Showing 81001 words to 84000 words out of 276165 words
Chapter 28 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
shi itama sosai kamar yanda yake yi mata, tana ganin mutunci da qimar shi, sannan tana kunyar shi, ga wani irin yanayi na musamman da take tsintar kan ta a game da shi a duk sanda yake yi mata magana cikin natsuwar shi da kamewar shi.
Zaune take a d'akin da suka sauke ta tin dawowar su tana shan chocolate ɗin da ya siyo mata tana ta tunani a ranta, sallamar shi taji tare da k'wank'wasa qofar d'akin nata, cikin sauri ta miqe ta isa bakin qofa ta buɗe masa tare da gaishe shi, haɗe fuska yayi kaɗan yana yi mata kallon nan nashi dake tsunduma ta a kogin qaunar shi a kullum,cikin muryar shi ta cikakkun mazaje masu cikar zati da haiba yace mata,
"Saddeqah ba na ce maki ki dinga sanya mayafi ba a dik sanda kika ji ɗaya daga cikin mu? Kar ki manta ba muharraman juna bane mu,sannan mu ɗin 'yan Adam ne masu rauni, Allah yayi haramci da kusantar zina bama aikata ta ba, ah ah kusanci da ita ma an haramta, to ki yi tunanin ya wanda ya aikata ta ko yake aikata ta zai fuskanci hukunci a wajen Allah akan qetare iyakar Allah? Ki qara hakuri na san kin matsu ki koma gida wajen iyayen ki, gashi kun kusan yin sauka ma ko? Dan an gayyace ni bikin saukar taku,dan haka kar ki damu ba zamu wuce sati ɗaya ba zamu gama abinda muke yi na samu hutu sai mu tafi gida tare,idan kuma kin gaji kina so ki tafi ba tare da an yi bincike akan wanda ya sace ki ba to zan iya baki kuɗin mota ki tafi,"
Cikin tsananin jin kunya tare da danasanin fitowa yawon karuwanci Mommy ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba a idanun ta,ta ina zata fara sanar da shi kafin a kai ga sace ta sai da ta fito yawon karuwanci da kan ta? Ta ina zata sanar da shi nasihar da yake yi mata kullum akan zina ta sha aikatawa? Idan yasan rayuwar ta ta baya ya zai ji ? Shin zai qaunace ta kamar yanda take qaunar shi ko zai tsaneta ne? Ya zai ji a lokacin da ya gano ita ɗin ba Saddeqa bace?
Hannun shi ya sanya a gaban fuskar ta yana kad'awa dan ya jawo hankalin ta, da sauri kuwa ta fito daga duniyar tunanin da ta afka tace,
"Ka yi hakuri zan kiyaye, ina da yawan mantuwa ne,"
"Yawan mantuwa ko kuma kina sane, so kike ki ja ra'ayin ɗayan mu mu yi aika-aika Allah ya yi mana luguden azaba to ta Allah ba taki ba in shaa Allahu mata tace zata fara b'are ni a leda,"
Abdul ne ya juya ya kalli Bilal dake zayyano zance kamar wanda ke jin haushin Mommy, ba tare da ya kula su ba ya amshe makullin motar Abdul ya bar gidan yana mita akan ya kamata Abdul yayi ya ɗauke musu Mommy a gida, yarinya me qira kamar lamba takwas za a ajiye musu a gida a matsayin su na mazaje lafiyayyu? A gaskiya ana cutar shi kuma ta Allah ba tasu ba ba me sashi aikata ba dai-dai ba se yayi aure, murmushi kawai Abdul yayi sannan ya sanya hannu a aljihu ya dakko dubu uku ya bawa Mommy yace,
"Ga wannan koda zaki sai abinda zaki ci idan baki son abubuwan dake cikin gida,bari mu je sai mun dawo da yamma ko?"
