawo yaso ya ganta amma Ummi ta hana ƙarshe ma cewa tayi idan ya kuskura ya ƙure haƙurin ta shi da ta bashi matar shi sai wani satin, ba dan ya so ba dole ya tafi d'akin shi,yana shiga kuwa ya dinga kiran ta a waya tana gani ta ƙi ɗauka saboda kunyar idon su Anisah.

Washegari da safe kuwa........
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI













RUBUTAWA:HAERMEEBRAEH ✍️✨








*SANARWA !*

*Ki na sha'awar karanta littattafan marubuciya HAERMEEBRAERH kema domin samun nishad'i da tarin ilimin zaman duniya? Bari to na lissafo maki littattafan da ta mayar da su document dan samun sauƙin karatun ku masoya wanda za ku biya 300 a kowanne littafi ɗaya kafin ku mallake shi.....*

*MAZAUNA GIDA 300*
*ƳAN ABUJA 300*
*A GARIN MU 300*
*KAI NE JARUMI 300*
*KUN MAKARO 300*
*TAUBASHI 300*

*KAR KU BARI A BAKU LABARIN SU MAHBOOB...JAMEELAH...OGA LAWWALI DA SULTANAN SHI...RASHIDAH DA SAKEENAH....JUWAIREREN MAMA DA SUWAIBA NONOLESS🙊💃🏻*
*IDAN ZAKI SIYA DIKA ZA KI BADA 1500 KACAL..09031416423.*

*KAR KU MANTA AKWAI KAYAN GYARAN JIKI A KANO, KADUNA DA KEBBI STATE.*

*FACE OIL*
*SKIN OIL*
*BODY SCRUB*
*HAIR OIL*
*HAIR CREAM*
*HAIR MASK*

*GA MASU SON SIYAN ƊAYA KO SARI SU NEMI WANNAN NO 09031416423*







PAGE 62:






Tin da safe Ummi ta shiga ɗakin Anisah dan ta tada su sallar asuba sai tagan ta zaune a saman abun sallah ita da Saddiqa suna ibada, k'warai hakan yayi mata daɗi duba da cewa a baya kullum sai taje ta tashi Anisah saboda nauyin bacci da ƙiwar tashi tayi ibada da take da shi,ja musu ƙofar tayi ta koma ta binciko lallen da take da shi da ganyen magarya, tafasawa tayi ta tace ruwan sannan ta ɗauka a bokiti ta koma ɗakin Anisah ta wuce band'aki,madarar turaren da ta dakko ta soft ita ta zuba a cikin ruwan ta saisaita shi dai-dai wanka.

Tana gamawa ta koma ɗakin tace,

"Idan kun idar da karatun Anisah ki jiƙa HAMIBRAH BODY SCRUB ɗin nan da ruwan d'umi ki murje mata jikin ta yanda kika ga nayi mata jiya, sai ta d'auraye da ruwan da na surka mata a band'aki zan kawo ruwan kaninfari da bagaruwa (kaɗan sosai ba da yawa ba) da white musk sai ta kama ruwa da shi,idan kun gama ki tabbata kin wanke wajen nan saboda kar ruwan lallen ya kama wajen, ke kuma Saddiqa kar ki fito sai ruwan ya tsane a jikin ki,idan kun gama zan kawo maki rigar da zaki saka idan kin karya ki koma bacci ki samu hutu sosai kar na gan ku a parlour ko na shigo naji hayaniya, bacci nake so tayi ta huta Anisah kafin yamma ina fatan kun ji ni."

Tinda Anisah taji Ummi na nanata magana to fa ta tabbata da gaske take bata so ta kama su suna hira a bar Saddiqa ta huta kawai, dan haka sai ta amsa mata da,

"To Ummi inshaa Allahu za a yi yanda kika ce."

"Allah yayi muku albarka."

Kan Saddiqa na ƙasa ta amsa a hankali sannan ta gaishe da Ummi, zuciyar Saddiqa cike take da godiya ga Allah da yasa a ranar bikin ta bata yi kukan rashin gata da rashin uwar da zata gyara ta ba,Innoh da iyalan ta sun ƙi zuwa kuma ta tabbata ko barin ta aka yi su gyara ta babu abinda za suyi mata, sai gashi tayi dace da suruka ta gari,hamdala tayi sannan ta hau yi musu addu'a har Abbah dake sakin kuɗi dan a yi hidima,bayan ta amsa gaisuwar Saddiqa sai ta ja musu ƙofa ta shiga ɗakin Khaleesat ta ja mata kunne akan kar ta ga ƙafar ta d'akin Anisah tana so Saddiqa ta samu hutu sosai, dan bata so azo dinner


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login