D'aga masa kai Mommy tayi tare da faɗin,
"Allah ya kiyaye ya bada nasara da sa'a,"
Yaji daɗin addu'ar ta sosai dan haka sai ya yi murmushi ya furta,
"Ameeen"
Sannan ya fita ya ja mata qofar ya rufe, a mota ya tadda Bilal nata mita amma be kula shi ba saboda ya tafi duniyar tunanin yanda zai gabatar da Mommy a wajen iyayen shi, dan kuwa da dikkan alamu har yanzu ba a farga cewa Saddeqa ta b'ata ba tinda Sultan na sanar da shi cewar tana nan lafiya, wataqila suna yin haka ne dan a kwantar masa da hankali,shi kuwa sai biye musu yake yi har kuɗi yake aikawa a sai mata abu a kai mata.
A can gidan kuwa suna fita Mommy ta shirya ta sanya facemask kamar yanda ta saba a baya, ta nad'e kanta da mayafin rantsattsiyar abayar da ta sanya ta saka takalmi ta ɗauki wayar ta da kuɗin da Abdul ya bata ta rufe musu gidan ta taka da qafarta zuwa bakin titi, adaidaita sahu ta shiga tayi masa kwatancen inda zai kai ta,zuciyar ta ke tsananin bugawa saboda tsoron abinda zai je ya zo.
Suna tsayawa a qofar katafaren gidan da ta kira da gidan 'yan wuta a yanzu ta fita ta cewa me daidaitan ya jira ta zai maida ita inda ya dauko ta.
Sai da ta buɗe facemask ɗin ta mai gadi ya gane ta sannan ya wangale mata qofar gidan yana murnar ganin ta tare da sanar da ita Hajiyan na ciki ita da Babyn ta, murmushi ta yi masa sannan ta yi godiya tace kar ya rufe qofar yanzun nan zata fito gaisawa kawai za su yi, sai ta shiga hantar cikin ta na kad'awa, a hankali ta hau buga qofar gidan tana jiran a buɗe mata, ba jimawa kuwa Sallau ya buɗe qofar yana yi mata kallon sani, buɗe facemask ɗin ta tayi ya gan ta ya kuwa buga salati tare da faɗin,
"Habaa ni fa in ce kamar na san me irin wannan shigar,ke kuwa ina kika shiga haka Hajiya duk ta damu bata da zance sai naki?"
"Za ka buɗe wa baqon da aka yi qofa ya shigo ko sai ka gama tsegumin naka ya tsohon kwarto?"
Da sauri Sallau ya bar jikin qofar Mommy ta bayyana a cikin gidan, cikin hanzari Hajiya K'waisa da Samuel suka qarasa sakkowa daga bene suka nufi wajen mommy za su rungumeta mommy kuwa tayi saurin ja da baya tana kallon su ɗaya bayan ɗaya tana zabga musu harara, kallon juna Samuel da Hajiya K'waisa suka yi sannan suka kyab'e baki tare da maida kallon su kan mommy suna kallon ta da alamun tambaya a tattare da su,cikin ɓacin rai Mommy tace,
"Banzo wajen nan dan kuyi murna da dawowa ta ba,na zo wajen nan ne dan in sanar da ku na dawo qasata Nigeria lafiya ba tabo ba nakasa idan ma abinda yasa kuka haɗa baki da Alhaji kenan kuka siyar dani wajen baturen da ya dinga haiqe min kamar ya samu katifa,to Allah ya isa tsakani na da ku inshaa Allahu sai kun yi mutuwar wulaqanci, na so na haɗa ku da hukuma amma na san babu abinda za a iya yi min saboda kun fini kuɗi, kuna tare da masu mulki dan haka baza ku tab'u ba,dan....."
Cikin tsawa da harare-harare Hajiya K'waisa tace,
"Ke qaramar 'yar balaja'u ya haka? Ya haka ana murna kin dawo lafiya ki hau ja min doguwa har da maganar siyarwa da hukuma? Idan ma wani abune ya faru ai zama ya kamata muyi a tattauna akai ko? Haka kawai se ki zo ki hau ja min doguwa salon nafi haka shiga duniya? Me ya faru? Ina kika shiga aka dinga neman ki babu waya babu saqo babu ɗan aike?"
Mommy kallon su ta tsaya yi a sheqe dan kuwa ta tabbata rainin hankali ne kawai irin na 'yan daudu za ayi mata,cikin hasala tace,
"Ya kake magana kamar baka san abinda kuka yi min ba? Da fari ka nuna baka san Alhaji ba ashe bakin ku ɗaya,kun haɗa baki an d'auke ni daga Uganda an siyar a New York wajen bature,to ina roqon Allah yanda ya yi min Allah ya kawo me yi miki irin haka ki ji idan da daɗi,"
"Tuf Allahumma ba amin ba dan ban san uwar da aka yi miki ba har ya jawo zage-zagen nan da tsinuwa, kai ka ji min 'yar iskar yarinya se jafa'i take jawo min daga taimako? Alhaji dai yanda kika ganshi haka na gan shi haɗuwar social media ne ban san sana'ar shi ba ban san ɗan wanne gari bane, da na san waye shi an faɗa maki da ban nemo ki ba da kaina? Kar fa ki manta ke ɗin tanadin Sanata ce e fa, qarshen shekarar nan za...."
"Aiko se dai ki bawa Sanatan uwar ki amma ba ni ba shege gardin banza ɗan asara, Allah ya isa tsinanne kwanan nan zan koma garin mu dani da bawan Allahn da ya kub'utar dani daga sharrin ku, kuma inshaa Allahu shine zai zama miji na na bi Allah na tuba na dena wannan rayuwar ta dabbobi kuma Allah ya shirya ku idan kuna da rabo idan babu kuma Allah ya sa ku wulaqanta matsiya...."
Wani irin naushi Samuel ya kai wa bakin mommy sai da jini yayi tsartuwa, K'waisa na gefe tana,
"Saɓa min kamannin matsiyaciya, ina ganin ki kamar za a more ki ashe kwalluwar shegiya ce ke? Kama bakin ka yi ta duka sai haqoran ta sun zube a qasa babu kuma abinda za a yi,"
Kukan kura Mommy tayi ta damqi tozon wuyan Samuel kamar wata zombi ta gartsa masa cizo duk yanda Hajiya K'waisa taso karb'ar babyn ta a hannun Mommy kasawa tayi, banda ihu babu abinda Samuel keyi, mommy na sakin shi ta damqi hannun K'waisa shima ta kafa haqoranta Samuel na ganin haka ya haye saman bene da uban gudu yana ihun a cece shi mayya zata shanye musu jini.
Dik abinnan da ake yi akan idon su Ruby ake yin shi,yau ce rana ta farko da Zubaida ta yi dariya a gidan tin da aka kawo ta aiki,ta ji daɗi sosai da Mommy ta bar harkar karuwanci fatan ta Allah ya shirya K'waisa dan kuwa yana da taimako da jin tausayin talaka, amma kuma an sadaukar da rayuwa wajen saɓawa Allah.
Hajiya K'waisa bata gama dawowa hayyacin ta ba daga zafin da ke ratsa hannun ta ta ji mommy ta damqi kunnen ta ta gatsa masa cizo, ihu ya k'walla yana tsinewa Samuel da ya gudu d'akin su, jin ihun Hajiya yaqi qarewa ne ya sanya Samuel d'akko wani dogon abun qarfe da suke zuba tokar sigari ya fito daga d'akin tare da kwararo ihu kamar mace zai sakko qasa, mommy na k'yalla ido ta hango shi tafe da makami sai ta saki K'waisa ta taka da gudu, Zubaida dake bakin qofa kuwa ta buɗe mata ta fita a guje, mai gadi na nan tsaye ya wangale qofa yana jiran komawar mommy suyi sallama ya ganta ta keto da gudu iska na kad'a rigar ta.
Ganin ta a guje ne ya sanya shi fita daga gidan shima a saba'in, me adaidaita sahu na qoqarin tada ɗan sahun sa ya gudu mommy ta afka tana faɗin,
"Taka wuta direba mu je !"
Banda haki babu abinda take yi, yana samun nasarar kunna ɗan sahun sa suka danna a guje Samuel na kurin bin bayan ta a mota K'waisa dake dura masa ashar tace,
"Sokon banza a gaban ka ta kafa min haqori zata kashe ni amma ka gudu shine yanzu za ka zo kana wani kurin banza,"
"Haba baby ki duba fa ki ga tozon wuyana yarinyar nan ta kama ta kafa masa haqori kamar ta samu goriba ta hau gaigaya, maza je ki shirya muje asibiti dan dole mu ga likita,"
Abu kamar wasa kuwa haka suka shirya suka yi asibiti, mommy kuwa na isa unguwar su Abdul ta sallami me adaidaita sahu, sai dai tana komawa ta ga gidan a buɗe, a tsorace ta furta.
"Na shiga uku waye kuma a cikin gidan, dan lokacin tashin su daga aiki be yi ba?............."[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 31:
Tsayawa tayi tana tunanin shin ta shiga ne ko ta gudu ta nemo taimako dan kuwa da dikkan alama b'arayi ne suka shiga gidan duba da cewa yanzu ba lokacin tashin su Abdul bane daga aiki, tana nan tsaye tana tunani taji an buɗe qofar a zafafe, Bilal ne ya leqo yana binta da wani irin mugun kallo yace,
"Dalla malama idan zaki shigo ki shigo,idan bazaki shigo ba ki kama gaban ki,"
Mommy na jin haka ta fara tafiya zuwa cikin gidan kamar wadda ake tunkud'awa, tana shiga taga Abdussaboor zaune a saman kujera ya dafe kan shi da hannu biyu yana juya shi cikin wani irin yanayi mai ban tausayi, ba tare da ta san kalar laifin da ta aikata ba ta durqusa a gaban shi tana zubar da hawaye tace,
"Yah Abdul dan Allah kayi...."
"Tashi daga kusa da shi munafuka, dama ni jiki na ya bani akwai wata manaqisar da kike qullawa, ke ɗin ba mai gaskiya bace,zaki sanar da mu sunan ki da asalin ki ko se na dakko wayar cajin can na yi ta zane ki da ita?"
A zafafe Bilal ke magana kamar zai shaqe Mommy, cikin in ina ta hau son tayin magana amma kalma ɗaya ta kasa fita daga bakin ta sai kuka da take yi kamar an aiko mata da labarin mutuwar Ɗan liti.
A hankali Abdul ya zaro wayar shi ya cire ta a key ya miqawa Mommy ba tare da ya ce mata komai ba, Karb'a tayi hannun ta na mugun rawa kamar mazari ta hau duba hoton da aka tura masa ta WhatsApp,hoton Saddeqa ne tsaye ta duqar da kan ta tana murmushi tare da wani bafulatanin matashi kyakkyawa,wanda tana ganin shi ta gano kamannin shi da Baabaa da kuma baffan ta wato Alhaji Baban Gida,rubutun qasan ta karanta wanda aka rubuta....
'Yayah wai dan Allah yaushe zaka zo ne? Yau kwana uku kenan da wannan guy ɗin yazo kullum shi yake kawo Gimbiyar garin Ba mugu makaranta a mota kuma shi yake zuwa ɗaukan ta, da dikkan alamu akwai soyayya da shaquwa a tsakanin su, ka yi sauri ka dawo kar ya riga ka fa!'
Tana gama karantawa jikin ta ya qara ɗaukan rawa kukan ta ya qaru, Bilal ne ya karɓe wayar a hannun ta dan kuwa sauran qiris ta sake ta ta faɗi a qasa,cikin tsawa yace mata,
"Wacece ke?"
Shiru tayi ta qi magana ta ci gaba da kuka sosai kamar ana dukan ta,cikin sanyin murya da gajiya Abdul ya furta,
"Wacece ke?"
"Yah...Yah....Ab..Ab..Abdu..."
"Bilal haɗa mana kayan mu muje gida please,"
Ba tare da Bilal ya sake cewa komai ba ya wuce cikin d'aki ya bar Mommy da Abdul a parlour, mommy na ta kirb'ar kuka Abdul na kwance a kujera ya kulle idanun shi yana jin yanda zazzaɓin da ya kama shi a lokaci ɗaya yake ragargazar qashi da b'argon jikin shi, ƙwaƙwalwa da zuciyar shi sai zogi suke yi mishi, be taɓa sanin yayi zurfi akan son yarinyar da yayi zaton Saddiqan shi bace sai yanzu da ya ji cewar ba ita bace,wani irin so mara misaltuwa Abdul yake yi wa Mommy wanda a yanzu tunanin yanda zai rayu rayuwa mai kyau da inganci yake yi idan babu ita a cikin tashi rayuwar.
Yana nan zaune Bilal ya fito da akwati sannan ya wurga wa Mommy tarkacen kayan da suka siya mata a jaka ya zare mata ido tare da nuna mata qofar waje da hannun shi, ɗaukan jakar tayi ta tsaya taqi fita tana ci gaba da kukan ta, Abdul ne ya tashi zaune da k'yar tare da dafe kan shi da hannu ɗaya ya miqe, jiri ne ya ɗauke shi zai faɗi Mommy tayi saurin kai hannu zata tare shi Bilal ya riga ta, a tare suka sakar mata wani mugun kallon da ya sanya ta ɗaukar jakar ta ta fara yin hanyar waje, zuciyar ta zafi take yi mata sosai, ina zata saka kanta taji daɗi? Tunawa da zafin da ta jiyo a jikin Abdul tayi dik da cewa bata taɓa shi ba amma hucin zafin ya dake ta, kuka ta qara fashewa da shi har suka fito suma daga cikin gidan Bilal ya rufe ya saka Abdul a mota ya tsaya yana kallon Mommy yace,
"Idan baki yi min shiru ba kika shiga motar nan kina yage wannan shegen bakin naki kamar na kada se na yanka maki mari sokuwa kawai maqaryaciya,"
Dif tayi ta dena kukan se zubar hawaye,baya ta buɗe ta saka jakar ta a can gefe ta rakub'e ta shige, banda kallon Abdul ta mirror babu abinda take yi har suka bar cikin garin kano.
***************************
Zaune take tana shan kunun tsamiya da alale a kyakkyawan parlourn Innah Laminde wanda me aikin ta ta gyara mata shi ta sanya mata turaren wuta sai tashin qamshi yake yi kamar ba a qauye ba,cikin yanga ta ce,
"A gaskiya wannan karon ko wata nawa zan yi ba zan koma ba sai na ga Yah Abdul,dan na kula kin dena kafa gwamnati na a wajen shi Innah,"
Murmushi Innah Laminde tayi sannan tace,
"Ba haka bane Bilkisu,na dai bari ne idan Allah yasa ya gan ki da kan shi yace yana son ki sai a yi wannan lamarin, amma idan ya nuna baya yi a kyale shi kema Allah zai kawo maki wanda ya fishi ma, ba zan so ace kin auri mutum kamar Abdul ba yazo yana wulaqanta ki ba,"
"Tabdijam ai Innah ni ko bi takaina ne ma yayi ba zan ce masa dan me ba, dan kuwa idan na rasa miji kamar Yah Abdul ba zan yi aure ba, wannan shine magana, dan haka gwanda ma ke da Ummah ku san ya zaku yi ya fara so na ba ruwa na ni,"
Billy ta qarasa maganar ta tana kurb'ar kunun tsamiyar ta,murmushi Innah Laminde tayi ta miqe zata shiga daki dan gabatar da sallar la'asar tace,
"Kin ji da shi, ni dai na faɗa maki idan ya nuna baya yi dake ki hakura kawai, dan kuwa ba zan yarda kowanne namiji ya wulaqanta min ke ba, ko wanene kuwa ba ma Abdul ba,"
Qara jaddadawa Innah Laminde Billy tayi,
"Ni dai shi nake so a matsayin mijin da zan aura bana son kowa,"
"Se kuma kiyi ai,"
Daki Innah Laminde ta qarasa shigewa ta bar Billy da ta kunna data ta hau online tana ganin videos ɗin da ta saka a TikTok tana jin daɗin yanda fans ɗin ta suka kai 2m,abinda ta kula da shi shine idan dai mace zata dinga bayyana surar jikin ta tayi shiga ta rashin mutunci ta kashewa jikin ta kuɗi to fa zata samu followers sosai,content ɗin batsa da zata dinga sakawa kuwa shi zai haukata account ɗin mace da